← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 86

Sashe 32

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Tun daga yanzu har kin karaya ke kuwa me aka yi da maza, kina ganin idan Bamaguje ya ganki yanzu ba zai yi miki dariya ba. Me kike ci na baka na zuba, idan kin bi a hankali da sannu za ki sa Takawa ya ƙarar da gishirinsa a dahuwar ƙaho." Zuciyarta ta wassafo mata waɗannan kalaman waɗanda suka yi tasiri a zuciyarta. Ajiye ƙahon ta yi ta mayar cikin akwatin ta rufe haɗe da saƙa da warwara a zuciyarta.

Guɗar da Jakadiya ta fito tana yi ita ta ƙara jan hankalun ilahirin mutanen da ke cikin masarautar, hannunta riƙe da zanin gadon ta fara shiga lungu da saƙon gidan tana nunawa cike da alfaharin Sailuba takai martabarta har turakar aurenta. Nan da nan aka shiga 'yan tsegungumi da ƙananan maganganu, Fulani Umaima na jin wannan saƙon baƙinciki ya sake lulliɓe ta tare da ɗaukan miyagun alwashi. Lokaci ɗaya ta saki dariyar ƙeta har tana tuntsirawa, don a wani lokacin ura kanta tsoron kanta take yi.

Ku taho mu je mu taya Sailuba murkushe daƙwalen kajin amarcin🙊🤭🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🤣🤣🤣🤣
SHU'UMAR MASARAUTA

18

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

"Masarutar Bahuswa ita ma na ɗaya daga cikin masarautun yankin ƙasar hausa. Sarakuna da dama sun yi mulki sai dai daga cikin waɗanda suka mulki masaratar nan sun haɗa da jinsin mutane da kuma jinsin aljanu, sai dai akwai ƙalubale, tirka-tirka da gwabzawar faɗa a tsakaninsu kafin birkitattun al'amura su daidaita a samu kyakkyawar fahimtar juna." Kusan lokaci ɗaya muka kalli juna, ƙwaƙwalwata ta famtsama kogin tunanin makomata, sakamakon al'amuran almara da suka kai kawo a cikin rayuwata.

"Kenan ni ma aljana ce? Ko kana so ka ce na fito daga cikin jinsin mutane? Ban fahimta ba, ka wayar mini da kai Sarki Hafiz don har yanzu ƙwaƙwalwata cunkushe ta da tarun tunaninnika." Tambayar da na yi wa kaina kenan a cikin zuciyata.

"Wannan amsar daga bakin Sarki Hafiz za ki ji ta." Na ji an furta daga gefena na hagu, waigar da zan yi na hangi wani Dattijo da nake ganin tamkar na taɓa ganin fuskarsa a wani wuri. Daga can gefe shi ma ya nemi wuri ya zauna sai da har lokacin mamaki bai kau daga saman fuskata ba, ya yin da shi kuma yake sakar mini murmushi.

"Mahaifina shi ne Sarki na biyar daga cikin Sarakunan mutanen da suka mulki masarautar nan, ya yin da Mahaifiyarki ta kasance Sarauniya ta farko wacce mace ke jan ragamar akalar mulki babbar masarauta kamar wannan. Ta samu wannan damar ne ta sanadiyyar mahaifinki wanda shi ne ainihin wanda yake kan karagar amma soyayya da ƙaunar mahafiyarki ta sa ya damƙa mata karagarsa. Mahaifiyarki sunanta Gimbiya Nuwaira yayin da mahaifinki sunan shi Sarki Fawwas..." Kaina na ji ya yi nauyi lokaci ɗaya na shiga ruɗani, don haka na katse shi.

"Sarki Hafiz ka na son ka ce ni ma na fito daga cikin jinsin aljanu kenan? Tun da ban ji ka ambaci sunan iyayena a cikin jinsin sarakunan mutanen da suka yi sarauta a gidan nan ba?" Fulani Umaima ta ta gagara ci gaba da karanta littafin sakamakon jin wani azababban ciwo da ya karta wa mararta. Cije baki ta yi tana yarfe hannu ta rufe littafin ruf da ƙyar ta iya mayar da littafin cikin akwatin sabida yadda ta ji naƙuda ta taso mata gadan-gadan, ga wani irin azababban ciwo da yake nuƙurƙusarta.

Mutanen Rumzu ba haka suke zaune kara zube ba, sun kasance suna da sarakuna da hadiman masarauta ta yadda suke gudanar da al'amuransu cikin tsari da girmama na gaba da su. Rumzu mutane ne masu daɗin mu'amala sai dai ko kaɗan ba su da haƙuri uwa-uba suna da matuƙar ruƙo a zuci musamman idan har ba su ɗauki fansa a kan wani abu da ya ɓata musu rai ba. Daga cikin waɗannan al'umma sun kasu kashi biyu, akawai waɗanda baka bambamce mazansu da matansu sakamakon ƙwal kwabo da suke yi daga maza har mata, kuma duka haka suke yawo daga su sai fatar da ke ɗaure a ƙugunsu. Idan har ka ga mace ta fara saka fata tana rufe ƙirjinta to an kaita ɗakin mijinta wato an yi mata aure. Akwai kuma waɗanda ko kaɗan ba sa aski gashinsu acukurkuɗe ya danƙare ga datti ga rashin gyara daga maza har matansu haka suke rayuwa. Su irin waɗannan yarinya tana fara girma za ta fara rufe ƙirjinta, amma daga ranar da aka kaita ɗakin miji ta daina saka komai a ƙirjinta. Suna da al'adu waɗanda suka haɗa da al'adun aure, na haihuwa har zuwa al'adun mutuwa da waɗanda suke gudanarwa duk shekara.

