← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 86

Sashe 15

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayarin dakarun masarautar da ke tafe da su Baffajo tafe suke cikin gajiya sakamakon doguwar tafiyar da suka yi, a farfajiyar wata bishiya suka yada zango suna hutawa sai bayan sun huta sannan suka ci gaba da tafiya, cikin zuciyarsu kowa da abin da yake ayyanawa. Ganin magriba ta fara dosowa ya sa suka yanke shawarar kwana a cikin dajin washegari da asuba sai su É—ora daga inda suke tsaya.

Ƙauyen Gangare

Ganin yanayin da Umaru ya koma gida da shi ya sa Mai gado shan jinin jikinta.

"Mai gida ya kuka yi da Mai gari na ganka duk a sanyaye." Ƙasa ya yi da murya ya furta. "Ina yarinyar nan take? Zan kai ta gidan Mai gari" Kallon rashin yarda ta bi shi da shi ta sake gyara goyon Jawahir da ke bayanta. "Me za ta yi a gidan."

Kamar zai yi kuka Umaru ya ce, "Malam Malmo Mai gado ban san ya za mu yi ba, sun buƙaci na mallaka wa Mai gari ita." Rass! Ta ji gabanta ya faɗi, sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi ƙasa da murya. "Ba zan iya rabuwa da Jawahir ba Mai gida, na san Malam Malmo sarai ba zai wuce tsubace-tsubbace zai yi da ita ba." Umaru ya waiga kamar wanda ake kallo duk a tsorace ya ce. "Ya zamu yi yanzu? Mene ne mafita?"

Masarautar Huddam

Wuni guda haka Fulani Umaima ta yi shi cikin rashin ƙwarin jiki, ba ta san dalili ba amma haka kawai za ta ji gabanta na faɗuwa. Har ta so dannewa ta ji zuciyarta na azalzala ba za ta iya jure rashin zuwa wurin Bamaguje ba.

Tsufansa ya sake fitowa sosai don jiki da hannuwansa har karkarwa suke yi.

"Ta zo duniya da ƙarfin iko, shi kuma yana gab da dawowa gidansu na gado."

Bamaguje ya furta bayan ya gama sauraron ƙorafin Fulani Umaima. Ta ɗago a hargitse bakinta na rawa, ƙirjinta na dakan lugude. "Su waye? Kuma daga ina suke."

"Garaje ga dami, daɗina da ke gaggawa Umaima. Na ɗauka za ki tambayi alaƙar shi da masarauta da ita kanta yarinyar." Ajiyar zuciya ta sauke. "Tamkar tagwaye haka suka kasance tsakaninta da Hidaya, sai dai waccan ruwan sanyi ce salam a kan wannan. Ban san a wanne muhalli zan tirke ta ba, abu ɗaya na sani ita ta kasance daga cikin wata irin zuri'a masu matuƙar hatsarin gaske. Na ga takobi a cikin jininta sannan wuta na gewaye sashenta, takaicina ɗaya Mahaifiyarta ta riga da ta binne duk wani al'amari da sirrin da ke ƙunshe a cikin rayuwarta. Daga ni har sauran matsafan duniya duk wani bincike da za mu yi ba za mu tantance takamaiman ainihin tushenta ba. Sai dai kuskure guda mahaifiyarta ta tafka wanda da shi kaɗai za mu iya cin galaba a kan wannan yarinyar."

Cike da zumuÉ—i Fulani Umaima ta furta. "Mene ne shi? Duk wuya duk tsaninsa zan nemo shi..."

