← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 86

Sashe 71

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dalilin da ya sa ba a shan kowanne irin Nono a masarautar nan ranar juma'a bai wuce wani mummuna saɓani da ya gifta tsakanin wata jikar Rabo da wani Sarki da aka taɓa yi daga cikin jinku ba, wannan faɗan har sai da ta kai ta kawo iyayena sun shiga ciki kuma a ranar aka tattarawa 'yar fulani kayanta aka fitar da ita daga Masarautar nan. To sai dai kafin ta tafi an kai ruwa rana da ita, har sai da ta kafa wannan sharaɗin na haramta shan Nono a ranar juma'a kuma babban kuskuren da Sarki Rufa'i ya aikata da kai tsaye ya amince da buƙatarta. An ce ta ce duk wanda ya sha Nono a ranar shi kenan an rasa shi gabaɗaya. Kuma a yanzu haka wanan 'yar fulani tana can gaɓar kogin Yulwa ta kafa zuri'arta a can, amma duk ranar Juma'a ta kan kawo ziyara gidan nan.

Shi kuma rafin tsamiya tsohon rafi ne da tun asalin zuwan kakan-kakana Huzaifa yake, a labarin da aka ba ni an ce shi kansa Huzaifa wannan rafin ya taɓa cinye masa 'ya'ya uku. Sai dai an ce duk tsananin bincikensa bai gano ainihin me yake sababba faruwan hakan ba, amma yau kusan shekara ɗari da ashirin kenan da na ji an ce Babban Malamin jinsinmu Sheik Saifullah da ke ƙasar Madina ya san da wannan tarihi, da musababbin faruwarsa. Kun san komai sai Allah ya nufa, har yau ban taɓa zuwa wurinsa don na jin yadda aka haihu a ragaya ba. Kuma a ƙallah na je na yi umara da aikin Hajji babu adadi. Ban sani ba nan gaba ko zan iya zuwa don na ji yadda za mu magance wannan matsalar.

Na gode wa Allah, da Allah ya sa na sauke nauyin da ke kaina na aminina kuma ɗan'uwana Marigayi Safwan. Tun a shekarun baya nake jin ina ma ace aure ya hallata a tsakanin jinsina da jinsinku, da mun ƙulla zumuncin da nake fatan kasancewarsa har gidan Aljanna." Dattijo Maharaz ya ƙarasa maganar a ɗan raunane.

Dattijo Maharaz ya miƙe tsaye, sai da ya bi ɗaya bayan ɗaya ya miƙa musu hannu suka yi musabiha sannan ya furta. "Ni a nan zan gusa Sarki Abdul'aziz, Kamalu sai wani lokaci idan Allah ya yarda." Lokaci ɗaya gabaɗaya suka ji babu daɗi, Kamalu ya riƙo hannun Dattijo Maharaz ya yi masa rakiya zuwa bakin ƙofa, waigowar da Kamalu zai yi ya neme shi ya rasa.

Mai martaba Mahaifin Fulani babba suma suka yi wa Sarki Abdul'aziz sallama, duk yadda ya so su kwana amma fir suka ƙi amincewa. Ya sa Bayi suka shiga haɗo musu kayan da ya tanadar na tsarabarsu, suka yi musu rakiya Sarki Abdul'aziz yana yi musu alƙawarin kai musu Kamalu idan aka kwana biyu.
*SHU'UMAR MASARAUTA*

*39*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx

Assalamu alaikum.
Ina kuke masu bukatar kayan kitchen masu kyau da quality.ina masu bukatar bedsheets blankets.ina Kuma masu bukatar takalma da jakunkuna masu kyau.ina masu bukatar latest kayan yara na maxa Dana. mata...albishirnku kukanku ya kare kuji joining group din R&U exclusive kitchen and more..kuga kaya latest masu kyau Wanda ake yayi a farashi mai sauki.

