← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 86

Sashe 62

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da suka fara tafiya tsakanin Fargi da Sulaiman babu wanda ya tanka wa ɗaya daga ciki, kallo ɗaya idan ka yi wa Fargi za ka fahimci matsanancin tsoron da take ciki. Har sun kusa fita titi ta waigo a hankali ta furta. "Haka kawai nake jin zuciyata tana bugawa, bugawar da ke alamta mini wataƙila wani al'amari ya faru a cikin zuri'ata."
"Saboda me kike tunanin haka bayan kin ɗinke duk wata ɓarakar da Shugaba zai iya gano halin da muke ciki?" Sulaiman ya furta yana ɗan dakatar da dokin da suke kai.
"Na fi kowa sanin waye Shugaba Zurufu! Na san bibiya da hatsabibancinsa, jikina yana ba ni zai iya bankaÉ—a labulen sirrina ko ba yanzu ba, kar fa ka manta ni ce mace ta farko da na auri É—an wata zuri'ar da ba tawa ba, shi ya sa..." Sarki Sulaiman ya katse ta.
"Ni kuma ina ji a jikina babu wani abu da zai faru da mu In shaa Allah."
"Me ya sa kake da ƙwarin gwiwa idan ka ambaci abin bautarku?" Ta wurga masa tambay.
"Saboda na gasgata Shi a matsayin Ubangijin sammai da ƙassai." Ajiyar zuciya ta sauke ba tare da furta komai ba, sannan ya kaɗa linzamin dokinsa suku fara tafiya. Da fara tafiyarsu babu jimawa sai Fargi ta rikiɗe zuwa surar Tantabara ta ɗane saman kafaɗarsa har suka ƙarasa cikin Masarautarsu.

Shigar Sarki Sulaiman tare da tantabarar da ke kafaɗarsa ya sa kallo gabaɗaya ya koma kansa, duk da ya san Fargi ba za ta ba shi kunya ba amma sai da ƙirjinsa ya buga yana tsoron kada a gane abin da yake tare da shi.
"Jarumin Sarakai daga ina ka samu kyautar wannan kyakkyawar tantabarar da ke kan kafaɗarka? Ta yi matuƙar birge ni ka san ni da son tsuntsaye." Mahaifiyar Sarki Sulaiman ta furta a lokacin da ya shiga sashenta ya gaishe ta. Cikinsa ne ya karta don lokaci ɗaya ya ji kansa ya kulle, "Amm... dama.. wani abokina ne ya... mini kyautarta ɗazu." Jinjina kai ta yi sannan ta ɗan haɗe fuska babu alamar wasa.

"Sulaiman!" Ya ɗago a sanyaye don ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi, ya san maganarta ba za ta wuce a kan matansa ba ne. "Yau kwana huɗu da ɗaurin aurenka amma babu wani bayanin farinciki da Jakadiya ta sanar a masarautar nan, kasan dai gabaɗaya idanun masarauta yana kanka ko?" Sai da ya ɗan waiga ya dubi Fargi da ke cikin siffar tantabar, ya ɗan sunkuyar da kai ƙasa yana jin babu daɗi sannan ya ce. "Allah ya taimake ki kin san tun kafin auren nan ba ni da lafiya, yanzu haka ƙafafuwana ne suka riƙe mini shi ne na ɗan zaga bayan gari. Amma In shaa Allahu za a yi abin da ya dace." Amsa masa ta yi sannan ya yi mata sallama ya fice. Kai tsaye turakarsa ya ƙarasa, tun bai ƙarasa shiga ba ya kira Jakadiya ya gargaɗe ta akan baya buƙatar ganawa da kowa har zuwa wayewar gari.

Inna wuro na kai idanunta kan Kamalu da sauri ta ƙarasa wurinsa ta riƙo shi idanunta na zubar da ƙwalla, kamar ƙaramin yaro haka ta fara tattaɓa fuskarsa tana duba jikinsa cikin kuka ta furta. "Kamaluna ina ka shiga? Babu dai abin da yake damunka ko yake yi maka ciwo?" Kamalu ya sake lafewa a jikin Inna wuro tamkar wani zai ƙwace shi, ya ɗaga kai yana kallon Baffajo ya ce. "Inna don Allah ki daina kukan nan kowa yana kallonki." Maganar Kamalu ta so ba wa Dattijo Maharaz dariya, jin yadda Kamalu yake maganar a shagwaɓe.

