Sashe 34
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Akwai dalilai da dama da ya sa na ƙauracewa dangina, asalina da tushena na guje su domin ni ban kasance tamkarsu ba, me ya sa kike son kawar da ƙwayar idonki a kan abin da yake daidai? Ke ba kamar sauran mutanen da ke rayuwa a cikin wannan masarautar ba ne hasali ma mutane da dama suna farautar rayuwarki." Shiru Jawahir ta yi tana sauraron matar da tun haɗuwarsu ta furta mata cewar ita mahaifiyarta ce. A hankali ta ga matar ta ƙaraso gabanta ta dafa kafaɗarta sannan ta ci gaba.
"Ki je sashen Sarkin cikin masarautarku ki tone abin da matarsa Fulani Umaima ta binne idan ba haka ba Fulani babba za ta mutu, idan kika bari Umaima ta ci gaba da yin nasara a cikin masarautar nan ina mai tabbatar miki sai ta yi nasara a kanki. Sai ta damƙa ruhinta ga hatsabibin boka Bamaguje kuma ki sani matuƙar ruhinki ya je gare shi babu wani taimako da ni ko abin bauta za mu iya yi miki." Tsoro ne ya mamaye zuciya Jawahir, a sanyaye ta furta. "Wallahi tsoro nake ji idan Fulani Umaima ta kama ni kashe ni za ta sa a yi."
Take annurin fuskar matar ya ɗauke, ta fara ja da baya a hankali sannan ta daki guntun tsaki. "Tun ranar da na buɗi ido a cikin zuri'ata ban taɓa jin kalmar tsoro ta fito daga bakinsu ba, tabbas Shugaba Zurufu ya yi gaskiya ga irin abin da yake guje wa zuri'armu dangane da auren bare, auren da ba zuri'armu ba." Sai da matar ta tsaya cak fuska a haɗe.
"Jawahir!" Ta ambaci sunanta cikin wata irin murya. "Ki gaggauta zuwa ki lalata tsafaffiyar butar da ta binne, ki É—ebi ruwan kogin tsamiya ki kwara a a sashen Fulani babba idan kika bari ta yi nasara a kanta nan gaba tana iya yin galaba a kanki, wannan umarni ne nake ba ki a matsayina na mahaifiyarki." Firgigit Jawahir ta farka daga nnnauyan baccin da ya É—auke ta mai cike da tarkacan mafarkai kala-kala.
A daidai lokacin Mai gado ta shiga ɗakin ta ajiye butar da ta yi alwalar sallar Asuba. "Jawahir tashi ki yi sallah kin san anjima kaɗan za ku tafi sassaƙar dawa." Da wani irin kallo ta bi Mai gado gabanta na faɗuwa, wani irin tsoro na lulluɓe ta. A hankali ta furta.
"Inna don Allah wata magana nake son yi miki amma don Allah kada ki buge ni." Rass gaban Mai gado ya faÉ—i, a hankali ta koma kusa da ita ta zauna.
Kasancewar Fulani Babba mai sanyin hali da rashin hatsaniya ya sa ko da aka kawo ta masarautar Huddam ba ta samu matsala da kowa ba, tana matuƙar girmama Mai babban ɗaki don ta ɗauke tamkar mahaifiyarta. Sai da Fulani Asabe ta gama karantar halayen Fulani babba tsaf sannan ta nemi jan ta a jiki don ta haka take son cim ma manufarta, idan ta janyo ta jiki ta dinga bugar cikinta tana jin sirrin Sarki Abdul'aziz daga ƙarshe kuma ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.
