Sashe 95
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 87
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Shi kuwa Hadi ya shige ciki jim kaɗan ya fito tare da wani babban mutum gaisawa sukayi kana suka kuma fita jim kaɗan da fitansu suka dawo.
Ido cike da kaɗuwa take kallon Sa'ad da Faisal dake biye dasu a baya, gefe suka zauna, fuska a tsuƙe ya nuna Faisal yana faɗin.
"Ka cire idonka kan matata tunda yanzu dai ka san matar aurece”.
Sai kuma ya dannawa Sa'ad matsiyacin kallon yace. "Kai dama ka san matar aurece da yake mayen matane kai ba kunya ba tsoron Allah kayi ta bibiyar matata”. Murya cike da sanyi Sa'ad yace.
"Kayi haƙuri mahaifiyata na cikin damuwa kuma kaine da kanka ka bani damar nemanta”.
Fasal ya kalla jin yana faɗin. "Ni wlh ban san matar aure bace”. Miƙewa tsaye Mahmoud ɗin yayi ya jawo hannunta yana fita yace.
"Ok Barrister a medasu ciki kawai”.
Daga nan ya juya ya fita Hadi ɗin na biye dashi a baya.
Daga nan Maitama suka wuce gidan Aunty Kubra ƙanwar Yah Saleh, anan ya barta ya kuma fita shi da Hadi.
Abral ne yar matashiyar Aunty Kubra da bazata gaza 16 years ta zuba wa Fariyda ido bayan tayi al'walan ta fito daga bathroom tana tattare gashin kanta dan wurin shafar kai ribbons ɗinta ya sule.
“Masha Allah Our Aunty kina da kyau dama Sajida ta tura min hotonki lokacin da kukaje Istanbul, itama ta kusan dawowa ai”. Tana tubke gashin ta amshi hijabin da Aunty Kubra ke miƙa mata, bayan ta idar da sallane sukayi ta hira da Abral ɗin da Aunty Kubra dan itama akwaita da sauƙin kai.
Sai ƙarfe takwas dai-dai Mahmoud ya dawo Hadi ne ya kaisu Airport ƙarfe goma dai-dai jirkinsu ya tashi zuwa Kano.
Tunda suka shiga jirgin duk hankalinsa na kan system nashi da alamu Abu mai mahimmanci yake yi, tsakin ta ɗan ja a hankali tana lumshe idonta, hannunsa yasa ya jawota jikinsa haɗi da ɗan kissing goshinta cikin raɗa yace.
"Bacci ko zo nan kwanta kiyi baccinki”. Ya ƙare maganar da gyara mata kwanciya.
A can Kano kuwa Hafiz ne zaune a parlour Ummi da Sulaiman da suka iso tun ƙarfe biyar na yamma, sai Huzaifa da bayan sallan isha ne ya kawo Sulaiman abincin da Amina tayi masa, Ummi da Goggo Dada na zaune anan suna ta hira Sulaiman na basu lbrin sanyin Gembu.
Text message ɗin da Mahmoud yayi masa ya duba yana faɗin.
“Hafiz zuwa sha ɗaya ka shirya zakaje Airport ka ɗauko Mahmoud sun taso”. Cikin zumuɗin yace.
"Uncle Sulai da wacce motar zanje da prado ko Hillux tunda kuna dawowa na kai an wanketa an gyarata tsab.
Yana ɗan cin snackers ɗin da Amina ta turo masa yace.
“Eh kaje da Hillux ɗin ga key ɗin”.
Goggo Dada tace.
"Allah ya kawoshi lfy”.
Amin Ummi tace kamar basu san inda yajeba duk da dai basu san har yanzu yana tare da Fariyda ba.
Karfe sha biyu dai-dai suka iso cikin gidan, cikin sauri ta buɗe idon daga bacci daya saceta tunda suka fito Airport ɗin.
Ido ta zuba mishi cikin mmkin ganinsu a harabar gidansu Abba suke da sauri ta ja ta tsaya murya cike da kaɗuwa tace.
“Appiy gidan nan kuma ba gidanmu zaka maidani ba”. Yana kallon Hafiz da ya ɗauki akwatin Fariyda ya nufi ciki Huzaifa riƙe da nashi jakar.
