Sashe 61
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shugaba Zurufu na sauke kansa zai fara karatun littafin ya ji giftawar abu a bayansa, ɗan waigawa ya yi amma bai ga komai ba. Daga can ƙarshen bango Fargi ce a tsaye ta harɗe hannuwanta ta zuba masa idanu, Shugaba Zurufu ganin bai ga komai ya sa ya sake mayar da kansa sannan ya buɗe shafin baya na littafin. Ga mamakinsa sai ya ga shafukan baya duk sun shafe, guntun tsaki yaki ya saki ya girgiza kansa a fili ya furta. "Lallai Shaddas ka cika hatsabibi!" Daga daidai wurin da Boka Shaddas ya tsaya a karatu Shugaba Zurufu ya buɗe ya fara karantawa.
"Kin san wace ce masoyiyar É—an autan Darri?" Sarki Hafiz ya sake furzo mini tambayar don ina tsamani ya zaci ban ji tambayarsa da farko ba. Girgiza masa kai na yi sannan na ji ya ci gaba da cewa.
"Sarauniya Hazima! Awancan lokacin ita ta sace zuciyarsa, don a yadda aka ba ni labari ɗan autan Darri ya kasance mai son matan tsiya. Kwatsam sai mahaifiyarki ta wayi gari da jin labarin ɗan autan Darri ya damƙa wa Sarauniya Hazima karagar da ta damƙa masa, a yadda kakana ya ba ni labari kuma an yi hakan babu jimawa a tsokane-tsokanensa ya taɓo 'Yar wani malami da ke ƙasar Saudiyya, babu jimawa mahaifin yarinyar ya ƙone shi ƙurmus don an ce an kai ruwa rana da shi a kan ya fita daga jikinta ya ƙi. A wancan lokacin an ce wannaan labarin ya kaɗa mahaifiyarki matuƙa na rashin masoyinta, a ɓangare ɗaya kuma ta faɗa kogin nadamar damƙa masa karagar mulkin da ya bayar da ita zuwa wani gidan.
Sarauniya Hazima ta shimfiɗa mulkinta cikin aminci da salama, hakan ne ma ya ɗan rage raɗaɗin da ke cikin zuciyoyin mahaifanki. Kuma tun da wannan karagar ta koma hannun Sarauniya Hazima sai da ta shekara sama da ashirin sannan ta yi murabus ta damƙa wa babban ɗanta mai suna Sarki Bilal. Tun da Sarautar gidanku ta koma gidan Sarauniya Hazima ba ta sake fita ba har zuwa kaina ni Sarki Hafiz da nake ba ki wannan labarin, akwai sarakuna da dama da aka yi a cikin Masarautar nan wasu sun ɗauki shekaru a kan mulki wasu kuma ba su daɗe ba, a cikin kundin tarihi ma na ji an ce akwai sarkin da kwana ɗaya tal ya yi a kan mulkin Allah ya yi masa rasuwa. Kin san dalili?" Na riski tambayarsa.
"Ban sani ba Sarki Hafiz." Na amsa masa a taƙaice don na ƙagu ya ƙarƙare labarin da yake ba ni ko na ji ina labarin iyayena da saurn zuri'ata suke.
"Saboda yadda masarautar nan ta ɗauki tsafi da muhimmanci domin cim ma manufar duk wani mai neman ƙudurin hayewa sarauta. Ke ba iya gidan nan ba, zan iya bugar ƙirji na ce miki a duk faɗin nahiyar nan babu wata masarauta da ba sa amfani da tsafi da sihiri, sai dai kin san a komai ba duka a ka zama ɗaya ba amma mafi rinjaye a kan doron haka ake." Kalamansa sun matuƙar ba ni mamaki, ina shirin wurga masa tambaya ya katse ni.
"Idan har kin fahimci labarin da na ba ki kin ga asalin sarautar gidan nan ta fito daga gidanku ne, sannan ta faɗo hannun zuri'armu. Amma kin san ya aka yi aka san da cewar ke ce za ki dawo ki karɓi kambun sarautarku?" Da sauri na ɗago na furta masa. "Ina sauraronka sai ka faɗa Sarki Hafiz."
Takun tafiyar da Shugaba Zurufu ya ji a bayansa ne ya sa ya yi saurin rufe littafin ya rungume shi a ƙirjinsa ya waiga da sauri, a jikin bangon dutsensa ya ga an yi rubutu da ajami cikin manyan baƙi an saka. "FARGI." A fili ya maimaita sunan nan take gabansa ya yanke ya faɗi, da sauri ya ƙarasa bakin ƙatuwar wutar tsafinsa da ke ci balbal sai da ya saki dariyar mugunta sannan ya wurga littafin ciki.
Bayan Fargi ta koma cikin dajinsu ware kanta ta yi a cikin bukkarsu ita kaɗai take sakin murmushi, wani irin farinciki take ji a ranta sai dai kuma ta ci alwashin bin duk wata hanya ta toshe ɓarakar da duk wani daga cikin zuri'arsu zai iya kawo mata dangane da alaƙarta da Sarki Sulaiman, musamman Shugaba Zurufu da take ganin take-takensa na nuna mama hassada a duk lamuranta. Ba mahaifianta ba hatta sauran mutanen zuri'ar Rumzu sai da suka fahimci farincikin da take ciki don haka a ranar ta yi shelar yin aikin sihiri da tsafi kyauta ga duk wanda yake da wata matsala, kuma hatta su kansu Aljanun da suke tayata aiki sai da ta gwangwaje su da tukwicin da take yi musu a duk lokacin da za su taya ta aiki.
