Sashe 64
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki gama tsinewa Bamaguje ni kuma na tabbatar miki da naki hukunci don na yi rantsuwa na ƙara, sai na shayar da ke ruwan azabar da ko mutuwa kika yi aka ambaci sunana sai kin farfaɗo." Bai Maimuna ta yi maganar cikin wata irin murya mara daɗin sauraro.
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*35*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Boka Shaddas na ɓacewa daga kogon dutsensa bai sauka a ko ina ba sai a bakin dutsen Shugaba Zurufu, ya jima a tsaye yana ƙarewa dutsen kallo sannan ya shiga ciki a lokacin duhu ya mamaye ko ina, shiru cikin kogon dutsen ya yi babu motsin komai sai sautin tafiyar da Boka Shaddas yake yi. Sai da ya je tsakiyar filin haske ya gauraye cikin dutse. Cak Boka Shaddas ya tsaya ya harɗe hannuwansa a ƙirjinsa, bai yi tsammani ba sai gani ya yi Shugaba Zurufu ya burtso ta ƙarƙashin ƙasa a gabansa har sai da ya ɗan tsorata. Baya ya ja suka fura wurgawa junansu kallo kowa da manufarsa a zuciya, Shugaba Zurufu ya katse shirin da cewa. "Barka da zuwa Boka Shaddas!" Bai amsa ba kuma bai yi alamun zai amsa ba, don haka Shugaba Zurufu ya ci gaba da cewa.
"Dama na san ko ba daÉ—e ko ba jima za ka kawo kanka..."
"Ina ɗana yake?" Boka Shaddas ya katse shi rai a ɓace.
Sai da Shugaba Zurufu ya koma can kan wani farin dutse ya zauna sannan ya furta. "Yanzu haka yana tare da kai, sai dai ba za ka taɓa tozali da shi ba har sai ka cika sharuɗɗan da zan gindaya maka."
"Idan kuma na haƙura da shi fa." Boka Shaddas ya yi maganar yana zuba wa Shugaba manyan idanunsa. Sai da Shugaba ya ɗauki wani garin magani ya watsa a cikin wutar da ke ci a saman cinyarsa sannna ya wara hannuwa alamun rashin damuwa ya ce. "Idan ka haƙura da shi ba ni da damuwa, amma ka sani haƙura da Basiru tamkar ka haƙura da kundun tsafinka ne gabaɗaya. Idan ba ka yarda ba ka koma can kogon dutsenka, ka binciki rijiyar tsafinka za ta ba ka tabbacin abin da nake nufi." Ajiyar zuciya Boka Shaddas ya sauke gabansa na faɗuwa, duk yadda ya so nuna dakiya don kada Shugaba ya fahimci rauninsa abin ya gagara. "Mene ne sharuɗɗan naka?" Boka Shadda ya wurga masa tambaya.
Shugaba na jin haka ya miƙe ya ɗauki sandar tsafinsa ya fara tafiya yana zagaye kogon dutsen da ita, sai da ya kammala sannan ya sake komawa mazauninsa na farko ya furta. "Sharaɗina guda ɗaya ne, don haka a yanzu sai da na toshe duk wata ɓarakar da mahaifiyarta za ta ba ni matsala, a baya ta yi yunƙurin binne mana tushenta amma bincikena ya haske mini ita. Sai dai Fargi ta kasance hatsabibiya kuma mai tsananin wayo, ta nesantamu da 'yarta don haka wani daga cikin zuri'armu bai isa ya sarrafata yadda ya dace ba. Dalili kenan da zan tura ta ka kawo mini JAWAHIR, yanzu haka tana can cikin Masarautar Huddam. Idan ka aikata mini haka na yi rantsuwa da girman tsafi da sihirina sai na dawo maka da ɗanka kuma na ninka maka ƙarfin iko da tsafinka."
