← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 86

Sashe 75

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya ta miƙa sosai har soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Yarima ɗan Sarki Hafiz, kuma hakan ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba aka ɗaura aurenmu muka ci gaba da rayuwa cikin farinciki a farkon auranmu.

Jawahir ta ɗago kanta tana sauke ajiyar zuciya a tunaninta ta kai ƙarshen labarin, daga can bangon ƙarshe ta ga wani guntun rubutu daga samansa an rubuta ABIN LURA, cikin rubutun ajami. Jingina ta yi da bango sannan ta ci gaba da karantawa.

ABIN LURA

Ga duk wanda ya mallaki wannan littafin kuma ya karanta shi, tamkar ya mallaki rabin abin da zai mallaka a nan gaba ne. Babban burina bai wuce jinina kuma ɗan asalina zuri'ata ya mallaki wannan kundin ba. Ina yi wa duk wanda ya kasance mai nasara da fatan alheri. A wannan lokacin da nake yunƙurin kammala rubuta tsakure daga cikin labarina, Hidaya ta san wace ce ita a gaɓar da ba ta taɓa tsammani ba, sanin tarihina ya sa na fahimci ba iya jinsina na bil'adam ne kaɗai suke da karamci ba riƙon amana ba. Haka kuma ba iya jinsina ne kaɗai suke da hatsabibanci gami da shantakewa da dauniya ba. Wannan kundin ya yi kaɗan na zayyane tarihina tun daga farko har ƙarshe, ga tsakuren kaɗan daga abin da ya faru da ni ba zan tona ƙalubalen da ya afkawa rayuwata ba, bayan tara iyalin da muka yi da mijina kuma uban 'ya'yana wanda shi ne mutum na farko da ya fara jefa ni a kogin bala'i, baƙinciki da nadamar kasancewar alaƙar da ta gindaya a tsakaninmu.

"Ƙarshe!"

Jawahir ta furta bayan ta kai ƙarshen labarin Hidaya, sai dai ba haka ta so ba don ta so jin ƙarshen abin da ya wakana tsakaninta da Ɗan sarki Hafiz wanda ya kasance mijinta.

Boka Shaddas ya ɗaga labulen ɗakinsu Jawahir, ya ƙarasa har bayan ƙofar da take tsaye, a tsorace Jawahir ta dube shi yanayin kamanninsa suka sake tsorata. Ihu ta ƙwallah da ƙarfi a daidai lokacin Malam Umaru tare da Bawa Lawandi suka sako kai za su wuce jin ihunta ya sa suka shiga ɗakin da gudu, wata jar hoda ya hura mata take ta yii yunƙurin zubewa ya riƙota da hannunsa ɗaya. Umaru ne ya kai masa duka ta bayansa a tsammaninsa ko ɓata rayuwar Jawahir ɗin zai yi. A fusace Boka Shaddas ya buga masa sandar tsafinsa aka, Bawa Lawandi na shirin futa domin ya yi kururwa neman taimaki shi ma ya buge masa a ka take shi ma ya zube a ƙasa. Ya saɓi Jawahir ya ɗora a kafaɗa yana matsa wata layar da ke ƙungunsa suka ɓace ɓat.

A kan wani farin dutse ya kwantar da ita da ke kogon tsafin Shugaba, Shugaba Zurufu ya fara zagaye ta sannan ya fashe da wata mahaukaciyar dariya ƙeta.

*SHU'UMAR MASARAUTA*

*41*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Sarki Abdul'aziz shi da Sarki Sulaimanu sun jima suna tattaunawa game da abin da ya shafi sabuwar maganar auren Kamalu da 'yar wurinsa, sannan ya yi masa sallama ya tafi. Sarki Abdul'aziz ba ƙaramin sha tara ta arziƙi ya sa aka haɗa masa ba, fadawansa suka rufa masa baya sannan suka nufi masarautarsu. Sarki Sulaiman ya so kafin ya tafi ya sake tozali da yarinyar da ta tsaye masa a zuciyarsa amma babu yadda ya iya haka ya koma har lokacin ƙwayar idonsa na sake hakaito masa kamanninta. Ko da ya koma kai tsaye wurin sassaƙaƙƙiyar tantabararsa ya nufa, ruwan mamaki ya mamaye shi sakamakon yadda ya ga hawaye bibbiyu na zuba daga idanunta. Hannu ya saka a sanyaye ya ji wani ruwan hawaye mai ɗumi na ci gaba da bin hannunsa, daga gefen fuka-fukin tantabarar ya ga wani sabon rubutu tamkar wanda aka yi da ruwan tawada.

"Hallitar da ka yi tozali da ita 'yarka ce!" Ya sake maimata rubutun babu adadi gabansa na faÉ—uwa.
"Ban san me yake faruwa ba, ban san me wannan rubutun yake nufi ba." Daɓar ya zauna a ƙasa tamkar ƙaramin yaro, idanunsa suka fara zubar da ƙwalla, lokaci ɗaya tunanin Fargi da alaƙarsu ta baya ta suka shiga dawo masa.

"Na san akwai lokacin da ƙwayar idonka za ta so yin tozali da ni, sai dai zanen ƙaddara ya shata mummunan layin da ya katange gangar jiki da ruhinmu. Abu ɗaya nake so da kai Sadaukina, kada ka manta da ni. Kada ka manta da tsantaar soyayyarka da ke narke cikin sassan jiki da ruhina." Kalaman Fargi na ba ya suka dawo masa raɗau a cikin kunnuwansa tamkar a lokacin take furta masa su.

