← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 86

Sashe 74

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Galadima ya yi ƙwafa sannan ya furta, "Yarima ya same ni da maganar ba ya son auren haɗin da ake shirin yi masa, don haka na ga ya dace na zo na soke wannan maganar sai kuma aka yi sara a kan gaɓa tun da kai ma ga ka a zaune Sarki Sulaimanu." Dumm Sarki Abdul'aziz ya ji ƙirjinsa ya buba, tamkar an buga masa guduma. Kunyar Sarki Sulaimanu ta lulluɓe shi.

"Mun riga da mun zartar da hukunci Galadima, sanin kanka ne ba ma yin magana biyu." Muhsin ya É—ago a zabure ya dubi Mahaifinsa.

"To a yanzu ba sai gobe ba za ka fara! Magana biyu ba, yau É—in nan za ka fara tun da yaro ya ce ba ya so, kai ma kuma na ga ba auren dole nan aka yi maka..."
"Galadima a bamu guri!" Sarki Abdul'aziz ya sake katse shi a fusace.

"Ka yi mini afuwa Mai martaba idan kalamaina za su sosa maka rai, ni ne dai mahaifin yarinyar nan kuma ni na tako har nan na nemi arziƙin haɗa wannan alaƙar. Kuma a yanzu ina mai neman alfarmar Sarki Abdul'aziz da a bar yaron nan ya auri wacce yake so, ita kuma 'yar wurina ina nema mata auren Kamalu idan hakan ba zai zama da matsala ba." Sarki Sulaiman ya furta yana zuba maganansa a wurin Sarki Abdul'aziz. A razane Kamalu ya dago jin furucin Sarki Sulaimanu.

"Faƙat! Shi kenan, an gama magana yaro ya auri son ransa dama ai matar mutum kabarinsa." Galadima ya furta.

A fusace Sarki Abdul'aziz ya ce. "Ba za mu ruguje maganar da muka gina a baya ba..."

"Idan har ina da alfarma a wurinka ka yi yadda muka buƙata Sarki Abdul'aziz." Sarki Sulaiman ya katse shi.

Rai a ɓace Sarki Abdul'aziz ya ce, "Ka sanar da iyayen yarinyar da kake so su turo magabatansu wurin Galadima ya aiwatar da duk abin da ya dace."

Daga Kalamu har Jawahir kusan mutuwar zaune suka yi kowa da abin da yake wassafawa a zuciyarsa, a ɓangare ɗaya tsoron Sarki Abdul'aziz ya mamaye su don tun ranar da asirin Fulani Umaima ya tonu ba su ƙara ganin ɓacin ransa haka ba.

"Ni babu wacce nake so sai Jawahir." Rass! Gaban Jawahir ya faɗi, jikinta ya ɗauki karkarwa tamkar mazari. Sarki Abdul'aziz ya ƙura masa idanu sannan ya saki murmushi irin nasu na manya.
"Kai Muhsin me kake nufi? Kana nufin duk wannan haƙilon da na yi ya tashi a banza? Na ɗauka za ka ce a haɗa ku da 'yar wurina Ummi?" A wannan karon ba Sarki Abdul'aziz ba har Sarki Sulaiman sai da ya saki murmushi, don gabaɗaya sun fahimci inda Galadima ya dosa.

"Ni gaskiya Ummi ba ma tsarar aurena ba ce, Jawahir nake so." Muhsin ya furta har lokacin idanunsa a kan Jawahir da ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Jawahir 'yarmu ce sai mun ji ta bakinta tukunna saboda ita ma ba za mu yi mata auren dole ba." Dam! Ƙirjin Muhsin ya buga, nan take hankalinsa ya tashi don ya san ko kaɗan Jawahir ba ta ƙaunarsa.

"Kamalu ka ji hukuncin da muka yanke a kanka?"
"Eh na ji ranka shi daɗe, Allah ya sa haka ne ya fi zama alheri." Kamalu ya yi maganar murya a sanyaye don wannan maganar ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ta yi ba, don dai ba ya san ya watsa wa mahaifinsa ƙasa a ido ne kawai ya amince.