Fulani babba zuciyarta ɗaya ta aminta da Fulani Asabe amma da yake mahaifiyar Sarki Abdul'aziz ta san halinta sarai sai watarana ta sa aka kira mata ita ɗaki ta nusar da ita halayen da ɗabi'un mutanen cikin gidan don haka dole sai ta yi takatsantsan. Ba ƙaramim daɗi ta ji ba ta sake godiya ga Allah, da Allah ya haɗa ta da mahaifiyar miji ta gari don koda ta san masarautarsu ba ta kai wannan girma ba ta san suma suna fama da kacaniyar makirci da tuggu don haka sai ta iya zama da kowa a ruwan sanyi.
Ganin hanyar da Fulani Asabe ta ɗauka ba za ta bille mata sai wata dabarar ta faɗo mata, ta ji daɗi sosai da wannan tunanin ya zo mata a daidai gaɓar da take buƙatar ɗauki. Ƙanwarta Zulai da ke aure a Masarautar Bhahdi ce ta faɗo mata da yake ta san tana da 'yan mata guda biyu, Umaima ita ce babba sai ƙanwarta Zannira, ta na da yayye maza da ƙanne maza. Takanas Fulani Asabe ta kai wa ƙanwarta ziyara don a wannan karon ba za ta aika da saƙo ba.
"Zulai aure nake so na ƙulla tsakanin Umaima da Abdul'aziz, amma aure ba na zama dundundun ba." Mahaifiyar Fulani Umaima ta ɗan yi jim. "Ban fahimce ki ba Yaya."
"Ina nufin za ki ba ni Umaima na tafi da ita, ni zan yi duk shige da ficen da zan yi wurin malamai da bokaye don ta saye zuciyarsa. Babban burina ya aure ta duk wani kuɗirina sannu a hankali zan dinga zana mata tana aiwatarwa. Ƙarfi da yaji so nake sarautar Masarautar Huddam ta dawo hannun wannan yaron, idan ma mutuwa ce ta dace da Abdul'aziz ni ban damu ba domin kin fi kowa sanin yadda na ƙallafa rai a kan karagar nan, saboda Masarautarmu ta sha bambam da masarautun nahiyar afirka gabaɗaya." Dariya mai sauti Zulai ta saki.
"Sai yanzu na fahimci inda kika dosa don na san bakya ƙwanki sai da zakara, ni dama tun da na fara jin kalamanki na san banza ba ta kai zomo kasuwa. Yanzu dai idan komai ya kammala me ye kasonmu?" Fulani Asabe ta bushe da dariyar farinciki tamkar buƙatarta ta gama biya. "Babu abin da za ki buƙata ba zan aiwatar miki ba Zulai, ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba."
Sai da Mai gado ta aro mayafin jarumta ta yafa wa gangar jikinta sannan ta furta, "Mene ne Jawahir? Gaya mini babu abin da zan yi miki." Jawahir ta ɗan fara murza hannunta a hankali tana jin gabanta na faɗuwa ga wani irin raɗaɗi da tambarin cikinta yake yi mata ta furta. "Inna wannan matar da ta ce ita mahaifiyata yau ma na sake yin mafarki da ita, wai ta ce mini Fulani Umaima ta binne abin da Fulani babba za ta mutu..." Gabaɗaya abin da ya faru ta kwashe ta gaya wa Mai gado, da sauri Mai gado ta sa hannu ta rufe mata baki. Sai da ta tashi ta je ta tura ƙofar ɗakinsu don kar wani ya ji abin da suke faɗa sannan ta koma wurin da Jawahir take zaune.
"Ki yi shiru da bakinki kin ji Jawahiruna. Ni kaɗai ce mahaifiyarki ba ki da kowa sai ni kin ji, sharrin sheɗanu ne suke saka ki yin mafarki amma zan sa Malam ya karɓo miki turaren miyagu. Koda wasa kada ki sake ki faɗawa kowa kin ji." Jawahir ta gyaɗa kai a hankali kamar mai nazari sannan ta ce. "Kuma ta ce abin bauta zai yi fushi da ni mai tsanani idan na bari Fulani Umaima ta yi galaba a kaina..."
