← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 86

Sashe 40

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka yi haƙuri Kamalu! Ina mai ƙara ba ka haƙuri a duk yadda rayuwa za ta zo maka, da duk labarin da za ka ji a nan gaba. Ban so haka ta kasance a tare da kai ba sai dai ka san ita rayuwa abokiyar tagwaitagar ƙaddara ce, ka sa a ranka duk abin da ya faru da kai shi ne mafi alheri. Na so a ce fuskokinku sun sadu da juna koda sau ɗaya ne, amma haka kundin ƙaddararku ya zana muku. Ka yi haƙuri na tabbata lokaci na tafe da sauƙi zai zo a gare ka." Shiru Kamalu ya yi yana sauraron Dattijo Maharaz a tunaninsa sai ya yi tsammanin yana ba shi haƙuri ne silar abin da ya ji daga wurinsu Baffajo.

"Babu koma Dattijo Maharaz kuma ina godiya da gudunmawar da kake ba ni. Na amince zan bi ka ne kawai don yayewar damuwar da nake ciki, a baya ban san waɗannan tarin matsalolin ba Dattijo Maharaz." Kamalu ya ƙarasa maganar cikin raunin zuciyata.

Ta cikin wannan zauren mai duhu suka shiga a tsammanin Kamalu za su fita ta cikin gida ne, sai kuma ya ga sun ɓilla bakin wani ɗan rami mai ɗauke da taɓo, daga gefe kuma a wata 'yar gajeriyar katanga jikinta ɗauke da sawayen hannuwan mutane. Da mamaki Kamalu ya furta.

" Ina ne nan Dattijo Maharaz? Wannan sawayen hannun su waye?"

Kamar saukar aradu haka Sarki Abdul'aziz ya dira a cikin ɗakin Fulani Babba, Mai gado ta ɗago ta dube shi take ta ji wani ƙunci da haushinsa sun mamaye ta. Uffan ba ta iya tanka masa ba ta ɗauke kanta gefe.

"Ka gafarce ni ranka shi daÉ—e bisa mummunan al'amarin da ya faÉ—o mana." Baiwa Zainaba ta faÉ—a jiki a sanyaye.

Bai amsa musu ba yana tsaye ƙwayar idonsa na kan gawar Fulani babba, a hankali ya fara ɗaga ƙafarsa ya isa gaban gawar tata ya tsugunna a gefen gadon. Hannunsa na rawa ya sa ya buɗe yaye zanin fusakarta ya kai kunnensa saitin ƙirjinta. Wani abu ya ji ya danne ƙirjinsa, kamar ƙaramin yaro ya ƙara kansa a gefen ƙirjinta hawaye bibbiyu na zuba. Daga Mai gado har baiwa Zainaba suka sunkuyar da kansu ƙasa suna zubar da ƙwallah, motsin da suka ji a gefensu ne ya sa suka ɗago Fulani Umaima ce a tsaye tana bin ɗakin da kallo. Ganin kukan da Takawa yake yi a jikin gawar Fulani babba ya sa ta taɓe baki cikin takaici, sai da ta ƙarasa gaban gawar sannan ta rushe da wani irin kuka. Yadda Fulani Umaima take kuka har da majina sai ka rantse mutuwar Fulani babba ba ƙaramin dukanta ta yi ba.

Jakadiya da Sailuba ne suka shiga sai dai ganin irin kukan da Fulani Umaima take yi ya sa suka yi turus, lokaci É—aya suka kalli juna hatta Mai gado sai da ta fahimci Fulani Umaima kukan makirci take yi.

"Ya Allah ga baiwarka nan Allah ka jiƙanta ka gafarta mata, kaico rayuwa Fatima ta tafi ta bar ni." Takawa ya furta a ɗimauce.

"Me ya sa za ki tafi ki bar ni Fatima!" Ya yi maganar a zauce.