Sannan Kuma masu hada lefe bata barku a baya ba.tana hada lefe na gani na fada a farashi daidai da aljihunku

Sannan wani abun dadinma masu bukatar kayan kitchen Yana yin adashin gata Wanda zaa baka account number kadinga Tara kudinka aciki iya adadin da kuke da bukata in kagama sai ka siyi abinda kake bukata ba cuta ba cutarwa.

R&U exclusive kitchen and more
Suna garin kano .sannan suna tura kaya kowanne state afadin kasar nan. Haka kasashen da suke makwabtaka da nageria duk muna tura kaya cikin amincin Allah
Duk maineman Karin bayani g number 07034559202

Cikin talatainin dare abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Fargi ta kasa kwance ta kasa tsaye. Ayarin tunaninnka suka cunkuso mata har ta fara jin sarewa a zuciyarta, tare da tunanin miƙa wa Shugaba kai bori ya hau.

"Matuƙar kika sare tun daga yanzu tabbas za a ci gaba da tafiyar da babu ci gaba a cikinta." Zuciyarta ta shawarce ta.

Miƙewa ta yi zaraf ta fice daga cikin bukkarsu a lokacin garin tsi sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabbobi da yake tashi. Daga can kogon dutsen Shugaba ta hango wuta na tashi wanda hakan ne ya alamta mata wani aikin siddabarun yake aiwatarwa. Kai tsaye wurin bishiyar bauta ta nufa zuciyarta a karye ta zube bisa gwiwoyinta, ta fashe wani irin matsanancin kuka.

"Kin ɓullo da abin da bai cika ɗore ba a cikin zuri'arku shi ya sa al'amura ke yunƙurin ƙwace miki." Daga jikin bishiyar ta ji an furta.

"Dalilin haka na kawo kuka gare ki domin ke ce mai yaye mini baƙinciki. Ina fatan yadda na zo a sirrance duka aikin da za a yi mini na sirri ne ba tare da wata hallita ta sani ba." Furgi ta faɗa jikinta a sayaye.

"A zubi da surar halitar abin da yake cikinki duk rintsi da tsanani zai zo duniya, sai dai kuma kash! Ƙaddara ta riga fata Fargi, akwai wani al'amari da zai iya giftawa a nan gaba. Za mu taimaka miki amma da shawararin da za ki bi amma kin san dole a yi ban gishiri na ba ka manta."

"Ina matuƙar son mijina, cikin jikina da tsafina abin bauta! Shugaba ya gindaya mini wani sharaɗi ni kuma ya mini tsauri ba zan iya sadaukar da tsafina ba."
"Ba za ki sadaukar da tsafinki ba! Hasali ma sai dai ki sadaukar da duk wata baiwarki ga abin da ke ɗauke a cikinki, mu kuma mun yi miki alƙawari sai mun kula da abin da za ki haifa ko bayan ba kya raye. Amma idan kin yadda da duk wani sharaɗi da za mu gindya miki?" Damuwar da take ciki ce ta ji ta fara yaye mata, ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "A shirye nake na karɓi duk sharaɗin da madogarata za ta gindaya mini."

"Idan kika ƙi amincewa Shugaba zai hallaka ki kuma zai hallaka ɗan cikinki da shi kansa mijin naki, matuƙar kika yi masa taurin kai wato kika bari ya fallasa cikin jikinki. Ga shawara ta fako; ko ki sadaukar da abin cikinki a wurin Shugaba, ko ki sadaukar masa da tsafinki ko kuma ke ki sadaukar da kanki domin kuɓutar abin da yake cikin?"
"Ban fahimci na sadaukar da kaina ba?" Cikin sauri ta wurga tambaya.

"Muna nufin ki haƙurcewa rayuwar gabaɗaya domin wannan ya kasance daga cikin zanen kundin ƙaddararki. Bari na fito fili na miki bayanin yadda za ki fahimta." Take jikin Fargi ya fara karkarwa.

