Sashe 58
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A yanzu wannan lokacin ba na damuwa ko ɓacin rai ba ne!" Sulaiman ya furta yana harɗe hannuwansa biyu a ƙirji haɗe da sakin murmushin farinciki. Ɗagowa ta yi ta goge hawayenta a madadin ta yi walwala sai ta sake fashewa da ƙuka, jiki a sanyaye Sulaiman ya ƙarasa wurinta. Ta sunkuyar da kai ƙasa tana murza yatsun hannuwanta.
"Na so a ce zamu yi rayuwar farinciki tamkar yadda sauran ma'aurata suke gudanar da rayuwarsu, sai dai kash! Ba lalle mu samu wannan damar ba. Domin ina tsoron ranar da Shugaba ko wani daga cikin dangina zai bankaɗa labulen sirrinmu...." Da sauri ya ƙarasa ya rufe mata baki yana sauke ajiyae zuciya. "A duk lokacin da kika yi wannan furucin ƙirjina yana bugawa, don Allah a duk lokacin da za ki yi tunani ki dinga yi mana na alkairi." Gyaɗa masa kai ta yi sannan ya ajiye mata gasassun 'yan shilan da ya sa aka gasa musu. Sannu a hankali Sulaiman da Fargi suka fara cin 'yan shilan hankali kwance tun tana noƙewa har ta saki jiki suka ci suka ƙoshi, sai da ya ja ta hira sosai don ya kawar mata da duk wani tsoro da fargabar auren nasu da ke cikin zuciyarta sannan ya ce ta shirya don ya mayar da ita. Murmushi ta sakar masa sannan ta haɗa hannuwanta ta tafa su nan take ta rikiɗe zuwa siffar tantabara, a daidai kan kafaɗar Sulaiman ta hau tana kaɗa fukafukanta. Shafata ya fara yi yana murmushi don ya fahimci tun da ta yi nasa haka ba ta buƙatar ya yi mata rakiya.
Sai gab da magriba Sulaiman ya koma cikin Masarautarsu a nan ya tarar an kawo masa amarensa biyu, wani irin takaici ne ya kama shi amma da ya tuna a yanzu Fargi ta zama matarsa sai ya ci gaba da walwalarsa har wasu daga cikin dangi suna tsokanarsa wai har ya sauko daga ƙiyayyar auren, saboda da farko ya nuna gabaɗaya ba ya ƙaunar auren haɗin da za a yi masa.
Boka Shaddas bayan ya mayar da littafin yana juyowa daga can wurin wannan rijiyar ya ji wata irin kuɗa ta ratsa majiyar sautinsa, ajiyar zuciya ya sauke don tun da ya ji wannan kuɗar ya san akwai wani muhummin taron gaggawar da ake buƙatarsa a fadar Sarkin Aljanun dajin Hubud. Sai da ya ƙarasa wurin Basiru sannan ya furta, "A yanzu haka na samu kiran gaggawa daga wurin madogarar da suke ba ni ƙwarin gwiwa dangane da sirrin tsafi da sihirina, duk wani aiki da ba zai gagare maka ba ka aiwatar da shi don na san kai ɗin gwani ne kuma hatsabibi ne." Wani ƙasaitaccan murmushi Basiru ya saki har sai da gaban Boka Shaddas ya faɗi, don bai san dalili ba haka kawai yake jin zuciyarsa na wasu-wasi a kan Basiru. "Yaushe za ka dawo? Don gaskiya ina da aikin da zan aiwatar a cikin tsakiyar dare kuma ba na jin a nan zan aiwatar da shi." Basiru ya faɗa wa mahaifinsa wannan maganar don ya kawar da tunaninsa daga zarginsa. A fili Boka Shaddas ya faɗaɗa fara'arsa munun fuskarsa ya ƙaru, kalaman Basiru suka yi tasiri a ransa. "Ka yi mini uzuri ba na jin zan shafe sa'a guda." Basiru na gama sauraron mahaifinsa ya wuce can bakin wutar da Boka Shaddas ya tanadar masa wacce yake binciken duk wani abin da ya shafi al'amarinsa na tsafi.