"Za ku iya ba mu wuri muna buƙatar tattaunawa da Sarki Sulaimanu, a sanar da Baffajo muna son ganinsa bayan sallar magriba." Tun Sarki Abdul'aziz bai gama magana ba Muhsin ya fice fuuu, da ma shi Galadima tun da ya ji sun raba hanya da Muhsin ya karkaɗe rigarsa ya yi gaba yana masifa da tsine-tsine. Kamalu da Jawahir kamar waɗanda aka zarewa laka a jika suka russuna suka yi godiya suka fice, har Jawahir ta fita Sarki Sulaiman yana bin ta da kallo.

Kamalu sauri ya fara yi tamkar zai ta shi sama ya wuce sashensa, yana shiga Bayi suka fara yi masa barka da shigowa ko kallonsu bai yi ba don yadda kansa yake sara masa tamkar zai tsage masa gida biyu. Damuwa ɗauke a fuskar Inna wuro ta shiga ɗakin Kamalu don ta ga lokacin da ya shiga fuska babu walwala, sallama ta yi masa da ƙyar ya iya amsawa yana ganinta ya tashi zaune. A gefensa ta zauna ta zuba masa idanu, a hankali ya fara motsa baki.

"Inna Mai martaba ne!"
Rass gabanta ya faÉ—i amma sai ta dake ta furta, "Me yake faruwa?"

"Wai aure zai yi mini, amma Inna kada ki gaya wa Baffajo don na ji ya ce zai same shi ya yi masa maganar na san kuma a kanta za su tattauna." Murmushi ne ya bayyana a fuskar Inna wuro.

"Kamalu don za a yi maka aure ne ka shiga damuwa? Ba ka san shi ne mutumcinka ba, kai don Allah bari na wuce wallahi har ka tsinkar mini da zuciya na É—auka wani abu ne. Kai Allah na gode maka Allah ka sa zan ga auren Kamaluna" Inna wuro ta yi maganar ta na ficewa daga É—akin cikin tsananin farinciki.

Jawahir kai tsaye sashensu ta nufa zuciya babu daɗi, can cikin ɗaki ta shige a lokacin Mai gado na ɗakin Abubakar tana koya masa yadda ake tafiya don lokacin ya fara tsaiwa har yana iya miƙewa tsaye ya tsaya ƙyam da ƙafafuwansa, sai dai har lokacin kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci ba shi da cikakkiyar lafiya. Jigum ta yi tana nazari don ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba za ta taɓa furta wa Sarki Abdul'aziz ba ta ƙaunar ɗansa ba. Kamar wacce aka tsikara da sauri ta miƙe ta ɗauko littafin labarin Hidaya, kamar marar gaskiya haka ta raɓe daga bayan ƙofa sannan ta buɗo shi ta ci gaba da karantawa.

Da mamaki Sarki Hafiz ya dube ni ya dubi wurin da nake kallo ya girgiza mini kai. "Idan har muka ce miki mun ga wata hallita a wurin can to mun yi ƙarya. Babu wanda muke gani, idan kuma ke ƙwayar idonki na gane miki sai dai idan fatalwarsa ce."
"Mece ce Fatalwa?" Na wurgawa Sarki Hafiz tambaya.

"Fatalwa wata hallita ce da take wakiltar mamaci take tsoratar da mutane ta cikin siffar mamaci, wata kuma ta ci gaba da gudanar da aikin alheri. Ke wata ma har fansa take dawowa ta ɗauka. A taƙaice dai ruhin mutum bayan ya mutu ne yake tashi ya dinga bin waɗanda suka san shi a baya yana tsorata su wasu kuma ba sa tsoratarwa." Jinjina kaina na yi don maganar na ji ta yi mini nauyi aka. "Kuma wannan harsashen gaske ne wanda ya mutu yana fatalwa? Ko kuma dai kawai camfi ne?" Na sake wurga masa tambaya.

