← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 86

Sashe 84

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba zan iya barinku ba ban san halin da za ku shiga ba..."
"Ki fita ki gudu na ce miki Fargi." Mahaifinta ya katse ta cikin ƙaraji. Duk yadda Fargi ta so sarrafa al'ƙalamin tsafinta domin ta gudu sai ta kasa, don haka ta faɗa ɗaki da sauri ta ɗauki wani sabon ganye ta ɗaure shi katamau a jikinta ta soka wata tsafaffiyar askarta a ƙugu da sauran tarkacanta, ta waiga tana ɗaga wa mahaifanta hannu sannan ta saɗaɗa ta bayan bukkar ta fice, duk da tana jin ciwon baya da marar hakan bai hana ta yin gudu tun ƙarfinta ba, sai da ta ɗan yi nisa sannan mutanen garin suka rushe duk wata bukka da ke gidan a ƙoƙarinsu na ganin sun gano Fargi ƙarfi da yaji, da suka fahimci ta gudu sai Shugaba ya ba su umarni da su rarrabu wuri-wuri ko za su samu nasarar kamo ta. Abu ɗaya ya ba shi mamaki yadda ya gagara sarrafa tsafinsa domin ya gano wurin da take, ya san dai ya dakushe na ta tsafin amma bai san me ya hana na shi ya yi tasiri ba. Abin da Shugaba bai sani ba tun da Abar bauta ta lura yana da niyyar kashe ta, a ranar sai ta dakusar masa da tsafinsa.

A galabaice ta faɗi a wani ɗan ƙaramin ƙauye ta ɗebi ruwa ta sha saboda gudun da ta sha, tana nan zaune ta fara jin taku a hankali. Miƙewar da za ta yi ta yi arba da waɗansu matasa biyu daga cikin mutanen garinsu, da sauri suka ƙaraso wurinta ɗaya daga ciki ya kai mata naushi a ciki. Azaba ta sa ta faɗi gefe ta ɗauki wani ganyen bishiya ta hura iskar bakinta ta wurga musu, ganyen na sauka a fuskarsu ta kama da wuta. Wani irin azababban ciwon mara ya da baya ne ya haɗe mata, a daddafe ta iya matsawa daga cikin wannan ƙauyen ta tsallake wani ƙasurgumin dajin da ke gabanta, a lokacin ta da isa ta galabaita sosai don haka ta faɗi a gefan wata bishiyar kuka, da faɗuwarta babu jimawa ta fara jin motsin tafiyar mutane a tsorace ta ɗago don a tunaninta wasu daga cikin mutanen nata ne suka sake cim mata, amma ganin baƙin fuska ya sa ta sake kwantar da kanta ciwo ya sake taso mata gadan-gadan, har zuwa lokacin da Mai gado ta ƙarasa wurinta Malam Umaru ya juya musu baya ta haihu.

Cikin ƙanƙanin lokaci mutuwar Malam Umaru ta karaɗe cikin masarautar Huddam, musammam ma Bayi ba ƙaramin kaɗuwa suka yi da jin mutuwarsa ba, kuma har lokacin ba su daina mamakin dalilin kwanciyar Malam Umar jinya da ɓatan Jawahir ba daɗin-daɗawa da suka ji abin da aka ce Malam Unaru ya faɗa kafin Allah ya yi masa rasuwa. Da farko an so a sallace shi a ranar amma kasancewar Magriba ta kawo kai ya sa aka bada shawarar barin gawarsa zuwa wayewar gari, Kamalu , Baffajo da sauran mutanen da suke mutumci da Malam Umaru ne suka ce za ku kwana da shi, domin kowa yaba kyawun halinsa yake da kyakkyawar mu'amalarsa da mutane.

Kunyar duniya ce ta mamaye Dela musamamn yadda ta ga mutane suke bin ta da kallon mamaki, wasu daga ciki har sun fara tofa albarkacin bakinsu yayin da wasu har kawo lokacin tsoranta bai gama barin zuciyarsu ba.

"Baba me kake so na ce maka bayan ka riga da ka gama tona mini asiri? Duk wannan wulaƙancin da kuka yi mini bai isa ba..." A fusace Babban Malami ya yi kanta ya kai mata duka, Dattijo Maharaz ya ɗan ruƙo hannunsa sanna ya furta. "Ka yi haƙuri Babban Malami ai In shaa Allahu komai ya zo ƙarshe. Idan za ta tuba sai a ƙyale ta ta ci gaba da rayuwarta..."
"Ba za ta taɓa tuba ba Maharaz! Na san wace ce Dela 'ya ta ce fa. Ya zama wajibi a ƙone ta kowa ma ya huta." Rufe bakin Babban Malami suka ci gaba da ƙone Dela da ayoyin Ubangiji.

".Na daina na tuba don Allah kada ku hallaka ni." Dela ta furta a galabaice, babu wanda ya saurara mata daga cikinsu har sai da suka ga ta faÉ—i gefe É—aya babu numfashi a jikinta.

"Alhamdulillah!" Ita ce kalmar da suka furta gabaɗaya, jikin mutanen Rumzu ba ƙaramin sanyi ya yi da ganin abin da ya faru ba. Waɗanda suke gaban Babban Malami lokaci ɗaya suka zube a gabansa ganin haka ya sa sauran da ke bayansu gabaɗaya suka tsugunna alamar sun sallama masa.

"A shirye muke da mu bauta maka tun da har muka ga ka kawo ƙarshen Abar bautar da muke bautawa tun iyaye da kakanni, tabbas mun gasgata ita ba abar bauta ba ce tun da har mun fahimci raununta." Tashin hankali ya bayyana ƙarara a fuskar Babban Malami don haka cikin hanzari ya furta.

