Sashe 39
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallo ɗaya za ka yi wa Jakadiya ka fahimci kwanciyar hankali ya yi ƙaura daga jikinta, yayin da tashin hankali ya mamaye gangar jiki da tsokarta. Ganin idan ta ci gaba da tsaiwa tana iya zubewa ƙasa saboda tashin hankali, ya sa ta fice daga ɗakin Fulani Umaima kai tsaye ta wuce Sashen Sailuba.
Take wani tunani ya faɗo wa Fulani Umaima da sauri ta fice ta wuce sashen Mai martaba, a gaggauce ta fara bubbuga ƙofar cikin nuna tashin hankali. A tsammanin Takawa Mai gado ce ta sake dawowa don haka ya yi biris da ita.
Kusan tun safe suka fara casar gero da sussuka, har kawo yamma abin da yake tsayar da su yin sallah ko cin abinci don haka Jawahir ta gaji liƙis sakamakon ta jima ba ta yi aiki mai yawa kamar na wannan ranar ba. A lokacin da suka fara ɓarar gyaɗa saman cikinta ne ta ji ya yi mata ɗauuuu kamar wacce aka ɗanawa dalma. A gigice ta kai hannu saman wurin da tambarin bishiyar yake wani irin zafi ta ji, har idon kunnenta ba gizo yake yi mata ba ji ta yi tamkar tambarin na fisgar hannunta. A sace ta fice daga wurin ba tare da kowa ya lura ba, can cikin dajin ta ɗan nausa sai da ta waiga hagu da sannan ta ɗaga rigarta. Jawur ta ga wurin ya yi zanen bishiyar ya ƙara fitowa raɗau, wani irin tsoro ya kamata ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri.
"A matsayina na mahaifiyarki ina mai alhinin sanar da ke daga yanzu a kowanne lokaci ƙofar ƙunci da damuwarki na iya buɗewa, ni na hango miki abin da ba ki hango ba Jawahir amma tun da haka kika zaɓa ga fili nan ga mai doki." A tsorace Jawahir ke kallon matar da ta taɓa gani ta zo mata cikin mafarkinta, sai dai a yanzu ƙiri-ƙiri ta ganta cikin sura da ta ganta a cikin mafarki. Ja da baya ta fara yi tsorace kafin ta yi wani yunƙuri ta ga matar na yin baya-baya har gangar jikinta ya nutse a kikin murgujejiyar bishiyar kukar da ke gabanta ta ɓace mata ɓat. Tsoro ne ya sake mamaye Jawahir da gudu ta falfala cikin tashin hankali ta nufi sashensu na Bayi. Uwar tuwo na ganinta ta fara ƙwala mata kira amma ko waigenta ba ta yi ba, can saman gadon karan Maigado ta faɗa ta janyo zanin gadon ƙirjinta na bugawa jikinta na karkarwa ta lulluɓa. Nan take zazzabin ya lulluɓe mata jiki a ɓangare ɗaya kuma raɗaɗin tambarin cikinta ya haddasa mata rashin kuzari, da ta runtse ido matar take gani a lokacin da take nutsewa cikin jikin bishiyar, wannan ya sake ɗaga mata hankali don ko a mafarki ba ta taɓa ganin haka ba.
"Ranka shi daɗe ka buɗe mini yau mun yi babban rashi Fulani Umaima ce ke magana, wayyo Allah Fulani kaico rayuwar duniya zancan banza." Takawa ya ji kalamanta sama-sama, tasowa ya yi ya buɗe ƙofar da sauri Fulani Umaima ta faɗa jikinsa haɗe da fashewa da matsanancin kuka. A ɗan rikice ya dube ta.
"Me yake faruwa da Fulani ta shiga cikin firgici haka."
"Wato ba ma ta Fulanin da ka ji na ambata kake ba kenan, ni dama ai haka nake so." Fulani Umaina ta yi maganar a zuciyarta.
"Ranka shi daɗe Fulani ce babu, Fulani babba ta rasu dai rai ya yi halinsa. Mun rasa Fulani yanzu Jakadiya ke gaya mini mutuwarta." Cak Sarki Abdul'aziz ya yi wani abu na yi masa yaaaammm tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa, ture Fulani Umaima ya yi. "Fulani ba mu san lokacin da muka fara wasa da ku ba! Har rainin ya kai a zo a faɗa mana waɗannan maganganun?" Kalaman Sarki Abdul'aziz suka ratsa ta a lokacin da ya jingina da bango yana jin kansa ya yi masa nauyi kamar zai tarwatse.
"Sarkina ka san tun da nake tare da kai ban taɓa yi maka ƙarya ba, yanzu ƙaryar ma sai na rasa wa zan yi wa sai Fulani babba, dama ana yin ƙarya da mutuwa Ranka shi daɗe?" Wani irin sanyi jikin Sarkin Abdul'aziz ya yi, kamar wanda aka zabura ya fita da sauri duk hanyar da ya bi sai dai Bayi su dinga zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa amma ko kallonsu ba ya yi ballanta ya tanka musu.
