← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 86

Sashe 56

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarki Sulaimanu Matansa Uku da 'ya'ya goma cif, yana da 'ya'ya maza huÉ—u sai 'ya'ya mata guda shida. Uwar gidansa Fulani Habiba tana da 'ya'ya HuÉ—u, uku mata sai namiji É—aya. Kuma babbar 'yar Sarki Sulaiman mace ce mai suna Raihanatu. Matarsa ta biyu Fulani Sa'adiyya tan da'yaya mata biyu sai 'ya'ya maza biyu, ita kuma Fulani Zabba'atu tana da 'ya'ya biyu duka mata.

"Assalamu alaimum. Muna buƙatar gabaɗayanku ku ba mu hankalanku domin mu sanar da ku abin da yake tafe da mu na alkhari." Sai da ya zayyane musu duk yadda suka yi da Sarki Abdul'aziz sannan ya ci gaba da ce wa, "A yanzu haka ni da Mai martaba mun zartar da lokacin aurensu Raihanatu nan da makwanni huɗu masu zuwa cikin yardar Allah. Ina fatan ke Raihanatu ba za ki watsa mini ƙasa a ido ba." Cikin ladabi Raihanatu ta gyaɗa masa kai, farinciki fal zuciyar mahaifiyarta ya ƙi ɓoyuwa don babu wanda ba zai so ya haɗa zuria'a da masarautar Huddam ba. Sai da suka ɗan taɓa hira a tsakaninsa da iyalansa sannan ya sallame su kowacce ta wuce sashenta. Baƙinciki ne ya mamaye zuciyar Fulani Sa'adiyya don a ganinta Yarima Muhsin da 'yarta Hansatu ya fi dacewa.

Dattiji Maharaz sai da ya duba lungu da saƙon cikin dajin amma ko mai kama da jinsin halittar ɗan adam bai gani ba, a galabaice ya zauna a bakin wata bishiya sannan ya faɗa duniyar tunani.

"Da wacce shaida zan koma na sanar wa Sarki Abdul'aziz? Shi kenan rayuwar Kamalu za ta koma hannun Furhussan da zuri'arsa?" Dattijo Maharaz ya furta a fili. "Sam ba zai taɓa yuwa ba." Ya yi maganar yana miƙewa tsaye rai a ɓace.

"Na ji daɗi har a kullin ƙwarin gwiwarka ne yake rinjayar rauninka, kai mai farar zuciya da jin ƙai ne don haka zan taimaka maka da baiwar da Allah ya hore mini." Dattijo Maharaz ya ji an furta daga bayansa, yana waigawa ya ci karo da Malam Liman. A fili ya bayyana fara'arsa ya ƙarasa wurinsa yana niyyar russunawa ya ɗago shi. "Kada ka damu Maharaz, babu isasshen lokacin da za mu ɗauka. Zan taimaka maka a ƙwato yaron nan domin shi ɗin ba jininmu ba ne kuma ba jinsin mu ba matuƙar aka bar shi a cikinsu an cutar da shi da iyayensa, kuma a kowanne lokaci suna iya sauya masa addini gabaɗaya." Jinjina kai Dattijo Maharaz ya yi sannan ya shiga zabga wa Malam liman godiya bisa karamcin da yake nuna masa da soyayyar addinin musulunci.

"Furhussam ya yi amfani da sirrin tsafi da sihiri, mu kuma sai mu karya shi da addu'o'in kariya daga ayoyin Allah. Ka dafa wannan dutsen da bismillah bayan ka yi alwala kuma ka ambata da yaƙini a zuciyarka Ubangiji Shi zai iya aiwatar da komai kuma da taimakonSa za mu samu mu kuɓuto da wannan yaron."