"Baffajo bismillah zauna." Sarki Abdul'aziz ya faÉ—a.

Jakadiya na ganin kamar hankulan mutane ba ya kanta ta juya har za ta fita Bamaguje ya katse ta. "Maharaz ka dakatar da Jakadiya za ta ba da shedata." Kallon da Sarki Abdul'aziz ya wurga mata ne ya sa jikinta ya yi sanyi gabanta ya ci gaba da faɗuwa, ta koma tsumu ta zauna. Tun da Jawahir ta leƙo cikin ɗakin Yarima Muhsin ya kasa zaune ya kasa tsaye, wani irin bugu zuciyarsa take yi tamkar za ta yi tsalle ta faɗo daga ƙirjinsa. Idanunta a saman fuskar Kamalu ta sake jingina a jikin ƙofar ɗakin, haka kawai ta tsinci kanta da shiga farincikin da ita kanta ba ta san dalili ba, duk da Kamalu ya kasance abokin faɗanta. Kamalu da har lokacin yake gefen Inna wuro ya ɗago ya wurga mata harara ganin haka ya sa Jawahir ta fara juya idanu tana yi masa fari haɗe da murguɗa baki.

"Jawahir!" Dattijo Maharaz ya furta da ɗan ƙarfi, silar haka ya sa ta ɗago da sauri; karaf idanunsu suka haɗu da juna. Ƙuri ta yi tana kallon ƙwayar idonsa wani irin yanayi ya fara ratsa ta, ƙirjinta ya shiga bugu da sauri fat fat fat. Tana shirin juyawa ya dakatar da ita. "Ki ƙarasa ki aiwatar da aikinki." Tun bai rufe bakinsa ba Jawahir ta faɗa cikin ɗakin, tafiyar da ƙafafuwanta suke yi take son dakatarwa amma tamkar wacce ake fusga haka ta ji ana yin gaba da ita.

Tamakar kazar da aka jiƙa da ruwan zafi haka Jakadiya ta ƙarasa gefe ta zauna jiki a saluɓe, a madadin aljanin da ke ɗauke da surar Basiru ya koma ɓangaren da Fulani Umaima take sai ya zauna a gefen Jakadiya, suna haɗa ido da Dattijo Maharaz ya yi saurin sunkuyar da kai ƙasa.

"Buguzu! Me kake yi a wurin nan?" Dattijo Maharaz ya tambaye shi. Buguzu ya sunkuyar da kai ƙasa sannan ya furta. "An dakatar da matata ya za a yi na tafi." Take cikin Jakadiya ya ɗuru ruwa, fargabarta ta ninku gumi ya ci gaba da keto mata.

"Wace ce matar taka?" Dattijo Maharaz ya tambaye shi da sauri don a tsammaninsa Jawahir yake nufi. Buguzu ya ɗago ya nuna Jakadiya ya ci gaba da cewa. "Ga amaryar tawa nan, na ga kun dakatar da ita a hakan ma ɗaga muku ƙafa na yi don akwai babban uzurina da zan aiwatar a daren nan." A razane Jakadiya ta ja baya cikin tashin hankali, har tana faɗawa kan Sailuba ba ta sani ba. "Wallahi ni ba matarka ba ce, ba za ta taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa."
"Basiru kana cikin hankalinka kuwa? Jakadiya ce a gabanka idan muka ji makamamciyar wannan maganar ranka zai yi mummunan ɓaci." Sarki Abdul'aziz ya tsawatarwa Buguzu a tsammaninsa Basiru ne.

"Wannan fa ba Basiru ba ne Sarki Abdul'aziz! Wannan ɗan autan aljani ne rikiɗa ya yi kamar yadda ni ma na rikiɗe zuwa wannan surar." Inna wuro da Baffajo a tsarace suka dube shi, lokaci ɗaya suka yi firƙai-firƙai da jin kalamansa.