A madadin kalaman Shugaba su faranta ran Boka Shaddas sai ya sake turɓune fuska, "Me ya sa sai ni? Me ya sa duk yawan bokayan da ke faɗin ƙasar nan ba za ka zartar da wannan hukuncin a kansu ba sai ni?"
"Saboda sara aka yi a kan gaɓa kuma faɗuwa ta yi daidai da zama." Shugaba ya katse Boka Shaddas, shiru ya yi har lokacin yana bin Shugaba da kallo.
"A daidai gaɓar da nake yunwar buƙatarta a wannan lokacin Jakadiyar Masarautar Huddam da ka taɓa kawowa ta kawo mini kanta a kan wata buƙata da take ci mata tuwo a ƙwarya, ganin haka ya sa na jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Wato na bata umarnin kawo mini Basiru domin na san kai jajirtacce ne za ka aiwatar mini da abin da nake buƙata, yanzu haka tun kafin ka dawo daga taron da aka gayyace ka na gama magana da Shugaba, ka aiwatar mini da abin da nake buƙatar ni kuma na warware maka zare da abawa." Guntun tsaki Boka Shaddas ya saki sannan ya furta. "Zan koma kogon tsafina domin na nazarci abin da ya kamata, duk hukuncin da na yanke za ka ji daga gare ni." Daga haka Boka Shaddas ya fice daga kogon dutsen ba tare da ya ji abin da Shugaba zai faɗa ba. Kai tsaye halawar tsafinsa ya koma yana jin zuciyarsa na tuƙiƙin ɓacin rai, a ɓangare ɗaya yana ayyana irin mummunan hukuncin da zai yanke wa Jakadiya.
Jin kalaman Baiwa Maimuna ya sake kaɗa hantar cikin Fulani Umaima, ta sharce ƙwalla tana sunkuyar da kai ƙasa don haka kawai take jin kunyar mutanen ɗakin. "Yanzu Ammi kina nufin duk abin nan da ake faɗa kin aikata? Wacce irin zuciya gare ki Ammi? Me ya sa za ki biye wa son ranki ki aikata wannan rashin imanin?" Yarima Muhsin ya yi maganar cikin matsanancin ɓacin rai. "Saboda a lokacin shaiɗan ya buga mini gangarsa don haka zuciya ta ingizani har na taka rawa son raina, rawar da ta shammaci ƙafafuwana zuwa faɗawa tekun nadama da da-na sani." Fulani Umaima ta tsahirta saboda yadda ta ji numfashinta na shirin ɗaukewa sakamakon wannan tsokar da ta tokaro ta, sai da zugin ya lafa mata sannan ta ci gaba zayyana duk abin da faru a rayuwarta tun farkon zuwanta cikin Masarautar taba budurwa, har zuwa aurenta da Takawa da rayuwar da suka gudanar ita da Fulani Babba. Ilahirin mutanen wurin jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, ban da hawayen tausayin Fulani Babba babu abin da suke yi. Sailuba ta kalli Jakadiya tana jin wani irin ɗaci a ranta, kunyar Sarki Abdul'aziz ta lulluɓe ta don ba ta san da wanne idon za ta kalle shi da laifin mahaifiyarta ba.
"Wannan mata amma ke dai kin cika azzaluma marar imani." Inna wuro ta furta wa Fulani Umaima tana share ƙwallar idonta. Kamalu ya waiga ya sake kallon halin da ɗan uwansa yake ciki, ya tuna irin gwagwarmayar da aka faɗi mahaifiyarsa ta sha sai kawai ya fashe da kuka yana ɗora kansa a kan cinyar Inna Wuro. A sanyaye Jawahir ta zauna tana jin tsanar Fulani Umaima na mamaye ta, ta waiga wurin Kamalu tana bin sa da kallon tausayi.
"Ashe dama Inna Wuro ba ita ta haifi Kamalu ba? Kenan a yanzu batsayinmu É—aya ba shi ba ya tashi daga matsayin Bawa?" Jawahir ta fara watsa wa zuciyarta tambaya.
