Sashe 60
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin kalaman Shugaba Zurufu ya sa kan Jakadiya ya sake girma, ta sunyar da kai ƙasa tana sakin murmushin farinciki. A ɓangare ɗaya kuma tana addu'ar Allah ya tsallakar da ita daga mu'amalar da aka ce ɗan autan aljan zai yi da ita. Kamar Shugaba Zurufu ya shiga ranta ya furta mata. "Ban taɓa tsammanin samun biyan buƙatar nan tawa a cikin ruwan sanyi ba, don haka Jakadiya mun ɗauke miki mu'amala da ɗan auta Buguzu. Sannan a daren yau ba sai gobe ba zan fatsama gudanar da aikinki a cikin halwar tsafina." Jakadiya ta sake sunkuyar da kai sannan ta fara zuba masa godiya, wata jar tsoka ya ɗauko ya miƙa mata wacce take ɗigar da wani baƙin jini mai wari. "Ki je ƙarƙashin gidan tururuwa ki binne ta a ciki, bayan kwana biyu ki saurari abin da zai biyo baya." Cikin matsanancin Farinciki Jakadiya ta miƙa hannu za ta karɓa da sauri Shugaba Zurufu ya matsar da hannunsa sai da ya jefa tsokar naman a ciki wata 'yar jakar fatar ya sake miƙa mata. "Kin so ki yi ganganci Jakadiya, da a ce kin taɓa wannan tsokar da duk abin da na yi niyyar ƙulla wa Umaima kanki zai faɗa." A razane Jakadiya ta ja baya, Shugaba Zurufu ya saki murmushi sannan ya Sallame ta. Har ta juya za ta tafi ta dawo da sauri idanunta a kan Basiru ta furta. "Ya kai Shugaba Zurufu shin a ta yaya zan iya mayar da Basiru cikin masarautar Huddam? Ina tsoron kada asirina ya tonu."
"Wannan ba aikinki ba ne Jakadiya! Ki bar mini komai a hannuna ni zan aiwatar da komai." Tsoro ne ya mamaye Jakadiya don sai a yanzu wani tunani ya faÉ—o mata. "Shugaba ina fatan ba za ka hallaka shi ba, domin ina tsoron kada wani abu ya faru da shi ni ma na shiga uku." Jakadiya ta yi maganar a firgice.
"Babu abin da zai faru da shi Jakadiya, kuma kada wannan ya dame ki domin zan aika wani aljanin ya rikiɗe zuwa surarsa ta yadda wani ba zai fahimci ba shi ba ne." Sai a lokacin Jakadiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fice daga kogon dutsen tana jin zuciyart fes tamkar buƙatarta ta gama biya gabaɗaya.
Bayan fitar Jakadiya runtse idanu Shugaba Zurufu ya yi ya fara karanta waɗansu ɗalasuman tsafi, ya ɗan jima yana yi nan take kogon dutsen na shi ya rufe ruf sannan ya zaro littafin yana jin wani shauƙi da farinciki ya lulluɓe shi. Saboda yanayin tsufa hannunsa sai karkarwa yake ya saka hannu ya buɗo littafin nan take ya ga a daidai wurin da Boka Shaddas ya tsaya da karatu. Ya saki malalacin murmushi sannan ya furta. "Tabbas ka rage mini aiki da yawa Boka Shaddas."
A wannan karon ba Kamalu ba hatta sauran mutanen da ke cikin ɗakin tsananin mamaki ne ya kamasu, Sarki Abdul'aziz ne ya yi ƙarfin halin kallon Boka Bamaguje don mafi yawan su ba ƙaramin tsoro ya ba su ba. A zaune yake jikinsa babu kaya sai ƙugunsa da ke ɗaure da wata fatar damunsa, jikinsa a lulkuɓe da gashi kansa zagaye da furfura har zuwa fuskarsa da ta yi buzu-buzu babu kyawun gani. "Dattijo Maharaz, tarin tunanninka sun yi wa kwanyata jerin gwanon da na gagara kunce koda ƙulli ɗaya ne, kuma lura da hakan bai sa ka fasa rikito mini da waɗansu ƙullin da suke sake dulmiya kwanta cikin taikun tunani ba. Wane ne wannan bokan da nake jin yana alaƙanta kansa da iyalina?" Dattijo Maharaz ya sake nuna Umaima sannan ya ci gaba. "A yadda na ji Bamaguje ya furta shi mahaifinta ne, ka ga ƙarin bayani muna saurare daga wurinsu Sarki Abdul'aziz. Amma kafin mu kai ga wannan shin Boka Bamaguje ko ka gane wannan yaron?" Bamaguje ya ƙura wa Abubakar idanu sannan ya saki wata irin dariya har sai da sauran mutanen suka ɗan tsorata.