"Mtsswww, aikin banza!" Fulani Umaima ta faɗa cikin suɓucewar baki don ba ta taɓa tsammanin zancen zucin da take yi zai fito fili ba." A hargitse Mai martaba ya waiga wurinta amma da yake ta san kanta sai ta juya wurin su Mai gado da ke zaune a ƙasa ta furta.

"Ku tashi ku fita mana ku bar mutane da abin da yake damunsu." Da sauri su Baiwa Zainaba suka fice jiki na rawa. Tsanarta ta sake mamaye zuciyar Mai gado, É—auke kansa ya yi don a tunaninsa a kan maganar da ta yi wa su Mai gado ne take yin tsaki.

"Allah ya taimaki ɗawisu, Ubangiji ya kwanta makwancin Fulani. Na ce ko za a yi mini izini na fitar da sanarwar wannan babban rashim da aka yi mana?" Kai kawai ya iya gyaɗa mata, Jakadiya ta fice da sauri. Shi kuwa Abubakar yana can gefe a zaune sai bin su yake da kallo ɗaya bayan ɗaya, kamar wanda ya ga sabuwar hallita haka ya tsaya yana kallon Takawa saboda rashin saninsa da bai yi ba, Mai martaba ya rufe Fuskar Fulani sannan ya ƙarasa wurin Abubakar.

"A lokacin da mahaifiyarka take raye babban burinta bai wuce ta ga warkewarka ba, ta fuskanci ƙalubalen rayuwa a wurina duk silarka sai dai kuma Ubangiji ya ɗauke ta a gaɓar da kake ci gaba da neman kulawarta. Allah ya gafarta miki Fatima haƙiƙa na yi babban rashin da har abada ba zan manta shi ba, na yafe miki duk abin da kika taɓa yi mini a rayuwa duniya da lahira." Wani haushi ya mamaye zuciyar Sailuba, ita kuwa Fulani Umaima ban da jefa masa harara babu abin da take yi.

"Ka gama iyayinka ina nan zaune za ka dawo ka same ni." Ta furta a zuciyarta sannan ta saki murmushi sakamakon kallon gawar Fulani Babba da ta yi, da kuma ta tuna a yanzu magani ɗaya ne ya rage mata ta ƙarasa aiwatarwa wanda za ta cusawa gawar Fulani ɗaurarriar fatar a gabanta sai farinciki ya mamaye ta.

Mai gado tana tafe tana kuka saboda tashin hankali duk wanda ya tambaye ta ba ta iya koda furta masa kalma ɗaya, ɗakinta ta faɗa ta zauna a gefe gado nan take ta sake rushewa da sabon kuka mai cin zuciya. A rayuwa bayan mutuwar mahaifanta wannan ce mutuwa ta farko da ta taɓa ta, sun yi wata irin shaƙuwa da Fulani ko kaɗan ba ta nuna mata kyara a matsayinta na shugabarta.

Jin kukan da Mai gado take yi ƙi ci ya ƙi cinyewa ya sa Jawahir ta ɗan zuro kanta daga cikin zanin don har lokacin jikinta bai daina karkarwa ba. "Inna... Innaaa me yake faruwa?" Jin yanayin muryar Jawahir ya sa Mai gado ta waiga, sai da ta share hawayenta ta furta.

"Me yake damunki Jawahir?" Kamar mai jira sai kawai Jawahir ta fashe da kuka, Mai gado na shirin kawo hannun Jawahir ta ji wani irin zafi zaauu da jikinta ya yi. Da sauri ta yaye zanin a hargitse ta furta.

"Ba ki da lafiya ne Jawahir."

"Inna wallahi wannan matar ce, tsoro nake ji Inna kar ta kashe ni." Ƙirjin Mai gado ya yi wata irin bugawa da ƙarfi. "Wace ce Jawahir? Ki kwantar da hankalinki In shaa Allah ba za ta yi miki komai ba."