Sun fara tafiya mai nisa Fargi ta dakatar da shi tana share hawayenta sannan ta furta. "Idan zuri'arka sun amince na aure ka na san halin zuri'ata har gaban abada ba za su lamunce na aure ka ba Sulaiman, hasali ma a yanzu matuƙar suka ji alaƙar da ke tsakaninmu gabaɗaya hallaka mu za su yi. Haƙuri shi ya kamace mu gwarzona, ina ganin dama can tsafina bai bincika mini daidai ba."
"Ba zan iya ba Fargi! Ba zan iya rabuwa da ke ba, idan kin lamunce zan kai ki a ɗaura mana aure a ɓoye idan ya so na dawo da ke cikin danginki kafin mu nemarwa kanmu mafita." Shiru Fargi ta yi tana nazartar kalamansa ganin kamar ba za ta amince ba ya sa ya shiga lallashinta da gaya mata daɗaɗan kalamai har dai Sulaiman ya yi nasara a kanta. Alkyabbar jikinsa ya cire ya rufa mata ya ɗora ta a kan dokinsa sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka fito cikin gari, tsoro ne ƙarara ya mamaye Fargi sakamakon wannan ne karo na farko da ta taɓa tsomo ƙafafuwanta cikin gari ta baro dajin da suke rayuwa.

"Ki nutsu Sarauniyata babu abin da zai kama ki, idan kina nuna firgici mutane za su dasa zarginsu a kaina." Sulaiman ya furta mata cikin sigar lallashi bayan ya gama naɗe fuskarsa domin kada a gane shi. Can bayan garinsu ya wuce da ita ya buɗe wani ɗan ƙaramin guda mai ɗaki biyu ya saka ta a ciki sannan ya ce mata yana zuwa. Da fitarsa kai tsaye gidan Waziri ya wuce aminin mahaifinsa, takanas ya ɗauko shi sai da ya kawo shi cikin gidan sannan ya zayyane masa duk abin da yake tafe da shi. Zuciyar Waziri ƙal ya amince da buƙatar Sarki Sulaiman don a ganinsa nan gaba wannan auren da zai yi ba ƙaramin naƙasu da damuwa zai kawo masa a harkar mulki ba tun da babu wanda ya san da auren, idan ya so nan gaba ko hayayyafa ta yi yana iya murje idanunsa ya ce bai san zance ba tun da har Mahaifinsa ya iya tsallake 'yarsa Shafa'atu ya aura wa Sulaiman wasu.

A wancan lokacin Sulaiman har sai da ya yi wa Fargi tayin addinin musulunci amma fir ta nuna masa ba ta aminta da shi ba, ko da za ta shiga addinin sai zuwa bayan wani lokaci. Sulaiman bai takura mata ba don haka shi da Waziri suka fice daga gidan, a can wani ƙaramin ƙauye Waziri na da wani amini sunansa Kalidu tare da Sulaiman suka tafi garin Waziri ya zayyane masa komai. Malam Khalidu ya amince zai zo a matsayin waliyyin Fargi shi kuma Waziri ya zo a matsayin waliyyin Sulaiman, suka tara mutane a ƙofar gida aka ɗaura auren Sulaiman da Fargi kamar yadda addinin musulunci ya hukunta.

Da É—an mamaki a fuskar Muhsin yake kallon mahaifiyarsa ganin yadda ta razana lokaci guda. "Ita ta ce mini za ta wuce mini gaba wurin Takawa a kan maganar auren yarinyar." Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke a fili tana juya kalamansa a cikin zuciyarta.

"Ruwa fa baya taɓa tsami banza ni na san akwai manufar Jakadiya a wannan maganar! To ko ta gano neman yarinyar nake yi ruwa a jallo? Da sannu zan fahimci inda ta dosa, don na yi rantsuwa da ƙarfin ikon Bamaguje Jakadiya ba za ta taɓa kwaye mini baya ba." Fulani Umaima ta wassafa zancan a cikin zuciyarta. Amma a fili sai ta ce. "Me ya sa ka yi mini haka Muhsin? Me ya sa za ka ce Jakadiya ta yi maka iso wurin Takawa, kamar ba ka san tsegungumin cikin gidan nan ba?"

