← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 86

Sashe 51

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan haka ne ba mu kaɗai muka karya alƙawari ba amma tun da haka ne yau ko sama da ƙasa za ta haɗe sai na ɓatar da yaron nan daga cikin masarautar nan." Da sauri Dattijo Maharaz ya ɗago ya dube shi, yana shirin magana Sarki Abdul'aziz ya furta. "Dattijo Maharaz ka fi kowa sanin ni ba ma'abocin son hayaniya da tashin hankali ba ne, don Allah ka lamunce masa ya ɗauki yaron na tun da shi ma yana daga cikin jinsinku na aljanu." Murmushi Dattijo Maharaz ya yi sannan ya kalli Sarki Abdul'aziz da ke cikin matsananciyar damuwa.

"Allah sarki Abdul'aziz! Tabbas na yarda rashin sani ya fi dare duhu, duk wannan cizawa da ake yi da ni saboda kai nake yin ta." Da mamaki Sarki Abdul'aziz ya ce. "Saboda ni kuma Dattijo Maharaz?" Dattijo Maharaz ya gyaɗa masa kai cike da ƙarfin gwiwa.

"Wannan da kake gani sunansa Sarki Furhussam, ya kasance Sarki kuma Shugaban baƙaƙen aljanun doron ƙasa. Tun a dubban shekarun da suka gabata mun yi zaman maƙotaka da su ga gida ga gida amma bisa yanayin ɗabi'a da mu'amalarmu da ta sha bambam sai ya zamana mun fara zaman doya da manja. Ka san mene ne muhimmiyar gabar da ta gifta a tsakaninmu?"

Dattijo Maharaz ya wurga wa Sarki Abdul'aziz tambaya. Girgiza masa kai ya yi sannan ya ci gaba da cewa.

"Yara ne suka shiga tsakaninmu, ba iya ku kaɗai ba hatta jinsinmu faɗan yara ya kan yi tasiri har zuwa kan iyayensu idan ba a kai zuciya nesa ba. A dubban shekarun da suka gabata Shugaba Furhussam yana da wata hatsabibiyar yarinya marar jin magana da rashin ganin giraman manya mai suna Hullat, ba zan ɓoye maka ba; ba iya nan ta tsaya ba har 'yan sace-sace da haddasa faɗa tsakanin ma'auratan jinsinku take yi. A lokacin shi kuma ɗana na uku wato Umaru ya tasa sai ya zamana shi mai zafin zuciya ne ba ya ɗaukan raini. Ana cikin haka sai faɗa ya haɗa su har ta kai Umar ya yi mata jina-jina, a lokacin da ƙafata na taka har zuwa wurin Furhussam a kan musamu maslaha na ba shi haƙuri a sasanta yaran, amma fir sai ya ƙi saurarata. In taƙaice maka dai sai ma ya ɗauki gaba da ni ko magana na yi masa ba ya tanka mini, sannu a hankali sai na watsar da lamarinsa da iyalansa. Ashe wannan abin da ya shiga tsakanin Hullat da Umar ita tuni ta faɗa ƙaunarsa har ta taɓa samunsa ta sanar da shi, shi kuma ya yi mata korar kare. Tun daga ranar duk yarinyar da Umar zai gani ya ce yana so ba ta sake kwana a duniyar nan Hullat take hallaka ta, sai da ta kai ta kawo ko ganin Umaru 'yan matan cikin jinsinmu suka yi ba sa tsayawa. Lokaci ɗaya ya zama tamkar mujiya ko kiran sunansa ba a son yi, daga ƙarshe da na yi bincike ma zurfi sai na gano da sa hannun Hullat a ciki. A ranar da na sanar da Umaru a ranar kuma kusan sai da samari goma suka kwanta dama a cikin zuri'ar Furhussam, a ciki kuwa har da yayan Hullat wanda shi ne babban ɗan Sarki Furhussam ɗin. Wannan rashin ne ya harzuƙa Furhussam ya shiga taya 'yarsa kisan zuri'ata, ganin haka ya sa matasan cikinmu suka mara wa Umar ɗan wurina baya aka yi ta ɗauki ba daɗi.

