← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 86

Sashe 25

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daga wurin Fulani babba nake zan kai saƙo wurin Abubakar." Lokaci ɗaya suka kwashe da dariya jin an ambaci sunan Abubakar, Jakadiya ta gimtse tata dariyar ta furta. "Ganin gida kare kan zagi kura amma ba a daji ba, na tabbaya ɗayanku bai isa yin dariya nan a gaban amale ba." Daga haka ta yi gaba a fili ta nuna tamkar ta ji haushin dariyar da suka yi, ita ma kuma a ƙasan zuciyarta dariyar take yi. Galadima da Ciroma suka duba wurin da suke zargin wani na laɓe amma babu kowa, sakamakon tun shigar Jakadiya Kamalu ya sulale ba tare da sun fahimta ba. Wannan ta sa suka ajiye ragowar maganar da suke yi ba tare da sun ƙarasa ba.

Yanayin da Inna wuro ta ga Kamalu a ciki ya sa ta zaunar da shi a gefenta, ƙura masa idanu ta yi lokaci ɗaya ta fahimci tashin hankalin da ke tattare da shi.

"Me yake damunka Kamalu?" Da yake a wannan lokacin Inna wuro sun samu 'yancin kansu ta hanyar mazajensu da suka yi ruwa suka yi tsaki suka haÉ—a bulo suka gina musu É—akuna kamar yadda suka ga sauran bayin sun killace iyalansu. Jiki a sanyaye Kamalu ya furta, "Inna don Allah kada ki min faÉ—a idan na gaya miki." Inno wuro ta gyaÉ—a masa kai. "Kada ka damu Kamalu ba zan maka komai ba."

"Inna bayan na kai wa Shamaki saƙonsa ina dawowa na ji wasu suna ce wa za su kashe mai martaba..." Tun bai ƙarasa maganar ba ta sa hannu ta toshe masa baki, take jikinta ya ɗauki karkarwa. Ta yi ƙasa da murya ta furta, "Babu ruwanka da kowa ka ji Kamalu, daga yau idan ka sake jin wasu na irin wannan maganar ka yi tafiyarka ka ji." Kamalu ya gyaɗa mata kai sannan ya hau shimfiɗarsa ya kwanta.

Jawahir ta yi wayo sosai yarinyar ɓul-ɓul da ita gwanin birgewa, musaman da take samun kulawa a ɓangaren Fulani Babba, sai dai abin da har kwanan gobe ke faruwa bai fasa ba dangane da ganin gawar saniyar da ake wayar gari da ita duk ranar asabar da asuba.

Fadar Sarki Abdul'aziz ta ƙayatu matuƙa da kayan alatu iri-iri irin na wancan lokacin. Waziri, Galadima, Ciroma da Malam Liman zaune suke a gabansa sai Dogarawan da ke tsaron ƙofa da sauaran Fadawan da ke zaune daga can gefe.

"Dalilin da ya sa muka tara ku saboda wata muhimmiyar magana da ke ci mana tuwo a ƙwarya sakamakon firgici da talakawanmu suke ciki." Sarki Abdul'aziz ya yi maganar cike da izzar mulki. Shiru suka yi gabaɗaya suka sauraronsa ya ci gaba da cewa. "Akwai zancan mushen saniya da ake gani duk wayewar garin asabar a sashen Bayi, wanda da farko da aka sanar mana ba mu ɗauki abin da muhimmanci ba sakamkon al'amuran almara da muka saba gani yau da kullin a cikin masarautar nan, har sai da muka ga abin yana neman zarce ƙa'ida. Duk cikin dobobbin da Allah ya albarkace mu da su mun sa a ƙidaya su amma babu guda ɗaya da muka ji labarin ta yi ƙwarzane ballantana ta yi mushe, shin mene ne mafita kuma me kuke ganin yana haifar da haka?" Wani Dogari daga bayan Sarki ya russuna cikin girmamawa sannan ya furta.