"Inna kin ga cikina fa, Allah mutuwa zan yi." Jawahir ta ƙarasa maganar tana buɗewa Mai gado cikinta. Zumbur Mai gado ta miƙe jikinta na karkarwa, tambarin cikinta ne ya daɗa yin wani irin ja a ɗan tsorace Mai gado ta miƙa hannu tana son taɓawa zuciyarta na harbawa. Da ƙyar ta yi ta maza ta ɗora hannunta a jiki wani irin zuuuu ta ji kamar ana fisgar hannunta, ta ja da baya da sauri a tsorace. "Wacce matar kika gani, kuma yaushe Jawahir?" Mai gado ta tambaye ta a firgice.

"Inna ina ɓarar gyaɗa kawai na ji cikina yana zafi..." Take ta kwashe duk abin da ya faru ta gaya wa Mai gado. Kamar wacce ruwa ya cinye haka Mai gado ta yi shiru, fargaba, tsoro da tashin hankali suka mamaye ta.

"Kada ku damu da sanin zubi da surar halittata, wannan 'yar tawa ita za ta fayyace muku asalin jinsin halittar da na fito." Kalaman mahaifiyar Jawahir suka dawo wa Mai gado cikin kunnenta, da yake zuciyarta a dagule take nan take ta sake fashewa da kuka domin ba ta zaɓin da ya wuce yin kukan.

"Inna wallahi tsoro nake ji ta ce abin bauta zai yi fushi da ni." Mai gado ta dafa ta a sayaye.

"Kada ki damu Jawahir idan Malam ya shigo zan sanar masa halin da kike ciki, babu abin da zai faru da ke sai alkairi." Mai gado ta furta tana kallon Jawahir.

"Inna wallahi Fulani babba ta ce ki daina hana ni shiga wurinta, don Allah ki bari na je kitso zan yi mata."

"Daga wurin Fulani babba nake na ci abinci kuma ga alkaki ta ce a kawo miki."

"Inna kin ga sabbin kayan da Fulani ta ba ni wannan ma warwaronta ne da yari ta ce na je na sanya ranar juma'a."
"Wallahi Inna Fulani tausayi take ba ni idan na ga tana kuka kamar ba matar Takawa ba, Allah da ina da dama sai na kori Fulani Umaima daga gidan nan." Ire-iren kalaman Jawahir na baya suka shiga dawo wa Mai gado, wanda Jawahir take gaya mata game da Fulani babba. Duk da ta san babu abin da suka haɗa da Fulani amma akwai shaƙuwa don haka tausayin Jawahir ya kamata ta san jin mutuwar Fulani babba ba ƙaramin kaɗa ta zai yi ba.

"Inna kukan me kike É—azu."

"Ina koka mana game da sabuwar rayuwar da za mu fuskanta nan gaba Jawahir, ina koka mana maraici, kaɗaici da alhinin da za mu shiga. Ta kasance gatanmu a lokacin da ba mu da gata, ta rungume mu hannuwa bibbiyu tamkar ba bayi ƙasƙantattu a wurinta ba." Take gaban Jawahir ya faɗi.

"Jawahir mun rasa Fulani Babba Allah ya yi mata rasuwa shi kenan Jawahir..." Kalaman Mai gado suka katse sakamakon kukan da ya ci ƙarfinta.

"Ki je sashen Sarkin cikin masarautarku ki tone abin da matarsa ta binne idan ba haka ba, Fulani babba za ta mutu. Idan kika bari Fulani Umaima ta ci gaba da yin nasara a cikin masarautar nan ina mai tabbata miki sai ta yi nasara akanki. Sai ta damƙa ruhinki wurin hatsabibin boka Bamaguje, kuma ki sani idan kika bari rihinki ya je gare shi babu wani taimako da ni ko abin bauta za mu yi miki. Kin ga kenan an ƙarar da gishiri duka a dahuwar ƙaho ba tare da buƙata ta biya ba, na tashi a banza ba tare da cikar muradina ba." Kalaman matar da ta zo mata a mafarki wacce ta gani a ɗazu suka dawo mata, hantar cikinta ta kaɗa zuciyata ta hau dakan lugude tamkar za ta yi tsalle ta hudo ƙirjinta.
Chapter 40 · 0% Book details