Sashe 8
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ki tabbata kin sa shi ya shiga bayan gida kafin ki saka wa Maimuna turare a gabanta."
Kalaman Boka Bamaguje ya dawo mata raɗau a cikin kunnuwanta. Miƙe wa ta yi ta furta. "Sarkina bari na haɗa mana ruwa mu ɗan watsa ko?" Ba ta jira cewarsa ba ta nufi banɗaki ta haɗa komai da kanta sannan ta zuba turaren da Bamaguje ya bata, bayan dawowarta ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa sannan suka wuce banɗaki. Da kanta ta ɗebi ruwan ta watsa masa cikin sigar tsokana, sai kuma ta yi farat ta furta. "Na yi mantuwa."
Kallon da ya yi mata ne ya alamta mata yana buƙatar ƙarin bayani daga gare ta.
"Ina zuwa." Kawai ta furta ta fice a gaggauce. Sai da ta tabbatar da ta rufe ƙofar ta baya sannan ta koma turakarsa cikin sauri ta ɗaga doguwar rigar Maimuna ta kwara mata turaren a ƙasanta sannan ta shafa mata a fuskarta, ita ma ta murtsuke jikinta da shi ta rage kayan jikinta ta sake komawa cikin banɗakin. Tana shiga ƙamshinta ya daki hancinsa, take ya ji wani irin yanayi ya tsarga masa. Buƙatar ya kusance ta ta yunƙuro masa, ganin saƙwannin da yake aika mata ya tabbatar mata da haƙonta zai cim ma ruwa, don haka ta fara neman shawarar da za ta yanke wa kanta. A hankali ta yakice shi tana faɗin, "Sarkina a banɗaki muke mu ƙarasa turaka." Bai musa mata ba, ta ƙarasa sheƙa musu ragowar ruwan sannan suka fito hannunta na riƙe da shi, idanuwansa a rufe suka ƙarasa don haka ko da ta zaunar da shi a gefen gado ta ga ya rarumo Baiwa Maimuna da ke zaune kamar gawa. Fulani Umaima ta koma gefe ta zuba masa ido zuciyarta ƙal, tana nan tsaye Takawa ya gama mu'amalarsa da Maimuna ya koma gefe ɗaya sai gani ta yi numfashinsa ya ɗauke. Da sauri ta ƙarasa ta ɗebi najasar jikinsu ta isa bakin rijiyar da tun da take shiga cikin turakar ba ta taɓa taka wurin ba, wata irin kuɗa ta fara ji a cikin kunnuwanta ga wata 'yar juwa-juwa da take ji sama-sama. A haka ta samu ta zuba najasar a kan rijiyar take murfinta ya buɗe, wata baƙar ƙura ta turnuƙe ta. Sai daga baya komai ya washe, ganin haka ya sa Fulani Umaima ta koma ta janyo hannun Baiwa Maimuna sai da suka je bakin rijiyar Fulani Umaima ta furta.
"Maza ki shiga rijiyar nan da ƙafar hagu."
Ba musu Maimuna ta ɗaga ƙafarta ta zura cikin rijiyar ta zauna a kan wani mulmulallan baƙin dutse. Kamar yadda Bamaguje ya gaya mata Maimuna na gama shiga murfin ya taso da kansa ya rufe ruf. Ta koma can gefen Sarki Abdul'aziz ta kwanta tamkar da ita Takawa ya gama mu'amala. Bayan ɗan wani lokaci Mai martaba ya fara motsawa, jin haka ya sa Fulani Umaima ta fara sauke ajiyar zuciyata tana rarumo shi cikin kissa da kisisina. Wani irin nauyi dum! Kansa yake yi masa don haka ya gagara tunano abin da ya faru a baya, ganin yanayin da suke ciki ya sa ya sakar mata ajiyar zuciya ya yunƙura suka wuce banɗaki don tsaface jikinsu. Irin rawar jikin da yake yi a kanta ne ya sake tabbata mata da tabbas alƙaluman tsafin Bamaguje ba su zube a ƙasa banza ba, ta ci gaba da narke masa tana cin karenta babu babbaka. Daren ranar a sashen Sarki Abdul'aziz ta ƙarashe shi har zuwa wayewar gari.
Cikin abin da bai fi wuni biyu ba, maganar haihuwar Fulani ta yaɗu cikin da wajen Masarautar Huddam, musamman da ya kasance an san Takawa ba shi da ɗa namiji sai a wannan lokacin. Manyan mutane da masu kuɗi haka suka dinga zuwa suna bada gaisuwa haɗe da yi masa barka da samun ƙaruwa, mafi yawa daga cikinsu har da sha tara ta arziƙi suke kawowa. Duk da Fulani Umaima ta san jaririn a nakashe yake hakan bai hana ta jin ƙyashi, baƙin ciki da ƙunci a kan kyaututtukan da Fulani Babba take samu ba. A lokacin sai ta tsiri kwanciya da tsirfar ciye-ciye wani lokacin har amai take ƙaƙalowa a turakar Mai martaba, duk da cikin jikinta babu abin da yake saka ta. Ganin haka ya ɗaga hankalin Takawa har ya aikata sashen magunguna aka kira masa Ungozoma da jikar Baushe don su duba ta su ba ta magani. Tashin farko aka sanar wa da Sarki cikin da ke jikin Fulani Umaima, farin ciki kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha. Ita kuwa Fulani Umaima ko kaɗan ba ta nuna wa Takawa ta san da cikin jikinta ba, nan ta shiga gwalangwaso da feleƙe wani lokaci hatta ƙamshin Turakarsa ce wa take ba ta so.
