← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 86

Sashe 48

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki rabu da maganar Takawa ki ji da annobar da kika haifo Umaima, kin fi kowa sanin rashin tausayi da ƙarfin zuciyata tun da na jimanta miki haihuwar ɗan bokan da kika yi kin san tsugunne ba ta ƙare miki ba. Basiri sai ya zame miki annobar da za ta nemi gagare miki domin mahafinsa ya jima da tsaface shi. Na san mahaifinsa Shaddas hatsabibin gaske ne kuma akwai wata 'yar jiƙaƙƙiyar tsattsamar alaƙa a tsakaninmu don haka babu wani abu da zan iya yi miki akai, ruwanki ne ki je wurinsa ku sasanta domin ya sakar miki ɗanki, ruwanki ne kuma ki bar masa shi gabaɗaya. Ku tashi ku ba ni wuri, Umaima sai na ji daga gare wato kawo mini yarinyar da za ki yi. Wataƙila na tausaya miki idan akwai wani taimakon da zan iya yi miki." Fulani Umaima har ta buɗe baki za ta yi magana Mahaifiyarta ta dakatar da ita, a sanyaye suka miƙe suka yi masa sallama sannan suka koma cikin masarautar zuciya babu daɗi.

Mahaifiyar Umaima faɗa ta yi mata sosai cikin ɓacin rai, Fulani Umaima tana hawaye ta sanar da mhaifiyarta duk abin da ya faru tsakaninta da Basiru. Babban tashin hankalinta bai wuce yadda Bamaguje ya tabbatar mata ta zarginta a kan Basiru ba, don ta jima tana ɗora ayar tambaya a kan shi.

"Kamalu shin ka ji zafin maganar da ta suɓuce daga bakinmu har ka nemi ƙaurace mana ne? Allah ya sani ba ni na haife ka ba Kamalu amma yadda nake jin A'iru haka nake jin ka a cikin zuciyata..." Da sauri Kamalu ya katse Baffajo. "Don Allah ka daina haka Baffajo, wallahi ba haka ba ne! Kuma daga yau ba na son ku sake kallona a matsayin wanda ba ku kuka haifa ba, da ku na rayu da ku na buɗe ido don haka ba ni da wasu iyayen bayanku. Na fahimci kowanne ɗan'adam da kalar tashi ƙaddarar Baffajo, wannan ita ce tawa ƙaddarar kuma ina godiya da Allah ya jefa ni hannunku. Wataƙila ma zamana a gabanku shi ne mafi alheri a rayuwata." Cike da jin daɗi Baffajo ya rungume Kamalu sannan suka ƙarasa wurin Inna wuro da ke cikin ɗaki cike da damuwa.

Kwanan Mahaifiyarta ɗaya suka tattara suka koma masarautarsu, Fulani Umaima ta shiga cikin matsananciyar damuwa lokaci ɗaya ta fige ta rame waɗanda ba su san halinta ba har gani suke tamkar mutuwar Fulani babba ce ta buge ta. Sai da aka shafe kwana uku cif Fulani Umaima na shige da ficen son ganin ta gano wannan baiwar da Bamaguje ya ba ta umarni a kanta amma ko mai ɓurmushin kamarta ba ta gani.

'Yan uwan Fulani babba na matuƙar ba wa Abubkar kulawar da ta dace, a haka kwanaki suka shuɗe har aka yi addu'ar sadakar bakwai suka tattara gabaɗaya suka koma masarautarsu. Mahaifiyar Fulani babba ta so a ba su Abubakar ta tafi da shi, amma sai Takawa bai amince da hakan ba don a lokacin wata irin soyayyar Abubakar da sauran 'yan uwansa yake ji har cikin ransa. Kuma a wannan lokacin ne Sarki Abdul'aziz ya zartar da umarnin gabaɗaya Bayin Fulani babba na baya za su ci gaba da ba wa Abubakar kulawar da ta dace, Mai gado ba ƙaramin farinciki ta yi da jin haka ba. Don haka ita da Baiwa Zainaba suka ci gaba da ba shi kulawa kamar yadda suka yi wa Mahaifiyarsa alƙawari tun tana raye, kuma da yake ya saba da su sosai babu wata matsala da ake samu daga wurinsa.

