Sashe 68
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da waɗannan Dattijan sarakunan suka ci suka sha suka huta sannan Sarki Abdul'aziz ya gabatar musu da Kamalu da matsayinsa a wurinsu. Mahaifin Fulani babba har sai da ya zubar da ƙwalla sannan ya rungume Kamalu yana jin ƙaunarsa a ransa, ɗaya bayan ɗaya haka Mai martaba da manyan yayyan Fulani babba suka dinga jan Kamalu har su Khadija suka rungume shi suna kuka, tare ta labarta masa irin halin ƙuncin da mahaifiyarsu ta shiga a lokacin da tana raye, musamman Khadija da ita ta fi sanin sirrin damuwar da ke damun mahaifiyarsu. Sai da wurin ya lafa da hatsaniya sannan Sarki Haruna ya fara magana.
"Sarki Abdul'aziz muna zaune takarda ta iso gare mu dangane da 'yata Umaima, na gagara fahimtar saƙon da ke ciki musamman da a ciki ka ce babu buƙatar a sanar da mahaufiyarta abin da yake faruwa." Tun da ya fara magana Fulani Kilishi ta yi zuru gabanta na faɗuwa, don tun da suka zo ba su ji a fitar sunan Umaima ba, kuma ba ta samu damar ƙeɓewa da Muhsin ba ballantana ta ji halin da mahaifiyarsa take ciki.
"Allah ya taimake ka ina ganin waƙa a bakin mai ita ta fi daɗin sauraro, ayi mini afuwa zan gabatar da waɗansu mutane domin tattaunawarmu ta samu abin da ake buƙata." Amsa masa ya yi sannan Sarki Abdul'aziz da kansa ya shiga uwar ɗakinsa ya yi magana a daidai shurin Dattijo Maharaz, bayan ya gabatar masa da abin da yake tafe da shi Dattijo Maharaz ya amsa da cewa. "Babu damuwa Sarki Abdul'aziz zan zo gare ku yanzu nan, don haka za ka iya sa wa a kawo ita Umaima domin a yi komai a fili ba tare da kowa ya ga an zalince shi ba." Cike da ladabi Sarki Abdul'aziz ya amsa wa Dattijo Maharaz sannan ya miƙe ya fice, bayan komawarsa ya bada umarnin a je a taho da Jakadiya da Umaima.
Sarki Abdul'aziz ya shiga babu jimawa sai ga Dattijo Maharaz sun shiga ɗakin, hannunsa riƙe da Boka Bamaguje suna tafe yana dogara sanda jikinsa na karkarwa. Daga can gefen bangon da ke fuskantar su Mai martaba Haruna suka zauna, suna zama aka shiga da su Fulani Umaima aka watsar da su a gefe tamkar kayan wanki, tun da suka shiga ɗakin ya dum! Saboda wari nan take kowa ya sa gefen rigarsa ya toshe hancinsa.
"Wannan tattaunawar ba za ta yiwu a haka ba har sai an tsaface su Sarki Abdul'aziz, shi kansa Bamaguje yana buƙatar kintsawa." Dattijo Maharaz ya furta.
"Babu wata kintsawa da zan yi ni wanka bai dame ni ba, shin ka taɓa ganin Boka ko mai sihiri irina cikin tsafta ne? Mu gabatar da abin da yake gabanmu domin a yanzu haka akwai wata tarzomar da ke dumfaro ni, bayan wannan kuma ba ni da wadatacciyar lafiya kai shaida ne Maharaz a lokacin da ka je ka taho da ni." Bamaguje ya furta cike da ƙagauta, ganin Bamaguje na som ba su matsala ya sa Sarki Abdul'aziz ya sa aka fara shiga da turarrukan wuta kala-kala ana sakawa domin samun sauƙin warin da yake addabarsu. Har Bamaguje zai fara magana Takawa ya sa aka kira su Inna wuro don ba ƙaramin girma da mutumci yake ba su ba. Sai da Sarki Abdul'aziz ya gabatar wa Bamaguje mutanen ɗakin sannan ya tsahirta suka zuba masa ido gabaɗaya suna jiran jin daga gare shi.
