← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 86

Sashe 27

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sakaryar banza da wofi, wannan ita kaɗai ce damar da ke gaban kuma idan ta wuce ta tafi kenan har gaban abada. Matuƙar kika bi umarnina nan da ɗan wani lokaci kema za ki zama Fulani a gidan wallahi ko tantama ba na yi, sai kin kasance matar Takawa kamar yadda Umaima ke ji da kanta." Jin haka ya sa Sailuba ta miƙe da sauri, cikin sanɗa suka nufi bayan ɗakunan Bayi, a bakin wata bishiyar kuka suka tsaya sai da Jakadiya ta kalli hagu da dama sannan ta kunto garin maganin ta juye shi a butar gabanta da ke cike da ruwa. Daga can jikin katanga Uwar tuwo ce a raɓe tana leƙen Jakadiya cike da mamaki, dawowarta babu wuya daga banɗaki ta ji kalaman da Jakadiya take yi wa Sailuba. Tana nan tsaye har Sailuba ta tuɓe kayanta Jakadiya ta fara watsa mata ruwan maganin har ya gama gauraye jikinta gabaɗaya, tana ganin sun tunkaro wurin ta yi saurin komawa ta faɗa ɗakinta. Jakadiya ce ta fara wucewa sai Sailube da ke lulluɓe kamar sabuwar amarya. Uwar tuwo na raɓe a jikin labulenta ta ga giftawarsu. Jinjina kai ta shiga yi cike da mamakin Jakadiya, wani tunani ya gangaro cikin kwanyarta lokaci ɗaya ta saki wani shu'umin murmushi mai ɗauke da wasu ma'anoni.

"Boka Bamaguje ya sanar da ni kin janye jikinki daga wurinsa, sai dai duk yadda na so jin dalilin haka abin ya faskara daga bakinsa. Me ya sa kike son jefa kanki a ƙangin rayuwar da ba za ta fisshe ki da komai ba, kin san muhimmanci Bamaguje kuwa da kike son watsa masa ƙasa a ido?" Mahaifiyar Fulani Umaima ta rattabo kalamanta cikin ɓacin rai. Fulani Umaima ta haɗe fuska, da farko kamar ta sanar mata abin da ya haɗa su, sai kuma ta ce. "Na samu wani sabon boka ne kuma aikinsa tamkar yankan wuƙa haka yake."

"Ai shi kenan tun da haka kika zaɓa kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi ba, ni kaina ba don taimakon Bamaguje ba kin san ni da ke da ba mu samu wannan fadar haka ba." Fulani Kilishi wato mahaifiyar Fulani Umaima ta faɗa, don ba ta son ja da nisa saboda ko kaɗan ba ta san abin da za ɓata mata rai.

Bayan kwana biyu tuni kowa ya watse ya rage sai ainihin mutanen cikin masarautar. Wataranar Juma'a da yamma Jakadiya ɗauke da tiren kayan marmari ita da Sailuba suka nufi sashen Takawa, fuskar Sailuba ta sha kwalliya kamar wacce za ta gasar kyau. A lokacin da suka shiga yana zaune yana rubuta wasiƙar da Sarkin Gumel ya turo masa a game da wani kasuwanci da yake son su fara ƙullawa, Jakadiya ce ta ƙarasa gabansa ta dire tiren hannunta.

"Barka da hutawa Uban gidana, farincikin talakawa da marayu. Hatta masu iyayen ma ka riga da ka gama musu komai. Allah ya ja zamaninka ya tsare gabanka da bayanka, gaba salamun baya salamun É—an toron giwa."
Sai da ya ƙarasa rubutun da yake ba tare da ya kalle ta ba ya furta, "Jakadiya an yi sara a kan gaɓa, don yanzu muke shirin aikawa a kira mana ke." Jakadiya ganin ba ya kallonsu ya sa ta ɗan zunguro Sailuba da ta yi galala tana ƙare wa falon hutawar Sarki Abdul'aziz, da ya sha kayan ado da ƙyalƙyali iri-iri.

