Sashe 47
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ka ƙarasa masarautarku a yanzu haka Waziri da Shamaki na ƙulla yadda za su cutar da mahaifinku, idan ka je ka ɗebo wannan ƙasar ka watsa musu su da kansu za su tona asirin kansu." Fargi ta ƙarasa maganar tana miƙa masa wani ƙullin magani. Jiki na karkarwa Sulaiman ya miƙa hannu ya karɓa, ya shiga zabga mata godiya. Fargi ta sakar masa murmushi sannan ta buga ƙasa da ƙafarta nan take ta ɓace ɓat, ganin haka ya sa ruwan mamaki ya sake mamaye Sulaiman cikin ta'ajibi ya kaɗa linzamin dokinsa ya bar wurin. Duk abin da yake faruwa tsakanin Fargi da Sulaima a kan idanun shugaba, don haka gabansa ya yi mummunar faɗuwa haka kawai yake jin kusancin yaron a gare su babu alheri a ciki. A ƙallah ya shafe shakaru masu yawan gaske amma bai taɓa tsintar kansa a irin wannan yanayin ba, don haka ya sauke ajiyar zuciya ya ƙarasa bakin halwar tsafinsa ya binciki abin da zai faru tsakanin Fargi da Sulaiman a gaba.
Hannuwa biyu a saman kanta cikin matsanancin tashin hankali ta faɗa cikin kogon tsafinsa, kuka take har da magina tamkar wacce aka yi wa bushara da wutar Jahannama. Boka Shaddas na zaune a kan wata halitta da ke tsugunne tana lasar wani baƙin jini da ke gabansa, da idanu yake bin Jakadiya har ta ƙarasa gabansa. Yaraf ta zube a ƙasa sannan ta sake fashewa da matsanancin kuka, har lokacin bai tanka mata ba sai ma idanu da yake bin ta da shi har sai da ta ci kukanta ta ƙoshi.
"Ya kai babban boka mai yi mini yau ya yi mini gobe, ya Boka Shaddas mai share mini hawaye gani gare ka na zo ka ɗaura mini zanin da Umaima ta kwance mini a bakin kasuwa har jama'ar cikinta sun fara fuskantar rashin kyawun tsiraicin da ke tare da ni..." Tun daga farkon abin da Sailuba ta gaya masa game da halin da take ciki har zuwa ita kanta ɗoyin da ta ji Sailuba na yi ta kwashe ta sanar da shi, ta ƙarashe maganar tana fashewa da matsanancin kuka. Sai da ya lakace jinin da ke gabansa ya sha sannan ya furta. "Bakin alƙalami ya riga da ya bushe Jakadiya! Kin san a kance idan junanka sammako wani a tafe ya kwana, Umaima ta riga da ta cutar da Sailuba da cutar mai matuƙar yawa, tun da har aka binne gawar kishiyarsu bakin alƙalami ya riga da ya bushe, tun kafin ki zo na san abin da ya faru don haka bincikena ya zartar mini Sailuba ba za ta taɓa warkewa ba. Sai dai zan iya taimaka miki na yi miko hanyar Shugaba Zurufu da ke Dajin Bururu ko zai iya shawo kan matsalar ya magance miki ita. Amma ina mai tabbatar miki yadda Umaima ta kassara rayuwar kishiyarta sai ta ninka abin da ta yi shi a kan Sailuba, mafita ɗaya ce ko ki ɗauki fansa ko kuma ki nemi makamin kare kanki."
Ajiyar zuciya Jakadiya ta sauke cike da damuwa ta furta, "Duk wacce za a yi a yi Boka Shaddas, ka taimaka mini ni da 'yata Sailuba muna cikin matsanancin tashin hankali." Jakadiya ta ƙarasa maganar tana dafa ƙafar Boka Shaddas.
