Sashe 66
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Duk da Fargi ta san cikin da take ɗauke da shi, sai ta nuna wa Shugaba Zurufu sam ba ta san abin da yake nufi ba. "Shin ka fara zargina ne Shugaba Zurufu?" Tambayar da ta wurga masa kenan don ta ɓatar da hankalinsa. Sai da ya saki murmushi sannan ya furta. "Yaro man kaza! Shin kina ganin za ki iya ɓoye mini halin da kike ciki ne Fargi? Kin san waye ni don haka wannan tambayar ina ganin ba ta da alfanu a gare ni. Shin wane ne mamallakin cikin jikinki?"
Gabanta ne ya yi mummunar bugawa ta tattaro mayafin jarumta ta yafa wa kanta, sannan ta furta. "Ba ni da masaniyar abin da kake nufi shugaba." Fargi ta furta tana barin wurin fuska a haɗe. Kaɗa kansa ya yi ya saki murmushin da shi kaɗai ya san manufar yin sa. "Ta yaro kyau take ba ta ƙarko, shi dai ciki ɗan duma ne don haka sannu-sannu ba ta hana zuwa."
Hankali a tashe Fargi ta nausa daji sai da ta yi tafiya mai nisa ta É—an hura huta sannan ta yi wani turare, tana kiran sunayen waÉ—ansu gungun manyan aljanu waÉ—anda suke taimaka mata a game da 'yan tsaface-tsafacenta. A cikin munanan hallitarsu suka bayyana a gabanta, "Wacce irin damuwa gare ki?"
"Shubana Zurufu shi ne matsalata! A yanzu haka ina É—auke da juna biyu, kuma take-take da yanayinsa na nuna mini yana son bankaÉ—o laluben sirrina."
"Zan yi miki aiki a kansa amma kin san taurin kai irin na Zurufu, don haka za ki yi mana yanka. Ina nufin ki zubar mana da jinin jarirai sababbin haihuwa guda uku, za ki ba mu fararen raƙuma biyu sauran aikin ki bar mana komai a hannunmu."
A ɗan tsorace ta dube shi sannan ta ce. "Dole sai ta haka? Haba Aljani Huburu ka san babu asarar rayuka a tattare da ni, ban taɓa kisa ba tun da na wayi gari a halwar tsafin da Shugaba ya horar da ni." Fargi ta furta cike da damuwa.
"Dole sai an zartar da haka Fargi, idan kuma ba kya muradi sai mu yi miki fatan sauka lafiya." Ajiyar zuciya Fargi ta sauke sannan ta yi musu sallama. Ta koma gidan mahaifinta.
"Fargi akwai abin da yake damunki na ga kwana biyu kin ɗashe, yanayinki ya sauya. Me yake damunki?" Mahaifiyarta ta wurga mata tambaya tana kafe ta da idanu. Shiru Fargi ta yi tamkar ba za ta yi magana ba sannan ta ce. "Kwana biyu ba na jin daɗi ne amma yau na ji ƙwarin jikina." Ta furta tana sunne kai ƙasa.
"Ba ni hannunki mu gani." Rass gaban Fargi ya faɗi, ba ta da zaɓi don haka ta miƙa wa mahaifiyarta hannunta. Sai da ta duba tafin hanunta sannan ta saka hannu ta gwale ƙwayar idonta. A ɗimauce ta sake ta tana ja da baya cikin tashin hankali. Ganin haka ya sake firgita Fargi ita ma ta ɗan ja da baya idanunta suka ciko da ƙwalla. Sai da Mahaifiyarta ta rufo ƙofa da windon cikin bukkarsu sannan ta sake jan hannun Fargi suka koma bakin gado suka zauna.
"Wa kika buɗewa sirrinki har haka ta faru? Me ya sa za ki yi mana haka Fargi bayan kin san matsayin da kike da shi a garin nan? Shin kin zaɓi ki tashi daga gurbinki na shugaba ki koma bautacciya bayan kin yi aure? cikin waye a jikinki Fargi?" Mahaifiyarta ta wurga mata tambayoyi yayin da Fargi ta sunkuyar da kai tana jin ƙirjinta yana bugawa.
Bayan kowa ya watse sai ya rage daga Sarki Abdul'aziz sai Kamalu, Muhsin, Ruƙayya da Yarima Muhsin. Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Muhsin da Kamalu. Abubakar kuwa yana zaune sai bin su yake da kallo. "Allah mun gode maka da ka nuna mana wannan rana mai tattare da farinciki haɗe da ɓacin rai. Ubangiji ka fi mu sanin dalilin da ya sa ka tsara mana wannan al'amari a gare mu, kuma muna roƙon ka ba mu ikon cinye jarrabawar da za ta ci gaba da samunmu mai kyau ko akasin haka." Suka amsa masa da Amin.
"Kamalu wannan ɗan uwanka ne sunansa Muhsin, ga ɗayar ƙanwarka nan Raƙayy."
"Na jima da sanin Yarima Muhsin ko don rashin mutumcinsa, wannan ce dai ban santa ba." Kamalu ya furta a zuciyarsa. Amma a fili sai ya furta. "Na ji daɗin kasancewata da ku gabaɗaya ranka shi daɗe, har yanzu gani nake tamkar mafarki nake." Murmushi Sarki Abdul'aziz ya yi ya ce. "Haka Allah ya tsara Kamalu babu bawan da ya isa ya kaucewa ƙaddararsa. Kana da yayye mata da ke aure a wasu garuruwan, In shaa Allah zan sa a aika musu da takarda har zuwa dangin mahaifiyarku." Murmushi Kamalu ya saki, haɗe da amsawa Takawa. Sannu a hankali Sarki Abdul'aziz ya dinga jan su Muhsin da hira don ya gusar musu da damuwar da ke ƙunshe cikin zuciyarsu. Jefi-jefi Muhsin yake saka baki daga ƙarshe ya miƙe ya yi musu sallama ya wuce ɗakinsa. Kamalu da su Ruƙayya suka kwana a sashen Sarki Abdul'aziz.