"Bincike ya bayyana mini tana da matuƙar tasiri a rayuwarsa. Ina nufin jaririn da kika sa Maimuna ta fitar da shi shekara goma sha ɗaya baya, shi yake gab da shigowa gidan sarautarku. Sai dai kuma ita da shi za su kasance tamkar wuta da ruwa a fannin gaba, kowannensu ba zai ƙaunaci ɗan'uwansa ba. Shigarsa tamkar dasa nakiyar da ke tashin zamani da alƙaryarki ne, ba tun yau ba; na gaya miki shi ba kamar ɗan uwansa ba ne. Ruhinsa ɗauke yake da zaratan dakarun da ke sarrafa zuciya da tunaninsa, tun ranar haihuwarsa na fahimci zanen ƙaddararsa ya wanzu dalilin da ya sa na baki shawarar matse kunamar nan a cikin bakinsa, ashe tagwaye ne halwar tsafina ya gagara nuna mini. Tun yana jariri ya sauka a fadar Sarkin fararen aljanun doron ƙasa, da ke tsakiyar dajin Wuruju a daidai wurin da Baiwa Maimuna ta dire shi. Sun naɗa masa kambun da babu mai iya sauke shi sai mutum ɗaya wato wannan yarinyar." Bamaguje ya ƙarasa maganar yana haska wa Fulani Umaima inuwar wata yarinyar. Ta tsinci muryarsa ya ci gaba da faɗin.

"Mu koma maganarmu ta baya na kuskuren da mahaifiyar Fargi ta tafka. Ta bar tauraron 'yarta a sake wanda duk wani matsafi kallo ɗaya ko bincike ɗaya idan ya yi a kanta zai fahimci muhimmancinta gare sa. Duk wanda ya mallaki ruhinta shi zai kasance mafi shahara a faɗin yankin nan a ɓangaren gawurtar tsafi da sihiri, runduna ce guda a tare da ita domin mahaifiyarta kafin ta mutu ta riga da ta juye mata nata jinin a jikinta."

"Mene ne mafita, don ta ni gabaɗaya a mutu har liman a rasa mai jan sallah." Cewar Fulani Umaima da zuciyarta ta gama ƙeƙashewa.

"A baya na fid da rai da samun wannan É—aukakar, amma idan kin yadda me zai hana mu jefi tsuntau biyu da dutse É—aya?"

Mai Gado

"Guduwa ita ce mafita, sai dai mu bar garin nan amma ka san muddin muna cikin ƙauyen nan Malmo ba zai bar mu da sauran numfashi ba." Shiru ya yi yana tunanin shawarar da ta kawo, ganin ya tsaya yana nazari ya sa Mai gado ta faɗa ɗaki ta ɗaura kayansu a cikin ɗankwali ta fito.

"Allah ya sani na ɗauki aniyar kula da yarinyar nan, Malmo azzalumin mutum ne, na san halinsa sarai tun da ya ƙallafa rai a kan yarinyar nan ko mun damƙa musu ita sai sun hallaka mu don gudun tonuwar asirinsu." Mai gado ta faɗa tana miƙa wa Umaru ƙullin kayansu, sai da ya karɓa sannan ya furta. "Na gode wa Allah ya sa kika fahimtar da ni da tuni na sa mun yi tsalle mun afka cikin rijiya gaba dubu. Yanzu dai babu sauran lokaci mu bi ta ƙofar baya." Cikin sauri Mai gado da Umaru suka hankaɗe katangar karan da ke gewaye da gidan, kamar masu shirin tashi sama haka suka dinga sauri suna kutsawa ta ciki bishiyu duk da a lokacin magriba ta kawo kai. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka ƙarasa wani ƙaramin gari a lokacin dare ya tsala sosai babu haske sai na farin wata, a gajiye suka zube a gefen ganuwar garin suna sauke ajiyar zuciya. Cike da galabaita Jawahir ta fara mutsu-mutsu sai a lokacin suka shiga damuwar abin da za su sama mata ta sha. Gorar ruwa Mai gado ta kunto ta ba ta sannan suka yi jigum-jigum, har sun zauna da sunan hutawa Umaru ya furta.

"Mai gado an ya wurin nan yana da kyau kuwa? Me zai hana mu ƙarasa cikin garin nan mu nemi alfarma?"