"Sai na zauna sai kin amince sannan zan auri wacce nake so? Me ye laifi don Jakadiya ta wuce mini gaba wurin Takawa?" Murmushin yaƙe Fulani Umaima ta ƙirƙiro ta furta. "Ba komai ba ne Yarimana kawai ina gudun ƙananan magangunu, yanzu dai ka tashi ka je ka ce wa Jakadiya mun gama magana da kai."
"Tun farko ke ce ba ki so haka ba ai da kin bada kai bori ya hau da haka ba ta faru ba." Muhsin ya furta wa mahaifiyarsa. Fulani Umaima ba ta ce uffan ba ta fice daga ɗakin. Tana komawa ɗakinta ta samu Ruƙayya da sauran Bayinta suna yi mata najanje-najanje, ganin Fulani Umaima ya sa suka miƙe da sauri kowannensu a tsorace don ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ta hana Ruƙayya shiga cikin Bayi a cewarta ba matsayinsu ɗaya ba. Amma ga mamakinsu sai gani suka yi ta wuce ɗaki uffan ba ta ce musu ba.

"Baraka don Allah ki ci gaba, kin ga na cire ƙafa ɗaya saura Lami da Fa'iza." A ɗan tsorace Baiwa Baraka ta ci gaba har lokacin hankalinta na kan ƙofar Fulani Umaima.

Gyara kanta ta sake yi ta feshe jikinta da turarruka kala-kala ta ko ina ƙamshi ne yake tashi, babban tashin hankalinta bai wuce wannan ruwan mai ɗoyi da yake zubo mata ba. Da wannan tsokar naman da ke zazzagowa.

"Yanzu a haka zan tunkari Takawa?" Fulani Umaima ta furta a sanyaye idanu cike da ƙwalla. Ba ta da wani zaɓin da ya wuce wannan don haka ta sake bulbula turare ta wuce sasahen Sarki Abdul'aziz da ita kanta ta manta rabon ta da shiga sashen shi. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga yana zaune da carbi a hannu, a taƙaice ya amsa mata ya ci gaba da jan carbi. Daga can gefe ta rakuɓe tana raba idanu, sai da ya shafa addu'a sannan ya zuba mata ido yana mamakin abin da zugar da ita lokaci guda. Amma kuma wari, ƙarni da turare mai hawa kai da ta sa ne ya sa shi ɗan yamuta fuska, yana shirin magana ta katse shi.

"Barka da hutawa Sarkina!"
"Barka dai Umaima yau an tuno da mu?" Murmushi ta saki na jin daÉ—in kalamansa. "Ranka shi daÉ—e a baya ma gani na yi tamkar ina takura maka tun da wanna larurar ta same ni." Umaima ta faÉ—a cike da kissa.

"Ba mu ƙyama ce ku ba Umaima, muna dai ta fafutukar nema muku magani ne. Yanzu haka akwai masu magunguna har mutum uku da muke jiransu daga yanki daban-daban." Sai da ya gyara zamansa sannan ya ci gaba. "Kin yi sara a kan gaɓa Umaima don yanzu nake shirin aikawa a kira mana ku." Rass gaban Fulani Umaima ya faɗi, tana ɗan fargabar abin da zai sanar da su.

"Ina yaron nan Basiru kusan mako guda ban ji hatsaniyarsa ba, Yarima ma yau kwana biyu kenan bai leƙo ni ba." Sarki Abdul'aziz ya furta da 'yar damuwa ɗauke a fuskarsa. "Ranka shi daɗe yanzu haka daga wurin Yarima nake maganarsa ce mata kawo ni, shi kuma Basiru ka san shi da nunkufurci ɗazu dai ya leƙo sashena." Fulani Umaima ta yi maganar tana ɗan sosai kai. Kafe ta ya yi da kallo yana son fahimtar wani abu daga gare ta. Bawa Sammani ya ƙwala wa kira cikin ladabi ya ƙarasa bakin ƙofar ya amsa ya tsaya yana jiran umarnin Takawa. Sarki Abdul'aziz ya ba shi umarnin ya sanar da Jakadiya ta haɗo masa kan iyalansa gabaɗaya har Abubakar yana son tattaunawa da su.
Chapter 56 · 0% Book details