← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 86

Sashe 82

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannu a hankali cikin Fargi ya ci gaba da girma har ya kai watanni tara, a madadin ta ɗan murje ta ciko sai ya zamana wata irin rama take yi saboda tashin hankali. Musamman waɗansu irin munanan mafarkai da take yawan yi a wannan lokacin, ta so sanar da mahaifiyarta halin da take ciki amma gudun tashin hankalinta ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Tun wayewar garin ranar ta tashi da ɗan ciwon baya da mara sama, amma da yake bai yi mata tsanani ba sai take ta gudanar da al'amuranta. Tana nan zaune saƙon kiran Shugaba ya je mata, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa zuciyarta ta fara saƙa mata miyagun zantuka a ranta. Da ƙarfafa gwiwar mahaifiyarta ta samu damar fita ta nufi kogon tsafinsa, kafin ta ƙarasa ta hangi mahaifinta zaune a bakin bishiya da alama hutawa yake. Har za ta gifta shi sai zuciyarta ta fisge ta zuwa wurinsa don haka ta ƙarasa ta zauna a gefensa.

"Na tafka maka babban kuskure da laifi mai girma mahaifina. Amma ina mai neman afuwa da yafiyarka don girman tsafi da sihirin da ka gada a wurin mahaifiyarka ka yi haƙuri ka yafe mini." Ta tsinci kanta da furta masa haka, don haka kawai take ji a jikinta wani mummunan al'amari na iya faruwa da ita, sai da ta saka mahaifinta ya yi mata alƙawarin ba zai hukuntata ko azabatar da ita b sannan ta fayyace masa duk abin da yake tsakaninta da Sarki Sulaimanu har zuwa cikin jikinta.

"Amma Shugaba ya san da wannan maganar?" Mahaifinta ya wurga mata tambaya zuciyarsa na zafi, ta sanar da shi yadda suka yi da Shugaba Zurufu tun daga farko har ƙarshe har zuwa yarjejeniya da sadaukarwar da ta yi da abar bauta.

"Babban kuskuren da kika tafka kenan Fargi, tun kafin na haifi yayyanki ba ma ke ba na san waye Shugaba. Na rantse da matsayin da na ba wa tsafi a matsayin madogarata Shugaba ba zai bar ki haka ba matuƙar ba ki bi abin da yake buƙata ba. Kuskure ne tun farko kika tafka shi, na sha faɗa miki abin da babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala ba zai gano shi ba."
"Ka gafarce ni mahaifina." Ta furta cikin kuka da tashin hankalin ganin fushin mahaifinta.

"Duk rintsi ni mahaifinki ne Fargi, a tsammanina tun da kina shirin zama mahaifiya ya kamata ki fahimci tasirin soyayyar da ke tsakanin ɗa da mahaifi. Ba zan taɓa juya miki baya ba sai dai ina tsoron abin da Shuga zai iya zartarwa, ina tsoron hukunci da zalincinsa..."
"Ya kamata a ce mun dagakatar da tsoron Shugaba daga cikin zuri'armu, Shugaba ba shi ne abin bautarmu ba don haka bai cancanci ya dinga bautar da mu yadda yake so ba." Fargi ta katse mahaifnta.

"Ba yanzu ba Fargi! Ba a yanzu nake hango bijire wa Shugaba ba sai dai ko zuwa wasunmu masu zuwa a nan gaba." Cikin rauni mahaifinta ya amsa mata.

"Tabbas ba a yanzu ba amma koda ba ragowar numfashi a tare da ruhina, ina fatan jinina ya zama silar wargajewar duk wani tasiri na Shugaba, da wannan mummunar al'adar da aka sa a gaba. Kuma jikina yana ba ni sauyi na gab da zuwa mahaifina, har a ciki zuciya da ruhina ina jin tamkar ni ce wacce zan zartar da wannan sauyin. Don matsayin abar bauta ka maimaita kalaman nan nawa a gaban Shugaba matsawar hakan ya faru a nan gaba." Ta ƙarasa maganar tana miƙewa zuwa kogon tsafin Shugaba Zurufu, da kallo mahaifinta ya bi ta yana maimaita kalaman cikin tsinkewar zuciya.

