Sashe 72
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da haka ta faru daga Ruƙayya har Kamalu da Abubakar Mai gado ce ke kula da al'amuransu, wannan ta sa Jawahir ta fara rage shiga sashen don babu shigar da za ta yi ba tare da wani faɗa ko yamutsi ya shiga tsakinsu ba. Shi kuwa Muhsin dama ko da wasa bai taɓa saka ƙafarsa sashen ba, don har lokacin yana ɗan jin zafin Kalamu don gani yake silarsa ce komai ya tarwatse ya watse musu.
Mai martaba tare da 'yan uwan Fulani babba a gajiye tuɓus suka koma gida, kallon fuskokinsu kaɗai zai tabbatar maka da ƙunsassun labaran da suke tafe da su. Sai dai kuma ƙarin wani farinciki tun mai martaba bai shiga cikin gida ba, ya samu kyakkyawan albishiri ɗin samu lafiyar Yaya Halima daga ciwon haukan da take yi shekara da shekaru. Saboda tsabar farinciki Takawa da kansa ya nufi ɗakin da Yaya Halima take zaune, jikinta duk a sanyaye ta bishi da kallo har ya ƙarasa gabanta. "Halimatuna wai da gaske kin samu lafiya?" Hawayen da take maƙalewa suka samu sukunin ɓallewa, ta rushe da matsanancin kuka haɗe da faɗa wa jikinsa."Ranka shi daɗe wai ni ce na yi ciwon hauka? Kai ma ka yarda a baya na yi ciwon hauka?" Ajiyar zuciya ya sauke, ya sa hannuwa biyu ya zaunar da ita sannan ya furta. "Halimatu ba na son rigima, don Allah ina son ki kwanta ki huta zuwa dare zan zauna mu tattauna da ke." Gyaɗa masa kai ta yi ya muƙe ya fice daga ɗakin. Kusan gabaɗaya iyalansa ya tara a babbar rumfarsa suka shiga mayar da abin da ya faru tun daga farko har ƙashe. "Ranka shi daɗe ba ƙaramin mamakin abin da ya faru da yarinyar nan muka yi ba. Baiwa Zahra'u ta kai mata abinci za ta fito kenan ta ji ta ƙwallah wata irin ƙara, ta shiga kururuwa kamar za ta tayar da gidan, da ƙyar muka samu aka rirriƙe ta kawai sai gani muka yi yarinya ta fara wata irin zabura tana karkarwa. Daga nan kawai sai gani muka yi ta yanke jiki ta faɗi, bayan an zuba mata ruwa ta farfaɗo sai gani muka yi tana bin mu ɗaya bayan ɗaya tana kallo. Daga haka ta fara wurgo mana tambayoyi har dai muka fahimci ta dawo hayyacinta." Fulani Sadiƙƙa kishiyar Mahaifiyar Fulani babba ta yi maganr cikin farinciki. Ita ce matar mai martaba ta huɗu. Mai martaba ban da murmushi babu abin da yake, "Tabbas addu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza kuma duk abin da ka yi haƙuri za ka ci ribarsa. Allah ya sake shiga tsakanin na gari da mugu." Gabaɗaya suka amsa masa da Amin. Bayan ya sallame su ya bada umarnin a yi gumba, ƙuli-ƙuli da tuwon sadaka domin godiya ga Ubangiji bisa waɗannan abubuwan farinciki da na akacin haka da ya same shi.
