Sashe 44
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da na sauke ajiyar zuciya ina mamakin wannan murÉ—aÉ—É—an labarin da Sarki Hafiz yake ba ni sannan na furta masa.
"Amma wannan labarin da kake ba ni kana ganin zai ɗauki shekara nawa? Kuma ya aka ƙarke tsakanin mahaifiyata da ɗan gidan Aljani Darri? Ya aka yi mahaifina ya yi galaba a kan mahaifiyata har ya tarwatsa soyayyar da ke tsakaninsu wacce ka ce tuni mahaifiyata ta damƙa wa Ɗan autan aljani wuƙa da nama na soyayyarta?" Murmushi Sarki Hafiz ya sakar mini, yayin da Fuskar Fulani Hawwa kulu take a tamke kamar magaribar ɗinya.
"Me kike ci na baka na zuba ne Hidaya? Ai duk gaggawar kwarto ya jira mai gida ya gusa kuma duk gaggawar ungozoma ta bari a haife." Murmushi na sakar masa sannan na ji ya ci gaba da cewa.
"An sha gwagwarmaya matuƙa tare da baƙin artabu kafin auren mahaifiyarki da mahaifinki, kuma tun lokacin da aka ɗaura auren iyayenki ƙofofin bala'i da na masifa suka fara buɗewa a cikin masarautar nan. Sannan kuma babu takamaiman adadin shekarun da zan iya sanar da ke domin ni kaina Kakana bai sanar da ni ba, abu ɗaya na sani shi kansa Kakana yau kimanin shekararsa ashirin da biyar kenan da mutuwa, kuma labarin auren mahaifiyarki zai iya kai wa tsawon shekaru talatin kenan tun da a bayanta an yi sarakunan da suka shuɗe."
A hargitse na dube shi cike da matsanancin mamaki har sai da ya gane mamakina ƙarara a fili, "Me kake shirin sanar da ni Sarki Hafiz? Da bakinka ce iyayena babu wanda ya fito daga cikin jinsin jinnu, amma kuma ya aka yi na kasance mai ƙarancin shekarun da ko sha biyar ban kai ba. Shin ya aka yi haka ta faru? Yanzu haka ina mahaifana? Me ya sa ba sa cikin masarautar nan?"
Boka Shaddas ya rufe littafin haɗe da kallon ƙofar kogon tsafinsa, sakamakon jin maganar wata baƙuwarsa da ta kawo masa ziyara. Bai amsa mata ba sai da ya ƙarasa har wurin da kayan tsafinsa suke sannan ya jefa littafin cikin wata ɓaƙar tukunyar ƙasa nan take littafin da tukunyar suka ɓace ɓat.
Lokacin da Fulani Umaima ta ƙarasa ƙofar ɗakin Takawa babu abin da yake tashi sai kukan tsintsaye da ƙananan dabbobi, cikin sanɗa ta ɗan bankaɗa labulen ɗakin sannan ta hura maganin hannunta. Komawa ta yi ta tsaya tana kallon abin da zai faru don ba taa yi tsammanin abin da Basiru ya faɗa zai tabbata ba, a hankali ta ga Sarki Abdul'aziz da Mai martaba sun fara hamma babu jimawa kowannensu ya ɓungire bacci ya yi awon gaba da su. Wani uban tsalle Fulani Umaima ta buga cikin farinciki ta faɗa ɗakin, sai da ta rufe ɗakin ruf sannan ta ƙarasa wurin da gawar Fulani babba take kwance sannan ta fara kunce ɗaurin da ke wurin ƙafafuwanta. Kafin wani lokaci tuni ta ware likkafanin cikin farinciki ta ciro wannan ɗaurarriyar fatar wurin Bamaguje ta tura mata a cikin ƙasanta, nan take gawar ta fara wani irin karkarwa sannu a hankali wani baƙin hayaƙi ya fara fita daga jikinta yana bi ta ƙofar yana fita kai tsaye hayaƙin ya wuce sashen Sailuba. Kamar yadda Bamaguje ya gaya mata sai da hayaƙin ya gama fita sannan Fulani Umaima ta mayar da likkafanin ta ɗaure ba tare da ta cire wannan ɗaurarriyar fatar ba. Ta karkaɗe jikinta sannan ta fice daga ɗakin, tana jin ta tamkar ta riga da ta gama da matsalolin gabanta na duniya gabaɗaya.