"Matso ki ji abin da zan faɗa miki!" Jiki na rawa Jakadiya ta matsa saitinsa nan take ta ji wani irin ɗoyi ya mamaye ta. Ya jima yana yi mata raɗa a kunne lokaci ɗaya Jakadiya ta bushe da wata irin dariyar ƙeta har da hawaye, ta jima tana abu ɗaya sannan ta furta. "Ka biyani ko ba sisi ubangidana, yadda ka ce haka za a yi a shirye nake ba ka haɗin kai matuƙar a kan Fulani Umaima ne domin ku kifar da jagorancinta."
Sai da Boka Shaddas ya ɗauko wani mudubi ya sa a gabansa ya ƙura masa ido sannan ya furta, "Amma da sharaɗi Jakadiya domin a baya ina yi miki aiki ne saboda hannu ya san na gida, a yanzu kuma dole za ki rama wa kura aniyarta." Jakadiya ko kaɗan ba ta damu da abin da Boka Shaddas zai buƙata ba don haka kai tsaye ta furta. "Duk abin da kake buƙata a shirye nake na aiwatar maka da shi duk rintsi duk wahalarsa matuƙar zai biya mini buƙatata." Boka Shaddas ya saki murmushi a karo na biyu sannan ya sake yi wa Jakadiya raɗa a cikin kunne, a hargitse ta ɗago cikin tashin hankali tana kallonsa, ya gyaɗa mata kai cikin halin ko inkula.
"Idan har kina buƙatar na yi miki jagora wurin Shugaba kuma na wanke ɓacin ran da Fulani ta dasa miki a zuciya sai kin aiwatar da abin da na sanar da ke, kuma ki san duk yadda za ki yi ki kawo mini duk abin da na buƙata cikin kogon tsafin nan." Nan take Jakadiya ta ji zuciyarta ta bushe ta dubi Boka Shaddas cike da ƙwarin gwiwa. "Na amince Shugaba zan an aiwatar da duk abin da kake buƙata." Boka Shaddas ya yi mata jinjina da hannu sannan ya ɗebo waɗansu garin magani da wata ƙyamurarriyar mage wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci an tsaface ta ya damƙa mata. Jakadiya ta yi masa godiya sosai sanan ta yi masa sallama ta baro Kogon zuciyarta fes.
Mahaifiyar Umaima ta tafi da gudu wurin da Umaima ke ƙame tana ambatar sunanta tana taɓa ta, tamkar dutse haka jikin Fulani Umaima ya koma ta ƙandare a wuri ɗaya ko ƙwayar idonta ba ta iya motsawa. Wannan ya sake ɗaga hankalin mahafiyarta don haka ta sake zubawa a guje ta nufi Bamaguje tana gunjin kuka. "Kai taimaka mini Bamaguje ka yi haƙuri duk da ban san laifin da Umaima ta yi maka ba, don Allah kada ka kashe mini ita Bamaguje..." Da sauri ya buga mata tsawa haɗe da katse ta.
"Idan kika sake ambatar sunan Allah a wurin nan sai na halaki, taɓaɓɓu kamarmu ba sa ambatar sunan Allah a wurin taɓewa kamar nan." Gyaɗa masa kai ta fara yi har lokacin kuka take ta furta. "Tuba nake Bamaguje tsafi ya shiga lamarinmu, ka dubi girman tsafi Bamaguje ka kada ka kashe mini Umaima. Duk cikin 'ya'yana ita kaɗai na fi ƙauna a zuciyata." Murmushin takaici Bamaguje ya saki sannan ya furta, "Gara ke kina da su da yawa idan kin rasa ta akwai 'yan uwanta. Kin fi kowa sanin Umaima ita kaɗai ce 'yar da na mallaka a duniya kuma bayan ita ba zan sake samun haihuwa ba. Amma hakan ba zai hana na hallaka ta ba idan za ta kawo mini cikas a harkar bokancina, abin da ba ki sani ba hatta mahafina ni na datse numfashinsa na ƙarshe don haka babu wanda ba zan iya kawarwa a faɗin duniyar nan ba." Tsoro ƙarara ya bayyana a fuskar Mahafiyar Umaima, nan take gumi ya shiga keto mata. "Ka da ka mini haka Bamaguje, Umaima duk ba ta san wannan alaƙar da ke tsakaninku ba, ka yi haƙuri kada ka hallaka ta." Bamaguje bai tanka mata ba ya nuna wurin da Umaima ke ƙame ya nuna ta da sanda, take ta zube ƙasa yaraf cikin kururuwa da tashin hankali ta shiga kwalla ihun azaba. Da wata irin murya ya ambaci sunanta mai amsa-amo, nan take Fulani Umaima ta shiga nutsuwarta. A tsorace ta sake ja da baya don ba ƙaramin tsoron Bamaguje ne ya mamaye ta ba, jikinta na karkarwa hawaye na zuba ta matsa ta ci gaba da ja baya.
