← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 86

Sashe 36

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wannan abin da yake faruwa Fulani babba ba ta san wainar da ake toyawa ba, sai dai ta lura da sauye-sauye tsakaninta da Maigidanta. Ya bijiro mata da sababbin halayen da ba ta san da su ba kamar; kyara, hantara, yawan faɗa, saurin fushi da ƙaurace mata, amma gudun tashin hankali a tsakaninsu sai ta riƙa takatsantsan. Amma kuma ta yi mamaki matuƙa da ta ga Umaima ta janye ƙafarta daga shiga sashenta har sai da watarana ta taɓa aika bayinta su gano mata ko lafiya kwana biyu ba ta zo mata ba. Duk da saƙon da Fulani babba ta tura wa Umaima bai sa ta taka ta je ba domin a ganinta ai buƙatar maje hajji sallah, buƙatarta ta riga da ta biya babu sauran wahalar da kai.

Lokacin da Mai gado ta ji saƙon kiran Fulani babba da halin da take ciki ba ƙaramin kaɗuwa ta yi ba, zani daban riga daban ko ɗankwali ba ta ɗaura ba ta ɗora mayafinta a kanta ta fice.

"Ko dai abin da yarinyar nan ta faɗa gaskiya ne?" Mai gado ta ayyana a zuciyarta. Kamar za ta tashi sama hake take zabga sauri tana shirin gifta ƙofar Fulani Umaima ta ji an furta. "Keee!" Cak Mai gado ta tsaya cikin saranda ta waiga. "Allah ya taimaki ranki shi daɗe."

"Ina za ki je?" Fulani Umaima ta tambaya don son jin halin da Fulani babba take ciki.
"Tuba nake ranki shi daɗe, Fulani ce ta aika na zo da gaggawa ba ta jin daɗi." Wani sanyi ya ratsa zuciyarta amma sai ta fuske. "Idan kin gama da sashenta ina son ganinki." Rass! Gaban mai gado ya faɗi don ko kaɗan ba ta san wata alaƙa da za ta shiga tsakaninta da Fulani Umaima musamman da ya zama duk cikin Bayi Fulani babba ta fi aminta da ita. "An gama ranki shi daɗe, ki huta lafiya." Mai gado ta furta a sanyaye sannan ta wuce bayan Fulani Umaima ta sallame ta.

"A gafarce ni uwar ɗakina idan na yi jinkirin zuwa." Mai gado ta yi magana tana ƙarasawa jikin gadon Fulani babba zuciya a tsinke. A madadin Fulani Babba ta iya tanka mata sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, hankali a tashe Mai gado ta matsa gabanta idanunta suka ciko da ƙwalla.

"Uwar É—akina akwai abin da yake damunki ne?"

Sai da Fulani babba ta yi kuka mai isarta sannan ta sanar da Mai gado duk abin da yake faruwa, ban da hawaye Mai gado babu abin da take yi, da ƙyar ta iya ɗaga Fulani babba ta jingina da bango ta sauya mata kayan jikinta ta ɗaura mata alwala tana yi tana zubar da ƙwallah.

"Ranki shi daɗe mai zai hana a aika da takarda ƙasar Rumm a sanar da Yadikko halin da kike ciki?" Fulani babba ta kalli Mai gado tana son ta girgiza kanta amma ta kasa. "Mai gado... mahaifiyata girma ya kamata, ga Yaya Halima da ke gabanta tana fama da lalurar hauka. Idan na sanar da ita hankalinta zai ƙara tashi." Mai gado ta share ƙwallar idonta tana shirin yin magana Fulani babba ta ci gaba da cewa.

"Ban sanki ba, ban san daga inda kika fito ba Mai gado, amma duk cikin masarautar nan da ke kaɗai na aminta." Kuka ya ci ƙarfin Yaya babba, Mai gado ta share mata hawaye duk da ita ma kukan ya gagara tsagaitawa daga ƙwayar idonta.