"A yau wa'adin kwanakin da na ɗibar miki suka zo ƙarshe game da maganar da muka taɓa yi da ke a baya. Fargi!" Ta ji Shugaba ya kira ta da wata irin murya, kafin ta amsa ta ji ya ci gaba da cewa.

"Kada ki raina mini hankali domin ko mahaifinki a tafin hannuna yake sai yadda na sarrafa shi ba ke ba. Na hangi kusantowar abin cikin zuwa duniya, a yau ba sai wani lokaci ba za ki damƙa mini tasirin tsafinki idan ba haka ba zan yaye miki laluben da kike taƙamar shi ne rufin asirinki. Zan bayyanawa kowa abin da kika aikata kuma sanin kanki ne irin ɗanyane hukuncin da ake zartarwa..."
"Tura ta riga da ta kai bangi Shugaba! A baya na yi makauniyar biyayya a gare ka, saɓanin yanzu da na san ciwo da 'yancin kaina. Duk wani hukunci da za ka ɗauka a shirye nake da na fuskance shi matuƙar zai kawo sauyi a rayuwar da zuri'armu take ciki, zan jure duk wata uƙubu daga gare ku kuma zan san duk yadda zan yi domin na tseratar da abin da yake cikina." A razane Shugaba Zurufu ya dube ta, ya sauke ƙwayar idonsa a kan cikin jikinta da ya rairaye ya yi ƙasa, murmushi ya yi mata sannan ya furta. "Ko a yanzu kin nuna mini ke rainona ce Fargi, don haka ni kuma zan nuna miki ba kada kura ke da wuya ba a feɗe ta shi ne aiki." Daga haka Fargi ta fice daga kogon tsafin kai tsaye ta nufi bishiyar abar bauta.

Kamalu na lura da yanayin jikin Malam Umaru duk wani abin buƙata shi yake yi masa, amma lokaci sai ya lura da rikicewar jikin nasa duk da ba magana yake iya yi ba, jikinsa ya ji ya ɗauki zafi zau cikin tashin hankali ya sa aka kira masa Waziri da waɗansu manyan hadiman fada don ya san ko ya kira 'yan uwan mahaifinsa su Galadima ba lallai su saurare shi ba.

"Baba Waziru jikin Malam Umaru ya yi tsanani ya kake ganin za a yi." Kamalu ya furta cikin damuwa.
"A aika yanzu a zo da Malam Sharu mai magani, In shaa Allah zai samu lafiya." Waziru ya ba da umarni.

Ba a ɗauki lokaci ba sai ga Malam Sharu mai magani ya ƙaraso rataye da jakar magungunansa na gargajiya.

"Zan... sha... ruwa..." Malam Umaru ya furta murya na rawa. Tun da ya kwanta wannan ciwon sai a wannan lokacin ya samu damar yin magana, cikin hanzari Kamalu ya tallafo shi ya ba shi ruwa sai dai kaɗan ya samu ya sha ya ƙware. Sai da tarin ya lafa masa sannan ya furta. "Wani... ne... ya ɗauke mini... Jawahir. Don Allah... Mai gado a sanar da Takawa... a nemo mini ita. Kuma a isar mini wasiyyata... wurinsa idan Jawahir ta... samu miji ya taimaka ya zama waliyinta..." Tari ne ya sake sarƙe shi cikin tarin ya furta. "La'ilaha'ilallah... Muhammadur Rasulilla..." Daga haka harshensa ya sarƙe numfashinsa ya shiga kaiwa da kawowa, kafin daga bisani ya ɗauke gabaɗaya. Cikin kiɗima Kamalu ya fara jijjiga shi yana kiran sunansa, ganin haka ya sa Waziri ya janye Kamalu sannan ya ƙarasa ya rufe masa idanu. Malam Sharu mai magani da sauran mutanen da ke tsaitsaye suka fice jikinsu a sanyaye.

