← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 86

Sashe 29

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dakata nan baƙar munafuka, na janyo ki jiki a tsammanina da ke za mu yi tafiya cikin mutumci ashe ke 'yar kunama ce. Ban taɓa sanin ke kura ce lulluɓe da fatar akuya ba sai yau, amma bari ki ji Jakadiya kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Wallahi-wallahi ba na ko kaffara tun da ke da makirar 'yarki kuka shiga gonata sai na sa kun girbe azababbiyar shukar da zan shuka ta da irin uƙubar da sai kun dinga gayyatar mutuwa da bakunanku, sai na shayar da ku tafasasshen ruwan mamaki; mamakin da har a zare numfashinku ba za ku taɓa mantawa da shi. Sai na jefa ku cikin jafa'in da boka ko wani mishiriki bai isa ya kuɓutar da ku ba, sai na dulmiya ku a kogin annoba, kogin da duk tsallan da za ku yi ba za ta ku taɓa yin iyo a cikinsa ba ballantana ki saka ran watarana za ki fito." A madadin kalaman Fulani Umaima su ɓata ran Jakadiya ko su razanata sai ta saki wata irin dariyar rainin hankali sannan ta tamke fuska ta furta.

"Ai kin riga da kin yi sake ɗan zaki ya girma Umaima, kuma idan junanki sammako wani a tafe ya kwana duk abin da za a wanzar zai faru a ƙwayar idonsa. Ni da kike gani sai na numa miki ni lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi, kuma Sailuba tamkar ta dasa furenta a Masarautar Huddam ne domin mai wuri ya zo dole mai tabarma ya naɗe."

Jakadiya ta ƙara matsawa gaban Fulani Umaima ido cikin ido ta ce, "Dube ni da kyau Fulani ko ga zubin ƙwayar idona kika kalla kin san ruwa ba sa'an kwando ba ne, tun wuri gara ki fara yi wa Sailuba biyayya ko kya shimfiɗa fada yadda kike so a wurin Mai martaba."

Kan haɗaɗɗiyar kujerarta Fulani Umaima ta koma ta zauna sai da ta saki murmushin takaici sannan ta dubi Jakadiya. "Da alama son mulki da son zuciya irin na ki ya san kin manta wace ce Fulani Umaima, amma ki sani ko an ci birnin kura ba a taɓa ba wa kare dillanci. Don haka mu zuba mu gani ni da ku shege ka fasa." Ba tare da Jakadiya ta tanka mata ba ta fice daga cikin ɗakin kai tsaye ta wuce ɗakinta ƙirjinta na dakan lugude don ita kanta ta san faɗa da aljani babu riba. Ta san wace ce Fulani Umaima farin sani, koma mene ne za ta iya aikatawa don cikar muradinta.

"Tun da na gan ki da tsakar ranar nan na tabbata da walakin goro a miya Jakadiyar Sarki Abdul'aziz." Boka Shaddas ya furta yana kallom Jakadiya da ta yi furƙai-furƙai cikin tashin hankali. "Ka taimaka mini ubangidana..."

"Duk na ga abin da ya shiga tsakaninki da Fulani Umaima, kuma hakan ba ƙara min ɓata mini rai ya yi ba." Jakadita ta sake yin tsuru-tsuru hantar cikinta na kaɗawa.

"Na so kin shawarce ni tun farko da ba ki ɓullo mata ta haka ba, sai mu ɓullo mata ta bayan gida mu ci birnin kura mu shinfiɗa fadarmu, so samu ki nuna mata ke za ki iya yi wa Sailuba baki ki tsine mata akan wannan auren da ake shirin yin, a taƙaice ki nuna mata ba kya son auren kuma ba da yawunki za a ɗaura shi ba, sai dai kash! Kin tarwatsa wannan matsayar, domin akwai wani sirrintaccan littafin da gawurtaccan matsafi Boka Bamaguje ya damƙa mata da na ci burin ki kawo mini shi ko ta halin ƙaƙa. Amma gabaɗaya kin ɓata goma ɗaya ba ta gyaru ba kuma dole mu sauya salo don na san a yanzu ba za ta sake aminta da kowacce irin Baiwa ba, ballantana a kawo mini littafin da zai sake ɗaga daraja ta."

Kamar kazar da aka jefa da wuƙa Jakadiya ta dube shi da shanyayyun idanunta ta ce. "A gafarce ni uban gidana me ye abin yi yanzu, domin kuskure na riga da na tafka shi?"

Boka Shaddas ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya sannan ya ce. "Taurarunta sun fara dakushewa daga gaban Mai martaba sakamakon aikin da na yi wa Sailuba, sai dai kuma har yanzu da sauran rina a kaba domin wannan dusashewar ta ɗan lokaci ce saboda aikin da Bamaguje ya yi mata har gaban abada matuƙar ba a tono shi ba, ba zai taɓa karyewa ba." Gaban Jakadiya ya yanke ya faɗi.

"Sannan kuma ina mai farincikin sanar da ke yanzu haka cikin da ke jikin Umaima cikina ne, da abin da za ta haifa zan yi ƙoƙarin cimma ƙudurina a kanta. A nan za ta tabbatar da ta haifi jinin Boka Shaddas, amma kuma ki sani wannan rufaffan siri ne da ban lamunce ki sanar da kowa ba domin a ranar da kika yi kuskuren faɗarsa a ranar za ki bar duniya don haka bakinki ƙanin ƙafarki." Da sauri Jakadiya ta sa hannuwa biyu ta toshe bakinta, wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Amma dole ta zarge linzamin harshenta ko don ta kwana cikin salama tun da kowa ya kwana lafiya shi ya so.