"A halin da nake ciki jikina yana ba ni ajali ya kusanto ni, tawa ta zo ƙarshe. Don Allah ko bayan rayuwata ki kula mini da Abubakar, na san wannan wahalallan alƙawari ne na damƙa miki domin ba ki da ikon kanki wataƙila ma a hana ki shiga al'amuran shi. Amma idan har kin samu dama ki kula mini da shi, na bar shi a hannun Allah da hannunki Mai gado."

"Ranki shi daɗe cuta ba mutuwa ba ce, ki daina faɗin haka In shaa Allah za ki samu lafiya." Murmushin yaƙe Fulani ta saki. "Na yi jinya kala-kala Mai gado, na gamu da cutuka mabambam amma wannan ciwon da na wayi gari da shi daban yake da sauran."

Lokaci ɗaya wani irin tari ya turnuƙe Fulani babba, ta fara kwara wani irin baƙin aman jini mai wani irin wari. A ruɗe mai gado ta kira Baiwa Zainaba suka fara gyra Fulani babba, a lokacin tuni zuciyar Mai gado ta gama karyewa.

Sai bayan wani lokaci Fulani babba ta dawo hayyacinta, Zainaba da Mai gado sai share ƙwalla suke don duk wanda ya ga halin da take ciki sai ya tausaya mata.

"Ranki shi daɗe na aika Zainaba wurin Takawa ba ta same shi ba." A wannan karon muryarta ta sake yin ƙasa sosai. "A sanar da Jakadiya idan ya dawo ta sanar da shi halin da muke ciki." Da sauri Baiwa Zainaba ta fita ta samu Jakadiya ta sanar da ita halin da Fulani take ciki.

Kamar wacce aka yi wa kyautar Aljanna haka farinciki ya lulluɓe zuciyar Fulani Umaima, ta koma cikin sashenta cikin murna tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Uwar ɗakinta ta faɗa ta tsinci kanta da ɗauko akwatin da ta adana littafin labarin Hidaya, sai da ta ɗauko ɗaurarriyar fatar da Bamaguje ya bata ta juya a hannunta tana sakin dariyar ƙeta sannan ta mayar ta ɗauko littafin. Sai da ta jingina da bango ta buɗe shafin da ta tsaya sannan ta ci gaba da karantawa.

Ban san me ya ba wa Sarki Hafiz dariya a cikin tambayata ba don haka na kafe shi da idanu ina kallo, sai da ya ɗan saita nutsuwarsa ya dube ni yana faɗin. " A tsammanina ko kaɗan bakya daga cikin wani jinsi bayan na bil'adama. A labarin da Kakana ya ba ni wanda shi kansa ya ce kusan labari ne na kunne ya girmi kaka, mahaifiyarki ta kasance 'ya daga wurin sarkin wanzamin garin nan wato Bala wanzam. Su biyu ne 'ya'yansa daga mahaifiyarki sai ɗan uwansa Shamsu, tun tasowar Mahaifiyarki mace ce mai sanyin hali da kyakkyawar mu'amala. Shi kuma mahaifinki ya fito daga zuri'ar Bargi waɗansu mutane ne da ke rayuwa a gaɓar tekunan da ke kewaye da su, waɗannan al'umma al'amuransu na da matuƙar ban mamaki sakamakon ba sa rayuwa a ko ina sai gaɓar teku, kuma duk hunturu ba sa barin wurin. Kuma an yi zargin mahaifinki jika ne ga sarkin ruwan yankin Dahwan, a yadda Kakana ya ba ni labari watarana wani masunci ne ya zo da 'yarsa gaɓar yankin da zuri'ar Mahaifinki suke zaune, sun yi mu'amala da arziƙi da shi yana shiru ruwa da zummar ya yi su, sai kwalakwalensa ya kife da shi. Duk iya ruwa da ƙwarewarsu da kogi ba su iya samo mutumin ba, dalilin haka ya sa mahaifin kakanki ya ɗauki yarinyar da ya bari ya ci gaba da rainonta har ta zama budurwa Kakanki ya aure ta.