"Ni ba Ubangiji ba ne kamar yadda Dela ba ta kasance Ubangiji ba, ni hallitar Allah ne kuma shi ne ya kawo ƙarshenta saboda ayoyinSa ne muka karanta har muka hallaka ta. Ni da sauran waɗannan bayin Allahn duka Shi muke bautawa, ku sani Dela ta yi wasa da hankalunku ne saboda waɗansu abubuwan almara da take aiwatar muku, shi ya sa har kuka ba ta matsayin da ba ta cancanta ba. Shi jinsin aljani ba kamar mutum ba ne, Allah ya huwace mana baiwar da za mu iya rikiɗa duk wata hallita da muke so, kuma muna iya aiwatar da duk siddabarun da muke so a wurin da addini haɗi da addu'o'i suka yi rauni. Don haka a yanzu ma ba ku makara ba, za ku iya karɓar wannan Addinin ku yi riƙo da shi kuma ya zame muku makamin da za ku yaƙi duk wani hatsabibi ko hatsabiyar da ke doron ƙasa duk makirci da ƙarfin tsafinsa, domin ba su isa su ja da ƙarfin ikon Allah ba. Yanzu idan kuka yi imani da ni watarana na mutu wa za ku riƙa a matsayin abin bauta?" Babban Malami ya wurga musu tambaya, gabaɗaya suka yi shiru don jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba ganin haka ya sa ya ci gaba da cewa. "

"Ubangiji shi kaÉ—ai ne abin bauta saboda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, Shi kaÉ—ai tal ba shi da abokin tarayya. Annabi Muhammad S.A.W BawanSa ne kuma ManzonSa ne, Ubangiji ba ya mutuwa ba ya tsufa don haka ku ji tsoron Allah ku hau turbar addinin Musulunci."

"Muna goyon bayan wannan Addinin kuma a shirye muke mu karɓe shi hannu bibbiyu." Gabɗaya mutanen wurin suka amsa masa.

Farincikin su Sarki Sulaiman ya bayyana a fili Dattijo Maharaz zai yi magana suka ga Sarki Sulaimanu ya fara zubar da ƙwallah.

"Yanzu shi kenan Fargi ba ta rabauta da samun wannan Addinin ba? Kaico rayuwa ban so haka ba. Na so a ce ta rabauta amma kullin gaya mini take za ta karɓi Addinin Musulunci idan lokaci ya yi Allah ya jiƙanki Fargi." Jin haka ya sa Jawahir ta fara zubar da ƙwallah, Sarki Abdul'aziz ya dafa kafaɗarsa sannan ya ce. "Sarki Sulaimanu ita rayuwa duk yadda ta zo wa Bawa dama can Allah ya ƙaddarar masa ita a haka, tun ran gini tun ran zane. Dama can Allah ya ƙaddari Fargi ba za ta karɓi kalmar Shahada ba, amma kuma wani ikon Allah sai ya zama silar ta ne Al'ummarta za su rabauta da shi, koda Fargi tana raye aka yi haka idan ba ta da rabo ko duniya za ta haɗu a kanta ba za ta karɓi Addinin Musulunci ba. Mu manta da rayuwar baya mu fuskanci ta gaba, ina ganin haka zai fi Sarki Sulaimanu." Rufe Bakin Sarki Abdul'aziz Alaramma ya ɗora da cewa.

"Akwai wani jan hankali da zan yi gare ka Sarki Sulaimanu da sauran mutanen wurin nan, duk da a yanzu girma ya kamaka. Ka sani kuskure ne babba yaro ya auri yarinya ba tare da sani ko amincewar iyayenta ba. Wallahi-wallai tun da Allah ya ƙaddari yarinyar nan Jawahir za ta fito tsakanin kai da Fargi da ka sanar da iyayenta babu abin da zai hana faruwar aurenku sai ikon Allah. Sau-tari akwai abin da idanunmu suke rufewa akai wanda ba alkairi ba ne amma idan muka yi haƙuru muka yi addu'a sai kuma mu ga abin ya zo mana ta ruwan sanyi." Ya waiga wurin Mahaifinsu Fargi sannan ya ce. "Babu camfi a addinin Musulunci ko tsubbu, don haka ya zama wajibi ku zubar da duk wasu tsubbace-tsabbace da tsafe-tsafe hatta wannan ɗabi'ar ta hana auren bare dole ku soke ta. Domin kuna ganin irin abin da ya haifar, ga dai yarinya har ta girma shin kun isa dakatar da ƙaddara ne?" Lokacu ɗaya suka ce.

"A'a."

Alramma da Malam Liman suka ci gaba da yi musu nasiha mai ratsa zuciya daga ƙarshe ya laƙanta musu kalmar Shahada yana faɗa suna maimaitawa. Mahaifi , mahaifiyar Fargi da yayyanta suka rungume Jawahir suna kuka gwanin ban tausayi.

Babban Malami ya umarci su Sarki Abdul'aziz da su koma Masarautarsu shi zai koyar da su yadda ake wankan shiga Musulunci da sauran hukunce-hukunce da suka shafi addini. Sarki Sulaimanu kai tsaye ya ce zai tafi da Mahaifan Fargi don idan suka tafi da Jawahir suma ba su yi musu adalci ba, saboda ya lura da tsantsar soyayyar da suke yi wa mahaifiyarta, kafin su kai ga tafiya labari ya iso gare su Shugaba Zurufu ya caƙa wa kansa wuƙa ya mutu har lahira.

Mai martaba sai da ya tara duka matansa sannan ya sa aka kira masa Yaya Halima, tun da ta shiga ɗakin gabanta yake faɗuwa don ta san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi ba. Sai da ya yi sallama suka amsa sannan ya dube ta ya ce.
Chapter 84 · 0% Book details