← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 86

Sashe 21

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taku ɗaya biyu idan Kamalu ya yi sai ya saki guntun tsaki sakamakon ɓacin ran da ke cinsa a zuciya, a madadin ya bi hanyar da ta kawo shi zuwa ga wannan shurin, sai kawai ya yanke shawarar bin wata doguwar hanya mai ɗauke da waɗansu gajerun bishiyu masu kauri sai dai kuma kowacce murgujejiya bishiya a ɓarin ta na hagu a akwai waɗansu gidajen tururuwa guda uku, da mamaki yake bin wurin da kallo a zuciyarsa yana ta'ajibin ganin yadda bishiyoyin suke jere kamar an dasa su. Haka daga jikin gidajan tururuwar tamkar waɗanda aka kasa su wuri-wuri, kowanne guda ukun suna kewaye da bishiyoyin.

"Kada ka yi mamaki Saraki."

Ya ji an furta masa daga bayansa, yana waigawa idanunsa suka yi tozali da mamallakiyar muryar.

Tun daga ƙofar sashen Mai martaba Dogarawan da ke tsaitsaye wasu suka fita ta ƙofar da Muhsin ya shigo, wasu kuma suka sha gaban Muhsin.

"Karya ake wane mutum ya taɓo Yarima duk hatsibancinsa kai ko aljani ne ya kwana da yunwa." Cike da fushi Muhsin ya tura ƙofar ɗakin Mai martaba ganin yadda ya shiga ya sa Mai martaba ya kafe shi da ido a lokacin Fulani Umaima na zaune a gefensa suna hira.

"Me yake faruwa da kai Muhsin? Na yi rantsuwa da girman Allah duk wanda ya taɓa ka sai na sa an zartar masa da mummunan hukunci." Fulani Umaima ta furta rai a matuƙar ɓace sakamakon ganin yadda Muhsin ya shiga yana zubar da ƙwalla idanuwa bibbiyu, ɓarin fuskarsa ta kumbura lokaci guda.

"Yarima me ya faru muka ga sauyin yanayi a tattare da kai?" Takawa ya furta murya ɗauke da damuwa . Rushewa ya yi da matsanancin kuka haɗe da zubewa ƙasa a gaban mahaifinsa. Jikin Fulani Umaima har karkarwa yake tana shirin sake tambayarsa ta ji ya ce. "Wani yaro ne ya mare ni, kuma kayan jikinsa ne suka tabbatar mini daga sashen bayi yake..."

"Ba a haifi mahaifinsa ba kowane ne, ƙarya yake ya mari Yarima ya kwana lafiya domin wutsiya raƙumi ta yi nesa da ƙasa har gaban abada." Fulani Umaima ta faɗa tana miƙewa tsaye.

"Fulani a kwantar da hankali za mu ɗauki matakin gaggawa nan ba da jimawa ba." Ba don ta so ba ta koma ta zauna zuciyar na tafasa. A daidai lokacin Jakadiya ta rafka sallama daga bakin ƙofa, babu ɓata lokaci Takawa ya bada iso ta shiga hannuwanta ɗauke da kayan lambu. Da sauri ta dire kayan haɗe da dafa ƙirji tana kallon Muhsin.

"A gafarce ni Ubangidan bisa al'amarin da ya faru da Yarima, yanzu na haÉ—u da su Bawa Ali yake sanar da ni mummunan al'amarin da ya faru da shi."

"Jakadiya daga yanzu zuwa dare ina buƙatar Bawan da ya aikata wa Yarima wannan ɗanyan aikin cikin gaggawa."Cewar Fulani Umaima da ta ja Muhsin jikinta tana shafa tsagin fuskar sa wacce ta yi jawur hannuwan Kamalu sun yi masa ruɗu-ruɗu. "Jakadiya a sanar da sarkin gida ya tattara mana Bayi akwai muhimmiyar sanarwa da za mu fitar. A cika umarnin Fulani kamar yadda ta buƙata cikin gaggawa." Sarki Abdul'aziz ya furta.

