← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 86

Sashe 79

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah kada ka cutar da ni Basiru, don na san nahaifinka ya gama horar da kai al'amuran tsafi da sihiri." Fulani Umaima ta yi maganar murya can ƙasa saboda galabaita.
"Kin san an ce kowa ya biya allonsa ya wanke, ba don kin ɓata rawarki da tsalle ba ai da tuni kina can kina cin duniya da tsinken tsire. Yanzu dai tun da kin tsinci talatarki a laraba haƙuri ya zame miki dole, kin ga nan gaba idan aikina ya biyo ta kanki shi kenan." Muhsin na gama maganar ya ture Fulani Umaima a ƙasa, tsafatacciyar askar hannunsa ya sa ya fara reɗar gashin kanta yana zubawa a cikin wani ƙanƙanin ƙoƙon tsafi, sai da ya aske gashin kanta tas sannan ya yanki faratan ƙafafuwanta. Bayan ya gama ya soki cinyarta da askar nan take jini ya fara tsattsafowa ya dinga lakuta da wani farin ƙyalle yana goge jinin. Tun da ya fara gogar jinin jikinta ta fara jin wani irin zuuu kamar ana zuƙe jininta, tana nan zaune hawaye ya wanke mata fuska babu yadda za ta yi, tana gani ya gama ya fice daga ɗakin. Sai ya fice Jakadiya ta samu sukunin sauke ajiyar zuciya, duk da ta san wace ce Fulani Umaima a ƙwarewa wurin mugunta amma ganin yadda siffa da kammainta ya sauya sai da ta bata tausayi, duk da ita ɗinma abar tausayin ce.

Sarki Abdul'aziz shiru ya yi bayan ya gama sauraren Dattijo Maharaz, ya dubi Kamalu da lokaci guda ya ga ya zabge sannan ya mayar da kallonsa wurin Dattijo Maharaz. "Yanzu me ye abin yi tsoho mai ran ƙarfe?"
"Tafiya ƙasar Sarki Sulaimanu! Don haka ne ma jiya da daddare ban ziyarce ka ba."
"Amma kuma mahaifiyarta tana cikin kiÉ—ima bisa abin da ya faru da mai gidanta, kuna ganin za mu iya sanar da ita abin da yake faruwa?" Sarki Abdul'aziz ya tambaya.

"Zuwa da Mai gado wannan garin yana da matuƙar muhimmanci, ni na san su waye al'ummar rumzu kuma na san kafiya da taurin kansu." Dattijo Maharaz ya waiga wurin Kamalu sannan ya ci gaba da cewa. "Kamalu ka kula da Malam Umaru sai ka nemi wasu Bayin su taya ka kula da shi." Kamalu bai so haka ba amma kuma mutumci da ƙimar Dattijo Maharaz ya sa ba zai iya musa masa ba.

A safiyar wannan ranar Sarki Abdul'aziz da kansa ya sa aka shirya masa keken dokinsa da sauran tantina, mutane sun yi matuƙar mamakin jin tafiyar Takawa a rana tsaka. Tuni aka aikawa da Mai gado game da tafiyar, Kamalu tamkar zai zubar da ƙwalla a lokacin da za su tafi.

Sarki Sulaimanu yana cikin turakarsa bayan ya koma daga dubo jikin mahaifiyarsa aka sanar da shi zuwan Sarki Abdul'aziz daga Masarautar Huddam tawagarsa, duk da bai san da zuwansu ba amma nan take ya sa aka shirya musu tarba ta musamman. Ba su É—auki lokaci mai tsayi ba Sarki Abdul'aziz ya furta.

"Sarki Sulaimanu mun zo ne domin ka yi mana wata alfarma." Sarki Sulaimanu fuska É—auke da mamaki ya furta. "Alfarma kuma Sarki Abdul'aziz? Wacce iri?" Dattijo Maharaz da ke gefe ya yi shiru yana jin tattaunawarsu.

"Zuri'ar Rumzu! Zuwa gare su muke son ka yi mana iso..." A zabure Sarki Sulaimanu ya miƙe tsaye jiki na karkarwa.
"Ya aka yi ka san da su? Wannan binannan sirri ne da iya mutum biyu ne kaɗai suka da shi. Ya aka yi kasan alaƙata da..."
"Ni na sanar da shi haka Sarki Sulaimanu. Kuma mun zo ne domin neman goyon bayanka zuwa cikin waɗannan mutanen domin akwai abu mai matuƙar muhimmamci da za mu aiwatar." Dattijo Maharaz ya katse Sarki Sulaiman.

"Ko da babu kowa na fargi a wurin zan je wannan garin ballanta mahaifi da mahaufiyarta suna raye." Sarki Sulaiman ya furta sannan ya sa aka yi musu shiri suka nufi garinsu Fargi. Mai gado tun daga Masarautar Huddam kanta ya kulle, sakamakon babu wani kyakkywan bayani da aka yi mata, ba don Takawa ne a gabanta ba da ta tambayi dalilin gayyato ta da zuwa wannan garin, amma ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba ta isa ta wurga masa tambaya ba. Abu ɗaya ne ya tsaye mata a rai jin sunan Fargi don idan ba ta manta ba ta taɓa jin Jawahir ta ce ita ce take yi mata iƙirarin mahaifiyarta ce.

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Ganin ƙofar ɗakin nasu a buɗe hanhai ya sa Jakadiya ta fara jan jiki a hankali ta zo baƙin ƙofar wurin da niyyar ta fita idan ya so ko guduwa sai ta yi tun da dare ya fara yi ba lallai wani ya ganta ba.
"Idan kin tafi ina za ki je? Waye zai karɓe ki a wannan yanayin da kike ciki? Ki rufa wa kanki asiri ki koma, zamanki a wannan wurin shi ne suturarki."
"Ki gudu kawai, yanzu zama za ki yi azaba ta kashe ki?"

