← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 86

Sashe 38

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Keee! Zo nan." Fulani Umaima ta kira ta, fuska É—auke da hawaye Maigado ta zube. "Ki mini aikin gafara ranki shi daÉ—e Fulani na cikin wani hali ta aika na kira mata Takawa cikin gaggawa." Sai da Fulani Umaima ta É—an waiga hagu da dama sannan ta furta. "Bayan ke waye ya san da wannan maganar?"

"Daga ni sai Jakadiya, amma ita tuni ta fice ta mu wuri." Maigado ta yi maganar a gaggauce.

"Yau Inna wuro ba ta jin daÉ—i don haka ki wuce ki gyara mini É—akina." A firgice Mai gado ta É—ago.

"Ranki shi daɗe idan na dawo daga wurin Takawa kenan?" Harara Fulani Umaima ta wurga mata kamar idonta zai faɗo ƙasa. "Maza ki wuce idan ba so kike na zartar miki da mummunan hukunci ba." Mai gado ba ta da zaɓi don haka ta miƙe ta wuce sashen Fulani Umaima tana zubar da ƙwalla.

"Mutuwa zan yi don Allah ki kawo mini Abubakar na yi masa kallon ƙarshe." Kalaman Fulani babba suka dawo cikin kwanyarta tamkar a lokacin take furta mata su. Jingina ta yi da bango tana sharce ƙwalla, sannan a gurguje ta ƙarasa aikin tana fitowa ta samu Fulani Umaima a rumfa (Falo) harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya.

"Idan kin kammala ina buƙatar tausa ƙafafuwana tsami suke yi." A wannan karon Mai gado amsawa ta yi a hankali don ta fahimci inda Fulani Umaima ta dosa. Sai bayan lokaci mai tsawo sannan Fulani Umaima ta sallami Mai gado, cikin zuciyarta tana yin dariyar ƙeta don ta san haƙarta ta kusa cim ma ruwa.

Cikin sauri a ɗan gurguje Mai gado take buga ƙauren Takawa, sakamakon ta yi dace sashen na shi shiru babu Fadawa a ciki.

Ta jima a tsaye har tana shirin juyawa ta ji Mai martaba ya buɗe, da sauri ta zube a ƙasa tana haki. "Allah ya taimake ka ya baka yawan rai, Fulani babba na son ganawa da kai..." Tun ba ta rufe ba ki ba ya katse ta a tsawace.

"Ba ma son shashanci a matsa daga gabanmu a ba mu wuri idan ba haka ba za mu ɓata muku rai. A ce mata ta yi haƙuri zuwa dare za mu ƙaraso ɗaki mu ji abin da yake damunta." Daga haka ya rufe ƙofar ba tare da ya sake jin ta bakinta ba.

Hannuwa biyu ya sa ya dafe kansa yana jin damuwa na mamaye shi.

"Shin abin da na ji daga wurinsu Inna wuro ne ya tsaye mini a rai ko mene ne?" Kamalu ya tambayi zuciyarsa.

"Ba tun yau na so sanar da kai ɓoyayyun sirrikan da ba ka san da su ba, na jima da fara yi maka hannunka mai sanda amma na lura har yanzu ba ka ankare da ni ba. Kada ka ji ɗaci don sun sanar da kai gaskiyar abin da suka sani, su ba iyayenka ba ne kamar yadda suka sanar da kai. Sai dai ya zama dole a jinjina musu sakamakon namijin ƙoƙarin da suka aiwatar game da rayuwarka..."

"Ya aka yi kasan waÉ—annan kalaman, alhalin daga ni sai su muka tattauna su? Me ya sa a kullin kake neman dulmiya ni cikin kogin tunani? A yanzu haka zuciyata ta yi nisan kiwo wurin zabarin mafitar da za ta dasashen É—acin da ke cikin zuciyata. Na jima ina É—ora ayar tambaya akanka amma wani tsagin na zuciyata na gargaÉ—ina a kan abin da nake zargi." Kamalu ya yi maganar cikin damuwa.

Dattijo Maharaz ya dawo gaban Kamalu yana murmushi, "Na so a ce ka jima da faÉ—awa kogin tunani akaina, sai dai yanzun ma ba a makara ba, duk zargin da za ka yi ina son ka yi shi a kan zato na alkairi." Shiru Kamalu ya yi bai tanka masa ba yana nazartar kalamansa.

"Ka biyo ni zan wuce da kai ta wani sirrintaccan zaure matuƙar ka amince mini a yau zan sanar da kai ainihin wane ne ni da alaƙata da wannan Masarautar." Kamalu kamar ba zai bi shi ba sai zuciyarsa ta ingiza shi suka fara tafiya kai tsaye suka nufi babban sashen Sarki Abdul'aziz ta ɓangaren sashen da yake makwaftaka da su Ciroma da Galadima.

Cikin matsananciyar damuwa Maigado ta koma sashen Fulani babba a lokacin Abubakar yana kwance yana yin gwarancinsa, kallonsa ta yi zuciya a karye ta faɗa ɗakin Fulani babba. Daga can gefenta ta tsugunna ta ɗora hannunta a saman na Fulani babba, "Allah ya taimake ki na je Takawa ba ya nan." Ta samu kanta da sauya kalaman saɓanin abin da Mai martaba ya gaya mata. Hawaye ta gani na gangarowa daga idanun Fulani babba, Mai gado ta sunkuyar da kai ƙasa hawaye na zuba. Wani tunani ta yi da sauri ta ƙarasa ta samu Baiwa Zainaba suka shiga ɗakin Abubakar suka fito da shi hannuwansa ɗauke da mari, ɗakin Fulani suka shiga da shi Mai gado ta zaunar da shi a gefen gadon da take kwance. Da ƙwayar idon Fulani babba suka lura da irin kallon da take bin Abubakar da shi hawayen idanunta na sake ƙaruwa. Hannu ya kai saman fuskarta yana jijjigawa yana dariya, take Mai gado da Zainaba suka fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Sororo ya yi ya fara kallonsu bayan wani lokaci ya sake kai hannu kan hannun mahaifiyarsa yana ɗago ta alamar ta tashi. Motsa baki ta fara yi Mai gado ta matsa gabanta da sauri ta kara kunnenta a wurin bakin Fulani babba.