A lokacin da saurayi ya ga budurwa ya ji yana sonta, zai ɗebi jajayan busuru biyu da baƙaƙen kaji cikin dare ya je bakin bishiyar kukar da suke bautawa ya ajiye su. Zai tuɓe kayansa gabaɗaya ya yi tsirara sannan ya faɗi abin da yake tafe da shi, duk maganganun da zai yi zai faɗa ne idanunsa a rufe. Yana gama faɗar buƙatarsa zai ji wata iska ta mamaye wurin bayan ya ji ta ɗauke sai ya buɗe idonsa, idan har ka ga waɗannan kajin da bunsurun da ka kai suna nan to soyayyarka ba za ta samu karɓuwa ba. Idan kuma ka neme su ka rasa to kai tsaye aure zai tabbata a tsakaninka da yarinyar da kake so.

Idan kuma aka tashi auren saurayi da budurwa kafin ayi bikin aure za a haɗa saurayi da amarya a ɗaki guda, mu'amala ta shiga tsakaninsu amma ba haka nan ake kai su ba a kan saka su da gawar mutum wacce aka tsaface wala dga dangin amarya ko dangin angon. Idan kuma babu ɗaya daga ciki za a je fadar Shugabansu akwai wani keɓaɓɓan ɗaki da tsaface ajiyayyun gawarwaki a ɗauki ɗaya a kai musu ita.

Ita gawar ita za ta fara shiga cikin ɗakin da ƙafarta, sai ta yi kwanciyar rigingine sannan saurayi da buduwar su ma shiga ɗakin. Da farko za su yanki gashin jikinsu su zuba a kan gawar da ke kwance, sai su tsallake gawar sau uku-uku sannan su koma wuri ɗaya su kwanta. Bayan an tabbatar da komai ya gama gudana a tsakaninsu za a buɗe ƙofar idan har aka ga jini yan fito daga ƙwayar idonta da can ƙasan gawar to wannan saurayi da budurwar sun kai mutumcinsu. Idan aka ga jini a kunnen gawar to saurayin ya taɓa mu'amala da wata macan kafin wannan ma'ana bai kasance saurayi dal ba da bai taɓa aikata komai ba, idan kuma aka ga jini ya tsattsafo a tafin ƙafar gawar to ita ma budurwar ba ta kai budurcinta ba, idan kuma ba a ga jini ba gabaɗaya a jikin gawar to wannan budurwar da saurayin duka ba su kai mutumcinsu ba wato dukkansu sun taɓa wata mu'amalar kafin wannan ranar.
Kuma hakan wani zunubi ne da har sai an hukunta duk wanda aka samu matsala daga gare shi kafin a yi musu auren. Kuma ko da an yi auren idan namiji ne yake da wannan matsalar har ƙarshen rayuwarsa zai zame wa matarsa tamka bawa, haka idan macen ce ta rasa budurcinta ita ma za ta zame wa mijinta tamkar baiwa sai yadda ya ga damar sarrafa ta.

Inna wuro ta gama duk wasu ayyukan da Fulani Umaima ta saka ta don haka ganin ta kammala ya sa ta rafka sallama daga bakin ƙofar ɗakinta. Shiru ne ya biyo baya hakan ya sa ta sake yin sallama, sai dai can ƙasa-ƙasa ta jiyo muryar Fulani Umaima. Tana son shiga cikin ɗakin amma tsoron kada ta yi laifi ya sa ta haƙura don a yadda kunnuwanta suke jiyo mata kamar Fulani Umaima ba ta da lafiya.

"Ranki shi daɗe shin akwai wani abu da kike buƙata?" Inna wuro ta yanke shawarar faɗar haka ko ta ji daga bakinta.

"Maza shigo ina son ganinki." Fulani Umaima ta faɗa murya can ciki alamun ta fara galabaita. Jiki na karkarwa Inna wuro ta shigar har uwar ɗakin Fulani Umaima, tana tafe tana kalle-kalle don tun da take ba ta taɓa shiga ciki ba. A zuciyarta tana mamakin irin ruwan dukiyar da aka narka saboda tsadaddun kumbayen da ke ɗakin. "Allah ya taimaki uwar ɗakina ko za a sanar da Takawa halin da kike ciki?" Girgiza kai Fulani ta yi, "Ba buƙatar haka Inna wuro, daga ke babu wanda yasan halin da nake ciki don haka ban ba da umarnin a sanar da kowa ba." Jinjina kai Inna wuro ta yi ta shiga jera wa Fulani Umaima sannu, ita kuwa ban da numfarfashi babu abin da take yi da sumbatu sama-sam. Da kanta ta nuna wa Inna wuro wurin da ta ajiye reza, zare da wata ƙatuwar ledar sugar. Da sauri Inna wuro ta ɗauko ta shimfiɗa, ta taimaka wa Fulani Umaima ta hau kai ta tsugunna. Yuuuu haka ta fara jin jiri na ƙoƙarin ɗaukanta, da sauri ta ruƙo ƙafafuwan Inna wuro sannan ta fara jin wasu irin surutai a saman kanta waɗanda ta gagar fahimtar abin da ake faɗa. Tana daga durƙushe ta ga kamar gilmawar mutum da sauri ta ruƙo Inna wuro ta ce. "Inna wuro kin ga gilmawar wani?"
Chapter 32 · 0% Book details