Tun daga tsakar gidanta ta fara cin karo da kayan ɗakinta a warwatse tamkar zaratan jarumai goma ne suka yi dambe a wurin, ƙirjinta ne ya yi wata irin bugawa nan take jikinta ya ɗauki karkarwa tamkar mazari. Kamar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Fulani Umaima ta shiga ɗakin jiki a saɓule tana fatan kada Allah ya sa zarginta ya tabbata da take yi a kan Basiru, cak ta tsaya wuri ɗaya tana jin wani irin abu yana mamaye tsarga mata tun daga tafin ƙafarta har zuwa tsakiyar kanta sakamakon hango akwatin ƙarfenta da ta yi a yashe a ƙasa, komai ya tarwatsa da alama babu komai a cikinta. Kamar wace take jin tsoron taɓawa haka ta ƙarasa a ɗarare, ta zauna daɓar irin zaman 'yan bori a ƙasa hawayen da ta rasa na mene ne ya fara bin kuncinta.
"Allah wadaran hali irin naka Basiru! Ban san ya zan yi da kai ba wannan wanne irin yaro ne mai taurin kan tsiya."
"Ummi me yake faruwa?" Muhsin ya furta daga bakin ƙofa. Jin tambayar Muhsin ya sa ta fashe da kuka tana jin zuciyarta na zafi. Mamaki ne ya kama Muhsin ya bi ɗakin da kallo sannan ya ƙarasa gaban mahaifiyarsa, a sanin halin mahaifiyarsa ya san rasuwar Fulani Babba ba zai ɗaga hankalinta har ta aikata wa ɗakinta haka ba.
"Muhsin ƙaninka ya zame mini alaƙaƙai dubi yadda ya yi mini da ɗaki, ni ya raina ni ba zan taɓa yin magana ya saurare ni ba." Ajiya zuciya Muhsin ya sauke sannan ya furta, "Ummi sai dai fa ki yi haƙuri, amma daga ni har 'yar uwata babu mai hali ko ɗabi'a irin na shi. Kin san kowanne yaro da yadda Allah ya halicce shi wataƙila nan gaba zai daina."
"Sai yaushe Muhsin? Yaushe kake tunanin Muhsin zai kintsu, rannan fa kamar ya ɗaga hannu ya dake ni." Jin haka ya sa Muhsin ya ɗan taɓe baki. "Ina Ruƙayya?" Ya wurga mata tambaya.
"Na haɗa ta da baiwa Inna wuro." Fulani Umaima ta yi maganar tana ruƙo hannun Muhsin.
"Muhsin ina jin tsoron ganin girman ƙaninka domin a yanzu ko shekara sha huɗu ba bai yi ba, amma ya gagare ni..." Ihun da Muhsin ya yi ne ya katse ta, ya matsa baya yana yarfe hannu cikin azaba. "Me ya faru Muhsin? Lafiyarka kuwa?"
Wani irin kallo yake bin mahaifiyarsa da shi, jiki a sanyaye ya jingina da bango nan take ta ga idanunsa sun ciko da ƙwallah. A tsarace ta kalle shi don ta san abin da zai sa Muhsin ƙwallah ba ƙaramin abu ba ne.
"Ummi!" Ya ambata da wani irin yanayi, Fulani Umaima na shirin amsawa ya ci gaba da cewa.