Mai gado ta yi murmushin takaici, "Duk in da za mu je matuƙar za su fahimci ba na shayar da yarinyar nan dole za su harbo jirginmu, kuma su ɗora mana zargi da tambayoyi a kanmu. Abin da muke gudu kuma ya faru ka ga an ƙi cin biri an ci dila." Umaru ya yi jum sannan ya furta. "Ina ganin mu ƙarasa bakin kasuwa mu kwana asubar fari sai mu bar garin, mu ɗora daga inda muka tsaya." Ta gamsu da shawararsa don haka suka yi gaba suna tambayar kasuwar garin har Allah ya datar da su, suna gab da shiga kasuwa suka ga wata mai fura da nono suka siya nono sannan suka ƙarasa. A bayan rumfunan kasuwar suka yada zango bayan sun take wa Jawahir cikinta da nono, babu jimawa baccin gajiya mai nauyi ya yi awon gaba da su.

Sanyin asuba ne ya bige su suka farka don haka kamar marasa gaskiya suka sake nufar doguwar hanyar suka ci gaba da tafiya. Ba su yi tafiya mai nisa ba suka tsaya suka gabatar da sallah sannan suka ɗora daga inda suka tsaya. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka tarad da wani ayarin mutane, yara, manya, maza da mata. Sai kuma Dogarawan da ke kai kawo a kansu, kallo ɗaya Umaru ya yi musu ya fahimci bayi ne aka kama. Da yake suna ɗan nesa da su da sauri Umaru ya ja hannun Mai gado ya furta, "Maza zo mu gudu idan Dogaran nan suka gan mu na tabbata kashinmu ya bushe don mun zama Bayi na har abada." Yana rufe baki suka juya da sauri. Cak! Suka tsaya cikin faɗuwar gaba, Mai gado ta riƙo hannun Umaru jiki na karkarwa.

"Gidan uban wa za ku gudu?" Kalaman Sojan masarautar mai ƙirar samudawa ya ratsa su, gabaɗayansu aka rasa mai bakin magana. Ganin haka ya sa Dogarin tsula wa Umaru bulala a baya, cikin azaba ya hau susar baya yana faɗin. "Tuba nake ranka shi daɗe ba guduwa za mu yi don Allah ku yi mana rai." Da hannu Dogarin ya nuna musu hanyar da sauran mutanen da ke zaune a ƙasa suke, babu musu Mai gado da Umaru suka bi hanyar ba tare da sun furta komai ba. Tun da suka tunkari wurin mutanen wurin suka zuba musu na mujiya suna kallonsu.

Bai san dalili ba haka kawai yake jin ƙirjinsa na bugawa, zuciyarsa kamar za ta yi tsalle ta hudo ƙirjinsa. Duk taku ɗaya da Mai gado take yi tana kusanto shi ji yake kamar ana ɗana wa zuciyarsa ruwan dalma, da wata irin ƙuda da wani surutai da ya gagare tantance harafi ɗaya ballantana ya yi wa kalaman nasu hisabi. Da yake hannunwansa biyu a ɗaure suke a jikin itace, kansa ya tura cikin ƙafafuwansa yana runtse ido. Bai yi aune ba ya fara jin sautin kukanta a tsakar kansa, yana yunƙurin buɗe idonsa kamar a mafarki ya ji an furta. "Ita daban ce don haka ta fito daga cikin wani irin ahali, tarayyarku alheri ce mai samar da taimakon juna a koyaushe. Sai dai zuciyoyinku za su gagara ba ku haɗin kan da za ku cimma manufarku ta alheri. " Firgigit ya ɗago kansa cikin mamaki, ba yau ce rana ta farko da ya fara jin waɗansu irin surutai a kansa ba. Amma na yau sun matuƙar dagula lissafinsa. "Wace ce ita?" Ya furta a fili. A daidai lokacin aka kama Umaru aka ɗaure ita kuma Mai gado aka kama ƙafarta ɗaya aka ɗaure, ta ci albarkacin jaririyar da ke bayanta.
Chapter 15 · 0% Book details