Duk yadda Muhsin ya so kawar da Jawahir daga zuciyarsa abin ya gagara, a ɓangare ɗaya kuma ga jinyar hannuwansa da yake yi don ma ƙonuwar ta fara warkewa. Ya sha tambayar kansa inda yarinyar take amma duk yadda ya kai ga yin bincike ya gagara gano ta, tun yana mu'amala da 'ya'yan bayi a tunaninsa za su gusar masa da sha'awarta har ya haƙura ya watsar. Idan tunaninta ya yi masa yawa har gani yake ko gamo ya yi da aljana bai sani ba take wahalar da rayuwarsa. A yadda yake jin ƙaunarta gani yake ko aljana ce zai iya zama da ita ko da kuwa zai koma cikin jinsin aljanu da zama.

Sai da Sailuba ta gama sauraron Jakadiya ta share hawayenta cikin matsananciyar damuwa ta furta.

"Yanzu Inna shi kenan haka zan dawwama cikin wannan warin? Ki duba ki ga irin korar karen da Takawa yake mini." Jakadiya ta ɗan juyar da kai ta tsartar da yawu saboda warin da ya bugo ta sannan ta furta. "Wannan matsalar za ta zo ƙarshe ki bar ɗaga hankalinki Sailubata, babban burina na cika wa Boka Shaddas alƙawarinsa. Yanzu bari mu fara da wannan kuliyar." Jakadiya ta zaro ƙyamusasshiyar Magen da Boka Shaddas ya bata, ta ɗorata a kan wani baƙin jini mai wari nan take Magen ta fara lasa jikinta na kammaninta suka fara rikiɗa suna sauyawa. Sannan ta fara ambatar sunan Fulani Umaima sau uku, tana gama ambatar sunan Fulani Umaima ta sunkuya daidai kan magen da kallon ƙwala-ƙwalan idanunta kan iya tsorata mai kallonta ta furta.

"Maza ki dawwama kina ambatar sunan Umaima da muryar tsoratarwa, ki saka mata wasu-wasi a kan muryar marigayya Fulani babba. Maza ki tafi da izinin Boka Shaddas da sirrin tsafinsa." Rufe bakin Jakadiya babu wuya sai magen ta fice a guje ta bi ta saman katanga, kai tsaye ta wuce sashen Fulani Umaima, ta shige ɗakinta da shigarta babu jimawa ta ɓace daga kamar babu ita.

Fulani Umaima na zaune ta zuba tagumi kamar a mafarki ta ji muryar Fulani babba tana faÉ—in, "Umaima kin cutar da ni." A firgice ta É—ago tana waige-waige cikin tashin hankali.

*SHU'UMAR MASARAUTA*

*27*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Tun daga ranar da mahaifiyar Fulani Umaima ta sa ƙafarta ta bar masarautar ta duƙufa wurin ganin ta yi duk abin da za ta yi dangane da 'yar uwarta Fulani Asabe. Tun a lokacin ta so Bamaguje ya kashe yayartata amma sai hakan ya gagara sakamakon da ragowar kwanakinta a gaba, dalilin haka ya sa ya yi musu aikin rufin baki ta yadda Fulani Asabe da su Galadima ba za su ƙara maganar mulki ko rabuwar Umaima da Sarki Abdul'aziz ba. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya tsakanin Fulani Umaima da Fulani babba babu wani zama mara daɗi, sai dai tun da Umaima ta auri Takawa kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninta da shi ta fara ja baya, don haka ba ta kawo komai a kanta ba tun da a yadda ta lura hatta mahaifinsa ya fara sauya masa ba ita kaɗai ba. Mahaifiyar Sarki Abdul'aziz ta rasu da watanni uku Sarki Usman, Fulani Rabi'atu da Fulani Asabe Allah ya yi musu rasuwa sakamakon hatsarin da ya afka musu a hanyar su ta zuwa gaisuwar mahaifin Fulani Rabi'atu da ke masarautar Nabaldu, wannan mutuwar ba ƙaramin faranta ran Umaima da mahaifiyarta ta yi ba don a yadda ta fahimta Marigayi Sarki Usman yana matuƙar son Fulani babba da 'ya'yanta. Kuma ta lura yana yawan yi wa Sarki Abdul'aziz kutse a cikin sha'anin mulki don haka bayan mutuwarsu ta ci gaba da cin karenta babu babbaka a cikin Masarautar Huddam.