"An gama ranka shi daɗe, farij jakada mai tarin dubun alkairai." Jakadiya ta yi maganar tana miƙe wa bayan da Takawa ya sallame ta.

Kafin wani lokaci tuni Dogarawan sashen Sarki Abdul'aziz sun bazama lungu da sakon cikin dajin duk da a lokacin ba su san takamaimai abin da ya faru da shi ba.

Ajiyar zuciya Kamalu ya sauke don ya gane shi sarai sannan ya furta. "Ya aka yi ka biyo ni har nan?" Murmushi Dattijon ya yi sannan ya ja hannunsa suka koma jikin bishiyar É—orawar da ke gefe, a kan É—aya daga cikin shurin da ke wurin Dattijon ya zauna shi ma Kamalu kai tsaye ya hau shurin da ke kallon Dattijon. Wani irin shuuuuu ya ji a saman kansa, take ya ga dajin ya fara juya masa. Hannu Dattijon ya kai saman goshinsa ya dafa nan take ya ji komai ya fara dawo masa, buÉ—e idanunsa ya yi yana fesar da iska mai zafi.

"Kada ka riƙa saurin taɓa lafiyar mutane domin kai ba kamar kowa ba ne." Dattijon ya yi maganar yana sakin murmushi. Kamalu ya bi shi da kallon mamaki, "Ya aka yi ka san wani abu ya faru?" Shi ma ya wurga masa tambaya.

"Ko kuma ba zan yi mamaki ba, domin jinin Sarki Muhammad Safwan idan bai yi zafin rai ba wa zai yi? Ai dama harbi ga É—an jaki gado ne."

"Wane ne kai? Waye Muhammad Safwan, kuma me ya sa kake alaƙanta ni da shi?" Kamalu ya furta fuska a haɗe, don ya ƙagauta ya san waye wannan Dattijon da ya ke son kutsowa cikin rayuwarsa. A wannan karon ma murmushi Dattijon ya sakar masa, wannan ya sake ɓata ran Kamalu ya saki tsaki cike da damuwa.

"Ko a kundin tarihi ban taɓa jin amintaka irin tamu ba. Ina matuƙar godiya ƙwarai aminina da wannan jajircewar da ka nuna mini. A dalilin haka zan sadaukar da jikan-jikana mai zuwa, ko da zai zama Sarki ko ba zai zama ba. A wannan lokacin na san ƙasa ta jima da binne idanuwana, amma duk rintsi kada ka wofantar da alƙawarin da muka ƙulla. Ka fi kowa sanin wane ne ni, don haka na tabbata zubi da surar halittarsa ita ce za ta bayyana daga tsatson da ya fito, matuƙar ya kasance jinina babu gauraye a ciki." Da sauri Dattijon ya dawo daga duniyar tunanin maganar da Marigayi Sarki Muhammad Safwan ya faɗa masa a lokacin da suke wata tattaunawa mai muhimmanci. Ganin Kamalu na bin shi da kallo ya sa ya furta. "Na tuna kalaman Aminina Mai martaba da muka taɓa yi da shi a baya game da zuwanka, tabbas na yi rashin amini na gari." Kamalu ya taɓe baki cikin halin ko-in kula ya yunƙura zai tashi don ya gaji da waɗannan kalaman Dattijon, sai kuma ya ji ya ce.

"Sunana Maharaz. Ni aminin kakan-kakanka ne kamar yadda na sanar da kai a baya, ni da shi duka mun gudanar da rayuwarmu ne a cikin wannan masarautar. WaÉ—annan bushiyoyin da kake gani ni da shi ne muka dasa su da hannuwanmu..."

Tafiya take kamar za ta tashi sama har ta ƙarasa sashen Bayi da tuni labarin abin da ya faru ya isa gare su, a tsaitsaye ta same su sun yi carko-carko cike da jimami. Jakadiya na ƙarasawa ta wurga musu mugun kallo cike da ƙasƙanci.

"Da alama labari ya iso gare ku, don haka ku san da sanin kun É—an É—aya daga cikinku ya tsokano muku tsuliyar dodo." Jakadiya ta yi maganar tana zagaye su É—aya bayan É—aya.