"Na gagara daina kukan rashinki Fargi! Na sha gaya miki kada ki nisance ni amma kika yi ɓatan dabon da har yau nake lalube a ciki duhu. Ya Allah idan Fargi na raye Allah ka bayyana mini ita da abin da yake cikinta." Sarki Sulaiman ya ƙarasa maganar yana zubar da ƙwallah. Jingina kansa ya yi a jikin ginanniyar tantabarar ya faɗa duniyar tunani daga haka baccin gajiya ya yi awon gaba da shi.

Ihunta ya fara ji a cikin kogon dutsen da sauri ya faɗa ciki hankali a tashe, daga can nesa ya hangi Fargi na ɗaga masa hannu tana kiransa, ya yunƙura da niyyar ya nufi wurinta ya hangi wata matashiyar budurwa da ta juya bayanta, Shugaba Zurufu na yarfa mata wani ruwan tsafinsa. A hankali ya ga naman jikinta ya fara zagwayenwa, Fargi ta nuna masa wurin cikin ƙaraji tana faɗin. "Ka taimaka wa 'Yarmu Jawahir zai hallaka mana ita..." Firgigit Sarki Sulaiman ya buɗe idonsa daga mummunan mafarkin da yake yi, gabansa ya ci gaba da faɗuwa jikinsa ya ɗauki karkarwa kamar mazari. Miƙewa ya yi tsaye ya nufi hanyar fita ya ji ginin tantabarar nan gabaɗaya ya ruguje, cak ya tsaye cikin firgici yana kallon yadda ginin ya fara wani katantanwa yana rushewa.

"Tabbas akwai abin da yake faruwa!" Sarki Sulaiman ya furta a fili sannan ya fice daga cikin É—akin.

Sai da aka kwana biyu Mai martaba Mahaifin Fulani babba ya sa aka kira masa Yaya Halima har cikin turakarsa, tun da ta doso É—akin ya zuba mata ido yana mamakin wai yau Halimansa ce ta samu lafiya garau kamar ba ita ba.
"Barka da hutawa ranka shi daÉ—e!" Kalaman Yaya Halima suka ratsa majiyar sautinsa.
"Barka dai Halimatuna ya sauƙin jiki?" Murmushi ta yi sannan ta ce. "Ni fa ranka shi daɗe babu abin da yake damuna, na ma yi mamaki da aka ce wai na yi cutar hauka har da kurumta."
Mai martaba ya miƙa mata hannunsa sannan ya ce. "Me ye wannan?" Baki sake take kallonsa haɗe da dariya ta ce. "Hannunka ne ranka shi daɗe.

"To a baya ba kya iya jin abin da nake faɗa ballantana ki ga abin da na nuna miki, Allah na gode maka Ubangiji ya ƙare mu da lafiya. Lokaci ɗaya Halimatu muka wayi gari kin kurumce, kin kuma makance. Tafiya na sake miƙawa sai muka lura da yadda kika fara sauyawa, kwatsam mu ka ga kin fara hauka tuburan. Amma da yake Allah ne mai yadda ya so a sanda ya so, sai ga shi yanzu Allah ya yaye miki." Sai a wannan karon ta gamsu da abin da ake faɗa, da ta ji daga bakin Takawa don ta san shi kaɗai ne ba ya ɓoye mata komai.

"Ranka shi daɗe na ji an ce rannan kun je Masarautar Huddam, ka tura wa Fatima takardar samun lafiyar da na yi kuwa?" Take idanunsa suka cicciko da ƙwallah.
"Halimatu." Ta ji ya ambaci sunanta da wani irin yanayi.

"Fatima tana wurin da ba kowanne irin saƙo ko aike ba ne zai isa gare ta, kin san wanne irin sako za mu iya aika mata a yanzu." Da sauri ta girgiza wa Mai martaba kai. "Ku yi mata addu'a ku yawaita yi mata addu'ar Allah ya yafe mata kura-kurenta. Saboda Allah ya yi wa ƙanwarki rasuwa!" Jin kalaman Mai martaba ya sa ta miƙe a zabure jiki na karkarwa, ya nuna mata wuri sanna ya furta. "Zauna dama muna son magana da ke Halimatu." Kafin ta zauna tuni hawaye ya wanke mata idanu.

"Ke musulma ce Halima don haka duk ƙaddarar da ta same ki ki rungume ta hannuwanki biyu, Allah shi ya ba mu Fatima a lokacin da ba mu sani ba kuma Ya karɓe ta a daidai lokacin da yake buƙata." Mai martaba ya furta cikin sigar lallashi. Sai da ta share hawayenta sannan ta furta. "Haka ne ranka shi daɗe. Allah ya gafarta mata, yanzu ina su Khadija wanne halin suke ciki?" Murmushi Mai martaba ya saki ya ce. "Halimatu shekaru fa sun tura, turawar da ta haifar da faruwar abubuwa mabambamta. A yanzu daga Khadija har Sakina kowacce tana ɗakinta da 'ya'yanta, wai ba ki ga Shatu ma ('Yarta) har da 'ya'ya huɗu ba? Lokacin da kika fara rashin lafiyar nan fa ko shekara biyar ba ta rufa a duniya ba. Ga shi matar Sabi'u ma ɗanta ɗaya, ai abubuwa sun tura sosai." Yaya Halima ta jinjina kai cikin mamakin wai ita ce har da jikoki biyar tsakanin babban ɗanta da ƙaramar 'yarta Shatu.
"Ranka shi daÉ—e amma me ya sa har yau Ibrahim bai zo ya ganni ba." A wanna karon ma yanayin mai martaba ya sauya sosai don sai da ya kwantar mata da hankali ya fara yi mata bayani.
Chapter 75 · 0% Book details