"Ki zo nan! Idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Tun bai rufe baki ba ta tafi da sauri ta zube a gabansa.
"Ka yi mini rai, tuba nake Bamaguje wallahi ba zan sake..."
"Dakata!" Bamaguje ya katse ta rai a matuƙar ɓace, ta sha ganin ɓacin ran Bamaguje da dama amma ba ta taɓa ganin irin ɓacin ransa na wannan ranar ba.
"Kalli can." Ya furta mata yana nuna mata sihirtaccan bangon dutsensa. Daga mahaifiyar Umaima har ita rige-rigen kallon wurin suke, nan take hoton Jawahir ya bayyana a dadai lokacin da take ƙwaƙulo butar da Umaima ta binne har zuwa zuba ruwan da ta yi a sashenta. Sai da suka gama gani hoto mai motsin ya ɗauke.
"Ba ta san kin binne ba, ba ta ganki a lokacin da kika binne ba hasali ma da ace wani ya ganki a lokacin sa kike gudanar da aiki, daga mutuwar kishiyarki har zuwa ɗoyin jikin Sailuba ba zai taɓa tabbata ba. Wace ce ita? Kuma wa ya sanar da ita wurin da kika binne har da yadda za ta gudanar da makarin aikin?" Bamaguje ya watsa wa Umaima tambayoyi fuska a haɗe.
"Wallahi ban santa ba, ban san wa ya sanar da ita ba. Hasali ma ban taɓa saninta a cikin masarautarmu ba, ina tunanin ma ƙila Jakadiya ce za ta turo ta..."
"Da ace Jakadiya ta san da wannan ba za ta nemi agajin kowa ba da kanta za ta tone ba tare da wani ya sani ba, kuma yarinyar nan na rayuwa a cikin masarautarku don haka ina buƙatar ki shiga lungu da saƙon masarautar ki kawo mini ita. Ina son sanin wace ce ita? Domin na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa, wannan asirin ba ita aka yi wa ba, ba ta da alaƙa da masarautar nan me zai sa ta tone asirin tun da ba amfani zai yi mata ba." Shiru Fulani Umaima ta yi tana nazari sannan ta furta. "Zan yi duk yadda ka ce Bamaguje."
"Kina shashanci ɗanki Basiru ta ɗauke littafina ya kai wa mahaifinsa, ki sani wannan shi ne kuskure na farko da kika tafka a rayuwarki. Kin yi biyu-babu, domin butar da aka tone ita ce jigon mallakar da aka yi wa Sarki Abdul'aziz, kin rasa zuciyarsa kin rasa iko da mallakar da kike masa Umaima. Kin san a yanzu wacce nasara kaɗai ta rage miki?" Da sauri Fulani Umaima ta girgiza kai, nasararki ɗaya an binne kishiyarki da fatar da kika saka mata a ƙasanta wanda hakan zai sa har abada Sailuba ba za ta warke ba, amma bayan wannan ba na jin akwai wata ragowar wata nasara da kike da ita."
"Kana nufin a yanzu Takawa zai iya juya mini baya?" Umaima ta tambaya cikin tashin hankali.