"Ƙaddararki ce da abin da za ki haifa, ba za ta rayu da ke ba, ba za ta taso a ƙarƙashin rayuwar tsafi da sihiri ba. Abu ɗaya na sani shi ne Mutuwa! Mutuwar ɗayanku na iya kasancewa bayan haihuwarki. Wannan ya zama dole a gare ku tamkar yadda kowanne mai rai yake numfashi."

"Ita dama rayuwar duniya sai wani ya rasa wani yake samu abin bauta! Matuƙar abin da zan haifa zai kasance shi ne silar kuma tsanin da mutanen yankin za su sauka daga kan doron mummunar wannan al'adar, zan amince da duk wani sharaɗi."
"Mun haura sararin samaniya mun riski mabambamdan bayanai dangane ita, haihuwarta da rayuwarta babbar nasara ce ba iya wannan yanki ba. Har zuwa yankin da za ta yi rayuwa a cikinsa."
Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya Fargi ta furta. "Na amince halllitar da zan haifa ta yi rayuwa a doron ƙasa."

"Amma hakan ba za ta kasance ba sai kin amince da sadaukar da ainihin ruhin da siffarki." Jim Fargi ta yi, lokaci ɗaya idanunta suka ciko da ƙwalla, hawaye bibbiyu ya fara zuba daga kwarmin idanunta. Hannunta ta kai saman cikinta, ta ji yadda ɗan tayin cikinta ke ta wutsil-wutsil. Ta ɗaga kai ta dubi murgujejiyar bishiyar kukar da ke gabanta mai ɗauke da mummunar siffar ban tsoro. "Duka na amince matuƙar 'yata za ta yi duk abin da ka furta mini abin bauta." Fargi ta ƙarasa maganar kuka na cinta.

Tun da Sarki Abdul'aziz ya sa aka sake mayar da su Fulani Umaima ɗakin duhu a kullin sau ɗaya ake kai musu ɗan ƙanƙanin abincin da ko yaron goye ba zai ishe shi ba. Cikin wawaso suke cafkar kwanon bai fi su yi loma uku ya ƙare ba. Jakadiya kusan kullin haka za ta ji an zo ƙarfi da yaji ana mu'amala da ita, a ɓangare ɗaya kuma kullin mamanta ɗaya ƙara zaftarewa yake yi yana zagwanyewa. Fulani Umaima kuma duk dare wannan mummunar hallitar ke zuwa ta saka tsinin bakinta mai matsanancin kaifi a wannan tsokar naman da ke zazzagowa daga ƙasanta. Haka take kwana tana ihu tun tana iya zulle-zulle har dai ta sulale ƙasa sumammiya, sanyin asuba idan ya doke ta ne yake farfaɗo da ita. Wannan dalilin ya sa ko harabar wurin ɗakin nasu ka dosa ban da wari da ƙarni babu abin da yake tashi sakamakon yadda ƙasan Fulani Umaima ke fita ruwa mai ɗoyi, ita kuma Jakadiya mamanta ɗaya yake fitar da ruwan mugunya mai wari. A ranar da Muhsin ya je ya gano mahaifiyarsa kai tsaye turakar Sarki Abdul'aziz ya wuce, shi kaɗai ne a zaune yana lissafa kuɗaɗen da suka shigo masa na ribar da aka samu na amfanin gonar da ake sayarwa a sassan yankuna.

"Mahaifiyata na buƙatar agaji, tana cikin mawuyacin hali ya kamata Mai martaba ya san abin yi." Ƙuri Sarki Abdul'aziz ya yi masa yana kallonsa sannan ya ce. "Muhsin ba shi da hurumi a kan wannan maganar." A razane Yarima Muhsin ya ɗago sakamkon jin yadda mahaifinsa ya ambaci sunansa kai tsaye, idan ba mantuwa ya yi ba rabon da Takawa ya kira shi da Muhsin zai kai shekara ashirin,
"Idan an kammala abin ake yi a bamu wuri muna buƙatar keɓewa." Kamar ba zai miƙe ba haka ya zuba masa idanu yana kallo, jiki a sanyaye Muhsin ya fice daga cikin ɗakin.
Chapter 71 · 0% Book details