Sannu a hankali Sarki Abdul'aziz ya sa aka ci gaba da ba wa Kamalu horon yadda 'ya'yan Sarki ke gudanar da al'amaransu, bai sha wata wahala ba tun da dama ya san waɗansu daga ciki al'adun don haka ba a ɗauki lokaci ba ya goge tamkar ba shi ba. Sai dai har wannan lokacin bai fasa hulɗa da sauran abokansa na baya ba waɗanda suka kasance 'ya'yan Bayi. Su Inna wuro tuni suka koma sashen da Sarki Abdul'aziz ya gina musu, ita kanta Mai gado a wannan lokacin Takawa ya ba su umarnin komawa wasu manyan ɗakuna da ke maƙotaka da sashen Fulani babba, sakamakon yadda take ba wa su Abubakar kulawar da ta dace tamkar ita ta haife su. Sai ya zamana ita ma Jawahir ta samu fada a wurin Sarki Abdul'aziz ya ɗauke ta tamkar 'yar cikinsa. Haka kawai wani lokacin idan Mai gado take zuba wa Kamalu idanu tana jin ƙwalla na zuba mata.
"Allah sarki rayuwa kenan, Allah ba ya taɓa barin wani don wani ya ji daɗi."
"Rayuwa darasi ce! Da ace mahaifiyarku na raye ban san irin farincikin da za ta yi ba, sai ga shi duk wata kulawa da farinciki da kuke samu ƙasa ta turɓuɗe idanunta."
"Allah Ya gafarta miki Fulani, ina ma kina raye Takawa yake ba wa iyakinki wannan kulawar da a kullin kike mafarkinta. Na sake aminta da ba kowanne abu ne mai rai yake nema ya samu ba." Ire-iren kalaman da Mai gado idan ta zauna zuciyarta ke saƙa mata, sai dai a hakan ma ba ƙaramin daɗi take ji ba don ba ta taɓa tsammanin bayan rasuwar Fulani za su samu koda arziƙin rabin kulawar daTakawa yake basu a yanzu ba. Kuma da faruwar haka babu jimawa Sarki Abdul'aziz ya rubuta wa Sailuba takardar saki har guda uku, a ranar Sailuba ta ci kuka tamkar ranta zai fita. Babu yadda ta iya haka ta tattara kayanta ta koma ɗakin mahaifiyarta da zama.
A wannan lokacin kuma duk lokacin da damuwa ta cunkushe Muhsin ba shi da wurin zama sai harabar wurin da ta raba ɗakunan mahaifiyarsa da sashen da su Jawahir suka koma. Wani lokacin yana cin sa'ar ganinta wani lokacin kuma haka zai ƙaraci zamansa har ya tashi ba tare da ya ga gilmawarta ba.
Watarana Kamalu na ɗakinsa ya aiki wani Bawa a kan ya kira masa Jawahir, lokacin da saƙon ya isa kunnenta kamar ba za ta je ba sai kuma Mai gado ta kora ta. Yana zaune a kan tabarmar kaba, ya ga ta yi masa ƙerere a ka.
"Lafiya ka aika kirana?" Jawahir ta furta ƙerere daga tsaye.
"Ki shiga ki gyara mini É—aki akwai kayan wankin da na ajiye ki haÉ—a ki wanke su, idan kin gama ki dawo ki..."
"Wallahi ni ba baiwarka ba ce, kai shaida ne ko wankin kayana wani lokacin Inna ke yi mini. Malam idan za ka ware wannan bunguzar rigar jikin naka ka share ɗakinka ka wanke kayanka tun wuri ka ware, yoo Allah na tuba aikin ƙarfi wanne iri ne ba ka iya ba. Lalla samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama..." Da sauri Kamalu ya katse ta. "Ba na son sakarci ni kike faɗa wa haka?"
Baki sake Jawahir take bin sa da kallo. Ya miƙe tsam ba tare da ya tanka mata ba, sai da ya datse ƙofar shigowa sashensa sannan ya zaro wata murtukekiyar dorina. A tsorace Jawahir ta ja da baya cikin zaro idanu.
"Don Allah ka yi haƙuri!"
"Kura kenan ga tsoro ga ban tsoro, a haka ta nuna tafi kowa rashin tsoro amma kuma farar kura ce." Kamalu ya faÉ—a a ransa.
