Sashe 73
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Jama'a Alhamdulillah ranka shi daɗe." Waɗansu zobunan azurfa ne guda uku dukkansu duk iri ɗaya, ya miƙa wa Kamalu sannan ya furta. "Ga kyautar azurfa daga gare ni, ga kuma ƙarin alkyabbu ka ɗauki naka da na sirikina sai kuma da abokin tagwaitagarka." Sarki Abdul'aziz ba ƙaramin farinciki ya yi ba. "Muna godiya ranka shi daɗe, Allah ya ƙara wa Sarki lafiya. Ubangiji ya tsare gabansa da bayanka."
Cikin jin daÉ—i Sarki Sulaiman ya amsa da "Amin ." Ya dubi Sarki Sulaiman.
"Sarki Sulaimanu me ya sa ba ka gajiya? A ce duk lokacin da za ka ziyarce mu sai ka...?"
"Kyauta ce daga mahaifi zuwa wurin 'ya'yansa." Sarki Sulaiman ya katse Sarki Abdul'aziz.
"Allah ya ƙara lafiya Sarki mai matuƙar karamci da mutumci." Sarki Sulaiman na shirin amsawa Sallamar Jawahir ta karaɗe dodon kunnuwansu. Ganin takalman Kamalu ya sake tabbatar mata da yana ciki don haka ba ta jira an amsa ba ta faɗa cikin ɗakin.
Muryarata har abada ba za ta taɓa zama baƙuwa a wurinsa ba, ko mutuwa ya yi ya dawo ba ya tunanin sautin muryarta zai yi masa gizo ballanta ya mantata. Tun da ya ji muryar Jawahir tsigar jikinta ta yi wani irin yarr, gabansa ya yi mummunar faɗuwa. Wani irin yanayi ya fara ratsa shi, da ƙyar ya ɗan daidaita kansa amma har lokacin ƙwayar idonsa na kan ƙofar, shigar Jawahir cikin ɗakinsa ya kusa haifar masa da dakushewar numfashi na wucin gadi, ya kafe fuskarta da kallo yana mamakin tsananin kamar da fuskarta ta yi masa da matar da har duniya ta tashi ba zai ta taɓa mantawa da ita. Sai da ta zube a gaban Sarki Abdul'aziz ka fashe da kuka.
"Ranka shi daɗe ƙararsa na kawo maka wallahi yau ba ƙaramin zalintata ya yi ba." Jawahir ta ƙarasa maganar tana nuna Kamalu, kunyar duniya ta lulluɓe Kamalu. Ya sunkuyar da kai ƙasa, yana jin tamkar ƙasa ta tsage ya shige ciki.
"Kamalu me ya haɗa ka da ƙanwarka Jawahir?" Sarki Abdul'aziz ya yi tambayar fuska a haɗe duk da kalaman Jawahir ba ƙaramin dariya suka ba shi ba. Jin sunan Jawahir ya sa gaban Sarki Sulaiman ya ci gaba da faɗuwa, jikinsa ya yi sanyi ya sake zuba mata ido. "Jahawir!" Ya ambata da wani irin yanayi, da sauri Jawahir ta dube shi jin yadda ya furta sunan nata.
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*40*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Tamkar yadda inuwar mutum ke bibiyar kowacce hallita haka Boka Shaddas yake bibiyar Jawahir domin ya samu nasarar kai ta kogon dutsen Shugaba Zurufu, sai dai a duk lokacin da ya kusance ta wata irin faɗuwar gaba da razani ne suke maye shi. Ya sha ruwan mamaki matuƙa da 'yar ƙanƙanuwar yarinyar take yunƙurin gagare masa, don har lokacin da ta tunkaro sashen Sarki Abdul'aziz yana biye da ita amma ya gagara sarrafa komai a kanta, dalilin da ya sa yake rikiɗa zuwa mabambamtan hallitu don ya yi nasara a kan. Laɓe wa ya yi a jikin wata bishiyar darbejiya, yana jiran fitowarta don ya ci alwashin a wanan karon ba zai bar ta ba.