Shugaba Zurufu ƙuri ya yi wa Jakadiya da ke gursheƙen kuka, kuma ya yi mamakin ganinta bayan ya san Boka Shaddas ne ya yi mata iso a can kwanakin baya. Yana shirin katse kukan nata ta sake rushewa da kuka tamkar wacce saƙon mutuwar Mahaifyarta ya riske ta. "Ya shugaba mai shugabancin wannan yankin ka taimaka miki ka shiga lamarina, duniya ta yi mini ƙunci yayin da bala'o'i suke rufto wa rayuwata da ta 'yar auta."
"Shaddas ya jima yana yaudararki don haka matsawar kika taɓe a wurinsa buƙatarki ba za ta taɓa biya ba." Shugaba Zurufu ya furta wa Jakadiya yana watsa wata jar ƙasa saman allon ƙarfen da ke ƙonewa a kan wuta. "Na jima da fuskantar haka Shugaba don haka na sato ƙafa a yanzu da na kawo ziyara wurinka domin kaine mai share mini hawayena."
"Abu ɗaya za ki yi mini matuƙar kina son buƙatarki ta biya, ni nan da kike gani tun da na sa tsafi a gaba nake ganin ci gaba don haka tsafi ba zai taɓa ba ni kunya ba. Yau ina matashiya Fargi da ke nuna za ta iya kara wa da ni, tana in a yanzu? Babu ita tun da na shafe babinta. Jakadiya buƙatarki za ta biya kamar yadda na faɗa miki amma sai kin kawo mini Basiru ɗan Boka Shaddas, kuma sai kin haɗo mini da littafin hannunsa. A yanzu haka zancen da nake yi miki Basiri ya mallaki wannan kundun littafin domin ba ƙaramin hatsabibi ba ne, Duk hatsabibancin mahaifinsa shafar mai ne a kansa. Idan kika cika wannan Umarnin Sailuba za ta warke, zan iya kashe miki Umaima idan kuma sabautata kike buƙata ayi nan take zan zartar da shi." Baki na rawa Jakadiya ta furta, "Shugaba a baya Boka Shaddas ya sha yi mini irin wannan alƙawarin amma ko kaɗan ba ta sauya zani ba..."
"Dataka Jakadiya! Shaddas ko ƙafarmu bai kama ba ballantana ki haɗa tsafina da na shi, idan kika kuskura kika sake yi mana wannan furucin za mu shafe ki a doron ƙasa." A razane Jakadiya ta hau girgiza kai, ta zube ƙasa tana ba shi haƙuri sai da ya karɓi tubanta sannan ya damƙa mata magunguna da kayan binne-binnen da za ta yi, ta shiga zabga masa godiya har ta juya za ta tafi Shugaba ya dakatar da ita.
"Waccan ziyarar Boka Shaddas ne ya biya miki tukwicin ziyararki, a yanzu kuma dole ki biya wa kanki domin wannan zuwan kanki da kanki ne." Gaban Jakadiya ya faÉ—i, a sanyaye ta furta. "Mene ne tukwicin ya shugabana?"
"Tun da wannan zuwan da kika yi zai zame miki tamkar zuwan farko ne, da farko zan haɗa ki da ɗan autan baƙaƙan aljanun ƙasan ruwa ya yi mu'amala da ke." Da sauri Jakadiya ta ja da baya hannuwa biyu dafe a ƙirjinta cikin tashin hankali ta furta.
"Yau ni Salame na shiga uku na lalace! Shugaba ka yi mini rai kada ka yi mini haka wallahi rabona da wannan lamarin har na manta, marigayi Malam Bukar yau shekara Ashirin da biyu kenan."
