Sashe 19
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
A yamutse Fulani Umaima take kallon Jawahir da goshinta ya tsattsafo da jini, ƙwayar idonta ta kaɗa jawur. Daga ɗan gaban Mai gado wata matashiyar baiwa da ba ta wuce shekara goma ba ta fara yin haɓo sakamakon daɗewar da suka yi a rana da kuma ɗaukan kayan da suka yi a safiyar ranar. Fulani Umaima ta kai dubanta wurin da yarinyar take zuciyarta na wasu-wasin ko dai yarinyar da Bamaguje ke magana ta iso cikin masarautar.
"Me ye wannan a goshinta?" Fulani Umaima ta tambaya fuska a haÉ—e.
Da yake Mai gado tana tsoron bayyanar wani abu daga wurin Jawahir sai ta furta. "A gafarce ni ranki shi daɗe kafin fitowarmu ne ina gaggawa na bige ta da garu har goshinta ya fashe." Taɓe baki ta yi a wulaƙance ta wuce har ta isa wurin yarinyar da ke haɓo, saboda yadda kowa yake tsoron ɓata ran Fulani Umaima suna ganin jini na zuba babu wanda ya iya taimaka mata har ta gama zagayen su, tana daga gefe ta nuna Inna wuro da wata baiwa ta furta. "Jakadiya akai waɗannan sashena za su ci gaba da yi mini hidima, a tabbatar da an ba su horo don ba na buƙatar rashin sanin yakamata." Ko kaɗan Inna wuro ba ta so haka ba domin a yanayin yadda ta fahimci Fulani Umaima sam ba za ta yi sauƙin hali da daɗin mu'amala ba. Kamar ta san abin da yake ran Inna wuro ta sake duban Jakadiya. "A sanar da su ƙa'idoji da tsarina tun kafin su fara aiki gobe, ba na buƙatar gidadanci a sashena." Tana gama maganar ta fice fuuu daga wurin, kamar 'yan matan amarya haka suka sake rankayawa suka koma can sashensu na Bayi.
Wani irin bacci mai nauyi Kamalu ya yi har sai da Baffajo ya tashe shi sallar asuba sau biyu, da gari ya waye ne ya lura da sabon raunin da ke gefen goshinsa. "Kamalu a ina kaji rauni da farar safiya?" Kamalu ya ɗan yi jim kamar ba zai amsa ba sannan ya ce, "A makewayi ne Baffa." Baffajo ya yi shiru yana ƙare masa kallo don haka kawai ya ji bai yarda da abin da ya faɗa masa ba, guntun tsaki Baffajo ya yi cike da damuwa.
Kwanansu biyu a cikin masarautar suka fara sabawa da al'amuran cikin gidan Sarautar tun daga kan ayyuka har zuwa yadda ake mu'amala da shugabannin gida zuwa sauran masu sarautun cikin masarautar. Kuma a wannan lokacin ne Fulani babba ta kira Jakadiya a kan ta sanar da Uwar bayi tana buƙatar ƙarin masu yi mata hidima musamman a ɓangaren Abubukar da kullin lamarinsa ƙara taɓarɓarewa yake. A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Mai gado sai bayi guda biyu Indo da Basira. Aka wuce sashen Fulani Babba da su, sun yi matuƙar mamakin ganin sauƙin halinta saɓanin na Fulani Umaima. Basira da Indo aka wuce da su sashen Abubakar, za su riƙa gyara shi suna ba shi abinci da wanke kayan da ya ɓata. Yayin da Mai gado za ta zauna a sashen Fulani babba tana taya Baiwa Zainaba yi mata waɗansu hidindimun saboda goyon Jawahir da take da shi, Shi ya sa Fulani babba ta bar ta a ɓangarenta.