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
*Daga jiya zuwa yau na ga ƙorafe-ƙorafe ta pc da cikin group, wasu ma na ji sun ce sun daina karantawa sai sun tabbatar da mutuwar Fulani wasu kuma sun tafi hutu to dai duka a yi haƙuri.*😄
*Kamar yadda kuka sani kowanne bawa fa da kalar tashi ƙaddarar, rayuwa ma'auni ce akwai wanda idan ka dubi rayuwarsa za ka Ubangiji ya yalwata shi da dukiya, 'ya'ya, dangi da duk wani abin more rayuwa na farinciki kuma har ƙarshen rayuwarsa, idan da wata matsala ma a ciki ba mai ɗaga hankali ba ce sai ka ga kamar shi ya tsara wa rayuwarsa haka. Akwai kuma wanda za ka ga Allah ya jarabce shi da talauci, rashin lafiyar 'ya'ya jarabta kala-kala, rashin mahalli da sarausu. Wasu kuma ka ga Ubangiji yana haɗa musu duka biyun.*
*Salon labarin nan na daban ne don na karanta littafai ba ɗaya ba ba biyu ba da zan ga an zalinci kishiya ko dai wani daga ƙarshe shi wanda aka zalinta ya ga ƙarshen wancen, wannan kusan ya zama gama-gari a cikin labarai ko ni na yi haka a ciki AN YA BAIWA CE. Alhalin a cikin duniyar nan akwai waɗanda za a cuta ƙarshe ma ba su san wanda ya cuce su ɗin ba har su mutu, sai dai su waɗanda suka yi abin daga ƙarshe su tona asirin kansu ko kuma sakayya ta bayyana ƙarara, kai wani lokacin ma sai shari'a a wurin Ubangiji. Akwai mahaukaciyar da na sani asiri aka mata ta haukace ƙarshe mota ce ta bige ta ta mutu a cikin haukan, sai 'ya'yanta aka kwashe, ita kenan sai a ce don me ba ta san wanda ya mata asiri ba kuma ba ta ga ƙarshen mai yin asirin ba? Ina san na nusar da cewa ita duniya ba komai kake nema ka samu, don akwai wacce na sani ta shafe shekaru ba ta taɓa haihuwa ba ta fuskanci ƙalubale daga dangin miji har shi mijin kansa, kwatsam ta samu ciki ba ƙaramin buri ta ci a kan cikin ba ƙarshe a wurin naƙuda ta mutu ita sai a ce don me ba ta ga abin da ta haifa ba? Wallahi Reality akwai wata maƙociyarmu da na sani, mijin ba shi da hali sosai ita matar ta yi wankau, sirfau, har gidajen masu hali take bi tana musu wanki daga baya Allah ya fara yalwata mijin a wannan gaɓar ita kuma Allah ya mata rasuwa, ƙarshe saboda iyali mijin aure ya yi kuma ya zama hamshaƙin mai kuɗi kuɗi sai da 'ya'yanta aka ci kuɗin da amarya, kenan sai a ce ita don me za ta mutu a wannn lokaci? Shin dama idan ka yi haƙuri a kan abu dole ne sai ka ga sakamako? Sam ba haka ba ne, akwai abin da za ka ga sakamakonsa wani abin kuma sai dai Ubangiji ya yi maka tukwici a kan haƙurin da ka yi, tun da dama Ya ce shi yana tare da masu haƙuri. Ita rayuwa sai wani ya rasa wani yake samu, kuma mutuwar wani tashin wani ce. A lokacin da wani zai mutu sai ka ga a lokacin ne shaharar wani take bayyana.*
*Masu cewa ya kamata Kamalu ya ji daÉ—in mahaifiya, su kuma 'ya'yan da suke tasowa a gidan Marayu ba su da kowa ya za su yi da rayuwarsu, shin muna tuna irin yanayin da suke ji a zuciyarsu? Ballantana Kamalu ya samu iyayen goyo na gari, masu ba shi kulawa. Wasu fa mahaifiyarsu na haihuwa take mutuwa kuma su taso cikin tsangwama kenan sai a ce don me?*
*Wasu na ganin ana nuna wa Fulani Umaima asirinta na yin tasiri kullin, kun manta duk mai bin bokaye da 'yan tsubbu gani yake a kullin duk abin da ya faru asirinsa ne yake tasiri? Duk fa wanda ya mutu dama lokacinsa ne ya yi sai dai ya kasance da sanadi, abin dariya wasu har cewa suke wai ƙarfin boka fi ƙarfin Allah? Kun manta da hadisin da ke magana akan samuwar bawa tun yana cikin mahaifiyarsa, ana ƙaddara wa Bawa duk abin da zai faru da shi tun yana cikin mahaifiyarsa? Dama can Fulani babba a wannan gaɓar ajalinta yake sai ya kasance da sanadin Umaima, ko ciwo fa wani bai isa ya saka maka ba sai dai idan dama can Allah ya ƙaddari hakan zai faru da kai. Kuma a baya a wurare da dama an nuna asirin nata yana sanyi har Fulani babba ta samu kusanci ga mijinta.*
*Kun saka ni rubutu da farar safiya da dogon sharhin da ban shirya ba 😄 ba fa ku kaɗai kuka ji mutuwar Fulani ba ni ma ta dake ni wallahi, to amma kun san an ce wata shari'ar sai a lahira don haka Fulani dai babu ita sai mu ga Umaima za ta samu yadda take so ko akasin haka? Kuma idan muka bar Fulani Babba ta rayu ai Umaima ta ci banza da yawa😄 ƙarshe sai a ce ta nemi yafiyarta kuma Fulani babba ta yafe? Haba ai gara duka su yi nadama a lokacin da nadamar ba za ta yi amfani ba.*🌚
*Yanzu dai a samu wata ta toyo mana wainar sadaka sai wasu su wakilce ni a rarrabawa maÆ™ota, don yanzu haka makaranta zan tafi.*ðŸ¤
Tamkar raƙumi da akala haka Kamalu ya ci gaba da bin Datijjo Maharaz sai dai babu wanda yake tankawa wani, suna gab da shiga wani soro mai duhu Kamalu ya ji gabansa ya bada rasa! Har sai da ya sa hannuwa biyu ya dafe ƙirjinsa, tun da ya zo duniya bai taɓa jin faɗuwar gaba irin wannan ba. Runtse idanunsa ya yi yana sauke ajiyar zuciya, Dattijo Maharaz ya matsa kusa da shi ya kamo hannunsa na dama.