Jawahir har ta nufi sashensu na Bayi sai kuma ta yi turus tana tunanin abin yi don haka ta rasa yadda za ta haɗu da Kamalu, dabara ce ta faɗo mata da sauri ta saka ƙaramar butar a cikin mayafinta ta ɗaure ta tamau ta ɗaure mayafin a ƙugunta ta yadda ko ka kalle ta ba lalle ka fahimci da wani abin a jikinta ba. Kai tsaye ta nufi sashen Inna wuro tana ɗan kalle-kalle ko za ta gan shi amma ba ta ga Kamalu ba, don haka ta ƙarasa ɗakin Inna wuro ta same ta ta fito hannunta ɗauke da kayan wankin Kamalu.

"Inna sannu da gida! Kamalu ba ya nan ne?" Turus Inna wuro ta yi mamakinta ya bayyana a fili don ta san Jawahir da Kamalu ko kaɗan ba sa jituwa tamkar mage da ɓera, ganin haka ya sa Jawahir ta ɗan sosa kai a kunyace. "Yawwa dama Bala ne ya aiko ni na duba masa shi ko yana nan, shi ya sa na tambaye ki Inna." Inna wuro ta saki murnushi ta ce. "Yawwa ko da na ji, shiga ciki yana ɗaki na ji dai ya ce fita zai yi." Inna wuro ta yi maganar tana wucewa, Jawahir sai da ta tabbatar da Inna wuro ta fita sannan ta kunto butar hannunta ta faɗa ɗakin a lokacin Kamalu ya shirya cikin kayansa na Bayi da alama wani wurin za shi. Ba ta tanka masa ba don haka kai tsaye ta miƙa masa, Kamalu na kai idanunsa kan butar ya ji wani irin yaaaammmmm kamar kiyashi na yi masa yawo a jiki.

"Ta mece ce wannan?"

"Idan ka karɓa za ka san ko ta mece ce." Jawahir ta furta masa a taƙaice tana bin sa da harara, ba don tana gudun mummunan hukuncin da matar nan ta mafarkinta ta ce za ta yi mata ba me zai kawo ta gaban Kamalu. Sai da ya saki guntun tsaki kamar ba zai karɓa ba sannan ya saka hannun hagu ya karɓa a yatsine. Jawahir tana miƙa masa ta juya ta fice, take jikinsa ya ɗauki karkarwa gumi ya shiga keto masa. Kansa ya ji ya yi masa nauyi dum kamar an ɗora masa dutse, don haka ya tsugunna ya sanya hannuwa biyu ya toshe kunnuwansa. Tamkar wanda ake hajijijiya da shi haka ya ga ɗakin yana juya masa, ya jima a cikin wannan yanayin sannan ya ji tamkar ana fisgarsa don haka ya fice daga cikin ɗakin har lokacin hannunsa ɗauke da butar.

"Ka yi gaggawar zuwa ka ɗora ta a saman gidan tururuwar da ke kallon shurin uwar ɗakin Sarki Abdul'aziz." Kamalu ya ji an furta masa a cikin kunnuwansa. Cike da ƙwarin gwiwa ya damke butar, kai tsaye ya wuce sashen Sarki Abdul'aziz.
Chapter 48 · 0% Book details