Sashe 57
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ranka shi daÉ—e me ye haÉ—in tattaunawar da za ka yi da musakin yaron nan Abubakar? Yaron da; da shi da babu duk É—aya ne..."
"Dakata Umaima!" Ba ma son shashancin banza da wofi, yadda Yarima yake a wurinmu haka muke jin Abubukar. Ke kin san ba don Allah ya hallice shi da wannan tawayar ba, da yanzu haka shi ne Yarima mai jiran gado. Idan muka sake jin makamancin shashancin nan daga bakinku ranku zai yi mumman ɓaci." Shiru Fulani Umaima ta yi tana mamakin kalaman da Sarki Abdul'aziz yake gasa mata.
"Lallai kura ta yi lafiya." Fulani Umaima ta furta a zuciyarta, baƙinciki ya mamaye ta da ta tuna yadda Takawa ya haɗa matsayin Abubakar da Yarima Muhsin.
Cike da ƙwarin gwiwa Dattijo Maharaz ya ƙarasa bakin wata ƙorama ya ɗaura alwala ya tunkarin mulmulallan dutsen bakinsa ɗauke da addu'o'i ya dafa jikinsa. Tamkar yadda ƙwan kaza yake rabewa gida biyu haka dutsen ya rabe gida biyu, haske ya mamaye cikin dutse cikin ƙarfin zuciya Dattijo Maharaz ya kutsa kai har lokacin yana tafe yana karanta addu'ar duk da ta zo bakinsa. Tun farkon shigarsa ya ga yadda hallitun wurin suke bin sa da kallo sai dai uffan babu wanda ya ce mata, a haka ya ci gaba da tafiya har sai da ya kai tsakiyar dutsen daga can nesa ya hango Kamalu ya miƙe d alama wani wurin za shi.
"Ina za ka je haka Kamaluna?" Aljanin da ke É—auke da surar Baffajo ya furta. "Sallah zan yi don ban yi sallar azahar ba."
"Na gaya maka ba na son jin zan can sallar nan wai dole ne?" Da mamaki Kamalu yake bin sa da kallo, da sauri Dattijo Maharaz ya ƙarasa yana faɗin. "Kamalu kada ka bari mashirika maƙiyan Allah su yi galaba a kanka, wannan ba Baffajo ba ne."
"Ko kaɗan kada ka yarda da shi Kamalu yaudararka zai yi ni ne Baffajo, wancan kuma Dattijo Maharaz ne shi kuma mai yi maka maganar mayaudari ne." Furhussam da ke cikin surar Dattijo Maharaz ya furta yana ƙarasowa a lokacin komai nasu iri ɗaya babu wani abu da zai iya bambamce su. Sororo Kamalu ya yi kansa ya ɗaure, tashin farko tsori ya mamaye Kamalu, murya a sanyaye ya ce.
"Dattijo Maharaz me yake faruwa ne?"
"Babu abin da yake faruwa Kamalu." Suka furta kusan lokaci É—aya. e
Baƙinciki ya mamaye Dattijo Maharaz ya dubi Furhussam a ƙufule. "Furhussam ba na son tarihi ya sake maimaita kansa don haka a komai nake biyo maka a cikin ruwan sanyi, ka ba ni yaron nan na wuce da shi idan ba haka ba wallahi abin da ya faru a shekarun baya zai sake dawowa." Furhussam ya tamke fuska sannan ya ce. "Kada ka raina mini hankali Furhussam kana nufin yadda ka rikiɗe wa Kamalu ni ma za ka rikiɗe mini?" Kamalu da ya gama shiga ruɗani ya koma ya zauna haɗe da dafe kansa da hannuwansa. Dabara ce ta faɗo wa Dattijo Maharaz don haka ya nuna jikin bangon dutsen nan take sai ga hoton su Baffajo da Inna wuro suna zaune zugum cikin damuwa. "Ka yarda da ni Kamalu waɗannan sune su Baffajo na ainihi har yanzu ba su san halin da kake ciki ba."
"Ƙarya yake Yarona ni n Baffajonka."
"Kada ka yarda da shi ni ce Inna wuronka mai dama maka fura da yi maka hidima." Masu ɗauke da surar Baffajo da Inna wuro suka yi maganar lokaci ɗaya. Ganin suna neman dagula masa lissafi ya sa Dattijo Maharaz ya nemi taimakon Malam Liman, bayan ya shigo suka haɗa baki suka fara karatun alƙur'ani. Tun aljanun da ke ɗauke da siffar su Baffajo na daurewa har suka fara ihu jikinsu ya fara soyewa, ganin haka ya sa zuciyar Kamalu ta fara aminta da Dattijo Maharaz wanda yake karatu, da gudu ya nufi wurinsa yana sauke ajiyar zuciya wani irin tsoro ya mamaye shi.
"Barka da hutawa Malam Liman! Shin me yake faruwa da tsakar rana za ku tako har cikin zuri'armu ku nemi cin zarafinmu bayan wannan daɗɗaɗiyar yarjejeniya ce." Babban malaminsu masanin addininsu na bauta ruwa ya furta a ɗimauce sakamakon kururuwar da ta ɗimauta shi na aljanun da suke ƙonewa. Duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe Dattijo Maharaz ya zayyane masa, bayan ya gama sauraronsa ya furta.