Yana gyara riƙo hannunta da take ƙwaceea yace.
"Angle kin dawo gidanki ne ai can kuma gidan Baba Malam ne.” ya ƙare maganar tare da ƙara jawato da sauri, ido cike da hawayen tace.
"Ni kam wlh bazan shigaba gidanmu zan koma”.
Abba dake kallonsu ta window bedroom nashi ne ya kafe idonsa akanta yadda take janye hannunta daga gareshi da yadda fuskar ke nuni da bata son shiga cikin gidan duk da baya iya jiyo mai take faɗa shiyasa yake ganin kamar kuka takeyi kuma a dole ya kawota.
Haka yasashi jan wani irin fusataccen numfashi fuska cike da fushi yace.
“Tabbas zanyi maganinka in kai ɗan yau ne nima tsowon yau ne, ba yadda za'ayi in zuba maka ido ka mulki rayuwar yarinya dan tana yiwa iyayenta biyayya su kuma suna maka kara, yadda take nuna bata son shigowa kaɗai ya tabbatar da gudun kasancewa da kai da takeyi, dan haka dole ka sake ta, ta samu mai sonta ya aureta bazan zuba ido kana cutar da ita da mari da duka harda targaɗata da karya ɗan ƴan uwnta, zanga ni da kai waye zaiyiwa wani biyayya!
Sake labulen yayi ganin ya ɗagata cak ya shiga ciki da ita duk da tureshi da takeyi.
A hankali ya zauna bakin gadonsa yana fesar da zazzafan numfashi.
A can wurin su Mahmoud ɗin kuwa a parlournsa ya direta nan ma dan kiciɓis da sukayi da Huzaifa da Hafiz ne, a hankali suka raɓa gefe suka wuce ba tare da sun kuma ɗago kansu ba.
Ita kuwa Fariydan can nesa dashi ta matsa tana bubbuga sawunta kaɗan haɗe da yarfa hannunta murya na rawa ido cike da bacci da hawaye tace.
"Ni wlh bana so ka maidani gidanmu ba zan kwana anan ba”.
Da sauri ya nufi inda take bayan ya ajiye briefcase nashi kan Centre table, cikin bubbuga sawunta ta koma can gefe tana yarfa hannunta haɗi da cewa. “Ni dai ka maidani gidanmu”. Da sauri ya jawota jikinsa haɗi da faɗawa kan kujerar dake bayansa da ita murya a sanyaye yace.
"Angle nan nefa gidanki ɗakin mijinki uban ƴaƴanki ina kike dashi a duniya da yafi nan, Please ki daina cewa in medake nifa mijinki ne”. Tana ƙoƙarin zillewa tace.
"Kowa fa yasan ka sakeni”. Da sauri yace.
"Amman ai ke kin san ba haka bane, kin san da igiyoyin aurena uku ras a kanki”. Tana tureshi tace.
“To ai babu wanda yasan da hakan sai ni da kai, kuma Mahaiafina da Mahaifiyata basu saniba ba izininsu ba komai kawai sai ka dawo dani nan nidai bazan iyaba”. Yana ƙara matseta yace.
"Ba abinda Malam zaice in ma yayi magna ni zan faɗa masa ba sakinki nayi ba, kuma zan nuna masa hujjata”. Murya na rawa tace. "Koma menene sai ka bari sai kayi magna dasu ka nuna musu hujjar taka su yanke hukuncin da sukaga ya dace akaina dole zan musu biyayya kamar yadda nayi musu a baya”. Tallabe kanta yayi yana kallon idonta dake sheƙin hawaye a hankali yace.
"Karkiyi musu biyayya in dai hukuncin rabamu suka yanke Please My Angel karkiyi nesa dani duk rintsi wlh bazan iya rayuwa ba tare da keba”.
Tana ɗan bubbuge ƙirjinsa tace.
"Ni dai ka maidani gidanmu wlh bazan kwana a nan ba, me zancewa Mamy na yanzuma duk sun koma saura ni kaɗai in naje ince mata ina na tsaya ni da waye”. Yana jawota jikinsa da kyau yace.