"Ina shakkun nasarar da kake hanga a kanta! Gani nake mahaifiyarta ba ta zuba ido a kanka har ka cutar da ita ba." Boka Shadda ya ji an furta a bayansa yana waigowa ya yi tozali da Dattijo Maharaz. Sai da ya turɓune fuska sannan ya furta. "Me ya sa kace haka? Ko ka manta da nawa hatsabibancin ne?"
"Ka manta wace ce mahaifiyarta da zamanin da ta yi? Tun wuri ina mai baka shawara ka haƙura, idan ba haka ba kuwa allura za ta tono garma." Dattijo Maharaz ya furta har zai wuce da sauri Boka Shaddas ya sha gabansa. "Soyayyar ɗana ce ta sa zan yi yunƙurin aikata haka, ko don ba ɗanka aka taɓa ba?" Murmushi Dattijo Maharaz ya yi ya ce. "Kuskuren da Mahaifiyarta ta aikata a baya kenan, Shaddas ka sani shi musulunci daban yake. Kuma a duniya wata hallita ba ta isa ba ta cutar da wata ba har sai Ubangiji ya ƙaddaro haka a cikin kundin ƙaddarorin kowanne bawa. Na ba ka shawara ne a silar zumuncin da ya taɓa giftawa tsakanina da wani kakanka kafin ya rasu wani abin farincikin a hannuna ya karɓi kalmar shahada.
Da za ka tuba ka koma ga Allah da ya fiye maka wannan mummunar turbar da kake kai wacce ba za ta dire ka ko ina ba sai a yankin azaba da uƙuba." Daga haka Dattijo Maharaz ya wuce ya ba wa Boka Shaddas hanya. Wani tunani ne ya faɗo wa Boka Shaddas har sai da ya saki murmushi a fili sannan ya wuce kogon tsafinsa.
Fargi ta jima a wurin bishiyar kukar da suke bautawa tana kai mata kokenta ba ita ta bar wurin ba sai kusan doshin Asuba, kai tsaye Masarautar Sarki Sulaiman ta wuce a saitin windonsa ta tsaya cikin surar tantabara ta fara kaɗa fuka-fukanta tana kuka. Jin haka ya sa da Sauri Sarki Sulaiman ya ta shi ya fice duk da har lokaci ba a kira assalatu ba. Da hannu ya ɗauki tantabarar ya zagaya ɗakin hutawarsa sai da ya rufe ƙofar sannan Fargi ta yi girgiza ta dawo cikin ainihin surarta. "Yanayinki kaɗai shi ya tabbatar mini akwai wani al'amari da yake faruwa." Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jin wani abu na yi mata yawo a rai, a hankali ya matsa gabanta ya riko ta tamkar wacce take jira sai kawai ta fashe da matsanancin kuka. "Gabansa ne ya ci gaba da faɗuwa, bai hana ta ba sai da ta yi mai isarta yana shirin yin magana ta furta.
"Ina ƙaunarka Sadaukina! Kuma ina ƙaunar abin cikina, ina yi mata so mai tsanani soyayyar da kowacce uwa take yi wa 'yarta. Don Allah ko bayan rayuwata ka kula mini da ita." A razane Sarki Sulaiman ya miƙe tsaye ya furta. "Me kike faɗa haka Fargi? Me yake faruwa da ke ne?" Murmushin ƙarfin hali ta ƙirƙiro ta share hawayenta sannan ta ce. "Sai wani abu ya faru Sarkina? Babu wani abu da ya faru da ni kawai ina tsoron kada nan gaba danginka su ƙi karɓarta a matsayin 'yar cikinka!" Guntun tsaki ya saki haɗe da ajiyar zuciya, sai da ya koma ya zauna sannan ya ce. "Na yi tsammanin wata maganar za ki faɗa, kada ki damu Fargi. 'Ya ta za ta taso cikin kulawar mahaifi da zuri'arsa. Bayan wannan akwai wani abu?" Kai ta girgiza masa tana bin sa da kallon tausayi.
Ta miƙa masa wasu wuri guda uku, ta sake miƙa masa wata ƙanƙanuwar jakar fata. Sannan ta ɗauko wata ƙatuwar azurfa ta haɗa masa da su, da mamaki yake bin ta kallo ganin yana buƙatar ƙarin bayani ta ce. "Ka yi mini alƙawarin za ka aiwatar da abin zan gaya maka."