Tun shigar Bamaguje Mahaifiyar Fulani Umaima take ta zabga gumi cikin tashin hankali, kuma yanayin da Fulani Umaima take ciki na sauyawar kammani ya sa babu wanda ya gane ta.
"Sarki Abdul'aziz wannan ai karatun baya ne ake son ƙara maimaitawa, me kuke so na ce muku bayan faɗin Umaima ɗiyar cikina ce? Ga Kilishi nan ita shaida ce, tun tana budurwa take ziyartar wurina har bayan aurenta da Sarki Haruna, ita ta sani har yarjejniya muka yi yanzu kuma me ya rage." A zabure Sarki Haruna ya furta. "Me wannan mashirikin yake nufi? Kana nufin Umaima 'yata ita ce 'yar cikinka? Sarki Abdul'aziz Ina Umaiman take ne?" Da hannu Sarki Abdul'aziz ya nuna wurin da Fulani Umaima take kwance, lokaci ɗaya jikinsu ya yi sanyi mamaki halin da take ciki ya kama su. Ganin Mai martaba Sarki Haruna na son nuna gardama ya sa Dattijo Maharza da Bamaguje suka fayyace masa komai tun daga farko har ƙarshe, idanunsa na zubar da ƙwallah ya waiga wurin Fulani Kilishi ya ce. "Shin abin da wannan Bokan ya faɗa haka ne?" Kuka ta fashe da shi cikin nadama ta ce. "Ka gafarce ni ranka shi daɗe wallahi sharrin shaiɗan.."
"Sharrin shaiɗan ko? Ki je Kilishi ke da Allah, amma ba zan iya ci gaba da zama da ke ba na sake ki saki uku! Ban san hukunci da Abdul'aziz zai yanke ba amma matuƙar ya sallame ta ke za ki ɗauki 'yarki ki tafi da ita." Murya na rawa hawaye na zuba ya waiga wurin Sarki Abdul'aziz sai da ruƙo hannunsa cikin ƙwalla ya ci gaba da cewa.
"Ka gafarce ni Sarki Abdul'aziz bisa duk rashin imanin da Umaima ta aikata, duk hukuncin da ya dace ka ɗauka a kanta kuma idan har akwai wani taimako dangane da hukuncin da za ka yanke a kanta a shirye nake na ba ka gudummawa ɗari bisa ɗari. Zan wuce gida don zuciyata zafi take idan na ci gaba da kallon waɗannan miyagun mutanen zuciyata za ta iya bugawa." Ya ƙarasa maganar yana yunƙurin miƙewa, fadawansa suka kare shi ya tashi har ya fara tafiya ya waigo ya kalli Fulani Kilishi. "Kin ci amanata kin zalince ni ki je ke da Allah, ga mahaifin 'yarki nan idan kin gama idda sai ki aure shi ki ɗora daga inda kuka tsaya." Daga haka ya saka kai fice zuciyarsa na yi masa ɗaci. Fulani Umaima ban da ruwan hawaye babu abin da take yi, wahala ta sa ko magana ta kasa yi.
Fulani Kilishi suka ji ta tsuntsire da dariya ta fara fisgar gashin kanta tana kai wa baki. Da sauri Sarki Abdul'aziz ya sa aka fita da ita ya bayar da umarnin da a fice da ita daga cikin masarautar gabaÉ—aya.
Lokacin da Dogarawan suka fita da ita keken dokin su Sarki Haruna ya fito, ganin haka ya sa ta bi keken dokin da gudu tana sheƙa dariya tana ce wa sai ta bi Sarki Haruna. Da Dogaran suka ga ta rage musu aiki sai suka juya suka koma cikin masarautar cike da jimamin abubuwan da yake faruwa.