Tamkar ƙaramin yaro haka Kamalu ya rushe da matsanancin kuka, don idan aka cire labarin mutuwar mahaifiyarsa da wahalhalun da ta sha wannan mutuwar ita ce mutuwa ta biyu da ta dake shi a duniya. Tun tasowarsa ya taso da bawan Allah mai matuƙar haƙuri, karamci da sanin yakamata. A ɓangare ɗaya kuma Jawahir ta faɗo masa da halin da za su shiga ita da Mai gado idan suka dawo suka samu labarin mutuwarsa.

Gama jin kalaman aljana Zumjuttu ya harzuƙa Sarki Sulaiman, wani irin ɗaci yake ji a zuciyarsa nan take jikinsa ya fara karkarwa saboda tashin hankali, a guje ya ƙarasa ya shaƙi wuyan aljana Zumjuttu yana girgiza ta. "Ke annamimiya ce azzaluma maciciya, sai na kashe ki da hannuwana." Da hannu ɗaya ta ture Sarki Sulaimanu har sai da ya kusa kai wa ƙasa, ta saki murmushi tamkar abin da ya yi mata bai yi mata ciwo ba.

"Ban san adadin irin waɗannan kalaman naka da na saurara a tsakar kunnuwana ba, don haka ka adana kalamanka idan ba haka ba yanzu kai ma za ka ƙarasa inda Fargi ta tafi. Wai ka san ma dalilin da ya sa abar bauta ba ta bi ta shafinka ba? Saboda ba ka san an haifa maka 'ya ba ballanta ka shiga duniya nemanta. Kuma na tabbata da ta san za ku sadu da juna da tuni kai ma ta hallaka ka don kar ka ba ta matsala." Zumjuttu ta furta cike da gadara.

Ilahirin mutanen wurin jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, tsararu daga cikinsu har da masu zubar da hawaye. Mai gado ta dubi Zumjuttu cikin kuka ta ce, "Tabbas biri ya yi kama da mutum domin tun da na zo duniya ban taɓa cin karo da gawar da ta tsaye mini a rai kuma ta ba ni mamaki ba tamkar ta mahaifiyar Jawahir. Don Allah don girman Allah da zatinSa ku ƙyale yarinyar nan tun da kun hallaka mahaifiyarta..."

"Mu je ki kai mu wurin abar bautarku mu gana da ita don ina son jin daga bakinta." Dattijo Maharaz ya yi maganar cikin ɓacin rai. Cikin halin ko-in-kula ta amsa masa ta wuce gaba hannunta riƙe da Jawahir da ta yi shiru sai bin mutane take da kallo, don jin abin take tamkar a mafarkinta.

Gabaɗaya mutanen da ke gaban kogon dutsen Shugaba Zurufu ne suka rufa wa su Dattijo Maharaz baya, wasu daga cikinsu suna murnanr ganin yadda Abar bauta za ta fusata ta yi musu mummunan hukunci, yayin da wasu suke zumuɗin ganin yadda dambarwar za ta ƙare.

"Ku faÉ—i ku yi sujjada a gaban Abar bauta." Zumjuttu ta furta.
"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaÉ—ai muke bautawa babu wata hallita ko mahalukin da ya isa ya sa mu yi masa sujjada." Kamar haÉ—in baki Sarki Abdul'aziz da Dattijo Maharaz suka furta lokaci É—aya.

Wani irin rugugi suka ji tamkar hadari ya haÉ—o, wasu daga cikin mutanen jin haka ya sa suka arce don gudun kada fushin Abar bauta ya faÉ—o kansu.

"Kun aikata babban zunubi don haka dole na hukunta ku, amma kafin nan me ya kawo ku wurin bautar da ake yi miki."Abar bauta ta faɗa cikin isa da ƙasaita.
Dattijo Maharaz ya zayyane duk abin da suka ji daga bakin Zumjuttu, sannan ya É—ora da cewar.
Chapter 82 · 0% Book details