← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 86

Sashe 77

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Fi ce mini daga ɗaki idan ba haka ba ranka ya yi mummunan ɓaci! Kai ba ka san bala'i ne a gare mu ba? Ka da ka ga ina ɗaga maka ƙafa ka nemi ka shigar mini hanci da ƙudundune, tun da ka bayyana gabaɗaya bala'i da musibu suke afkowa cikin masarautar nan wallahi kai ba ƙaramin annoba ba ne..." Cikin hanzari Kamalu ya katse shi. "Wallahi-wallahi tun kafin gari ya waye ka fito da ita idan ba haka ka fuskanci hukuncin da mahaifiyarka take fuskanta a yanzu." Daga haka Kamalu ya fice daga ɗakin a zuciye. Duk da dare ya fara yi sosai hakan bai hana ganin mutane sun yi carko-carko ba kowa cikin alhini da jimami, Kamalu har zai wuce sashensa Dattijo Maharaz ya faɗo masa da sauri ya nufi sashen Sarki Abdul'aziz, a lokacin da ya shiga ya samu mahaifinsa yana zaune. Sai da suka sake gaisawa sannan ya ɗan sunkuyar da kai ƙasa ya furta.

"Dama Ranka shi daÉ—e wata magana ce gare ni."

"Tafi kanka tsaye Kamalu!"
"Allah ya taimake ka dama ce wa na yi ko za a ji daga bakin Dattijo Maharaz a kan ɓatan Jawahir, domin na ji daga bakin Dogarawan ƙofa babu wanda ya ga fitarta." Kamalu ya yi magnar yana duban yanayin Sarki Abdul'aziz.
"Mun yi wannan tunanin amma sai muke ganin mai zai hana mu bari zuwa wayewar gari, kada mu shiga haƙƙinsa idan yana da wani uzurin." Ba haka Kamalu ya so ba amma sai bai nuna komai ba, ya yi wa mahaifinsa godiya sannan ya fita. Kai tsaye sashensa ya nufa yana shirin buɗe ƙofar shiga ɗakinsa ya ji sallamar Dattijo Maharaz, har a fili Kamalu sai da ya sauke ajiyar zuciya ya faɗaɗa fara'arsa. Sai da ya amsa masa sannan ya buɗe masa ɗakin suka shiga ciki, Kamalu ya buɗe baki zai yi masa bayani Dattijo Maharaz ya dakatar da ni.

"Mahaifinka dattijon ƙwarai ne da sanin ya kamata, don haka ban baƙunce shi a wannan lokacin ba kamar yadda ya yi mini uzuri. Duk abin da yake faruwa na san komai Kamalu, kuma ka daina zargin ɗan uwanka Muhsin don ba shi da hannu a ɓatan Jawahir. Sai dai akwai babban hatsari a wannan tafiyar domin karawa ce tsakanin zuri'a biyu, kuma dole wannan tafiya za a yi ta ne da Sarki Sulaimanu."

"Sarki Sulaimanu fa? Ko dai kana nufin Mahaifina Dattijo Maharaz?"

Boka Shaddas shi da Basiru na isa kogon tsafinsa Basiru ya kafe ahi da idanu har sa gaban Boka Shaddas ya faÉ—i. "Ba ni hatsabibiyar aska!" Basiru ya furta yana sake kafe mahaifinsa da kallo.

"Ya aka yi ka san da ita? Kuma me za ka yi da ita..." Tun bai rufe baki ba Basiru ya ɗauke fuskar Boka Shaddas da hatsabibin mari nan take ƙwayar idonsa na hagu ya faɗo, wata irin azaba ta ratsa shi cikin kiɗima ya kwarara ihu cike da azaba. Babu shiri Boka Shaddas ya turbutsa hannu a cikin ƙarƙashin ƙasa ya zaro wata ƙanƙanwar aska, jikinsa na rawa ya miƙa wa Muhsin don bai manta ba da ita ya hallaka mahaifinsa har lahira. Muhsin yana karɓa bai ko waiwaye shi ba kai tsaye ya nufi Masarautar Huddam.
*SHU'UMAR MASARAUTA*

*42*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Tun daga ranar da Fargi ta ziyarci bishiyar da suke bautawa ta fara horar da abin da yake cikinta tare da ba shi duk wata kariya, musamman da ya zaman ta bincika halwar tsafinta ta; ta san mace za ta haifa. A wani lokacin ta kan zauna jigum ta dinga tunanin makomar rayuwar abin da za ta haifa, fargabarta ɗaya kada bayan ta mutu Shugaba ya cutar da abin cikinta, sai zuciyarta ta shawarce ta da ta damƙa ta a hannun mahaifinta ko ta taso cikin kulawar mahaifinta don tana da tabbacin ko bayan ba ta raye zai kula da ita. A ɓangare ɗaya kuma wata zuciyar tata ta ƙi ba ta haɗin kan amincewa da haka.

Wannan yanayin da ta tsiro da shi na killace kanta da tsafin da take yi wa cikinta, bai sa ta janye jiki daga wurin Shugaba ba don gudun kada ya zargi shirinta, kuma kusan kullin sai ya tuntɓe ta don ya ji shawarar da ta yanke amma kullin bagarar da shi take tana nuna masa har lokacin nazari take yi, shi kuma babban burinsa bai wuce ta damƙa masa ƙarfin tsafinta ba.