"Ai wanda bai gaji arziƙi ba dole sai ya nuna tsiya, ban da iskanci a ce kana ƙasƙantacciyar hallita amma za ka nemi cin zarafin ɗan masu masarauta. Tun wuri wallahi tun ba a je ko ina ba duk wacce ta san tana da ɗanta ne ya aikata wannan zunubin ta yi gaggawar fito da shi ida ba haka ba, za ku bambamce wa Fulani Umaima tsakanin tsaba da tsakuwa." Uwar Bayi ta yi maganar rai a ɓace.

Take gaban Inna wuro ya faÉ—i, fargabar ta É—aya kada a ce Kamalu ne ya aikata wannan mummunan aikin.

"Allah Inna babu yaron da ya isa ya nuna mini yatsa ban karya shi ba ko É—an gidan uban waye." Lokaci É—aya kalaman Kamalu na baya suka dawo mata a lokacin da faÉ—a ya haÉ—a shi da É—an Gunduman rigarsu. Wani abu ta ji ya tsarga mata take gumi ya shiga yanko mata cike da tashin hankali.

"Ruwanku ne ku sauƙaƙa wa kanku azabtarwar da ke tunkaro ku don yanzu haka Takawa da Fulani Umaima ne suka umarce ni da na yi gaggawar tara ku a harabar sashenta." Rufe bakin Jakadiya hayaniya ta fara tashi kowa da abin da yake tofawa, sai dai a mafi yawan daga cikinsu kowa zame ɗansa yake ƙoƙarin yi. Inna wuro tana tsaye jigum ko motsin kirki ta gagar yi, ana cikin haka ta fakaici ido ta ƙarasa wurin Baffajo da shi kansa yana tsaye suna jajanta abin da ya faru. Sai da suka keɓe bayan ya kalli hagu da dama ya furta. "Inna wuro ina tsoron kada Kamalu ne ya aikata wannan abin." Idanun Inna wuro ya ciko da ƙwallah. "Wallahi abin da na zo sanar da kai kenan, ai kuwa yau da kwananmu ya ƙare." Ta ƙarasa maganar hawaye na zuba, da sauri ya katse ta. "Kul Inna wuro kada ki sake wani ya fahimci halin da muke ciki yanzu ina Kamalun?"

"Tun la'asar rabon da na ga gilmawarsa, har A'iru na aika ba ta gan shi ba." Jinjina kai ya yi ya ce. "Koma can maza kada wani ya fahimci ba kya nan." Da sauri Inna wuro ta wuce jiki a sanyaye kamar akuyar da ta bi ta mahauta, a lokacin tuni Bayi sun fara bin hanyar da za ta sada su da can babbar haraba. Suna tafe ƙwai da fure Jakadiya Uwar Bayi sai zazzaga musu masifa suke cikin kyara, tsangwama da wulaƙanci, sai da suka isa babbar harabar sannan Jakadiya ta isa sashen Takawa ta sanar da Fulani Umaima da Mai martaba ta sanar da su ta cika umarninsu. Fulani Umaima da kanta ta riƙo hannun Muhsin suka ƙarasa wurin da Bayin ke tsaitsaye, fuskarta a matuƙar ɓace ta dube su cike da ƙasƙanci. "Ina mai ba ku shawara da tun ƙofar haƙurin da ta danne zuciyata ba ta buɗe ba ku yi gaggauta fito da yaron da ya nuna wa Yarima rashin ɗa'a, idan ba haka ba wallahi sai na shayar da ku ruwan mamaki." Hayaniya ce ta fara tashi sama-sama take Jakadiya ta buga musu tsawa sannan suka yi shiru. Ganin babu wanda ya nuna mai laifin a ciki ya sa Fulani Umaima ta sa Jakadiya ta rarraba layi-layi, sannan Muhsin ya fara bi ɗaya bayan ɗaya yana dubawa ko zai ga Kamalu.
Chapter 21 · 0% Book details