← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 86

Sashe 70

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tabbas haka ne Ranka shi daɗe, kuma wancan shurin da yake ɗakin Sarki Abdul'aziz a nan muma masarautarmu take, an faɗa mini wannan ya samo asali tun a kan Sarki Saddiƙu jinsinmu suka fara ƙirƙirarsa domin ƙulluwar alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu. Kuma an ce a watarana ne Kakana Sarki Ishaƙ ya samu Sarki Sadiƙƙu a cikin ɗakinsa, Sarki Sadiƙƙu ya tsorata da ganin Kakana amma da ya zauna ya yi masa magana ta fahimta sai suka fahimci juna ya kuma ja shi har uwar ɗaki ya nuna masa asalin wurin da suke rayuwa. Tun daga wannan ranar zumunci mai ƙarfi ya shiga tsakaninsu, don an ce wani lokacin haka kakana zai ziyarce shi su sha hira kuma duk abin da ya ga Sarki Sadiƙƙu zai yi ba daidai ba zai yi masa gyara. Kuma an ce suna matuƙar ba wa juna shawarwari akan abin da ya kamata da harkar masarautunsu, har dai tafiya ta miƙa Sarki Sadiƙƙu ya kwanta dama. An yi sarakuna da dama daga jinsina zuwa naku a cikin masarautar nan har kawo lokacin da muka haɗu da amini marigayi Muhammad Safwan." Idanun Dattijo Maharaz suka ciko da ƙwalla, ya ɗan haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ya ci gaba da cewa.

Kafe shi da idanu Fargi ta yi tana mamakin yadda aka yi Shugaba ya gano gabaÉ—aya halin da take ciki, ta furzar da iska mai zafi sannan ta ce. "Ya aka yi kasan da haka?"
"Kamar kin manta a gaban wanda kike Fargi?"
"Shi ya sa na tambaye ka, don da wani ne ba kai ba sare kanshi zan yi."
"Kin manta hukuncin wanda ya aikata abin da kika yi kisa ne a cikin zuri'armu?" Shugana ya wurga mata tambaya.
"Ina sane da haka, kuma dalilin hakan ya sa nake son ruguje wannan mummunar É—abi'a ko al'adar da ba ta da amfani."
"Idan na bayyana wa mutanen gari kin san take za su zartar miki da hukunci." A razane Fargi ta dubi Shugaba Zurufu, fuska da muryarsa ko kaÉ—an babu alamun wasa a ciki.

"Idan kika ce da tashin hankali za ki biye masa tabbas za a yi biyu babu, zai sa a kashe ki kuma ki rasa abin cikinki. Tun wuri ki san abin yi tun talatarki ba ta ƙare a raba ba." Zuciyarta ta wassafa mata bayanai. Sai da ta gyara zamanta sannan ta dubi Shugaba Zurufu ta ce. "Me ya sa za ka yi mini haka Shugaba? Ka san dai kai ne mai lullaɓa mini bargon sutura ya kake yunƙurin yaye mini wanda na lulluɓa wa kaina?"
"Saboda tun farko kika bijire mini a kansa, ina nufin Sarki Sulaiman." Shugaba Zurufu ya yi maganar zuciyarsa fes don ya lura da samun nasarar da ya yi a kanta.

"Yanzu me ye abin yi Shugaba? Ina son mijina kuma ina son abin da yake cikina!" Fargi ta furta tana zuba masa manyan idanunta.
"Zan taimaka miki har ki haife abin cikinki ba tare da wani rai mai numfashi ya fahimci halin da kike ciki ba. Na rantse miki da gawurtar tsafina ko mahaifinki ba zai san da cikin jikinki ba ballantana ya san ranar da za ki haife shi."
"Ina matuƙar alfahari da kai Shugaba Zurufu..."
"Amma da sharaÉ—i." Shugaba Zurufu ya katse ta.

"Wanne sharaɗi ne? Matuƙar zan iya masa na amince zan cika maka shi."
"Za ki mallaka kuma ki sadaukar mini da dukkan tsafinki." A zabure Fargi ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa, "Kana nufin tsafin da nake rayuwa a doronsa?" Fargi ta jefa masa tambaya a ɗimauce. Gyaɗa mata kai Shugaba ya yi, wani tunani ya faɗo mata ta koma ta zauna murya a sanyaye ta furta. "Kalamanka sun gigita ni Shugaba amma zan yi tunani game da wannan furucin naka! Ina son Tsafina, ina son mijina kuma ina son cikina! Dole zan zaɓi abin da zai fi dacewa da rayuwata." Shugaba Zurufu ya ji daɗin kalaman Fargi, ta yi masa sallama cike da damuwa ta fice daga kogon tsafinsa.

Tun a daren ranar Fargi ta nemi Sarki Sulaiman ta sanar da shi halin da take ciki dangane da abin da Shugaba ya ɓullo mata da shi, ya kaɗu matuƙa har sai da ya yi yunƙurin zuwa wurin Shugaba don ya ci masa mutumci amma Fargi ta dakatar da shi don ta san matuƙar ya aikata wannan kuskuren Shugaba sai ya hallaka shi. "Faɗa da aljani babu riba! Ka bar mini komai a hannuna, na san ta yadda zan ɓullowa al'amarin."
"Na rantse da girman Allah matuƙar ya taɓa mini mata ko abin da yake cikinta sai na tozarta shi."
"Ba na son jin haka daga gare ka gwarzona, kamar yadda na ce ka bar mini komai zan san hanyar da zan ɓullo masa ta ruwan sanyi."