"Na amince, ina jinki."
"Ka shafa jinin jikinka a jikin kowanne abu da na baka, sai ka ɗauke shi zuwa bakin kowacce irin bishiyar kuka ka haƙa rami mai ɗan zurfi ka binne. Wanne suna kake muradin a sanyawa abin da zan haifa?" Jim Sarki Sulaiman ya yi sannan ya furta.
Gudun kada su fahimci yanayin da yake ciki ya sa Sarki Sulaiman ya saki murmushi ya furta, "Suna mai matuƙar muhimmanci da ma'ana!" Daɗi ya mamaye Jawahir, ta dubi Kamalu da ke sunkuye da kai ta yi masa gwalo haɗe da faɗin. "Ka ji dai mai ranka shi daɗe ya ce suna ma ba irin naka ba." A wannan karon gabansa har ya fi na baya faɗuwa, bakinta ya bi da kallo yadda take sarrafa shi tamkar yadda Fargi take magana.
"Kada sake shiga harkarta Kamalu, ka bi ka hana yarinya sakat idan ba haka ba ranka zai ɓaci." Sarki Abdul'aziz ya gargaɗi Kamalu.
"Allah ya taimake ka wanki fa kawai ta yi mini." Da sauru Sarki Abdul'aziz ya dubi Kamalu, ya sake haɗe fuska ya ce. "Mun soke wannan aikin daga yau, idan kuna buƙatar a yi muku wata hidimar ku nemi Bayi a saka su." Cike da ladabi Kamalu ya amsa yana jin haushin Jawahir a ransa. Sarki Abdul'aziz zai sake yin magana suka ji sallamar Galadima shi da Muhsin.
Kallo É—aya Sarki Abdul'aziz ya yi masa ya fahimci akwai abin da ya kawo shi, ganin Sarki Sulaiman ya sa Galadima ya É—an haÉ—e fuska. Sai da suka gaisa sannan Galadima ya furta. "Ranka shi daÉ—e muhimmiyar magana gare ni, kasan dai ko da ka kasance kai ne Sarki mu kuma yayyanka ne dole mu..."
"Galadima a tsumaye mu muna ganawa da Mai martaba, idan muka fito za mu tattauna."
Sarki Abdul'aziz ya katse shi cikin hanzari, don ya san maganar da Galadima zai kawo masa ba mai daÉ—i ba ce.
"Ka ga Abdul'aziz wannan maganar ta yi daidai da lokacin yin ta, domin faɗuwa ce ta zo daidai da zama. Ga ka ga Sarki Sulaimanu ga yaron nan Muhsin yanzu me ya rage? Ko ka fi son sai ya tafi idan ya ɗauko magnar ka ce kun riga da kun gama yanke hukunci? To ba za ta saɓu ba, yaron nan ya je ya same ni da magana don haka ni ne gaba da kai dole zan iya yanke hukunci a kan abin da ya kamata." Galadima ya yi maganar cikin haƙiƙancewa don wannan botsarewar da Muhsin ya yi ba ƙaramin daɗi abin ya masa ba, ko ba komai ya samu kafar da zai cusa 'yar wurinsa ga Muhsin tun da ya nuna ba ya son haɗin da mahaifinsa zai yi masa. Kunyar duniya ta lulluɓe Sarki Abdul'aziz, ya sauke gwaron numfashi ya nuna can gefe sannan ya furta. "Bismillah muna sauraronku." Cikin gadara Galadima ya zauna, Yarima Muhsin ya ja ƙafafuwa ya zauna yana sunkuyar da kai ƙasa.
"Sarki Sulaimanu ka san dai Abdul'aziz ƙanina ne wurin na biyu, amma da yake bai ɗauke ni da ƙima ba sai da kuka ci kuka cinye a maganar auren yaran nan ba tare da an sanar da mu komai ba..."
"Galadima a tafi kai tsaye." Sarki Abdul'aziz ya katse shi rai a ɓace.