Sashe 22
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ka na nufin Baffajo na da sarauta ban taɓa sani ba? Idan haka ne me ya sa bai taɓa sanar da ni ba.?" Kamalu ya tambayi Maharaz bayan ya gama sauraron guntun jawabinsa. Shiru Dattijon ya yi yana nazari, kamar ya sanar da shi gaskiyar lamarin amma sai ya ga ƙuruciya mararan a ƙwayar idanunsa, don haka ya karkatar da akalar labarin. "Ni yanzu ba tsoho ba ne? Ka ga ai zan kai shekarun kakan-kakanka? Shi ya sa na ce maka ni aminin kakanka ne." Sai a lokacin Kamalu ya jinjina kai, "Kai a ina kake kwana? Kuma me ya sa ba ka saka kayan bayi irin namu?"
"Lokaci na nan da zan warware maka dukkan zare da abawa."
Sai da Muhsin ya zagaye Bayin da ke wurin gabaɗaya amma ko mai kama da Kamalu bai gani ba, ran Fulani Umaima ya yi ƙololuwar ɓaci. A fusace ta ja hannun Muhsin ta wuce sashenta tana umartar Jakadiya da tana son ganinta cikin gaggawa. Lungu da saƙon da ke cikin Masarautar babu wurin da ba su shiga ba amma babu hallitar da suka gani illa tsuntsaye da ƙananan dabbobi. Shi kansa Takawa ya yi matuƙar mamakin rashin ganin mai laifin daga ɓangaren Dogarawan har zuwa ɓangaren Muhsin.
"Allah ya huci zuciyar uwar ɗakina ya sanyaya ran uwar gijiyata, an aikata babban kuskure kuma duk wanda ya aikata wannan ɗanyan aikin sai ya shiga uku, domin matsi shi ke sa kalangu tsami." Jakadiya ta yi maganar tana duƙar da kai ƙasa. "Idan kiɗa ya canza dole ma rawa ta canza Jakadiya. Na fara zargin Fulani babba da yi wa Yarima turen iska, jikina yana ba ni a masarautar nan ban ga bawa ɗaya da zai yi gangancin tsinka wa Yarima mari ba. Amma ba ta sanni ba, da yake yaro bai san wuta ba sai ya taka."
"Kowa ya aikata abin da yake so zai ga baƙi ciki, Fulani babba ta tafka babban kuskuren da zai kai ta ga danasani. Yarima dai dashen Allah ne, kuma sai mun tabbatar mata da ko cikin tumaki rago ke zuwa fada."
Fulani Umaima ta É—an yi jim sannan ta ce, "Yanzu me ye abin yi?"
"Abin yi a juyar mata da aniyarta kanta, ni na fahimci hassada ƙarara a wurinta tun da tana ganin ita ce uwar gida kuma Yarima ba ya gare ta."
"Ki saka mana ranar ziyarar bokan da kika yi aike da jimawa." Jakadiya ta russuna. "Tamkar kin je gare shi buƙata ta biya uwar gijiyata."Fulani ta saki shu'umin murmushi sannan ta furta. "Tabbas sai na tabbatar wa Fulanu birnin kura ba a taɓa sa kare dillanci." Cike da banbaɗanci Jakadiya ta yi mata jinjina da hannu. "Allah ya taimaki uwar ɗakina, shi ya sa duk faɗin masarautar ba ni uwar ɗaki kamar ki." Fulani Umaima ta yi wa Jakadiyar kyautar ɗan kwalaye da alkaki sannan suka yi sallama ta bar sashenta.
Miƙe wa Kamalu ya yi yana kaɗe jikinsa sakamakon ƙasar shurin da ya kwaso sannan ya furta. "Zan ƙarasa don Inna wuro kar ta ji ni shiru." Tsoho Maharaz ya miƙe suka fara tafiya ya ce. "Ni ma zan wuce sai an kwana biyu kenan?" Cikin halin ko-in-kula Kamalu ya ce, "Sai an jima." Daga haka Tsoho Maharaz ya bi ɓangaren da Muhsin ya bi hanyar da za ta sada shi da sashe Mai martaba, shi kuma Kamalu ya wuce can sashensu na Bayi. Yanayin yadda ya gansu ne ya tabbatar masa da abin da yake faruwa, da yake suna da yawa bai sa sun fahimci ba a yi binciken babu Kamalu ba. Alwala ya ɗaura yana shirin wucewa ya ji Baiwa Mai gado da wata baiwa suna jajanta abin da faru, taɓe baki ya yi don ba don Maharazu ya ce kar ya faɗa ba babu abin da zai sa shi bai sanar wa Inna wuro ba.