Abu kamar wasa ƙaramar magana sai ta zama babba, tun ina ɗaukan faɗan a matsayin na wasa har abu sai da ya kai mu ga gagarumin yaƙi. Bayan da ƙurar yaƙin ta lafa kowannenmu sai da ya rasa wani tsagi daga ɓangarensa, sai Malam Habu limamin cikinmu da shi da Shugaban da ke koyar da su Furhussam na su addinin na bautar ruwa suka haɗu aka tsayar da matsaya cikin maslaha. Shugabanninmu ne suka tsayar da matsayar kowannenmu kada ya kuskura ya shiga sabgar waninmu, ko azabartar da waninmu ko kuma ɗaukan waninmu ba tare da haƙƙinsa ba. Sakamakon mu muna daga cikin jinsin fararen aljanun doron ƙasa, shi kuma Furhussam yana daga cikin jinsin baƙaƙen aljanun doron ƙasa. Daga ƙarshe ma sai suka yi ƙaura daga cikin mu sai dai lokaci-lokaci sukan dawo mahallansu su kwana biyu su ƙara gaba." Ajiyar zuciya Sarki Abdul'azi ya sauke, Dattijo Maharaz ya ci gaba da cewa.

"Dubi can Abdul'aziz." Da sauri Takawa ya kalli wurin da Dattijo maharaz yake nuna masa.

"Wannan tafkeken gidan tururuwar da kake gani shi ne ainihin muhallinsu, shi ya sa sai a kusa shekara ba ka ga giftawar turuwa ta fito ko ƙwaya ɗaya ba. Idan ban manta ba ka taɓa yi mini ƙorafi a lokacin da turuwa ta addabe ku na ce maka wannan ba hurumina ba ne. Wannan shurin da kake gani shi ne ɓangarena da zuri'ata da muke rayuwa cikin aminci, sai kuma idan mun yi sha'awa ko iyalanmu mata idan za su yi aiki suka fita cikin jinsinku ba tare da ku kuna ganinsu ba.

Fulani Umaima ta yunƙura da sauri da niyyar ɗauko ƙahonta don ziyartar Bamaguje, ta ji wani irin ɗauuuu a ƙasanta tamkar zai zazzago, da sauri ta koma ta zauna tana runtse ido cikin azaba. Jin abin na sake tunkuɗo mata ya sa ta kai hannu da sauri nan take ta ci karo da wani mulmulallan abu ya tokare ta tamkar kan ɗa ne zai fito. A galabaice ta fara yarfe gumi ta leƙa don ganin baƙon yanayin masifar da rufto cikin rayuwarta babu tsammani, tashin hankalinta ya nunku sakamakon cin karo da ta yi da wata mulmulalliyar baƙar tsoka ta tokare ta, sannu a hankali wasu baƙaƙen tsutsotsi suka fara faɗowa ɗaya bayan ɗaya. Da rarrafe da jan gwiwa ta fara ja har ta ƙarasa da ƙyar ta iya ɗauko ƙahon ta busa don ƙarasawa wurin Bamaguje ko ya magance mata damuwa da al'amuranta.

"FaÉ—uwa ta yi daidai da zama Umaima! Yanzu nake shirin É—auko ki sai kuma aka yi katari gaki kin kawo kanki!" Kuka ta fashe masa da shi, a wannan karon duk wata al'ada da take yi ta ziyartarsa ba ta tsaya ta aiwatar ba saboda azaba.

"Ka taimaka mini Bamaguje ka dubi halin da nake ciki."

"Ki saurara mini Umaima don yanzu haka a kan hanya nake, dama na yi niyyar ɗauko ki ne domin na kai ki dajin Bururu wurin Tsoho kuma Shugaba Zurufu. Shi zai yi mini iso wurin gawurtattun Baƙaƙen al'aljanu domin na samu nasarar dawo da littafina da ke hannun Shaddas, sharaɗi ne ya gindaya mini a kan tilas ne sai na zo da ke domin ke ce mahaifiyar Basiru akwai tambayoyin da zai gudnar miki." Take cikin Fulani Umaima ya ɗuru ruwa, tana shirin yin magana Bamaguje ya dafa kanta nan take suka ɓace, sai ga su a cikin kogon dutsen Shugaba Zurufu da har wannan lokacin shi yake shugabantar Al'ummar mutanen Rumzu.