Cikin wannan yanayin aka ɗebi kwanaki mai jego tana ɓangarenta tana jego ita kuma Fulani Umaima tana rainon cikinta, gabaɗaya gidan sarautar ya zagaye da ƙananan maganganu. Jin labarin cikin Fulani Umaima da Fulani Babba ta yi ba ƙaramin faranta ranta ya yi ba, kuma rashin ganinta kwana biyu a ɓangarenta ko kaɗan bai dame ta ba don ta san yadda laulayin ciki yake ba shi da daɗi. A ɓangare ɗaya Fulani Babba na cikin matsanancin tashin hankali sakamakon yadda fitsarin da yake zuba daga jikinta yake sake ta'azzara, tun tana ɓoyewa har ya zamana sai da Baiwa Zainaba ta fahimci halin da take ciki, ga shi abin kullin gaba yake yi da ta kwanta ko bacci minti biyar ba ta yi tana farkawa sai dai ta ji ta sharkaf da fitsari, ga kuma jinin biƙi duk shimfiɗarta ta haɗu ta dagule. Ana gobe suna da asuba bayan ta tashi ta sake ganin wurin ya yi sharkaf da wani irin zarnin da ke tashi har ya wuce misali. A wannan lokacin take zuciyarta ta karye ganin lalurar tata a kullin gaba take yi ba baya ba, a daidai lokacin yayarta da suka zo daga Masarautar Bassar ta shiga ɗakin, ganin ta a zaune ya sa ta ɗan yamutsa fuska.
"Fatima wai mene ne yake wari ne?"
Da yake mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashi awaki take Fulani Babba ta fashe da matsanancin kuka, da mamaki Halima ta furta, "Fatima me yake faruwa ne?" Sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe tana nuna wa yayarta ta ce.
"Ki duba ki gani Yaya Halima wai ni ce yau nake malala fitsarin kwance. Ni dai na fi zargin tun ranar na haihu na haÉ—u da wannan iftila'in, duk yadda zan yi takatsantsan ina runtse idona duk gajarta bacci sai dai na tsinci kaina a cikin fitsari." Jakadiya da ta zuro kanta da niyyar sanar da Fulani Babba ruwan wankanta ya yi zafi ta yi fakare tana sauraronsu. Yaya Halima cike da damuwa ta jinjina kai.
"Kin sanar da Mai martaba?"
Girgiza mata kai kawai ta yi don ba ta son ta buɗe baki har ta iya sanar da danginta zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Takawa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta furta, "Ya zama wajibi na sanar da Yakumbo a nemar miki magani, domin wannan fitsarin ba na lafiya ba ne. Ni fa dama zuciyata da hankalina ba su taɓa aminta da wannan kishiyar taki ba..." Da sauri Fulani Babba ta katse ta. "Yaya kada ki zargi Umaima domin ban taɓa zarginta a kan wani mugun abu ba, zamana da ita babu wata matsala ni dai a yi mini magani amma Allah ya sani babu sa hannun Umaima a lalurata." Inuwar da Yaya Halima ta hango a wurin labule ya sa ta furta.
"Waye a wurin nan?" Jikina na rawa Jakadiya ta faÉ—a É—akin tana faÉ—in, "Allah ya taimaki Fulanin Takawa, uwar yariman gobe da yardar Allah. Dama ruwan wanka na kwashe na zo sanar da uwar gijiyata." Daga cikin É—akin Fulani Babba ta furta.
"Saƙonki ya isa Jakadiya."
"Godiya nake zinariya fara mai farar aniya bangon talakawa da marasa gata, Allah ya raya mana yarima ya gaji karagar da babu kamarta a faÉ—in nahiyar nan." Yaya Halima ta amsa tana bin Jakadiya ta kallon tuhuma. Sai da ta ga Jakadiya ta fita sannan ta furta.
"Da alama wannan farar zuciya taki na iya kai wankin hula ya kai ki dare, jikina yana ba ni idon masarautar nan yana kanki."
"Yaya Halima shi zato zunubi ne! Don haka..." Da sauri ta katse ta. "Dama ki ajiye zurfin cikinki kin amayar mini da abin da yake cikinki domin abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa." Idanun Fulani Babba ya ciko da ƙwalla don ita kaɗai ta san zafin da zuciyarta take yi mata, amma sanin Yaya Halima na daga cikin irin marasa haƙuri ya sa ta danne damuwarta ta furta. "Babu wani abu da yake damuna Yaya Halima, idan ma akwai na fauwala wa Allah saboda saniyar da ba ta da jela Ubangiji ne ke kore mata ƙuda." Yaya Halima ta taɓe baki ta fice ba tare da tanka mata ba, Fulani Babba da ta yi shirin wanka tana kai idanunta kan jaririnta. A kullin ta kalle shi zuciyarta na wasu-wasi a kan ingancin lafiyarsa, sai dai babu yadda za ta yi tun da ba fada gare ta a wurin Takawa ba balle ta yi masa bayanin halin da jaririn yake ciki.