"Magana ta gaskiya Galadima na jima da ƙudurta wa zuciyata haɗa Saifullahi da yarinyar nan Khadija, ko babu komai na san matsayina a masarautar nan zai ƙaru amma yanzu wani ƙishin-ƙishin nake ji kamar Mai martaba na son ba wa ɗan Sarkin ƙasar Farrom aurenta." Ciroma ya yi maganar cikin jimami. Galadima ya jinjina kai don shi kansa a kwai wani ƙuduri a zuciyarsa amma shi kam ba shi da matsala tun da Yarima da sauran lokaci kafin ya yi aure.
"Ashe tunanin da ke ƙunshe a ƙwaƙwalenmu tamkar ɗan'juma ne da ɗan'jummai, tun da Allah ya ba wa Maryamu ciki nake addu'ar Allah ya sa ta haifi ɗiya mace. Ko ba komai idan ta girma na san ƙulle-ƙullen da zan yi har Yarima Muhsin ya aure ta, to ka ga kenan faɗuwa ta zo daidai da zama. Sai dai kuma dole mu yi takatsantsan domin ka san Fulani Umaima ba kanwar lasa ba ce, dole sai mun lura idan ba haka ba sai mu sha ruwa da ciyawa ko kuma mu yi shuka a idon makwarwa." Lokaci ɗaya Ciroma ya bushe da wata iriyar dariyar, sannan ya tsagaita haɗe da yin ƙasa da murya ya furta. "Wane mutum in ji mutuwa ai na tabbata matuƙar ba kai za ka bada ƙofa ba kwaɓar mu ba za ta taɓa yin ruwa ba, tun da idan ka ga ruwa ya gurɓace yana zaune wuri ɗaya ne." Ciroma ya kalli hagu da dama haɗe da sake yin ƙasa da murya ya ce, "Mai zai hana mu kawar da Mai martaba Abdul'aziz ida ya so baya biyan buƙatarmu. Ka ga Ɗana yana auren ƙanwar sarki kai kuma 'yarka na auren sarkin shi kansa, yoo me ya rage idan babu Abdul'aziz? Ka ga a fakaice ba mu za mu riƙa sarrafa masarautar da sarautar gabaɗaya ba?" A firgice Kamalu ya sake maƙalewa a kusurwar soron jin kalaman da su Galadima suke yi,jikinsa ya ɗauki karkarwa gumi na keto masa. Bai san dalili ba amma haka kawai ya ji zuciyarsa na bugu a kan kisan da za a yi wa Sarki Abdul'aziz. Bai yi tsammani ba ya ji wani irin tari ya taso masa, da sauri ya sa hannu biyu ya toshe bakinsa don ya sa matuƙar azzaluman nan suka gan shi kashinsa ya bushe. Ciroma da Galadima suka yi sororo haɗe da kallon juna sakamakon jin tarin Kamalu da suka yi, cikin sanɗa suka tunkari wurin da Kamalu yake tsaye.
Kamalu kana ta jefa kanka a bala'i.🤔
SHU'UMAR MASARAUTA
13
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Jin takun tafiyar su ya sa gaban Kamalu ya ci gaba da faɗuwa jikinsa ya ɗauki karkarwa, can jikin bango ya sake maƙalewa yana fatan kada Allah ya sa su cim masa don shi kansa ya san idan suka gan shi tsaf za su iya kashe shi, ba su yi tsammani ba suka ga Jakadiya ta faɗo cikin soron hannunta ɗauke da aci bal-bal. Tana hango su Galadima ta kalle su da mamaki, "Yautai mugun tsuntsu ma sha miyarka sai ya yi dare.Daga ina kuke da tsohon daren nan?" Ta yi maganar tana kallon Ciroma. "Tararuwa mai wutsiya ganinki ba alheri, ina zuwa haka?" A yatsine ta kalle shi.
"Jikina yana ba ni akwai ƙullin da kuke ɗaurawa don banza ba ta kai zomo kasuwa!" Ciroma ya wayance."Daga cikin gida muke ke fa ina za ki?"