"Kul Jawahir kina son ki jefa mu cikin kogon bala'in da za mu yi tsallen da har abada ba za mu iya fitowa ba?" Jawahir ta girgiza kai. "To kin ga daga yau duk ranar da kika yi mafarki da ita ki ce ke ba ki san wani abun bauta ba kin ji." Jawahir ta amsa sannan ta miƙe har ta je bakin ƙofa ta dawo ta zauna.
"Inna wallahi Yaya Habu tausayi yake ba ni saboda da guba a jikinsa." Wannan karon Mai gado ba ta dakatar da ita ba sai ma tambaya da ta wurga mata. "Guba wacce iri Jawahir?"
Fulani babba sai da dare ya tsala sosai ta farka sakamakon yadda ta ji wuyanta ya sage mata, a hankali ta tashi har ta je bakin ƙofa ta koma ta sumbaci Abubakar. "Allah ya baka lafiya Abubakar ya nuna mini lokacin da zan ganka ka koma kamar kowa." Ta furta a hankali sannan ta wuce ɗakinta. Tana kwanciya babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita, cikin bacci ta riƙa jin wani abu na yunƙurin fita daga cikin ƙasanta tamkar ɗa yana son fitowa daga ƙasanta. Da sauri ta buɗe idanunta a hankali ta furta.
"Yau me nake ji haka a cikin daren nan?."
Ta so ace safiya ko rana ce da ta yi turare miyagu ko ta ɗan ji daɗin jikinta. Kwanciya ta sake yi sai dai a wannan karon bacci ya ƙaurace mata, sakamakon yadda take jin duk wata gaɓa ta jikinta kamar ana fusgarta da ƙarfi. A ɓangare ɗaya kuma wani irin zafi ne yake ratsa lungu da saƙon cikinta, babu jimawa kuma ta ji wata irin iska mai daɗi na shiga jikinta wanda hakan ne ya yi sanadiyyar da bacci ya yi awon gaba da ita.
Tun asubar fari Fulani Umaima ta so yi wa Sarki Abdul'aziz sallama don ta koma sashenta ta baza kunnuwa ta ji rahoton da zai fito daga ɓangaren Fulani babba da Sailuba, amma gudun kada ya fahimci wani abu ya sa ta haƙura har sai da gari ya waye tangararan.
Tana shiga É—akinta ta samu Basiru ya hargitsa mata É—aki yana bincike, da mamaki take bin shi da kallo don tun daga rumfa (Falo) har zuwa uwar É—aki a birkice yake.
"Me kake nema da ka hargitsa mini É—aki?"
Kafe ta ya yi da jajayen idanunsa fuska a turɓune, kallon ƙwayar idonsa ya hadda sa mata mummunar faɗuwar gaba. Kammaninsa da na Boka Shaddas suka sake bayyana ƙarara, har sai da ta ji wani kwarjini da shakkunsa ya mamaye ta. "Tambayarka nake me ka ajiye mini da kake birkita mini ɗaki za ka ɗauka?" Fulani Umaima ta sake tambayarsa cikin dakiya.
"Wani littafi nake nema?" Ras! Gabanta ya faÉ—i.
"Kai ka ajiye shi?"
"Ni da ɗakin mahaifiyata sai na ajiye abu zan ɗauka?" Da mamaki take bin sa da kallo, ba tun yau ba ta lura da tsagerancinsa. Duk da shi kansa Muhsin ba kanwar lasa ba ne wurin rashin kunya amma na Basiru ya dame shi ya shanye, dalilin haka ya sa ko kaɗan ba su cika ga maciji da Takawa ba. Saboda har Takawa Muhammad bai bari ba idan ya so tata masa rashin mutumci. Idan Fulani Umaima ta fara wassafa miyagun ɗabi'unsa a zuciyarta har mamakin ƙanƙantar shekarunsa take yi da hatsabibancinsa.
"Fice mini daga É—aki!" Ta furta fuska a haÉ—e.