Jin shirun Mai gado da ya yi yawa ya sa Jawahir ta diro daga kan gado ta janyo ƙofar ɗakin ta rufe, sannan ta leƙa can ƙarƙashin gadon ta zaro littafin. Haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa ta haye can saman gadon ta buɗe shafin baya, ta ga duk ya shafe babu ko ɗigon rubutu a jiki. A hankali ta ci gaba da buɗewa har ta kai shafin da ya fara da rubutu, ta yi jim kamar mai nazari sannan ta ɗago ta ci gaba da karantawa.

Sai da Sarki Hafiz ya kurɓi ruwan da ke gabansa sannan na ji ya ci gaba da cewa. "Na ji labarin an ce Kakana ne ya kai ziyara wurin wani babban boka, a binciken da yake yi masa ne ya tabbbatar da cewar Mahaifiyarki na ɗauke da kwantaccan cikinki, kuma matuƙar ya bari aka haife ki duk daren daɗewa sai kin karɓi kambun sarautarku ya dawo hannun zuri'ar mahaifinki. Dalilin da ya sa Kakana ya shiga binciken wurin da Mahaifiyarki take, kuma abin da bai sani ba tuni wani aminin mahaifinki aljani Sadi ya ɓoye mahaifi da mahaifiyarki. Sakamakon tuni ya sanar da su abin da yake faruwa." Jin Sarki Hafiz ya yi shiru ya sa na dube shi, sai kawai na ji muryarsa ta yi rauni ya furta mini. "Ki yi haƙuri da wannan furucin da zan furzo miki." A sanyaye na dube shi ina yunƙurin yin magana na ji ya ci gaba da cewa. "In taƙaice miki labari an ce a ranar da alƙadarin zamanki a cikin mahaifiyarki ya ƙare ita kuma a ranar Allah ya yi mata rasuwa, a yadda na ji labari an ce ko fuskarki ba ta iya gani ba ballantana ta san kalar hallitar da ta haifa.

Mutuwar mahaifiyarki ba ƙaramin ɗaga hankalin mahaifinki ta yi ba, an ce sai da ya shafe sama da watanni yana jimamin mutuwarta. Daga lokacin da ta haife ki sai rainonki ya koma wurin mahaifinki da amininsa Aljani Sadi, kuma kin shaƙu matuƙa da mahaifinki kwatsam! Watarana ya wayi gari da ciwon ajali wanda a sanadinsa ne rai ya yi halinsa." A razane na dubi can gefen da nake ganin mutumin da a kullin yake ce mini shi mahaifina ne. Jikina na karkarwa na nuna wurin da yake tsaye yana sakar mini murmushi na furta. "Shi kuma wancan da nake kallo a matsayin mahaifina waye shi?"

"Jawahir lafiya kika datse mini ƙofa?" Kalaman Mai gado suka katse Jawahir daga karatun littafin da take yi, da sauri ta rufe littafin ta tura shi can ƙarƙashin gado sannan ta zare sakatar ɗakin. "Inna wallahi sanyi nake ji shi ne na rufe ɗakin, har kin dawo?" Mai gado ta kafe ta da idanu tamkar tana son gano gaskiyar abin da Jawahir ta gaya mata. Kai kawai ta gyaɗa mata sannan ta wuce cikin ɗakin, Boka Shaddas da ke laɓe a bayan ɗakun nan Bayin ya yi ƙwafa yana sake laɓewa don ya ci alwashin a wannan ranar sai ya ɗauke Jawahir ya kai wa Shugaba Zurufu ko ya fanso Basirunsa.

"Allah ya gafarta wa aminina." Dattiji Maharar ya furta jiki a sanyaye. Kamalu ya ƙarasa gabansa ya zauna a gefensa, cikin sigar lallashi ya furta. "Tabbas na fahimci abin da kake ji a zuciyarka Dattijo Maharaz, na fahimci haka ne bayan rashin su Inna wuro da na yi a kusa da ni. Addu'a ita za ka bi amininka da ita tun da duk mai rai mammaci." Jinjina kai Dattijo Maharaz ya ci gaba da cewa.

"Mahaifina ya ba ni labarin cewar tun ina rarrafe muka haɗu da Sarki Muhammad Safwan a lokacin da mahaifiyarsa take shiga da shi turakar mahaifinsa, wannan abota tamu ta kai har zuwa samartakarmu, duk inda aka ga Sarki Safwan za a ganni a wurin. Hatta wurin zance ni nake yi masa rakiya, don ko ita marigayya da ya aura ba ta taɓa sanin ni ba jinsinku ba ne har sai bayan ɗaurin aurensu.

Faɗar irin shaƙuwar da muka yi da Marigayi abin zai ɗauke mu lokaci mai tsayi, amma abu ɗaya na sani ni da shi aminai ne da muke fatan saduwa har ranar gobe ƙiyama."

"Ma shaa Allah! Allah ya cika buri Dattijo Maharaz." Mahaifin Fulani Umaima ya furta zuciya a karye.

"Ba tun yau ba mahaifina ya sanar da kai tasirinka a cikin masarautar nan, ya sanar da ni bincikensa ya nusar da kai wanzuwarka. Shin ka tuna wurin da na kai ka Kamalu? In da na ce ka ɗauki taɓo ka shafa a bangon wurin?" Da sauri Kamalu ya furta. "Na tuna Dattijo Maharaz."

"Duk wanda ya samu sanar aiwatar da duk abin na sa ka aiwatar ana yi masa kyakkyawan zaton kasancewa Shugaba kuma Sarki a Masarautar Huddam, ashe alaƙar da ke tsakaninmu da kai ba ta wuce gurbin da Futhussam yake ƙoƙarin ajiye ka ba. " Dattijo Maharaz ya sake numfasawa sannan ya ci gaba.
Chapter 70 · 0% Book details