"Ni dai da idanuna ban taɓa ganin fatalwa ba, na dai ji ana faɗin haka tun iyaye da kakanni. Amma gudun shakku, za ki iya tambayarsa domin muma mu ji daga gare shi." Tun Sarki Hafiz bai ƙarasa kalamansa magana ba na hangi mahaifina ya tunkaro ni, sai da ya ƙaraso gabana ya furta. "Tabbas a kalaman Sarki Hafiz babu ƙarya gabaɗaya ba sa ganina amma yanzu zan buɗe musu idanu." Rufe bakinsa na ga su Fulani Hawwa kulu sun ɗan ja da baya a tsorace. "Kada ku tsorota haƙiƙa ni ba mai cutarwa ba ne " Ya furta musu sannan ya sake harɗe hannuwansa a ƙirji.

"Ban so na bayyana ba amma ya zame mini wajibi tun da a yanzu kin haye karagarki, ni ba mahaifinki ba ne. Ni aminin mahaifinki ne wanda ya yi rainonki tare da mahaifinki. Na zaɓi na ci gaba da zuwar miki a siffar mahaifinki ne domin na ɗorar da alƙawarin aminina. Kuma lokaci ya yi da zan mallaka miki takobinki, takobin da burin mutane da dama suke mafarkin mallakarsa. Akwai wata yarinya da za ta zo cikin zamani mai tsawo, matuƙar ta samu sukunin mallakar wannan takobin sai ta gagarewa duk wani hatsabibi da matsafi a nan duniya. Ita kanta yarinyar mahaɗi ce, mahaɗin duk wani silar gawurta da shahara a faɗin duniya. Waɗannan mahaɗan ba za su taɓa tasiri ba har sa sun mallaki wani kundin littafi da zan mallaka miki, kundin da nake fatan za ki zayyane duk labarin rayuwarki tun daga farko har ƙarshe." Murmushi na sakar masa cikin girmamawa na furta. "Tabbas ka kasance amini na gari, ire-irenku sun yi ƙaranci a duniya domin amana ta yi rauni. Amma wani hanzari ba gudu ba, a kwanaki na ji wani matashi yana ce mini ya samu 'yanci a lokacin da nake rufe, shin me hakan yake nufi?"

"Yana nufin ya kuɓuta daga ɗaurin da Sarauniya wato ssrauniyar da ta kasance daga zuri'ar Sarki Hafiz, ita ta sa aka yi masa ɗaurin, Boka Tanko ne ya yi mata aikin a waɗansu shekaru da suka wuce." Aminin mahaifina da ke ɗauke da siffar mahaifina ya furta mini.

Mun jima muna tattauna waɗansu muhimman maganganu kafin daga bisa, ya ɗauko wannan littafin da na juye tarihin rayuwata a ciki ya damƙa mini. Ya haɗa mini da takobin da ya alƙawarta mini. Daga ƙarshe kuma ya ɗauke ni muka yi tafiya mai nisa sannan ya kai ni bakin wani shuri ya ce na zura takobin da hannuna tare da yankar gefen hannuna na tsartar da jinina a kai, bayan na aiwatar na ga yana kallona.

"Ina fatan yadda kika zura takobin nam, wacce za ta tono shi ta kasance tana daga cikin tsatsonki ce." Sam ban fahimci abin da yake nufi ba, daga haka muka baro wurin muka koma cikin masarautarmu.

Tun daga wannan ranar sarautar masarautarmu ta dawo hannuna, na ci gaba da kulawa da ɓangaren Bayi hatta wahalar da suke sha a baya sun samu afuwarta. Ban bar Sarki Hafiz haka ba har sai da na ba shi sarautar Wazirin masarauta, tun Fulani Hawwa kulu na nuna ƙyashu da hassadarta a kaina har ta zubar da makamanta.
Chapter 74 · 0% Book details