"Da a ce Umaima ta nuna ƙima da mutumcina a idanun tarin waɗannan mutanen ciki har da Sarki Abdul'aziz, ina ganin da babu abin da zai hana ban lulliɓa mata bargon rufin aziri na wanke ta ba. Amma tun da ta kwaye mini baya ta nemi cin zarafina, babu abin da zai hana ni bankaɗe mata laluben sirrinta kuma daga ƙarshe ko ta ƙi ko ta so na ɗauke ta zuwa kogon tsafina ta dawwama a wurina." Da ace su Sarki Abdul'aziz na ganin yadda zuciyar Fulani Umaima take bugawa da babu abin da zai hana ba su yi tsammanin tarwatsewarta a wannan lokacin ba.
"Wannan yaron tun yana cikin mahaifiyarsa ba baƙona ba ne domin daga shi har mahaifiyarsa, na yi rikitattun ayyuka da dama a kansu. Sannan tsafi ya ba ni nasara don a wancan lokacin zan iya yin komai domin farincikin 'yata Umaima, saɓanin yanzu. A taƙaice dai ni ne na yi asirin da ya kasance shagiri-girbau wato marar hankali." Lokaci ɗaya ɗakin ya ɗauki salati ciki har da Yarima Muhsin da Sailuba. Wani irin tuƙuƙin baƙinciki ne ya turnuƙe zuciyar Sarki Abdul'aziz, a sanyaye ya juya ya ƙura wa Fulani Umaima idanu da ta jiƙe sharkaf da gumi idanunta sauka yi tsilli-tsilli kamar shege a rabon gado.
"Kada ka aminta da abin da ya faÉ—a ranka shi daÉ—e wallahi sharri yake yi mini! Bakinsu É—aya da Dattijo Maharaz so suke su haÉ—a mu da kai. Wallahi-tallahi ban san duk abin da yake faÉ—a ba."
"Umaima shi fa shure-shure ba ya taɓa hana mutuwa! Da tun farko kin mutumta ni ba zan kwaye miki baya ba, kuma wannan ba shi ne karo na farko da kike dagula mini lissafi ba. Don haka Maharaz idan ka gama da ni zan sa a ɗauko mini Umaima mu ƙara gaba."
"Amma dai ku tsinannu ne Allah ya tsine muku albarka. Allah ya isa tsaninmu da ku..." Kalaman Sarki Abdul'aziz suka katse sakamakon matsanancin kukan da ya ci ƙarfinsa. Jikin Kamalu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Ruƙayya da ke gefe ta ƙarasa wurin Takawa ita ma ta saka kuka. Shiru ɗakin ya yi sai sautin kukan da ke tashin yayin da Fulani Umaima ke gefe tsuru kamar an jiƙa ɓera a buta.
"Sarki Abdul'aziz na jima da jin kalmar tsinuwa a kaina, a bakin mahaifiyata na fara jin ta a farkon fara koyon tsafina lokacin da zan haike mata. Ka ga kuwa faɗarka ba za taɓa ɗaɗa ni da ƙasa ba, tambaya ɗaya na yi shin an gama da ni na ɗauke 'yata na yi gaba ko da saura?" Dattijo Maharaz ya jinjina kai don dama ya san dole ranar za ta zo, ranar da Sarki Abdul'aziz zai ji miyagun labaran da za su nemi tarwatsa kwanyarsa. Ya dubi Bamaguje ya furta. "Ba mu gama da ku ba Bamaguje, shin a tunaninka ɗanyan aikin nan da kuka aikata zai tashi a banza ne?" Cikin halin ko in kula Bagauje ya ɗaga kafaɗarsa sannan ya furta. "Zan ci gaba da gudanar da aikina duk abin da ake ciki ina sauraronku, ke kuma Umaima ki saurare ni."