Kwana biyu a tsakani ba ta ga Sulaiman ba; ba ta ji motsinsa ba hakan ya sa ta shiga matsananciyar damuwa a tunaninta yana can wurin amaransa yana shan amarci don haka wani tuƙuƙin haushi da ɓacin rai ya mamaye ta. Tana zaune a bakin wata ƙatuwar bishiyar tsamiya, hawaye ya shiga gangaro mata. Daga samanta ta hangi inuwar mutum tana ɗagowa karaf idanunsu suka haɗu wuri ɗaya. "Me ya sa ake mini asara hawaye?"
"Saboda mamallakinsa ya yi watsi da shi."
"In ji wa?"
"Zuciyata ce ta sanar da ni." Sarki Sulaiman ya saki murmushi. "Zuciyarki ba ta gaya miki gaskiya ba." Juyar da kanta gefe ta yi ya zagaya ya tsugunna a gabanta.
"Kwana biyu kin ji ni shiru ko ki tuntuɓi lafiya Fargi." Wani abu ta ji ya soki zuciyarta sai da ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce. "Saboda ba na son shiga hurumin matanka." Ya fahimci kalamanta cike suke da kishi, sai da ya yi murmushi a fakaice ya ruƙo hannunta. A sanyaye take bin sa da kallo, ta ji ya ce. "Na zo tafiya da matata." Rass! Gabanta ya faɗi, bai jira cewarta ba ya ƙarasa da ita wurin dokinsa, ilahirin jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi. Ya fahimci tsoronta a fili amma sai ya yi tamkar bai son tana yi ba, sai da ta zauna sosai sannan ya hau suka fara tafiya. Sun kusa fita cikin gari Sulaiman ya shafi saman kan dokin da suke kai take suka ɓace, zuciyarsa fes don a yadda mahaifansa suk matsa masa a kan iyalinsa alwashi ya ci ba zai fara sanin kowacce macce a duniya ba sai Fargi domin ita ce zaɓinsa.
Bawa Ɗan Sani har ɗaki ya ƙarasa ya sanar da Jakadiya a lokacin ta dawo daga binne tsokar da Shugaba ya ba ta babu jimawa, ko da Bawa Ɗan Sani ya sanar da ita saƙon Takawa ba ta kawo komai a ranta ba, har za ta wuce Bawa Ɗan Sani ya yi ƙasa da murya sannan ya sanar da ita ganin idanunsa biyu ya ga Kamalu a turakar Sarki Abdul'aziz. Jakadiya tana isa ɗakin Inna wuro ta same su suna zaune suna 'yar hira ita da Mai gado da Jawahir, sai da ta sanar da ita saƙon Takawa bayan sun fito Jakadiya ta ɗan tsegunta mata ganin Kamalu da Bawa Ɗan Sani ya ce mata ya yi, amma da sharaɗin idan da gaske ne za ta ba ta tukwici, cikin farinciki Inna wuro ta amince ta leƙa ta gaya wa Mai gado saƙon farincikin da ta ji a wurin Jakadiya, ta yi maganar tana yin ƙasa da murya. Sun nufi hanyar fita daga sashen Bayi suka haɗu da Baffajo a nan suka sanar da shi saƙon Takawa, gabaɗaya suka nifi hanyar sashen Mai martaba ta bayanta Jakadiya ta ji ance. "Jakadiya zan biyo ku." Muryar Basiru ta ji, nan take gabanta ya faɗi da ta tuna Shugaba ya ce mata zai turo aljani a surarsa, amma gudun kada wani ya fahimci lagonta ta wayance da cewar. "Mu je mana ranka shi daɗe Basiru dama ai wurin Takawa za mu je." Jawahir da ke laɓe a bayansu sai da ta ga sun wuce sannan ita ma ta rufa musu baya.
Da sallama gabaÉ—aya suka shiga cikin É—akin jikin Inna wuro sai rawa yake tana fargabar abin da za su tarar, Jakadiya ta yi turus tana kallon mutanen da ke cikin É—akin.
"Faɗuwa ta yi daidai da zama Maharaz! Ina buƙatar sa bakin Jakadiya akan ƙaryatawar da Umaima take mini dangane da aikin yaron nan da na yi Abubakar." Boka Bamaguje ya yi maganar yana nuna Jakadiya. Jawahir na zuro kanta cikin ɗakin kanta ta ji ya yi wata irin sarawa, juya ta fara ɗaukanta. Wani irin luuu ta ji tamkar ana fisgarta, "Ki buɗe rijiyar uwar ɗakin nan domin wannan aikinki ne. Dalilin haka ya sa tun farko ban ɗago zancanta ba tun da ba hurumina ba ne." Dattijo Maharaz ya furta wa Jawahir.
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*34*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*