"Allah ya baka yawan rai muna godiya da wannan nuna yabawar." Sai a lokacin Sailuba ta ɗan sake maƙe murya ta ce.

"Barkanka da hutawa Sarkin sarakai, fari mai farar aniya bangon sikari a bika a lasa idan babu kai a zubar da ƙwalla." Jin sauyin murya a kan wacce ya saba ji ya sa ya ɗago a hankali ya dubi wurin da Sailuba take, ganin haka ya sa a yangance Sailuna ta isa gabansa da ragowar kwandon kayan marmarin ta ajiya tana faɗin. "Idan Mai martaba ya lamunce shin zan iya yanka masa kayan marmarin a yanzu ko sai zuwa an jima." Wata irin ajiyar zuciya ya sauke har lokacin idanunsa ƙirr a kan Sailuba, mamakinsa ɗaya bai wuce yadda ƙaramar yarinya ta iya wassafa kalaman ban girma a mai girman matsayi kamarsa ba.

"Idan kuma Mai martaba ba ya buƙata zan jira a ƙofa har zuwa lokacin da zai buƙaci a yanka masa. A gafarce ni idan akwai kuskure a kalamaina ranka shi daɗe." Sailuba ta ƙarasa maganar tana sunkuyar da kai ƙasa kamar sabuwar amaryar da ke gaban surukarta.

"Muna da buƙatar kayan marmarin." Sarki Abdul'aziz ya furta a takaice, sannan ya janye idanuwansa da ƙyar ba don zuciyarsa ta daina azalzalarsa a kanta ba. Jakadiya ta lura da yanayin da Mai martaba ya shiga don haka ta saki murmushin yin nasara a fakaice. Ta russuna tana faɗin, "Ranka shi daɗe a yi mini izini na tato maka ruwan 'ya'yan ibini." Gyaɗa mata kai ya yi sannan ta fice daga falon zuciyarta fes. Hakan da Jakadiya ta yi ne ya sa Sailuba ta samu damar yanka kayan marmarin tana yi tana karairaya cike da jan hankali. A fakaice Takawa yake satar kallonta da ta ɗago sai ya ɗauke kansa ya ci gaba da abin da yake yi, suna nan zaune Fulani Umaima ta shiga cike da isa da ƙasaita.

Ganin Fulani Umaima ya sa zuciyar Sailuba ta yi baƙi ranta ya yi mummunan ɓaci, a ciki-ciki ta dubi Fulani Umaima ba tare da ta rissina ba ta ce.

"Barka da shigowa."

Galala ta yi tana kallon Baiwa Sailuba don ba ta jin akwai wanda ya taɓa yi mata irin wannan gaisuwar ta rashin ladabi.

"Dakata!" Cak! Sailuba ta tsaya tana kallonta kanta a ƙasa.

"Lokaci na nan zuwa da za mu fara haɗa kafaɗa, ba dai taƙamarki Takawa ba. Da sannu sa na mayar da ke bora fiye da yadda kika mayar da kishiyarki." Sailuba ta yi maganar a cikin zuciyarsa.
"Ko mahaifiyarki ta cancanci ki gaishe ta a haka ballantana ni?" Fulani Umaima ta faɗa a wulaƙance. Shiru ya ratsa ba tare da Sailuba ta amsa ba, kuma ba ta jin za ta iya amsa mata don gani take a yanzu marabarsu kaɗan ya rage.
"A ba mu wuri muna buƙatar keɓewa." Sarki Abdul:aziz ya furta ba don ya gaji da zaman Sailuba ba sai dai don ba zai juri ganin yadda Fulai Umaima take daka mata tsawa a gabansa ba.