Sannu a hankali suke gudanar da rayuwa cikin masarautar, har ta kai shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Jawahir da su Khadija. Suna matuƙar son ta don wani lokacin idan suka ɗauke ta sai dai idan ta yi kuka su kira Mai gado su damƙa mata ita. A ranar juma'asu ta biyu da zuwansu Masarautar duk yadda Mai gado ta so nema wa Jawahir abin da za ta sha abin ya gagara tun da ta yi ƙanƙantar da za a bata kunu a wannan lokacin. Babu yadda ta iya haka ta zuba wa sarautar Allah ido har dare ya fara tsalawa, cikin fargaba Mai gado ta kwanta da tunanin irin kukan da Jawahir za ta yi cikin dare. Sai dai ga mamakinta tun tana gadin Jawahir har bacci ya yi awon gaba da ita, cikin baccinta ta fara jin tsotso da dariyar Jawahir kamar yadda ta saba ba ta nonon awaki ko na shanu idan dare ya yi. Da mamaki take bin Jawahir da ke faman yin amai alamar ta sha nono ta ƙoshi, ta tashi ta tallafo ta, ta sake rungume ta bayan ta tsagaita da aman ta kwantar da ita suka koma bacci. Asubar fari suka wayi gari da ganin mushen saniya a harabarsu, cike da kaɗuwa kowa yake bin saniyar don saninsu ne filin dabbobin Mai martaba ba ƙaramin nisa yake da shi ba tsakaninsu da wurin. Take Dogarawa suka janye ta gefe bayan gari ya waye aka sanarwa da Mai martaba, sai dai wani abin mamaki ko da aka je garken shanun Takawa babu ko ɗaya da ta yi ɓatan dabo, hasali ma kwance suke cikin kwanciyar hankali, haka aka ɗauki gawar saniyar aka kai ta wani ƙaton ramin da ake zuba bola a ka banka mata wuta. Mai gado ita kaɗai take mamakin wannan al'amarin, har ta saki jikinta ta ci gaba da gudanar da rayuwa kamar kowa. Da farko ta fara fuskantar ƙalubalen ɗan abin da take siya wa Jawahir Nono, ganin haka ya sa ta fara sana'ar ɗinkin muhuci tana ba wa Umaru yana fita bakin kasuwa yana siyar mata. Ɗan abin da suka samu da shi suke siya mata nono da sauran abin da ba a rasa ba. Daga baya da zama ya yi zama har su Khadija suka ji labarin nonon da jawahir take sha sai Fulani Babba take sa wa ake tatso nonon awakin Takawa ana ba wa Mai gado take shayar da Jawahir, sai dai babban tashin hankalin da suka ci gaba da fuskanta bai wuce duk sati da kalar mushen saniyar da za su yi tozali da ita da Asuba ba, zancan da ya karaɗe ciki da wajen masarautar har ya kai ga kunnen Fulani Umaima.
A lokacin da Fulani Umaima ta sallami su Jakadiya kai tsaye ɗakinta ta koma, cikin damuwa take kai-kawo. Ganin ba za ta iya jure halin da take ciki ba ya sa ta ziyarci Bamaguje ko ta san abin da zai iya faruwa a gaba.Don haka kawai take jin zuciyarta na wasu-wasin akwai abin da zai iya faruwa a cikin masarautar. Tun isarta wurin ta fahimci yana cikin matsanancin ɓacin rai, ba ta damu da sanin halin da yake ciki ba don haka ta amayar masa da damuwar da ke cikinta dangane da rashin gane hallitu biyun da ya ba ta umarni. Ƙarasa kalamanta ya yi daidai da sauke yatsunsa biyar da Bamaguje ya yi a saman kumatunta, a firgice ta ja da baya cikin kaɗuwa da zallar tashin hankali.
"Ni ka mara?" Ta wurga masa tambaya cike da ƙasaita da tsananin ɓacin rai.
"Kin ɓata mini shiri kin kuma wargaza mini tanadina, me ya sa kin san ba za ki kawo mini yarinyar nan ba kika ɗaukar mini alƙawari har kika sa na je fadar Baƙaƙen aljanu na gana da Shugaba, ba fa iya ganawa muka yi ba da ƙyar da suɗin goshi na samu zai aiwatar mini da aikin da nake son cim ma muradina a kanta." Bamaguje ya faɗa jiki da muryarsa na karkarwa sakamakon tsufan da ya yi tukuf. Murmushin takaici Umaima ta yi don sai a yanzu ta fahimci manufarsa sarai, wato so yake ya yi amfani da iya wurin cim ma ƙudirinsa ita kuma ko oho.
"Sai yanzu na fahimci in da ka dosa, tun ziyarar baya na fara ɗora zargi a kanka, idan ba ka manta ba a wani zuwa da na yi da bakinka ka ce mini ita yarinyar nan Yarima ba zai taɓa hawa karaga ba har sai ya aure ta. Daga baya ka ce mini na yi duk yadda zan yi na kawo maka ita domin aiwatar da aikinka a kanta, ashe ban sani ba tsuntsu biyu kake son jifa da dutse ɗaya. Duk duniya babu wanda ya taɓa yi mini abin da ka yi mini, kuma na yi alwashin wannan shi ne karo na ƙarshe zuwa fadarka. Ka san ni sarai Bamaguje ba na yafiya kuma ba na mantuwa don haka ina nan tafe zan waiwaye ka ko ba daɗe ko ba jima, ka riƙe duk wani taimako da kake ganin za ka iya yi mini." A zuciye Umaima ta juya za ta tafi, ta ji Bamaguje ya bushe da dariya.
"Na san wannan ranar za ta zo da za ki bijire mini. Amma ki sani ta yaro kyau take ba ta ƙarko, ni ne dolenki idan aure bai kawo ki ba shika zai kawo. Da sannu ya za ta ɗakin ƙanwa idan da yawancin kwana..."