"Idan ba ki wuce kin aiwatar da abin da na saka ki ba wallahi sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Kamalu ya yi maganar cikin tsare gida. Kamar sabuwar munafuka haka Jawahir ta sunne kai ƙasa ta wuce tana aikin lokaci-lokaci tana yi masa Allah ya isa ƙasa-ƙasa don kar ya ji.
"Mai martaba mun tako ne sakamon mun samu labarin duk abin da faru, na daɗi da rashinsa, don haka muka ce ƙafa da ƙafa sai mun ƙaraso. Allah ya kiyaye gaba, Muna taya ku murna matuƙa da bayyanar wannan yaro Kamalu." Sarki Sulaiman ya furta bayan sun gama gaisawa da Sarki Abdul'aziz cikin mutumci da karamci.
"Mai martaba Sarki Sulaimanu kuma fa faÉ—uwa ce ta yi daidai da zama." Sarki Abdul'aziz ya faÉ—a yana gyara zama.
"Ai haka ake so Sarki Abdul'aziz wacce magana ce a bakinka?"
"Maganar auren yaran nan, dama a cikin raina nake shirin turo da Shamaki domin ya nemo mana izini a wurinka. Za mu zo gaisuwar iyaye da kawo kuÉ—in na gani ina so." Fuskar Sarki Sulaiman ta sake faÉ—aÉ—a da fara'a."
"Muna muraba da wannan maganar Sarki Abdul'aziz Ubangiji ya tabbatar mana da alherinsa." Sarki Sulaimu ya furta sannan suka amsa lokaci É—aya.
Tun Jawahir na noƙewa har ta sake jikinta ganin yadda Kamalu ya tsare gida yake buga mata tsawa, wani abin takaici da ya cika ta bai wuce yadda ya buɗe ƙofar gidan Bayin da ke hidima a sashensa suka dinga shiga suna ganin irin wulaƙancin da yake yi mata ba. Sai da ta gama wanke jinga-jibgan rigunan alkyabbunsa sannan ta koma gefe tana yarfe gumi, tausayi ta ba shi har ransa, ya gintse murmushin da yake cinsa.
"Akwai alkaki da nakiya a rumfa idan kin gama." Harara ta wurga masa murya a ciki ta furta. 'Ba na ci." Ɗaga kafaɗa ya yi cikin halin ko in kula ya juya zai shiga ɗaki Bawa Bala ya ƙarasa cikin girmamawa ya zube ƙasa ya furta. "Allah ya taimake ki Takawa yana buƙatar ganinka yanzu." Da kai kawai Kamalu ya amsa wa Bawan ya juya, hanyar fita ya nufa take wasu Bayi maza guda biyu suka rufa masa baya. Hannu ya ɗaga musu da sauri suka koma ya ci gaba da tafiya, ƙwafa Jawahir ta yi tana bin igiyar da ta shanya kayan da kallo wani takaici ya sake lulluɓe.
"Da ace ina da iko da tuni na karɓa na fanshe ki masoyiyata." Kalaman Bawa Auwalu ya ratsa ta, ba tun yau Auwalu yake nuna mata soyayya ba amma ko kaɗan ba ta ba shi fuska ba. Harara ta watsa masa ta fice daga gidan, har za ta wuce sashensu wata dabara ta faɗo mata. A fili ta saki murmushin ƙeta don ta ci alwashin Kamalu ba zai ci banza ba a kan mugunta da wulaƙancin da ya yi mata, sai da ta shiga sashensu ta sauya kayan jikinta sannan ta nufi sashen Sarki Abdul'aziz.
Bakin Kamalu ɗauke da sallama ya shiga ɗakin saukar baƙin Sarki Abdul'aziz, sai da suka amsa masa sannan ya shiga ciki. A ƙasa ya zube cikin girmamawa ya dubi Sarki Sulaiman ya furta. "Barka da zuwa ranka shi daɗe, da fatan an samu al'ummar Masarautar Huddam lafiya."
"Barka dai Sadauki, ya fama da jama'a." Sarki Sulaiman ya furta ya saka hannu a cikin aljihunsa.