"Ga Abubakar nan...don Allah ki kula mini... ki kula mini da shi... Duniya da Lahira... na mallaka miki shi... Mai gado mutuwa zan yi, ƙirjina ciwo yake ki danne mini shi." Cikin kuka Mai gado ta sa hannuwa biyu ta danne ƙirjin Fulani babba.

"La'ilaha'ilallahi... Muhammandur... Rasulillah..." Fulani Babba ta furta cikin sarƙewar murya idanunta a kan Abubakar numfashinta ya fara yin sama daga ƙarshe ya ɗauke.

"Ranki shi daɗe! Ranki shi daɗe!" Mai gado ta furta a firgice tana jijjiga Fulani babba, a sanyaye Baiwa Zainaba ta ƙarasa ta rufe wa Fulani babba idanu haɗe da jan zani ta rufe mata fuska. Daɓar ta zauna a gefen gado kamar haɗin baki ita da Mai gado suka rushe da wani irin sabon matsanancin kuka.

"Mai gado duk ranar da na ga Abubakar ya warke sai na 'yanta ba yi goma, kuma sai na raba dukiyata biyu na bayar da ita sadaka."

"Mai gado kin san rannan mafarki na yi wai Abubakar da Yaya Halima sun warke, kin ga dai a cikin mafarki ne amma wallahi kar ki ji farincikin da na ji."

"Da Allah ya sa Abubakar lafiyayye wallahi babu abin da zai hana ban haÉ—a shi aure da Jawahir ba, saboda jin Jawahir nake tamkar 'yar cikina."

"Tsakanin ke da Abubakar ban san wanda ya shiga tsakanina da 'yata Jawahir ba, ta shafe kwanaki ban ganta ba an ya Mai gado ba a matsa wa Jawahir da aiki kuwa?"

"Wani abu ne yake damuna Mai gado, na san dai da ina raye da ba na raye Allah ne yake kula da Abubakar amma duk ranar da ƙasa ta rufe idona ban san yadda rayuwar Abubakar za ta kaya ba." Mai gado ta sake rushewa da matsanancin kuka sakamakon tuno ire-iren kalaman da Fulani babba take yawan furta mata a duk lokacin da suke zaune suna attaunawa.

"Kai wai mene ne yake faruwa kuka cika mana gida da kuka kamar masu zaman makoki..." Kalaman Jakadiya suka katse sakamakon ganin Fulani babba a lulluɓe, babu wanda ya tanka mata don haka ta ƙarasa bakin gadon ta yaye zanin da aka rufe ta, hannu ta kai saman ƙirjinta a razane ta ja da baya.

"Mai gado me yake faruwa?"

"Babu Fulani babba, Jakadiya mun rasa Fulani wayyo Allahna!" Rass ƙirjin Jakadiya ya buga, ta jingina da bango wata irin zufa na tsattsafo mata. Da sauri ta fice daga ɗakin kai tsaye ta wuce sashen Fulani Umaima.

"To Fulani Umaima shi kenan ƙurunƙus! Ta faru da ƙare an yi wa mai dami ɗaya sata. Burinki ya cika Fulani ta bar miki duniyar sauran abin da ta bari sai ki haɗa ki cinye." Jakadiya ta furta wa Fulani Umaima da ke harɗe a kan kujera. Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta shi kenan muradi da burinta zai ka ga ciki, amma a fili sai ta furta.

"Jakadiya ya kamata ki iya zarge limzamin harshenki idan ba haka watarana za ki yi ɓarin zancan da zai kai ki ga turnar danasani. Ko Fulani ta so ko kar taso idan lokacin tafiyarta ya yi sai ta je, Allah ya jiƙanta ya gafara sai ki sanarwa Takawa a yi a binne ta kin san jinkirin gawa yana kawo ƙwanƙwamai cikin gida. Haka kawai su dinga firgita mu da tsakar dare, muna kasa fita fitsari."

Kasaƙe Jakadiya ta yi tana sake jimanta tsantsar rashin imanin Fulani Umaima.

"Wacce irin ƙeƙasasshiyar zuciya gare ki Umaima?"

Fulani Umaima ta saki murmushi cike da izza, isa da ƙasaita. Sai da ta zagaye Jakadiya ya kai sau biyar sannan ta furta.

"Tambayar da a kullin nake wurga wa zuciyar tawa kenan amma har yau ta gagara nusar da ni alƙibikarta, abu ɗaya na sani dangane da kaina Jakadiya." Sai da ta koma kan kujerarta ta zauna, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ta ce.

"Duk wani abu da nake so nake ƙauna to zai kasance nawa ni kaɗai har abada, ina da matsanancin kishi ba iya a kan mijina ba. Dalilin da ya sa nake kawar da duk wani abu da nake ganin zai zame mini shamaki a gabana, Jakadiya ba zan tsawaita miki ba amma ke kanki kin san Umaima ba kanwar lasa ba ce. Lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi idan kin so ki kira ni da suna cinnaka ban san na gida ba. Ki ci gaba da shiri Jakadiya kada ki fasa domin kwanciyar kura ba shi ke nuna yin nasara a kanta ba."
Chapter 38 · 0% Book details