Tagwayen shawarwarin suka fara shawagi a zuciyarta.
"Kamar ba ki san a cikin gidan da kike ba? Kin manta ke Jakadiya ce labarinki ya gama karaÉ—e ciki da wajen masarautar nan a kan abin da kika aikata? Ki rufa wa kanki asiri kawai ki koma ciki." Zuciyarta ta sake ba ta shawara. Babu yadda ta iya a hankali ta sake jan jiki ta koma cikin É—akin, har lokacin Fulani Umaima na wurin da Muhsin ya bar ta tana zubar da hawayen nadama.

"Ban san haka duniya take yi wa mutum atishawar kaji ba sai da layinta ya zagayo kaina. Kaicon rayuwar da ba ta da amfani, ni Umaima na cuci kaina." Fulani Umaima ta yi maganar cikin galabaita da tsantsar nadana.

Abin duniya ya haɗe wa Sailuba goma da ashirin sakamakon yadda mutane suke ƙyamatarta da wulaƙantata dangane da laifin mahaifiyarta, ko guri ta je tana zama kowa yake darewa sai dai a barta ita kaɗai. Lokaci ɗaya ta fige ta rame ta lalace Uwa-uba cutar kwarkwatar da ke damunta, don ta samu ruwan da ke fita daga ƙansata ya yi sauƙi sosai. Sai a wannan lokacin da ta bambamce tsakanin tsaba da tsakuwa take dana-sanin wulaƙancin da ta dinga yi wa Bayi a baya, sai ga shi Bayin da take hantara take kyara a wannan lokacin sun fita ƙima da mutumci a idanun manyan masarautar da sauran mutanen cikin gidan gabaɗaya.

Idan ta yunƙura don ta je ta gano halin da mahaifiyarta take ciki fargaba sai ta mamaye ta, sau ɗaya ta taɓa zuwa ta gano ta ranar ko baccin kirki ba ta iya yi ba saboda damuwa. A wannan ranar ne ta yanke shawarar sake zuwa ta gano halin da Jakadiya take ciki, ta tafi da wani guntun busasshen ƙanzo a leda ta tafi mata da shi don ta san abinci sau ɗaya suke ci a wuni guda.

Duk irin dakiyar da ta gayyato wa kanta sai da warin wurin ya addabe ta, don haka ta sa hannu ta toshe hancinta tana jin wani irin amai yana taso mata. Kwamacalar fitsari da tsutsotsin da ke cikin ɗakin ya sa Sailuba ba ta iya shiga ɗakin ba, sai daga bakin ƙofa ta iya wurga wa mahaifiyarta ledar ƙarzon da ko daka shi ba ta yi ba. Kamar kaji haka suka fara kokawa a kan ledar sabida yunwar da ke addabarsu, suna cikin haka ledar ta yage suka ci gaba da ɗibar na ƙasa suna cinyewa. Wani irin kuka ne ya zo wa Sailuba ta juye za ta bar wurin ta hangi wasu ƙaratan Dogarai sun nufo wurin da ƙofa a hannunsu, basu kula ta ba suka fara kiciniyar mayar da ƙofar wurin ganin haka ta sa ta wuce sashensu Bayi zuciyarta a dagule.

Gyaɗa kansa Mahaifin Fargi ya yi ya ce mata. "Amma Fargi me ya sa kika yi nisa da mu? Me ya sa kika guje mu? Mun jima muna bulayin nemanki amma ko mai kamarki ba mu taɓa gani ba sai a yau da na yi tozali da yarinyar nan."
"Akwai rikitattun labarai da zan bayar game da Fargi, amma sai na kai Jawahir binne littafin labarin Hidaya sannan ta É—auko sihirtacciyar takobin da ta Hidayan ta binne. Da sauri Jawahir ta fara ja da ba ya ta ce. "Don Allah ki kaini wurin Inna na san tana can cikin damuwa." Jawahir ta furta kamar za ta yi kuma.
"Innarki ta taho yankin nan kada ki damu Jawahir." Shiru Jawahir ta yi ba ta amsa ba. Tana nan tsaye mutane suka ci gaba da tuttuɗowa ana shigowa cikin kogon dutsen, kallonsu ta fara yi ɗaya bayan ɗaya tana sakin murmushi sannan ta riƙe hannun Jawahir sosai ta furta musu. "Ku dakace mu zuwa wani ɗan lokaci kaɗan." Daga haka suka ɓace daga wurin ba su tsaya a ko ina ba sai a cikin wata farar sahara, bakin wani koren kogi suka ƙarasa ruwan cikinsa garai-garai kana iya kallo duk abin da yake ciki. Sannu a hankali Fargi ta fara jan Jawahir har cikin ruwan, wani irin sanyi ta ji yana ratsa ilahirin jikinta. A tsamaaninta kogin mai zurfi ne sai dai har suka je tsakiyarsa a yadda yake haka suke tafiya.

"A shakaru masu yawa da suka wuce ainihin gurin nan ba teku ba ne, ko lokacin da Hidaya ta binne takobinin babu ruwa a gurin nan. Saka hanunki a nan ki ɗauko takobin nan." Fargi ta yi maganar tana nuna wa Jawahir wani zabgegen farin takobi da ke tsaye cak a cikin gidansa yana walwali da ɗaukan ido. Babu musu Jawahir ta saka hannunta za ta ɗauka ƙam ta ji takobin ya fara fisgarta can ƙasan ruwa, a tsorace ta fara kwarara ihun sai bayan wani lokaci ta ji komai ya lafa sannam ta riƙo takobin hannun nata.
Chapter 79 · 0% Book details