Tamkar wasu dabbobi haka aka dinga jan Jakadiya da Fulani Umaima aka wuce da su ɗakin duhu, kamar wasu kayan wanki hakan dogaran suka watsa su ciki sannan suka janyo ƙafar suka datse. Jakadiya ban da kuka da kururuwa babu abin da take yi, ita kuma Fulani Umaima sai ido da take bin su da shi da jinjina darasin rayuwa da mamakin wai yau ita ce Dogarai suke yi wa tsawa.
"Allah ya tsine miki Umaima duniya da lahira, wallahi tarraya ta da ke ba ta amfane ni da komai ba." Jakadiya ta yi maganar cikin ɓacin rai.
"Wai kina ina ne ba na son na farwa wacce ba halaliyata ba." Buguzu ya furta yana laluben Jakadiya. Tashin hankalinta ne ya ninku suka ci gaba da wasan ɓuya shi da Jakadiya, Fulani Umaima na shirin mayar wa da Jakadiya martani ba ta yi aune ba ta ji wata irin azaba ta ratsa saman kafaɗarta sakamakon cizon da Aljani Guzzu ya kafa mata a kafaɗa. Jini ne ya fara tsartuwa, cikin azaba Fulani Umaima ta kwarara ihu tana neman taimako. Cikin shammata ta sake jin ya sake zuba mata haƙora a gadon bayanta kuma duk wurin da ya sa haƙoransa da naman jikinta yake ɗagowa.
Kasancewar ƙarfin mutum da aljan ba ɗaya ba tuni Buguzu ya turmushe Jakadiya ya kafa haƙoransa a saman mamanta ɗaya, tamkar wacce ake zuƙewa jini haka Jakadiya ta dinga jin ana zuƙarta. Duk yadda ta so ta yakice Buguzu sai abin ya gagara, don haka ta shiga kuka har da majina tana neman ɗauki amma ko motsi ba ta ji ba ballantana ta saka ran wani zai shigo ya kawo mata ɗauki.
"Ba zan kashe ki ba, sai na gama ɗanɗana miki mummunar azabar da za ta gigita ruhi da gagar jikinki." Aljani Guzzu ya furta wa Fulani Umaima sannan ya ware faratan hannuwansa masu matuƙar kaifi ya shiga karta mata a jiki yana wasa su tamkar yadda ake wasa wuƙaƙe. Fulani Umaima tun tana iya gudun ceton rai har ta galabaita ta faɗi tana jan ciki ƙarshe numfashinta ya ɗauke ta sume a wurin.
Tun isar su Inna wuro sashensu na Bayi kyakkyawan labari game da Kamalu ya fara yaɗuwa, take sashen nasu ya kacame da hayaniya aka shiga tattauna maganar kowa yana mamaki da ta'ajibin wannan lamarin. Sai a wannan lokacin kowa ya samu damar furta damuwar da ke cikinsa dangane da Fulani Umaima, Bayi da dama suka shiga bankaɗo miyagun laifukanta da suka sani na zahiri. Suka shiga tattauna ɗumbin haƙurin da Fulani babba ta yi a lokacin da take raye, har zuwa halin da Abubakar yake ciki na ban tausayi. Wannan ya tsinka zuciyar Jawahir da Mai gado suka shiga ɗaki suka sha kukansu, ga dai ranar yabon Fulani babba amma ba ya raye. Sai da suka daidaita nutsuwar suka shiga wurin Inna wuro aka ci gaba da tayata barka. Don ko ba a faɗa musu ba sun san a yanzu su Inna wuro sun yi musu fintinkau don suna da tabbacin Takawa ba zai bar su haka ba, sai ya gwangaje su da tukwici mai girma. Tun a daren wasu suka fara yi mata fadanci da nuna soyayya abin har mamaki ya ba ta don ta san wacce suke kashewa su binne a cikin gidan dama Mai gado ce, Sai da dare ya tsala sosai sannan su Mai gado suka yi wa Inna wuro sallama suka koma nasu ɗakin.
Asubar fari Masarautar Huddam ta wayi gari da samun mabambamtan labarai, wasu daga ciki sun samu labarin tun a daren ranar yayin da wasu sai da gari ya waye suka samu labarin abin da ya faru. Kuma tun da asubar Sarki Abdul'aziz ya sa aka rubuta takardu zuwa wurin mahaifan Fulani babba, Fulani Umaima da su Khadija domin a sanar da su abin da yake faruwa. Sarki Abdul'aziz da kansa ya zaɓowa Kamalu kayan 'ya'yan sarakai na alfarma, ya umarce shi da ya sauya na jikinsa don kayan Bayi ba su kamace shi a matsayinsa na ɗan sarki ba. Ba musu Kamalu ya karɓa ya saka a ɓangare ɗaya yana sake tausaya wa rayuwarsu ta Bayi, don har lokacin jinsa yake tamkar bawa domin ya rayu a cikin bautacciyar rayuwa ta 'ya'yan Bayi.
"Don Allah ranka shi daɗe idan komai ya lafa a duba rayuwar Bayi da 'ya'yansu." Kamalu ya furta a ɗan ɗarare don har lokacin bai gama sakin jikinsa ba. "In shaa Allahu za mu yadda ka buƙata Kamaluna." Sarki Abdul'aziz ya furta.