Jakadiya sai da ta share ƙwallar idonta tana shirin neman yafiyar Sarki Abdul'aziz ba ta yi aune ba zuruf ta ji hannun Buguzu a saman rigarta, da sauri ta ɗago za ta yi masa magana ya katse ta haɗe da wurga mata ƙwala-ƙwalan idanunsa. "Kada ki dakatar da ni don na lura abin ba na ƙare ba ne, ni fa ba haka muka yi da Shugaba Zurufu ba. Ya mallaka mini ke har abada kuma tun a farkon dare nake son ɓarje amarci amma sai cikas ake kawo mini." Buguzu yana gama maganar ya sake zura hannunsa, kafin Jakadiya ta yi wani yunƙuri tuni ta ji hannunsa ya murɗe mata mamanta tamkar zai tsinke mata su, dalilin haka ya sa Jakadiya da Buguzu da ke ɗauke da siffar Basiru suka fara kiciniya. "Dakata Buguzu! Kada ka nuna mana rashin ɗa'a. Duk uzurunka ba ka kai waɗannan bayin Allahn ba, don haka wannan rashin girmamawa ne." Dattijo Maharaz ya yi maganar rai a ɓace. Ba don ya so ba Buguzu ya saki Jakadiya, ganin haka ya sa ta yi tsalle daga wurin da koma can gefen Fulani Umaima. Ta sunkuyar da kai ƙasa cike da nadama, "Ka fafarce ni Ranka shi daɗe, wallahi sharrin shaiɗa..."
"Ku adana tubanku Jakadiya ba ma buƙata." Sarki Abdul'aziz ya katse Jakadiya murya a kausashe. Ya ɗago ya dubi Fulani Umaima yana jin wani irin ɗaci a ransa, da sauri ta sunkuyar da kai ƙasa gabanta na faɗuwa. "Yanzu wanne irin hukunci kike so na yi miki Umaima?" Shiru ya ratsa ɗakin kowa da abin da yake ayyanawa a ransa. "Don Allah ka yafe mini..."
"Hukunci na tambaye ki." Takawa ya sake katse ta.
"Duk wani hukunci da za ka aiwatar mini duk azaba da raɗaɗinsa zan iya ɗauka, amma don Allah don girman Allah kada ka tsame ni daga ƙarƙashin inuwarka. Kada ka yanke jajirtacciyar alaƙar da ke tsakaninmu ta auratayya, ba zan iya jure rashinka ba. Allah ya sani kishi da ƙaunarka sune tsanin da suka kai ni ga duk wani mummunan aikin da na aikata ranka shi da..."
"Yanzu idan na ce zan ci gaba da zama da ke za ki amince Umaima? An ya kin tuna irin miyagun ayyukan da kika aikata mini? Idan Fulani kishiyarki ce shi wannan yaron ba jinina ba ne?" Shiru Fulani Umaima ta yi ban da hawaye babu abin da yake zarya a saman fuskarta.
Sarki Abdul'aziz ya juya wurin Bamaguje sannan ya furta. "Bamaguje kake ko? Ka zo da waɗansu kalamai da suka rikita mini kwanya amma a wannan gaɓar ba zan yanke hukunci ba, don haka za a sake saka mana lokaci domin wannan maganar dole za ta je wurin Mai martaba wato mahaifin Umaima."
"Ba gaban Mai martaba ko gaban wa za a je ina nan zaune a tsibirina Sarki Abdul'aziz, ku yi duk wacca za ku kowa ya gama aiwatar da uzurinsa ni dai magana ɗaya na faɗa. Ko ba daɗe ko ba jima sai na ɗauke 'yata zuwa halwar tsafina." Bamaguje ya sake tabbatar wa Sarki Abdul'aziz ƙudurinsa. Kalamansa ba ƙaramin ɗaga hankalin Ruƙayya da Yarima Muhsin suka yi ba, musamman da suka hangi irin mummunan yanayin da Bamaguje yake cikin da ƙasurgumin dajin da yake rayuwa.