Sashe 30
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Inna wuro yanzu shi kenan rayuwar Bayi a haka za ta ƙare? Ba mu da 'yanci ba mu da gata ba mu da lokacin kanmu ballanta mu amfani kanmu da kanmu? Inna wuro na gaji ki zo mu bi dare kawai mu gudu ina ganin sai mun fi samun kyakkayawar rayuwa." Ƙwalla ta zubo idanunta jin hannunsa yadda ya bushe ya yi tauri kamar katako a saman hannunta, duk wahalar da suke sha nasu nafila ne a kan mazan cikin masarautar.
"Kamalu haka Allah ya ƙaddara mana, shi ne gatanmu yana kallon duk halin da muke ciki. Idan muka ce za mu gudu ina za mu je?" Kamalu ya cusa sandararran tuwon dawar bakinsa yana turawa da ƙyar yana share hawaye, a hankali Inna wuro ta riƙa lallashinsa har ya watsar da maganar guduwa daga cikin gidan. Inna wuro ita da Mai gado ta su ta fi zuwa ɗaya duk cikin sashen Bayin, sai dai kuma 'ya'yansu ko kaɗan ba sa jituwa duk da sun kasance ba sa'annin juna ba. Ko kaɗan Kamalu ba ya taɓa zama wurin da Jawahir take zaune, haka kawai ya ji ya tsani yarinyar musamman idan ya kalli ƙwayar idonta da yake ganin wata murgujejiyar bishiyar kuka a ciki. Ita kuma Jawahir duk lokacin da Kamalu ke zaune a wurin da take wani irin zafi ne yake ratsa ta, sannu a hankali kuma sai ta riƙa ganin tururuwa na fita daga jikinsa duk wacce ta ƙarasa jikinta sai dai ta ji tana gasa mata cizon da ke ƙoƙarin ɗaye fatarta. Dalilin da ya sa Kamalu na zama ita kuma za ta riƙa zunduma ihun neman agaji.
Yana gama cin abinci ya miƙe ya zagaya ta can bayan rumfar bayi ya ci gaba da tafiya har ya isa bakin bishiyar tsamiyar da ke kallon bayan ɗakunan Bayin. Tun bai kai ga zama ba ya ji muryar dattijo Maharazu. "Assalamu alaikuma!" Bai san ya yi rashinsa na kwana biyu ba sai a yanzu da ya ji muryarsa, "Dama kana nan wai ina ka shiga?" Kamalu ya tambayi Maharzu cike da yarinta.
"Kada ka bari rauninka ya bayyana a fili ta yadda magauta za su fahimci lagonka har su nemi cin galaba a kanka. Kalli can wurin." Dattijo Maharaz ya furta masa haɗe da nuna masa bayansa. Wani yaro ya gani kusan sa'ansa ne a shekaru kwance a ƙasa sai birgima yake yi yana ɗiban ƙasa yana ci yawu na dalala daga bakinsa. Hankali a tashe ya furta.
"Waye wancan kuma me yake yi a wurin nan?" Murmushi Dattijo Maharazu ya yi ya kama hannun Kamalu suka ƙarasa gaban Abubakar sannan ya furta, "Idan har ɗan sarkin Masarutar nan zai kasance haka me kake tsammani a kanka?" A razane Kamalu ya dube shi, "Ka na nufin wannan a masarautar nan yake kuma ɗan sarki ne?"
Kafin Dattijo Maharzu ya ba shi amsa Kamalu ya ga matashin ya ɗago yana cizgar gashin kansa, gabansa ne ya faɗi. Jikinsa ya yi matuƙar sanyi, haka kawai yake jin kamar ya taɓa ganin mai yanayin kamanninsa duk da wannan kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci ba shi da lafiya sakamakon yadda surar hallitarsa ta koma. Daga can bayansa ya ji muryar Inna wuro ta ƙaraso tana faɗin. "Kai Kamalu me kake yi a wurin nan da doshin magriba?"
Idanun Kamalu suka ciko da ƙwalla ya nuna mata Abubakar ya furta, "Don Allah Inna wuro ki duba wannan wai shi ma ɗan Mai martaba ne ki dubi irin halin da yake ciki." Sororo Inna wuro ta yi tana kallon wurin da yake nunawa babu abin da ta gani, tana shirin yin magana ta sake jin Kamalu ya furta.
"Amma Dattijo Maharazu me ya sa Sarki ba ya ba shi kulawa, wacce irin larura gare shi?"
Bayan sallar Isha'i Fulani Babba tana zaune saƙo ya iso gare ta wai Mai martaba na gayyatarta cikin turakarsa, ta cika da mamaki matuƙa jiki a sanyaye ta yi wanka ta gyara jikinta haɗe da feshe ko ina da turare sannan ta nufi sashen na shi gabanta na faɗuwa. Banbarakwai take ji wai yau Takawa ne yake son tarawa da ita a turaka, farincikinta ya nunku don idan ba ta manta ba rabonta da Takawa tun da cikin Abubakar, sai kuma mafarkin da take yawan yi yana mu'amala da ita ƙarfi da yaji a cikin mafarkinta.
SHU'UMAR MASARAUTA
17
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
A sanyaye Fulani babba ta ɗaga labulen ɗakin ta same shi kishingiɗe ya ci ado cikin jajayen kayan saki waɗanda aka ratsa cin bakinsu da zaren zaiba, ba ƙaramin kyau ya yi mata ba don rabon da su keɓe kamar haka har ta manta.
"Ke zinnariyar mata ce samun kamarki ko an duba dubban mata babu kamarki, wani lokacin idan na zauna sai na dinga gode wa Ubangiji da ya mallaka mini kyakkyawar sura da kyawun halayenki." Fulani babba ta saki murmushi a kunyace.