"Yanzu kai Maharaz mene ne alaƙarka da yaron nan bayan shi ba jininka ba ne? Ina ganin wannan yarjejeniyar iya kan zuri'ar kowannenmu ce?"
"Yaron nan ya kasance tamkar jini da tsokata, idan ka cire alaƙar da ke tsakanina da kakan-kakansa ko a iya shi kaɗai zan iya tsaya masa. Ballantana idan ba ka manta ba, na taɓa gaya maka Furhussam ya kiyaye hatta bil'adam ɗin da ke rayuwa a tare da mu ne saboda kyakkayawar alaƙarmu."
Shiru ne ya ratsa a wurin, daga Fulani Umaima har Sailuba ban da wurga wa junansu harara babu abin da suke yi. "Ina Basiru yake?" Takawa ya tambaya.
"Ina jin ya fita ranka shi daɗe." Yarima Muhsin ya faɗa cikin zaƙuwa don a tsammaninsa zancan Jawahir mahaifiyarsa ta yi wa Takawa ne ya sa aka tarasu. Ƙwafa sarki Abudul'aziz ya yi sannan ya buɗe zaman nasu da sallama, bayan sun amsa Sarki Abdul'aziz ya ci gaba da jawabi.
"Maƙasudin zaman da na taraku yana da nasaba da kai ne Yarima," Yarima Muhsin ya saki murmushin farinciki. "Ka san dai yanzu kai ba yaro ba ne, sa'aninka har da masu 'ya'ya a duniya. Don haka ni da Sarkin ƙasar Bahdi muka yanke hukuncin haɗa ku aure tare da 'Yarsa Raihana." A razane Yarima Muhsin ya ɗago ya dube shi, "Ranka shi daɗe wai ni za a yi wa aure? Gaskiya ni ina da wacce nake so wai Ammi dama ba ki sanar da shi ba ne yadda muka yi da ke?" Shiru ne ya ratsa, Abubukar da ke jikin Sarki Abdul'aziz ya saki dariya yana nuna Muhsin da ke kumfar baki. "Mu kake furta wa haka Muhsin?" Muhsin ya ɗauke kansa gefe yana ƙananun maganganu.
"Wannan ne uzuri na ƙarshe da zan iya yi maka Furhussam, dole ka fuskanci mummunan hukuncu domin idan ba ka manta ba a shari'ar da na yi maka da jikan Malam Idi ce maka na yi idan ka kuma ɗauko mana magana za ka fuskanci hukunci mai tsanani kuma ka amince. Furhussam me ya sa kai da zuri'arka ne kaɗai kuka fita zakka a cikinmu? Ba za mu lamunci wannan isakancin ba, don haka Maharaz ka ɗauki yaron nan ka wuce kuma daga shi har zuri'arsa duk wanda ya kuma shiga gonar yaron nan na ba ku umarnin ku ƙone shi." Farinciki ya lulluɓe Dattijo Maharaz, Malam Liman ya shiga zabga masa godiya sannan Dattiijo Maharaz ya sa hannu ya rufe wa Kamalu idanu nan take suka ɓace sai ga su a ɗakin Sarki Abdul'aziz.
A razane duka mutanen cikin ɗakin suka miƙe waɗansu daga ciki har da masu neman wurin ɓuya, shi kansa Sarki Abdul'aziz sai da ya yi ta maza ya iya tsayawa. "Dattijo Maharaz kai ne?" Sarki Abdul'aziz ya furta cikin tsananin farinciki.
"Shin ka ba ni dama na ƙaraso cikin iyalanka?" Dattijo Maharaz ya wurga masa tambaya.
"Kai da kaya duka mallakar wuya ne Dattijo Maharaz! Na baka wuƙa da nama, ka ƙaraso ka warware mini zare da abawa don tun tafiyarka ka bar ni a cikin duhu." Dattijo Maharaz ya ruƙo hannun Kamalu suka ƙarasa cikin rumfar suka zauna, da idanu su Fulani Umaima suka bi su da kallo.
"Ko ba ka faÉ—a mini ba, na san ka sha gwagwarmaya farin Dattijo mai farar zuciya da dattako!" Sarki Abdul'aziz ya yi maganar cike da girmamawa.
"Kusan alhakina ne yin hakan Abdul'aziz, kuma na yi farinciki da na sauke wannan nauyin da yake kaina. Ga É—anka nan halak-malak na dawo maka da shi, Kamalu ga mahaifinka nan kai É—an gaban goshi ne, mai gata ne kuma É—an asali ne kai." Da mamaki Kamalu ya dubi Dattijo Maharaz. "Ni É—in kuma Dattijo Maharaz? Ka san me kake faÉ—a kuwa? Ka manta me Baffajo ya furta mini dangane da asalina?"
"Akwai tarun tambayoyi a bakina Dattijo Maharaz ban san yadda aka haihu a ragaya ba." Sarki Abdul'aziz ya faÉ—a a sanyaye. Dattijo Maharaz ya saki murmushi irin nasu na manya sannan ya nuna Fulani Umaima.
"Ba za a taɓa jin mutuwar Sarki a bakina ba Abdul'aziz, Umaima ita za ta warware mana zare da abawa domin ita ce ta san yadda aka haihu a ragaya."
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*32*
.*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Bayan É—aurin auren sabon Sarki Sulaiman da Fargi cikin farinciki ya shiga É—akin da take zaune a takure wuri É—aya ta zuba uban tagumi.