"Idan na fahimta kenan babu wanda ya asan asalin Kakata kenan?" Na katse Sarki Hafiz daga bayanin da yake yi mini sai dai ko kaÉ—an kwanyata ta gagara jera kalmominsa a ma'aunin da suka dace.

"Mutane da dama sun yi harsashe sai dai har kawo wannan lokacin babu amsa ƙwaƙƙwara kuma mai tushen da za a kafa hujja da ita." Ajiyar zuciya na sauke na sake zuba masa idanu.

"A labarin da aka ba ni kakanki tun tasowarsa ya kasance hatsabibi mara tsoro, don an ce waɗansu daga cikin jinsin aljanu har tsoronsa suke ji. A wannan lokacin kuma a kwai ɗan sarkin baƙaƙen aljanu Darri da ya taso cikin taƙadiranci da hatsabibanci kuma ko kaɗan ba sa ga maciji da kakanki, a wannan lokacin sai shi Aljani Dharri ya so auren Kakarki dalili kenan da ya ƙara tsaurara tsattsamar alaƙarsu. Da yake sun buɗe wa kakanki idanu sai ya zamana yana ganinsu muraran har su yi ta sa'insa, daga ƙarshe dai Kakanki ya yi galaba a kanshi don haka sai ya karya ƙadarin Darri, duk hatsabibancinsa sai ya yi laƙwas kuma ya zubar da makamansa.

Kwatsam babu zato bayan waɗansu shekaru masu tsayi sai aka wayi gari ɗan autan Dharri ya kamu da matsananciyar soyayya da mahaifiyarki. Da farko mahaifiyarki ba ta san Buhsu ba mutum ba ne, domin idan ya tashi zuwar mata a surarsa ta bil'adam yake zuwa. Sai da ya fahimci soyayyarsa ta yi ƙarfi a zuciyarta sannan ya bayyana mata ainihin zubi da surar hallitarsa. Da yake shi so ƙundunbala yake ya hana ganin laifi ko gezau mahaifiyarki ba ta ji za ta iya rabuwa da shi ba, sai ma soyayyarsa da ta mamaye zuciyarta. Akwai abin da na manta ban sanar da ke ba." Jin kalaman Sarki Hafiz ya sa na ɗago da sauri ina kallonsa, ya jinjina mini sannan haɗe da faɗin.

A razane Fulani Umaima ta rufe littafin babu shiri sakamakon jin muryar Jakadiya raɗau a tsakiyar ɗakinta, da sauri ta mayar da littafin ta miƙe ta fito fuska ba yabo ba fallasa.

"Umaima wani sabon labari na ji da farar safiyar nan shi ne na zo na ji wanne tuggun kika haÉ—a wa baiwar Allahr da ba ta ji ba; ba ta gani ba?" A yamutse Fulani Umaima ta dube ta.

"Wai dama kura ce za ta ce wa kare maye? To wai ma wane dare ne jemage be gani ba? Zuwa kika yi ki raina mini hankali Jakadiya da za ki kawo mini wannan maganar?"

"Fulani na san rashin imaninki sarai, ni kin gan ni na fara tuba ga Ubangiji don zalinci da muka shuka a gidan nan na fara fargaba da tunanin ranar girbarsa." Jakadiya ta yi maganar kamar wacce tsoron Allah ya samu matsuguni a zuciyarta. Shewa Fulani Umaima ta yi sannan ta furta.

"Duk ma abin da kika yi tsammani zan iya aikatawa Jakadiya, kin fi kowa sanin wace ce Umaima don haka ƙofa a buɗe take da za ki iya zartar da hisabinki a kaina." Gaban Jakadiya ya faɗi, don wata irin fargaba ce ta dirar mata. Ganin ba ta da abin faɗa ya sa ta fice daga ɗakin kai tsaye da faɗa sashen Fulani Babba.
Chapter 36 · 0% Book details