"Yadda kake so haka za a yi ingarman mazajen sarakuna, sarkin sarakai mai riƙe da kambun da babu masarautar da ke ɗauke da shi a kaf faɗin nahiyar nan. Ka huta cikin aminci ranka shi daɗe hasken talakawa, na barka lafiya bujimi namijin fama." Cikin wata irin murya mai fusgar hankali Sailuba ta yi maganar sannan ta miƙe kamar ba za ta taka ƙasa ba cikin kariraiya ta fice daga ɗakin. Daga Takawa har Fulani Umaima da ido suka raka ta sai dai kowa da manufar kallon da yake yi mata. Fulani Umaima kallon mamakin kalaman yarinyar ta yi waɗanda duk mai hankali idan ya saurara zai fahimci sannu a hankali take isar da saƙonta. Shi kuma Takawa kallon shauƙi da birgewa yake bin Sailuba da shi, take zuciyarsa ta fara raya masa wani abu. Ganin har lokacin hankalinsa na kan ƙofa ya sa Fulani Umaima ta zungure shi tana faɗin. "Ya dai ranka shi daɗe, me yake faruwa?"

"Kin san fa su irin waɗannan bayin sai ana bin su a sannu don gaskiya da sauran ƙuruciya a tattare da su." Mai martaba ya yi maganar cikin wayancewa. Ba don Sailuba baiwa ba ce kuma ta san ko a mafarki ba sa'ar tsaran Takawa ba ce da tuni Fulani Umaima ta dasa wani zargi a kanta, amma a cikin zuciyarta take ayyana dole za ta gyara wa yarinyar zama don ta ga raini ƙarara a ƙwayar idonta.

Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya, tun Jakadiya na jan Sailuba a ɗaiɗaikun ranaku zuwa sashen Takawa har ya zamana idan ita kaɗai ta je sai ya sa an kira masa ita, haka kawai yarinyar taka birge shi musamma da daɗaɗan kalamanta da kuma ƙuruciyarta. Fulani Umaima ko kaɗan ba ta san wainar da ake toyawa ba, don haka tun tuni ta manta da shafinta ta ci gaba da harkokin gabanta. Sai dai ta lura da ɗan ja baya da ta yi Mai martaba ya yi bai cika aikowa kiranta ta taya shi hira ba kamar yadda yake yi a baya.

Jawahir ta yi wayo sosai don har ta fara tafiya da ƙafafuwanta a lokacin shekararta ɗaya har da rabi, tana da matuƙar shiga rai da saurin sabo da mutane ta saba sosai da su Khadija don a yanzu wani lokacin har kwana take a wurinsu. Ta kama abinci sosai babu abincin da ba ta ci sai dai kuma wani abu da yake ciwa Mai gado tuwo a ƙwarya ba bai wuce duk yadda za a kaɗa a raya da ita ba, ba za ta taɓa ci ko shan komai ba ranar juma'a. Kuma har kawo wannan lokacin ba a daima ganin gawar mushen saniya ba ranar Asubahin asabar. Da ta fara kuka kuma sai kunnuwanta su fara fesar da jini, lamarin da a kullin yake sake karya zuciyar Mai gado kenan.

Akwai lokacin da wasu Bayi suka taɓa ɗaukan mushen saniyar suka shiga cikin daji suka feɗe ta suka haɗa wuta suka gasa kowannensu yanka ɗaiɗai ya ci take cikkunansu suka fashe kayan cikinsu duk ya fito waje, dalilin da ya sa aka gano gawarwakinsu wani matashin Bawa ne ya ce ya ga lokacin da suka wuce cikin daji da mushen saniyar.

Wannan al'amarin ba ƙaramin ɗaga hankulan Bayin da ke cikin masarautar ya yi ba, hakan ne ya sake saka su kowannensu ya shiga taitayinsu, tun daga ranar babu wanfa ya sake yin gigin ɗaukan saniyar da niyyar ya gasa don ya kai namanta bakinsa.
Chapter 27 · 0% Book details