Shugaba Zurufu ya tamke fuska don tuni Jakadiya ta fara tunzura shi, ya nuna ta yatsa yana faɗin. "Kada ki kawo mana wargi yanzun nan na mayar da ke Fanteka ko kumbo. Jakadiya wannan doka ce ga duk wanda ya ziyarce mu a ziyararsa ta farko. Don haka da ki amince da karki amince Aljani Buguzu zai amarce da ke a daren yau, gata ma na yi miki da ban haɗa ki da Bulku ba, domin shi zai iya yin fata-fata da ke." Jakadiya ba ƙaramin firgici ta shiga ba, cikin tashin hankali ta fashe da kuka har da majina tana faɗin. "Ka yi mini rai Shugaba kada ka sa Aljani Buguzu ya turmushe ni wallahi ni ko ɗan autan bunsuru ban taɓa ma'amala da shi ba, idan ka haɗa ni da ɗan aljan ban san ta ina zai fara ba, ka dube ni komai ya ƙare ya tsumbure."
Rai a haɗe Shugaba Zurufu ya ce. "Na rantse da gawurtar tsafin da ke cikin dajin nan da muka gada tun iyaye da kakanni idan kika sake magana sai na shafe ki Jakadiya. Ki fice ki ba mu wuri don yanzu haka Buguzu yana can yana amsar horo daga wurin Kabdu." Jakadiya ba ta sake furta koda kalma ɗaya ba, sai kuka da ta saje rushewa da shi ta fice daga cikin tsibirin don rabonta da sharɓar kuka kamar wannan tun mutuwar marigayin mijinta.
Tun da Dattijo Maharaz ya fara magana Fulani Umaima ta yi wata irin zabura, cikinta ya yi wata irin murÉ—a wani irin zazzafan gumi ya fara keto mata. "Me... kake faÉ—a... ne? Wai ma... waye.. kai?" Fulani Umaima ta yi maganar cikin in'i'na.
"Ranka shi daɗe me wannan tsohon yake faɗa ne? An ya ba mahaukaci ba ne..." Tun Muhsin bai gama magana ba Sarki Abdul'aziz ya sauke masa yatsu biyar a fuska. "Idan kuka nemi ku kawo mana rashin ɗa'a ranku zai yi mummunan ɓaci." Ilahirin mutanen da ke wurin jikinsu sanyi ya yi, hatta Abubakar ganin haka sai da ya sa shi ya fashe da kuka yana janye jikinsa daga Sarki Abdul'aziz don gani yake tamkar shi ma zai hukunta shi. A jikin Kamalu ya kwanta, ya saka hannuwa biyu ya riƙe shi yana cusa kansa a jikinsa.
"Wannan da kuka gani ba iya kaka na ɗauke shi ba, na ɗauke shi jini da tsokar jikina. Ina matuƙar girmama shi har ban san yadda zan fasalta girma da matsayinsa ba. Ba kai ba ko mahaifiyarka ba ta isa ta furta magana marar daɗi a kansa ba." A wannan karon tuni Fulani Umaima ta yi fuƙai-furƙai, ban da goge gumi babu abin take yi. "Dattijo Maharaz kalamanka na shirin kawo ruɗani a cikin iyalina, ban fahimci abin da kake nufi ba."
"A ƙallah na yi zamani da mahaifin kakanka Abdul'aziz, a zubi da tsarina ka san ni ba yaro bane. Ina da zuri'a ina da 'ya'ya da tarin jikoki, idan na furta waɗanan kalaman don na kawo ruɗani ko tashin hankali a tsakaninka da iyalanka shin wacce riba zan ci? Ka na tunanin zan furta maka ƙarya ne Sarki Abdul'aziz?" Kunya ce ta lulluɓe Sarki Abdul'aziz da jin kalaman Dartijo Maharaz, ba tun yau ba ya kan ji ana cewa wasu daga cikin jinsin Aljanu sun iya sharara ƙarya musamman idan suka fahimci mutum yana anfani da abin da suke faɗa. Amma a wannan fannin zai iya bugar ƙirji a ko ina ya tsame Dattijo Maharaz daga cikin waɗanda ake wa kallon maƙaryata.