"Allah ya taimaki amale, É—awisu mai yawan ado sikari ba ka yi farin banza ba."

Daga gefe Waziri ya gyara zama sannan ya fara magana.
"Allah ya taimake ka, ni ina ganin wannan ba abin mamaki ba ne duba da sanin wannan masarautar ba irin kowacce masarauta ba ce, a tawa fahimtar a ji daga bakin makusantan gidan na ainihi idan ya so daga baya sai a san abin yi ko a nemi shawararsu. Amma fa a harsashena kenan ranka shi daÉ—e." Lokaci É—aya gabaÉ—aya suka aminta da shawarar Waziri, Sarki Abdul'aziz shi ma ya aminta da haka dalilin da ya sa ya yanke shawarar jin ta bakin zuri'ar da ke rayuwa a daular shuri. Daga haka suka shiga tattaunawa a kan abin da ya da ce, dangane da harkokin masarautar.

Zaune yake a can cikin turakarsa a gaban ƙaton shurin ya tanƙwashe ƙafafuwansa sannan ya ɗora hannunsa na hagu a kan shurin ya furta. "Assalamu alaikum. Gafaranku dai ya ku ahalin cikin masarautar nan?" Daga cikin shurin ya ji an yi gyaran murya sannan aka amsa masa. "Wa'alaikas salam. Barkanka dai Sarki Abdul'aziz me kuma iyalaina suka yi maka? Don rabon da ka kawo mini ziyara har na manta."

Da yake a wasu shekaru da suka wuce Sarki Abdul'aziz ya taɓa kai ƙarar jikan Dattijon sakamakon wata ɓarna da ya yi masa.

"Ba ƙara na kawo ba Dattojo Maharaz, na zo ne dangane da wani muhimmin abu da yake faruwa a cikin masarautar nan." Murmushi aka yi daga cikin shurin sannan Maharaz ya ce, "Ba tun yau ba miyagun al'amura da ƙazaman abubuwa na faruwa a cikin masarautar nan kuma suna ta ci gaba da faruwa, sai dai kuma ban san wanne irin bacci kake yi ba Abdul'aziz." Takawa ya yi jim ba ya son ya bada ƙofar da za su haɗa shi da mutane don haka ya shashantar da zancen da cewar. "Wannan wata muhimmiyar magana ce..."

"Dangane da Saniya ko?" Dattijo Maharaz ya katse Sarki Abdul'aziz don ya lura ba ya san sanin matsalolin da ya É—auko masa waÉ—anda ke faruwa a cikin masarauta. Sai da Dajjito Maharaz ya numfasa sannan ya ci gaba da cewa.

"Waɗannan saniyoyin da suke mushe ba daga gare mu suke ba, sun fito daga cikin zuri'ar RUMZU su suke shayar da 'yarsu cikin fushi, kuma idan har hakan bai zama illa ko wani tashin hankali ba kada ka yi gaggawa a kansu. Suna da matuƙar hatsari fiye da tunaninka, yanzu haka 'yarsu na cikin masarautar nan sakamakon zanen ƙaddararta da ya gindayo ta kanta har ta faɗo cikin masarautar da duk faɗin duniya babu shu'umar masarauta kamarta. Hasali ma akwai daɗaɗɗiyar gaba a tsakanin zuri'ata da su zuri'ar RUMZU, sai dai hakan ba zai sa mu ɗauki matakin a kan jikarsu ba, domin har a yanzu ita ba ta san asalin abin da ya faru ba ka ga kamar mun zalince ta ne. Kuma idan har muka taɓo su na tabbata zuri'arka da mazauna cikin masarautar nan sai ta fi shiga tashin hankali sama da mu, za a zubar da jini kamar gobe. Wataƙila ma tarihi ya sake maimaita kansa, tun da na ganta na ji a jikina zuwanta na tafe da muhimman al'amura masu warware matsalolin da ke tsakaninmu." Cikin ɗaurewar kai Mai martaba ya furta. "Yanzu haka za mu zura ido kenan? Kuma ina fatan zamanta ba za ta cutar da ahalina da talakawana ba ko?"