"Kice mata wurin mijinki kika tsaya tare dashi”. Kuka ta saka a sakalce cikin iyakar gaskyarta da tsanar kwana a nan ɗin murya na rawa tace. “Abba nefa da kanshi ya maida ni ta yaya kuma zan dawo gaba gaɗi, ni bana son gidan nan”. Cikin fargaba yace.
"To naji zan maidake amman kingafa yanzu har sha biyu ta gota, kiyi haƙuri da asuba zan maidaki ko su Abba bazasu san nan muka dawo ba”. Kai ta rinka jujjuyawa cikin gajiyar wuni zirga-zirga Taraba to Abuja, Abuja to Kano, a hankali ta fara sassayan kuka mai haɗe da ɗan dukan ƙirjinsa tana faɗin.
"Ni dai yanzu, ka maidani gidanmu, bana son Mamy na ta gane tare da kai muka tafi, bazan iya kallon su Ummi ba, me zan cewa Malam da Abba da ya maidani gida da kansa”. Ta ƙare maganar da alamun bacci ya fara danne kuzarinta dan muryarta tayi ƙasa, cikin hikima yake ɗan jijjigata yana lilata haɗe da shafa bayanta a hankali yake faɗin.
"Naji ni zan medake da kaina da asuba”.
A hankali tace.
"Ni dai yanzu..”. sai kuma tayi shiru alamun bacci ya kwasheta.
Ajiyan zuciya ya sauƙe haɗe da gyara zamansa, yana kallon fuskarta, murmushi mai cike da shauƙine ya subce masa tuno daren da sukaje Gembu yadda ta rinƙa yi masa abubuwa cikin maye, ta bashi dukkan farin cikin da yake buƙata a hankali yace.
"Yau ɗinma da na ɗura miki maganin murar ai ki bani kakan daɗi na”.
Sai wuraren ƙarfe ɗaya ya miƙe da ita caɗak bedroom nasa ya nufa da ita, kan ƙasaitaccen gadonsa, numfashi mai sanyi ta fesar lokacin daya kwantar da ita, duvet ya jawo ya ɗan rugeta zuwa ƙirjinta, a hankali ya ɗan zauna gefe hannunsa ya ɗaga ya Azkarul Naum ya tofa a hannunsa ya shafa mata, idonsa ya tsaida kan lips ɗinta yana ganin yadda takeyin kamar wacce ta samu sweet haka take tsotsan lip ɗinta na saman a hankali yace.
"Shi yasa kika ƙware a iya tsotso duk abinda kika ritsa da tsotso sai kin masa irin tsotsar da bai taɓa jiba.
A hankali ya yunƙura ya shiga bathroom, wanka yayi gami da al'wala yana fotowa ya zira 3 quarter irin mai laushin nan, a hankali ya dawo kan gadon ya kwanta haɗi da jawo ta ya ɗaura kan ƙirjinsa yana mai yin Azkarul Naum.
A can gidansu kuwa tunda suka iso duk sukayi wanka suka cicci abinci sai kuma aka dasa hira.
Mamy ne ta kalli Saddiga data shigo goye da Zaitoon tana faɗin.
"Mamy bari in kwantar miki da princess anan ɗakin mamanta yana cike surutun su Salma da Rashida ya hanata bacci”.
Kwaffa Mamy tayi kana tace.
"Ai sai ki kira ƙanwar taki ki gaya mata su zo su ɗauki yaransu, kuma suyiwa mutane bayanin munafurcin me suke ɓoyewa ni dai nasan in dai Mahmoud ya saketane kuma babu idarsa akanta kamar yadda ta faɗa bazai je ya ɗauketa suyi ta yawon hotel ba, dan haka ki gaya mata duk inda suke suzo su ɗauƙi yaransu danni ba ƴar raino bace tasan dai Raihana tayi aure yanzu ni kaɗaice anan in kun koma Khadijah da Nana da suke garinma ba kullum suke zuwaba bare ita da kullum suna cikin yawon ƙasashe tun Aminullah ɗinma bare shi wannan Yaron Mahmoud yafi Aminullah ɗin fita waje, dole suzo suyi mana bayani musan matsayin aurensu dan ba ɗaukar sakarcin zamuyiwa ba”. Ita dai Saddiqa tunda Mamy ta fara magna batace komai ba tana kwantar da Zaitoon ta koma gefe ta ɗan zauna a hankali tace.