"ÆŠan autan aljan fa kace Dattijo Maharaz? Basiru fa nake nufi da yake gefen Jakadiya." Mamaki ya sake bayyana a fuskar Sarki Abdul'aziz bayan ya je wa Dattijo Maharaz tambaya.
"Ni ma shi nake nufi Sarki Abdul'aziz, amma mu je zuwa mahaukaci ya hau kura za ka tabbatar da zancena."

Jawahir na shiga cikin ɗakin ta ji wani irin dum! Tamkar an buga mata guduma a kanta, hannuwa biyu ta sa ta toshe kunnuwanta sai da ta daina jin kuɗar ta cire hannunta. Wata irin ƙara da ƙaraji ta fara ji a wurin rijiyar, a ɓangare ɗaya kuma wani sauti ta ji yana ambatar sunanta sa wata irin murya. A hankali ta ƙarasa bakin rijiyar, ta ɗaga rigarta take tambarin cikinta ya sake fitowa raɗau ya yi jajir, haskensa ya mamaye saman rijiyar tamkar an dasa ƙwan fitila. Hannunta ta kai saman cikinta duk da tana jin ɗumin zafin da ke fita daga cikin tambarin bai sa ta sauke hannunta ba, wata irin ƙara ta sake jin an ƙwallah ta sake kai idonta kan rijiyar da wani baƙin hayaƙi ya fara fitowa. Sauke hannunta ta yi ta sa iya ƙarfinta ta buɗe rijiyar nan take wani irin ƙauri da baƙin hayaƙi ya mamaye ɗakin.

Tamkar yadda gajimare yake ƙara haka ilahirin mutanen da ke cikin ɗakin suka fara jin wani irin rugugi, tamkar aradu za ta faɗo musu a tsakar ka. Jawahir ta sauke rigarta sannan ta fito daga ɗakin zuwa rumfa wurin da su Fulani Umaima suke zaune. A wannan karon Fulani Umaima jikinta ya jiƙe sharkaf da gumi, ga wani irin karkarwa da jikinta yake yi saboda matsanancin tsoron ganin yanayin da za ta yi tozali da Baiwa Maimuna.

"Wace ce ita Dattijo Maharaz? Me ta aiwatar a ɗakinmu wanda ya sababba wannan rugugin da baƙin al'amura? Shin ko ita ma tana daga cikin zuri'arka ne?" Sarki Abdul'aziz ya yi tambayar a ɗan ruɗe, don lamarin abin da yake faruwa ya daina ba shi mamaki tsoro yake ba shi.
"Ko kaɗan ba ta daga cikin zuri'armu Sarki Abdul'aziz, bil'adam ce tamkar kai. Hasali ma wannan yarinyar a shekarin baya mun taɓa tattaunawa a kanta, idan har ba ka manta hirar da muka yi a kan zuri'ar Rumzu da ake shayarwa da Manyan shanu duk ranar juma'a ba." Sarki Abdul'aziz ya mayar da kallonsa wurin Jawahir da ke tsaye a gefe ƙyam, daga bayanta suka fara jin wani irin taku ƙwas kwas kwas tamkar ana taku da takalmi mai tsini. Sautin ba ƙaramin jam hankulan mutanen wurin ya yi ba don haka suka mayar da kallonsu, ita kuwa Jawahir ko motsi ba ta yi ba idanunta sauke a kan Fulani Umaima. Tafe take idanunta a ƙwaƙƙwaƙwale, duk taku ɗaya idan ta yi sai wata irin baƙar ƙura da yana ta faɗo daga jikinta. Kayan jikinta duk sun yi baƙi ga wani irin gashi buzu-buzu da ya lulluɓe ilahirin jikinta. Kallo ɗaya idan ka yi mata ba za ka taɓa tsammanin hallitar bil'adam ba ce sakamakom yadda surar jikinta ta sauya, ganin tana tun karo su ya sa gabaɗaya mutanen rumfar suka miƙe hankali tashe ciki har da ita kanta Fulani Umaima da ta fi kowa shiga tashin hankali.

"Shi kenan ƙurunƙus! Ta faru ta ƙare an yi wa mai dami ɗaya sata." Bamaguje ya furta yana tafe hannuwansa haɗe da miƙewa tsaye.
Chapter 62 · 0% Book details