"Babu abin da za ta yi muku domin haifiyarta kafin ta mutu ta yi mata musayar jini da nata, yanzu haka zuri'arta nemanta suke ruwa a jallo don tana ɗauke da kambun da mutane da dama ke burin mallakarta. Matsafa da bokaya na yunwar samunta domin matuƙar suka same ta tamkar jari za ta zame musu, kuskuren mahaifiyarta kenan da ba ta ɓoye tauraruwarta ba. Kai dai abu ɗaya zan sanar da kai, kamar yadda kuke ganin al'amura mabambamta a masarautar nan kuma kuke tafiyar da ita a yadda ta zo muku wannan ma ku ɗauke ta a haka. Ko da wasa har iyalanka kada ka sanar da su wannan mushen San ba daga gare mu ba ne, domin faɗar taka na iya jefa duk mutanen cikin masarautar nan a cikin halaka. Ba ka sani ba ko akwai wanda yake burin mallakarta a cikin masarautar nan, to kuwa muddin ya ɓallo maka ruwa babu makawa sai kun gwammace kiɗa da karatu."

Gwaron numfashi Sarki Abdul'aziz ya sauke sannan ya furta, "Na yi maka alƙawari ya kai wannan Dattijo mai cikakken karamci." Murmushi Dattijo Maharaz ya yii ya furta. "Na san ba za ka taɓa bijire mini ba don haka nake sake godiya da irin girmamawar da kake yi mini. Ina mai yi maka albishir da wani alheri na nan tafe cikin iyalinka, duhu zai yaye sannan haske zai mamaye ka da ahalinka wala'alla ma ya tsamo ka daga wata irin sarƙaƙiya. Sai dai kuma akwai ɓacin rai, ɓacin ran da ka iya kai ka ga yin nadama a lokacin da nadamar ba za ta yi maka amfani ba."

Gaban Sarki Abdul'aziz ya yanke ya faÉ—i, cikin rashin kuzari ya ce. "Wanne irin haske ne wannan da ke iya tsunduma ni cikin nadama...?"

"Ba haske ne zai kai ka ga nadama ba, sai dai ƙulli da murɗa-murɗar da ke kanka ce za ta yi tasirin ko kuma silar tafiyarka kan turbar nadama. A ƙarshe ina mai yi maka fatan alheri mai ɗorewa kai da iyalanka, na barka lafiya Sarkin sarakuna." Ko kaɗan ba haka Takawa ya so ba, ya so a ce ya samu damar sake tattaunawa da Dattijo Maharazu amma babu yadda ya iya haka ya taso daga gaban shurin ya koma kam gadonsa, ya ji ma shi kaɗai yana maimaita kalaman da Dattijo Maharaz ya furta masa. Ganin babu wata mafita ya sa ya shiga banɗaki ya gabatar da al'awala don gabatar da sallar Isha'i. Bai san dalili ba amma haka kawai wani lokacin yake jin ba ya sha'awar yin salloli a kan lokacinsu, sai ya kai zuciyarsa nesa yake gabatar da su.

"Kamar yadda muka alƙarwarta muku mun tattauna da Dattijo Maharazu har ya kara yi mana fashin baƙi." Sarki Abdul'aziz ya yi maganar bayan ya tara fadawa da sauran masu sarautun cikin masarauta. Cike da girmamawa suke jinjin kai sannan ya ci gaba. "Gabaɗayanku ba baƙi ba ne dangane da waɗansu al'amura da ke faruwa a gidan nan kamar shan nono ranar juma'a, rafin tsamiya, busar sarewar shuri da sauran abubuwan da aka saba gani yau da kullin." Sai da ya ɗan tsahirta ya ci gaba da jawabi.
Chapter 25 · 0% Book details