"To Mamy zan gaya mata, ni ɗazuma na kirata Mahmoud ɗin ne ya ɗaga”. A kufule Mamy tace.
"Nima da na kira jiya shi ya ɗaga yana ta min kame-kame, kawai ki gaya mata malam ne ke son ganinta”. Tana gyada kai tace. "To”. kana ta juya ta fita, a bakin ƙofa sukayi kiciɓis da Mimy maman Salam kenan da Matar Uncle Muhd suna shiga ɗakin Mamy suna faɗin.
"In mun biyewa hirar Fariyda da Mahmoud da Raihana da Bashir sai muyi kwanan zaune, mazane Allah ya basu ƴan soyayya”.
Dariya tayi ta wuce tana faɗin.
"Ina kuka manta Rashida ita da mijinta soyayyarsu bata tsufa, gacan Salma da Salim wlh har tausayi wayarsu nakeji wuni da kwana fa sukeyin magna a waya na rasa me suke faɗawa juna”. Dariya sukayi suka wuce riƙe da tray abincin da Amira tayi musu.
Anan gidan Abba kuwa.
Ido Ummi ta zuba wa Goggo Dada bayan Sulaiman ya tasa ƙeyarsu Hafiz da Huzaifa sun tafi part ɗin da suke.
"Hmmm Mahmoud yana son takalo fushin Abbansa ne, ya jamin ɓacin rai dan yanzu gani zaiyi kamar da sanina ya tafi Taraba ya kuma kwaso yarinya ya dawo da ita bayan ya saketa gaban su yanzu kuma ace yayi gaban kansa ya dawo da itane ko kuma ya haukacene so yake ya lalata mata tarbiya”. Numfashi mai nauyi Goggo Dada ta sauke haɗi da cewa.
"Ai kina da shaidu baki saniba, kuma kinji Sulaiman fa cewa yayi to ba matarsa bane mene dan ya dawo da ita, nifa ina ji a jikina wlh Mahmoud baiyi sakin nanba, tunda dama kawai ce masu yayi na tura mata”.
Kwaffa tayi haɗi da miƙewa tace.
"Saida safe zamuga iya gudun ruwansa da iyakar tsaurin idonsa.”
Daga nan sukayi saida safe.
5:48 Am ta fito parlour da sassarfa tana gyara mayafin ta, tana taka Downstairs a hankali gudun kar a jita tafiyar take tana mgnar zuci.
"Yah Allah kasa har in haɗu da kowa har in fita, kafin ma su dawo masallaci na isa gidanmu”.
Ta ƙare maganar zucin tana yin ƙonon sauƙowar.
Dai-dai lokacin kuma Samira da Mamanta ke tsaye bakin ƙofar parlour Ummi dake cikin corridorn inda zatabi ta wucen Knocking Maman Samira takeyi Samiran na gefenta dan saboda Hafiz yace yana da lectures 7:00 Am shiyasa suka shigo da wuri dan ɗaura kari, Ummi ne ta buɗe musu ƙofar haɗi da ɗan ja da baya tana faɗin. “Hafiz ya saku tasowa da wuri ai da kun barshi yasa tea ya tafi”.
Maman Samira na shiga, sai kuma duk suka juyo ita da Ummi jin Samira ta saki ɗan sautin jin daɗi haɗe da cewa.
"Oyoyo Aunty Fariyda kai Alhamdulillah”. Sai kuma kawai ta ƙarasa gaban Fariyda data ƙarasa sauƙowa tana karkaɗawa mata kai haɗi da mata alamun tayi shiru, rungume Fariyda tayi tana faɗin.
"Kai naji daɗi Hafiz ina kuke gidanmu zaiyi daɗi Our Aunty ina twins?”. Jin haka ne yasa Ummi da Maman Samira fitowa, Ita kam Fariyda shiru tayi kamar bata wurin sai kanta data sunkuyar cike da tsananin kunya mai kashe jiki da ido ta kasa koda ɗaga idon ta bare ƙafarta.........
By
*GARKUWAR MARUBUTA*