Saboda matsanancin gudun da Jawahir take yi ko kallon gabanta ba ta iya yi, babban burinta bai wuce ta ganta a sashensu na Bayi ba ko don ta ceci kanta. Bayan fitowar Muhsin da sauri ya rufa mata baya, duk inda suka wuce ban da idanu babu abin da ake zura musu wasu kuwa tuni suka fara tsegungumi. Mafi yawa daga cikinsu tsammanin da suke yi Jawahir ta yi wa Muhsin babban laifin don haka yake bin ta zai hukuntata. Kafin wani lokaci tuni Bayi suka ci gaba da kacalcala maganar, masu ƙarfin halin ciki suka rufa wa Muhsin baya don gano ƙwal uwar dakan abin da zai faru.

Da matsanancin gudu ta faɗa ɗakinsu kai tsaye kan gado ta haye jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi, a bakin ƙofar ɗakin ya tsaya yana ƙare mata kallo nan take ya ji tausayinta ya kama shi. A hankali ya fara takawa har zuwa bakin gadon, jin motsinsa ya sa Jawahir ta ɗago ƙirjinta na bugawa. Kafe ta ya yi da kallo don sura da ƙirarta ba ƙaramin fisgar hankalinsa suke ba, hannunsa ya kai kan fuskarta yana shirin yin magana ya ji wani irin ɗaaauuu tamkar wutar lantarki ta ja shi. Yarfe hannu ya shiga yi yana kai ƙwayar idonsa ya ga ɗan yatsan da ya taɓa ta ya yi baƙi wuluk.

"Ki yi haƙuri a kan abin da mahaifiyata ta yi miki." Muhsin ya furta a sanyaye sannan ya juya ya fice daga ɗakin.

"Kamar yadda Maharaz ya sanar da kai sunana Furhussam, ina fatan za ka kasance mai adalci a gare mu bayan sauraron kowanne ɓangaren. Wannan yaron tun a ranar da ya zo duniya rainonsa cakokam ya dawo hannuna da iyalina, idan ban manta ba kusan kimanin shekara ashirin da ɗoriya kenan. Wata rana da doshin asuba wata yarinyar ta dire shi a kujerar da na damƙawa babbar jikata ta wurin 'yata da na fi so a duniya wato Hullat. Tun lokacin da Hullat take da cikin yarinyar na yi mata alƙwarin mallaka mata ragama da shugabancin da na ke kai, kwatsam a daidai gaɓar da na tashi domin a ɗora jaririyar sabuwar haihuwar sai kuma na riski Kamalu a lokacin da yake jariri a kwance ko ɗigon sutura babu ajikinsa. A ƙa'idar masarauta da kujerar mulkin da nake kai ba kowanne jariri ne ake ɗora shi a kujerar ta yi daidai da shi ba sai mai tsananin rabo, sau tari wasu jariran ma ana ɗora su suke mutuwa ko su kamu da matsananciyar jinya. Kuma matuƙar ka hau kanta ka zama jagora mai aiwatar da duk wani hukuncin da ya dace, a lokacin da haka ta faru na ji baƙinciki sosai har sai da na ji tamkar na kashe Jaririn amma sai na fasa, a kan dole na naɗa masa kambu a kansa wanda a zahirin Baffajon da ya tsince shi ya ga zagayayyan jini da tururwa a goshinsa. 'Yata Hullat da kanta ta ba ni shawarar na ɗaura wa Kamalu da Fartuhmu aure, saboda yadda kyakkyawar surarsa ta birge ta don haka take fatan yarta ta aure shi. Ba zan ɓoye maka ba a siffar hallita da ƙira nesa ba kusa ba jinsinku na mutane sun fi mu kyau, dalilin haka yake sa muke auren matayenku da dama don ko ni ina da matan bil'adama sun kai goma.
Chapter 51 · 0% Book details