"Wallahi kin yi asara duniya da lahira Umaima, yanzu ke ashe dama 'yar boka ce har kike shuka iskancinki son ranki a gidan nan?" Sailuba ta yi maganar tana wurga wa Fulani Umaima harara.
Dafa kafaÉ—ar Sarki Abdul'aziz Dattijo Maharaz ya yi ya girgiza masa kai sannan ya ce. "A iya sanina kai ba mai raunin zuciya ba ne Abdul'aziz, kai jajirtaccan namiji ne me ya sa yanzu za ka aro É—abi'ar raunanan sarakuna ka yafa wa kanka?"
"Na tuno Fatima ne Dattijo Maharaz! Na tuna irin wahala da ƙalubalen da ta fuskata a wurina sanadin yaron nan. Na tuna irin ɗawainiya da faɗin-tashin da ta yi a kan ganin ya samu lafiya, da tarin burukan da ta ci a kansa. Me ya sa kake tsammanin ba zan koka a kan wannan ba? Fatima ta fuskanci ƙalibalen da har abada ba zan taɓa manta shi ba Dattijo Maharaz." Jinjina kai Dattijo Maharaz ya yi sannan ya furta. "Duk da na aminta da kalamanka, kuka bai cancanta a gare ka ba, don a yanzu haka kana gaban wanda yake buƙatar lallashinka shi gabaɗaya ma bai santa ba, bai taɓa ganinta ba hasali ko ɗumin da kowanne jariri yake ji na mahaifiya bai sani ba. Ya kake tsammanin shi zai ji a zuciyarsa?"
"Wane ne shi? Ban fahimce ka ba Dattijo Maharaz."
Daga bangon ɗakinsa Bamaguje ya furta. "Yaron da ke gefenka! Ina nufin Kamalu abokin tagwaitagar Abubakar. Shi ma ɗanka ne, a ƙiyasi da lissafi shi ne babban ɗanka a maza domin shi ne Fulani babba ta fara haihuwa kafin Abubakar, ina nufin tagwaye ne Hasan da Hussaini. Na san za ka yi mamaki Sarki Abdul'aziz amma ba abin mamaki ba ne idan ka yi la'akari da sunana Boka Bamaguje kuma mahaifin matarka, wataƙila ka ƙaryata kalamaina amma shi Maharaz zai iya tabbatar maka idan ma ƙarya nake ko kuma gaskiya nake faɗa maka."
Zumbur Kamalu ya miƙe tsaye yana kallon Bamaguje da Dattijo Maharaz bakinsa sai motsi yake amma ya gagara furta koda kalma ɗaya ce. "Zauna Kamalu!" Dattijo Maharaz ya furta a taƙaice, bayan Kamalu ya zauna ya ci gaba da ce wa. "Na fahimci yanayin da kake ciki Kamalu, Sarki Abdul'aziz ka tura yanzun nan aje a kira maka Baiwa Inna wuro da Baffajo a sashen Bayi. Wataƙila ganin iyayen da Kamalu ya saba da su ya sa shi samun nutsuwa har ya fahimci duk abin da ake tattaunawa."
Nan take Sarki Abdul'aziz ya aika Yariman Muhsin don ya kira Dogari Ɗan'Sani da ke can bakin ƙofa, da fitar Muhsin babu jimawa sai ga Dogari Ɗan'San ya shigo. Ɗaga lalubensa ke da wuya idanunsa suka sauka a kan Kamalu da ke zaune shiru hawaye na zuba.
"A je a sanar da Jakadiya ta yi gaggauta kawo mana Baiwa Inna wuro da Baffajo." Cikin girmamawa ya amsa sannan ya fice daga É—akin.