Sannu a hankali Mahaifinta da manyan yayyanta suka fahimci yanayin damuwar da take ciki, watarana har sai da mahaifinta ya zaunar da ita ya tambaye ta dalilin da ya sa take keɓe kanta kullin a bukkar da take gudanar da al'amuran tsafinta. Don ta kawar masa da shakku da damuwa sai ta nuna masa wasu manyan ayyuka take gudanarwa, a lokacin da mahaifiyarta ta ji haka ta tausaya mata matuƙa duk ita ma ba ta san abin da Fargi take aiwatarwa ba, amma haka kawai jikinta yake ba ta akwai dalilinta na yin haka don haka watarana ta taɓa samunta a bukkar.
A lokacin da mahaifiyarta ta shiga a zaune ta same ta gaban sihirtacciyar wutar da ke gabanta, da sauran tarkacen kayan tsafinta. Wani farin hayaƙi ne yake tashi sai ya je kan allon farin ƙarfen da take tsafi da shi sannan ya dawo ya shige cikinta, duk wani abu da take gudanarwa tana yin sa ne a kan abin da yake cikin jikinta. Shiru Mahaifiyarta ta yi tana kallonta sai da ta ga ta kammala sannan ta furta.

"Ko ba za ki sanar da kowa ba ni mahaifiya ce, ki sanar da ni dalilin aiwatar da wannan sabon aikin da kike yi ba dare ba rana. Ko kina tsoron kada na yaye miki labulen sirrinki ne?" Cike da gajiya Fargi ta miƙe ƙafarta ta fara yi mata tsami ta ɗan jingina da bango.

"Ko da ba za ta gaje ni game da al'amarun tsafi da sihirina ba, ina katange ta daga kaidin Shugaba da duk wani mai sharri. Na san waye Shugaba da zuri'armu, sanin kanki ne matuƙar wannan cikin ya bayyana a gare su ba za su taɓa ƙyale mu ni da abin cikina ba. Ko na haife ta kin san su da bibiya ba za su bar ta, akwai wani sirri da nake son sanar da ke dangane da yarinyar nan." Fargi ta yi shiru tana bin cikin jikinta da kallo, mahaifiyarta ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Ina sauraronki."

"Yarinyar nan ta kasance mahaÉ—i ce na kowanne matsafi ko gawurtaccan mai sihiri zai so ya mallake ta, babu wani boka da ba zai so ta zame masa tsanin da zai hau da zai kai shi ga tudun shahara da gawurta ba."
"Ban taɓa jin irin haka ba, wanne dalili ne zai sa ta zama haka shin kina nufin ba za ta samu sukunin rayuwa ba kenan?" Mahaifiyarta ta wurga mata tambaya.
"Saboda taurarin abar bauta sun sauka a kanta, sara na yi a kan gaba a lokacin da na kai kokena gare ta. Ta zubar mata da jinin shanu marasa adadi, akwai muhimman saƙƙonni a kanta, zan labarta miki kaɗan daga ciki idan dare ya tsala." Cikin gamsuwa da maganarta mahaifiyarta ta amsa mata, sannan suka ci gaba da hira.

Dattijo Maharaz ya girgiza wa Kamalu kai sannan ya ce. "Sunan Mahaifinka Sarki Abdul'aziz, shi kuma Sarki Sulaimanu ai daban yake."
"Amma me ye alaƙar Sarki Sulaimanu da ɓatan Jawahir? Ko dai akwai wani mummuna ala'amari da ya gudanar a kanta. Na rantse da girman Allah, matuƙar aka same shi da hannu a ɓatanta sarautar da yake taƙama da ita ba ta isa ta ba shi kariyar hukuncin da za a yi masa ba. Sai dai duk wani ruguntsumi da zai faru ya faru..." Murmushin Dattijo Maharaz ya katse Kamalu cikin mamaki Kamalu ya bi shi da kallo.
"Ina ma za ka bari abin da yake ƙasan zuciyarka ya bayyana a fili, ina ma ba wannan haɗin Sarki Sulaimanu ya zartar ba, da kuwa tabbas haɗin mabambamta zuri'ar nan sun yi daidai. Kwatankwacin yadda ake ɗora ƙwarya a gurbint." Kamalu sam bai fahimci maganar Dattijo Maharaz ba, yana shirin yin magana ya katse shi.

"Sarki Sulaiman na tare da wata alfarma ko sirri wanda zai zame muku tamkar fitila da za ta haska muku hanya a cikin duhun dare. Yanzu abin da nake so da kai dai, idan Allah ya kaimu gobe zan samu mahaifinka mu yi magana da shi, kasan ba a shiga dawa haka nan dole sai an yi masa shiri." Jinjina kai Kamalu ya yi ya ji kusan kaso mai yawa na damuwar da yake ciki ta ragu, har Dattijo Maharaz ya miƙe zai tafi Kamalu ya katse shi.

"Jikina a sanyaye yake a kan wannan lamarin, ina tsoron kada abin da ya faru da ni ita ma ya kasance a kanta, wallahi ba za ta iya jura ba. Ni na san Jawahir farin sani, cika bakinta da tsiwarta a iya fatar baki ce. Don Allah ka yi wani abu farin jakada idan har za a cutar da ita." Kamalu ya ƙarasa maganar cikin damuwa.
"Ba a iya fatar baki waɗannan kalaman naka suke fitowa ba, da alama suna fitowa daga cikin zuciyarka ne. Kusan abin da ya faru da kai ne ya faru da ita, sai dai suna da matuƙar bambamci domin ita gida ta koma, ta koma tsatsonta ne saɓanin kai da babu dangin iya ballantana na baba." A zabure Kamalu ya dafe ƙirji ya ce. "Kana nufin ita ma 'yar cikin jinsinku ce?" Dariya sosai Dattijo Maharaz ya yi sai ya yi mai isarsa ya ce. "Idan hakan ne akwai wata damuwa ne?"
Chapter 77 · 0% Book details