"Ta shammaci zuciyata a lokacin da zuciyar tawa ta sakankance a nisan kiwon da za ta yo kalacin abin da za ta ciyar da kanta, ta mamaye gangar jiki da ruhina a lokacin da ban yi zato ba. Kwatsam soyayyarta ta mamaye ni har ta kai komai da kowa na gudurata idan ba tunaninta ba, babu zato soyayyarta ta kewaye duniyata, ta ruhin da nake taƙama da shi. Ruhin da a kullin yawon zabarin nemanta yake ko zai yi tozali da ita domin ya samu sauƙin zugi da raɗaɗin da ke tare da shi, sai da kash! Da alama ban yi dacen ajiye ƙwarya a gurbinta ba, ban santa ba ban san asalinta ba. Ni dai abu ɗaya kawai na sani ina sonta, ina ƙaunarta! Ina jin ta a cikin jiki, zuciya da hantata. Ba na jin zan ci gaba da rayuwa matuƙar babu ita, a duk bugun numfashina yana fita ne tare da kewa, bege da ƙwadayin tozali da ita." Fulani Umaima sakin baki da hanci ta yi cike da mamaki tana kallonsa, lokaci ɗaya kuma tsoro ya kamata don tana gudun kada wata ta asirce mata ɗa don ko akuyarta ba za ta bari a asirce ballantana Yarima guda mai jiran gado.
"Wace ce ita?" Fulani Umaima ta tambaye shi a taƙaice.
Idanu cike da ƙwallah ya furta, "Ban santa ba! Ban san wace ce ita ba a cikin gidan nan! Ganin da na yi mata na biyu shi ne wannan abin da ya faru da ni." Muhsin ya ƙarasa maganar yana nuna wa mahaifiyarsa hannunsa, ganin yadda hanunsa ya kwaile ya ƙone da wuta ya sa ta miƙe zumbur.
"Waye ya yi maka haka?"
"Ina tsammanin ba mutum ba ce!" Muhsin ya furta a sanyaye.
"A ina take?" Fulani Umaima ta sake wurga masa tambaya, nan take Muhsin ya zayyanewa mahaifiyarsa duk abin da ya taɓa faruwa tsakaninsa da Jawahir, shiru ta yi tana nazari sannan ta sake kai idanunta kan hannuwan Muhsin. "Tashi ka je duk abin da yake faruwa zan kamo bakin zaren, mu bar wa zuwa wayewar gari ka san Mahaifinka a yanzu yana cikin halin jimamin rashin matarsa. Amma mu yi haƙuri zuwa ɗan wani lokaci. Muhsin ya miƙe jiki babu ƙwari har ya zai fita ya hangi wani ƙaramin ƙoƙon kan mage, da mamaki ya tsugunna ya ɗauke yana juyawa.
"Me ya kawo wannan abin cikin ɗakin nan?" Rass! Gaban Fulani Umaima ya faɗi. "Za ta iya yuwa ɗan'uwanka ne ya shigo da shi, ba ni nan idan ya dawo zai mini bayanin dalilin da ya sa ya kawo mini shi ɗaki." Fulani Umaima ta yi maganar tana karɓar ƙoƙon kan magen da ke hannunsa wanda Bamaguje ya taɓa ba ta da jima ta saƙalewa a kusurwar ɗakinta.
Tun da Muhsin ya fita Fulani Umaima ta saka zaune ta kasa tsaye, damuwa goma da ashirin ta cunkushe zuciyarta. Ta rasa wacce za ta fara magancewa, matsalar Basiru da ke neman gagare mata ko ta littafin da ya ɗauke mata? Ko kuma ta wurin Yarima Muhsin da ta lura ana neman zautar da shi ta ƙarƙashin ƙasa.
"Galadima ko Ciroma." Ta furta a fili. "Na tabbata cikinsu akwai mai niyyar salwantar mini da rayuwar Yarima, kuma har abada ba za su yi galaba a kaina ba matuƙar ina da Bamaguje a faɗin duniyar nan." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar cikin cin alwashi.