Shiru ɗakin ya ɗauka kowa da abin da yake jimantawa a zuciyarsa, Yarima Muhsin tun da aka shigo da mahaifiyarsa ya kauda kansa gefe yana zubar da ƙwalla. "Duk da ta aikata babban laifi mafi girma ita ɗin uwar 'ya'yanka ce, me ya sa ka sa aka aikata mata wannan mummunan hukuncin? Wannan yaron Kamalu dama can Allah ya ƙaddara wannan ƙaddarar a kansa, yanzu ka ga a silar shi waɗannan bayin Allahn suka shigo cikin masarautar nan. Ka ga kuwa bai da..." A ɗan hanzarce Sarki Abdul'aziz ya katse Mai martaba mahaifin Fulani babba don ji yake zuciyarsa na tafasa.
"Ranka shi daɗe kada ku manta ita fa ta raba mu da uwargidanmi kuma uwar 'ya'yanmu, ta raba shaƙuwar tsakanin ɗa da mahaifiyasa, hasali ma ta raba ta da duniyar bakiɗaya." Sarki Abdul'aziz ya ƙarasa maganar muryarsa tana rawa. "Wallahi ko da Umaima ko babu Umaima sai Fatima ta mutu a wannan lokacin, kada ka manta kowanne bawa a rubuce kundin ƙaddararsa yake tun kafin zuwansa duniya, duk wani ciwo da ka ga ya samu Fatima dama can Ubangiji ya ƙaddara mata faruwarsa sai dai ta kasance ita ce sanadinta." Ajiyar zuciya Sarki Abdul'aziz ya sauke ya ɗan haɗiyi yawu mai ɗaci, sannan ya russuna cikin girmamawa ya furta. "Ku gafarce mu ranka shi daɗe idan kalamanmu za su sosa muku rai, amma Allah Ya sani ba za mu iya yafe mata cin kashin da ta aikata wa Fatima ba." Daga haka Sarki Abdul'aziz ya sa aka sake fitar da Jakadiya da Fulani Umaima zuwa ɗakin duhu.
Kalaman da Sarki Abdul'aziz ya furta ba ƙaramin faranta zuciyar mahaifiyar Fulani baba da 'yan uwan ya yi ba, Dattijo Maharaz ya dubi Mai martaba ya ce. "Ranka shi daɗe ni kuma wata alfarma na zo nema ban sani ba ko zan iya samu a wurinka?" Gabaɗaya mutanen ɗakin suka tattara hankulansu wurin Dattijo Maharaz, "Ina sauraronka Dattijon arziƙi wacce irin buƙata ce?"
"Ina nemar wa Sarki Abdul'aziz arziƙin sake nema masa iri a wurinka, ina nufin ina nema masa auren ɗaya daga cikin 'ya'yanka domin ta maye gurbin Marigayya." Wani daɗi Sarki Abdul'aziz ya ji har cikin ransa, ya ɗan saki murmushi amma shi kansa ya san zai yi wuya mai martaba ya sake aura masa wata 'yar ta sa.
"Mun karɓi alfarmarka Dattijo Maharaz, za mu duba a cikin iyalanmu wacce ta fi dace wa da shi. Bayan ita ko akwai wata buƙatar?"
Tashinta daga bacci kenan ta ji kanta ya sara mata, ta jima ba ta ji irin haka ba don haka ta ɗan jingina da bango tana murza idanu. Ba ta ga Mai gado a ɗakin ba kuma da ma ta san ba lallai ta ganta na tun da suna can suna hidimar abincin tarbar baƙi, lalubulen ɗakin ta ji yana kaɗawa a hankali ta kai idanunta wurin. A firgice ta miƙe tsaye gabanta na faɗuwa tsoro ya mamaye ta, kamar yadda ta saba ganinta cikin shirgarta ta kullin yau ɗin ma a haka take a tsaye tana sakar mata murmushi. A ɗan tsorace Jawahir ta takure a bango, sai ta ga matar ta shigo cikin ɗakin ta zauna a gefen gadon da take kai.
"Me ya sa a kullin ba kya sabo da ni? Me ya sa kika tsoron tozali da ni? Ko kinsan tsoro ba ya daga cikin hali da É—abi'ata me ya sa muka bambamta da ke a fagen halitta da sura?" Jawahir ta zuba wa matar da a kullin suka haÉ—u take tunasar da ita cewar ita mahaifiyarta ce.