"Duk abin da kace ni mai bin umarninka ce madogarata."

"To ai ba a nan gizo yake saƙar ba, yanzu hatta kishiyarta uwargidan Takawa martabarta ta dawo a idonsa. Sai dai kuma a banza man kare tun da Umaima ta riga ta kashe al'aurarta, har abada ba za ta sake moruwa ba. Tabbas barewa ba za ta yi gudu ɗan ta ya yi rarrafe ba domin Umaima ba yar a ƙasa ba, kin ga kuwa kamar kumbo kamar kayanta. Ungo wannan ki tabbatar da kin binne shi a bakin bishiyar ɗorawa, wannan ne zai sa duk buga-bugar da Umaima za ta yi ba zai hana komai game da auren Sailuba ba, tun da a yanzu taurarunta sun riga da sun yi ƙasa, a kowanne lokaci za ta iya yin faɗuwar baƙar tasa." Boka Shaddas ya ƙarasa maganar yana ɗauko wani baƙin bera wanda aka tsire jikinsa da allura da waɗansu ƙananun layu. Har ƙasa Jakadiya ta zube tana yi masa godiya sannan ta fice daga wurin.

Sai da Ciroma da Galadima suka janyo ƙofar ɗakin ruf ta yadda wani ba zai ji abin da suke tattaunawa ba sannan suka kalli jun fuskokinsu ɗauke da damuwa.

"Maganar gaskiya Takawa ya shammace ni ba zato ka na gani ya bayar da yarinyar nan Khadija yanzu mene ne mafita?" Ciroma ya yi maganar rai a ɓace. Guntun tsaki Galadima ya yi sannan ya furta, "Yanzu saboda wannan har ka sa sai mun zo nan?" Ciroma ya furta a taƙaice.

"Ina gudun kada mu yi shuka a idon makwarwa kwaɓarmu ta yi ruwa tsululu, don haka na ce mu nemi ɗakin da za mu kashe mu binne ba tare da idon masarautar nan ya gifta a kanmu ba.

"To me zai ɗaga hankalinka alhalin yarinyar nan ba ita kaɗai ba ce, ba ga 'yar uwarta nan Sakina ba, tun wuri ka samu Mai martaba da zancen aurensu wallahi a wata majiyar na ji an ce Waziri ma so yake ƙarfi da yaji ya aura wa ɗan wurinsa Bala ita, ka ga kada mu zo mu yi bori da sanyin jiki mu ga samu mu ga rashi." Riƙo hanunsa ya yi cikin jin daɗi. "Na matuƙar jin daɗin wannan maganar taka, dama an ce aikin mai shawara ba ya ɓaci sai da kuma ba shi da sirri." Galadima ya bushe da dariya, "To ai dama abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa ka ga sai mu ci mu lashe ba tare da wani ya sani ba." Ciroma ya ba shi amsa sannan ya yi masa sallama.

Yana fita Zulai matar Galadima ta shiga ɗakin da sauri ta yi ƙasa da murya, "Mai gida an ya kana ganin ka yi farar dabara kuwa? Kar fa Ciroma ya..."

"Haba Zulai kamar ba ki san mijinki ba?" Galadima ya katse ta.
"Ai duk inda mai aro za shi da sanin mai kaya ne. Kina tsammanin a banza zan ce Ciroma ya yi wa Mai martaba magana game da auren haɗin da yake son yi tsakanin ɗansa da Sakina? Tsuntsu biyu na ke son jifa da dutse ɗaya don na san waye Abdul'aziz ba na jin zai bayar da 'yarsa ga mashayi, kin ga a lokacin kowa ya san da buƙatar Ciroma idan Takawa ya hana auren a daidai gaɓar ni kuma ƙit zan kashe shi, kin ga zargi zai hau kan Ciroma bayan an tura shi gidan yari kafin a naɗa Yarima sai na san yadda zan ɓullo a haɗa aurensa da yarinyar nan. Bayan wannan me ya rage Zulaihatuna?" Galadima ya ƙarasa maganar yana kallon Zulai.

"Ayyiriyiriyiriiii! Shi ya sa ko kaɗan ba na kaicon zaɓar ka da na yi a matsayin mijin aure, ka biya ni ko ba sisi billahillazi da an ga sabuwar sarauta a ƙasar nan."

"To tun da mu Marigayi ya ƙi mu da sarautar ba sai mu dasa 'ya'yanmu a kai ba, matar sarki idan ta iya jan birki ai ita ce Sarkin mai jan ragamar masarautar." Gabaɗaya suka kwashe da dariya.

Tun bayan rabuwar Kamalu da dattijo Maharaz bai sake ganinsa ba kuma ko kaɗan ba damu ba saboda a kullin suka haɗu da tsohon bai wuce ya riƙa gaya masa maganganun da bai cika gane makamarsu ba, sannu a hankali ya saba da aikin wahalar da Bayi mazan suke yi sune saran itace, yin gine-ginen har fasa dutse ba a bar shi a baya ba. Lokaci ɗaya hasken fatarsa ya disashen ya yi duhu sosai don kusan kullin idan Inna wuro ta gan shi sai tausayinsa ya kamata. Watarana suna zaune bayan Kamalu ya dawo daga fasa dutsen da aka saka su hannuwansa duka sun farfashe, ya zauna yana cin abinci ya dubi Inna wuro idanu cike da ƙwalla.
Chapter 29 · 0% Book details