"Kin kasance lantarkin da ke haske birnin zuciyata don Allah ki kasance da ni har ƙarshen rayuwa Fatima." Muryar Takawa ta daki kunnuwanta cikin wata irin murya mai ɗauke da shauƙin so da ƙauna, tare da son nuna tsantsar kewa da begen masoya.
"Ban san gaibu ba Fulanina amma ina mai kyautata miki zaton ke 'yar aljannah ce."
"Na sani Fulanina ta dabance mai farar zuciya da ladabi da biyaya."
"Idan ina kallon sura da kyawun halittarki sai na ga a duk faɗin duniya babu wanda ya kai ni sa'a, sa'ar da nake fatan kasancewa da ita har cikin aljanna. Idan na raɓa gangar jikina a naki ji nake tamkar na dawwama a haka ba tare da zare jikinki ba. Ke 'yar Aljanna ce sarauniya kuma gimbiya a wurina, ki adana waɗannan kalaman duk rintsi ba zan iya rabuwa da ke ba." Lokaci ɗaya ire-iren kalaman da Takawa yake yawan furta mata a shekarun baya suka dawo mata, ta tattaro murmushi tana jin wata irin ƙwarin gwiwa na ratsa ta har ta isa cikin tsakiyar ɗakin. Hannuwa ya buɗe mata yana daga kwance haɗe da sakar mata murmushi, a kunyace ta sunne kanta ƙasa ta ƙarasa jikinsa kusan lokaci ɗaya suka saki ajiyar zuciya.
"Me ya sa kike ɗari-ɗari da mijinki ko don na ce zan ƙara aure ne Fulanina?"
"Ko kaɗan aurenka bai taɓa ɗaga mini hankali ba, da ace zan samu wannan kulawar ko mata ɗari idan ana yi ka je ka yi babu ruwana." Fulani Babba ta faɗa a zuciyarta. Amma a fili sai ta furta. "Ba haka ba ne Sarkina." Ita kanta sai da ta ji wani iri a kalaman da ta furta masa, ta yi mamakin yadda ta ga Mai martaba yake ba ta kulawa hatta abinci tare suka ci wani abin da ya daɗa sanyaya ranta bai wuce yadda har kawo lokacin fitsarin da ke fita daga jikinta bai fita ba ballantana ya ɓata mata jiki. Daga haka sai hirar ta su ta fara sauya salo, tun Fulani babba na jin nauyi da kunyar mayar masa da martani har ta saki jikinta take sarrafa mijinta cikin kyatatawa. Wani sanyin daɗi da farinciki ne yake ratsa da ta ɗora ƙwayar idonta a kan Takawa da ke yunƙurin mu'amala da ita, ita ma yau jin ta take kamar sauran mata don idan ba ta manta ba rabonta da shi an ɗauki shekaru masu yawan gaske.
Wani irin zafi ne ya fara ratsa ƙasanta tamkar an sa kaifaffiyar wuƙa ana yunƙurin fisgo ƙasanta ta ƙarfin tsiya, wata irin ƙara ta ji Takawa ya saki a ɗimauce ya ja da baya hankali a matuƙar tashe. Jinin da ta gani yana tsattsafowa daga jikinsa ne ya sake tarwatsa ragowar ƙwarin gwiwarta.
"Ni ba na kishi da ke domin na san na riga da gama da shafinki, domin da ke da babu a wurin Takawa ɗaya kuke." Kalaman Fulani Umaima suka dawo mata ranar da wani saɓani da bai taka kara ya karya ba ya haɗa su.
"Ni fa hankalina bai kwanta da wannan kishiyar taki ba an ya kuwa babu sa hannunta a wannan ciwon naki?" Sai a yanzu kalaman Yaya Halima suka sake samun gurbin zama a zuciyarta. Numfashin Mai martaba ya katse mata tunani.
"Don Allah ka yi haƙuri! Ban san me ya haifar da hakan ba." Fulani babba ta faɗa jiki a sanyaye, a ɓangare ɗaya kuma wata irin kunya ta mamaye ta.
Da kallon tausayi ya bi ta sannan ya furta, "Kada ki damu In shaa Allah ranar Juma'a idan Malam Liman ya dawo zan sa a nema miki magani." Farincikin Fulani babba ya bayyana har a fili, ta share ƙwallah tana sake jin ƙaunar mijinta na taso mata.
"Na gode ranka shi daɗe. Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya har ƙarshen rayuwarmu." Murmushi ya sakar mata sanna ya yunƙura har lokacin jikinsa bai daina tsatssafar da jini ba, ga wani ɗan zugi-zugi haɗe da raɗaɗi da yake ji. Ƙai tsaye ya wuce banɗaki don ya gyara jikinsa.
Da sauri Inna wuro ta janyo hannunsa gabanta na faɗuwa, wato ana murna baƙo ya tafi ashe yana bayan gari. Tun suna Rigar Arɗo suka fahimci irin gane-ganen da yake yi tun yana ƙaramin yaro, ƙirjinta na bugawa ta dubi shi. "Babu abin da nake gani Kamalu don Allah daga yau kada ka sake zuwa wurin na." Kamar zai yi kuka ya bi ta da kallo.
"Inna kin ga abin da yake yi." A ɗan tsorace Inna wuro ta waiga wurin da yake nuna mata amma babu abin da ta iya gani. "Don Allah koma waye yake ƙoƙarin taɓa mini ɗa ya yi haƙuri, ku yi haƙuri In shaa Allah ba zai sake zuwa wurinku ba." Inna wuro na gama magana ta ja hannun Kamalu yana ɗan cijewa da sauri Dattijo Maharaz ya ƙarasa wurinsu ya ce.