← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 95

Sashe 35

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mama ne da Jidda zaune gaban bokansu turaren tsumin sihirin da yayi musu tsawon mako ɗaya cib yana tsumashi tun ranar da sukazo dare-dare suka ce mai ranar ya dawo kuma duk aikin da akayi ba alamun ya kamshi, haka yasa ya sake musu sabun shiri turaren ya miƙawa Jidda bayan ya buɗeshi birkitaccen ƙamshin turaren mai hawa kai ya ratsa musu hanci tsirrr da karfi.
Haka yasa ta janye kanta Mama kuwa ta toshe hancinta, dariya mai karfi yayi har Saida yar bukkar ta amsa.
“Yadda ƙamshin turaren nan ya zaman masa wajibi ya shaƙa muddin kika samu kika fasa yar kwalbar a inda yake to dole zai aureki ko yana so ko baya so dole ya soki ya aureki”. Cikin gamsuwa sukayi godiya kana suka kama hanyar gida.
Washe gari bayan sallan asuba zaune suke a parlour Abba harda Salim da shima daga masallaci ya biyo su.
Goggo Dada ta haɗa musu tea. Ummi ta haɗawa Abba da Goggo Dada sai nata. Abba yace.
“Sulaiman yaushe zaka koma Gombe?”.
Cikin sanyin halinsa yace. “Abba a satin nan zan koma”. Cikin gamsuwa yace. “Allah yayi maka al'barka, sai kuma batun aure kayi shiru da yawa fa”. Kai Goggo Dada ta jinjina cikin zaƙuwa tace.
“Ai shi kamar ma baya tuna yin aure a rayuwarsa”. Maman nashi ya kalla cikin sanyinsa yace.
"To Goggo Dada ni ba me sona fa”. Murmurshi Ummi tayi cikin son halin nitsuwarsa tace.
Akaso masu rawar kai da muguntama bare kai salihi mai sanyin hali ai in sha Allah mata sai ka tarje”.
Dariya Salim yayi yana kallon Mahmoud daya zuba mata fuska yasan shi take nufi mugu tunda ya targaɗa hamnun Fariyda take mishi kallon mugu.
Murmurshi Abba yayi yace. “Ai kuwa Malam Ibrahim yace min zai baka mata in ba wacce muka ajiye maka”.
Mahmoud ya ɗan kalli Salim da aka kira wayarsa zaro wayar yayi sai kuma yayi saurin meda ita aljuhunsa yana kallon Mahmoud dasu Abba yana mai sauƙe numfashi yace.
“Abba ni zan wuce”. Cikin tuhuma Mahmoud ya bishi da ido bayan ya fita.
Hafiz da ya shigo ne ya zauna kusa da Mahmoud tare da gaishi shi da Sulaiman kafin ya gaida kakannin nasa.
Tray kayan tea ɗin ya jawo ya fara haɗawa kanshi yana faɗin.
“Huzy yazo fa Ummi wai kar ku shiga kitchen Mom tayi breakfast, kuma anjima itama zata zo”. Murmurshi Ummi tayi tare da cewa.
"Allah yayi mata al'barka, yasa ku rama mata abinda take mana”. Abba yace. “Amin amman dai ta daina wannan hidimar da haƙƙin mijinta”. Da sauri Huzaifa dake shigowa yace.
“To Abba ku da kullum Yah Hafiz yana gidanku yana cinye muku abincinku gashi nima yanzu Uncle Mahmoud yace wai zan dawo nan ai Daddy kuka hutar”. Hafiz ɗin na shafa tumbim Huzaifa da ya zauna gefensa yace.
“Gsky dai kai kam Huzy riƙe babban aikine, kaje ka motsa jiki, ai zaka dawo nanne dan a samu ka sace”. Kai ya lankwaɓar ganin Mahmoud ya jinnina kai alamun eh.
“Yaushe zaka koma Office Mahmoud”. Abba ya tambayeshi a nitse yace.
“Next week zan koma kafin nan kayan mu sun iso har nan Kano”.
Abba yace.
“Allah ya kaimu”. Amin suka amsa. Murmurshi Salim yayi ganin Abba na kallonsa da alamun tambayar amarcin bai ƙare bane sai yaushe zaka koma bakin aiki, yana dariya yace.
“Abba nima next week zamu koma tare da Mahmoud”. Kai ya gyaɗa mashi.
Mahmoud kuwa daga nan ya miƙe ya haura sama. Sulaiman kuma ya wuce BQ duk da an gyara part ɗin da Abba ke harin yayi aure a ciki, ga kuma part din Yah Amin da yanzu ba komai a ciki a cewar Abba komai na kayan dake ciki gadon Fariyda da yarantane shiyasa aka saida komai aka raba musu shi kamar yadda shariya ta tsara.
Ƙarfe goma dai-dai na safe ta shigo parlour Ummi da sauri ta ƙarasa cikin parlour tana kallon Ummi dake tsaye ido a rufe Salim na durƙushe a gefenta, Sulaiman ma gefen Ummi yake tsaye cikin fuskar dake nuna fushi yake kallon Salim, Goggo Dada kuwa kai take jujjuyawa kawai tana faɗin. "Salim bama son ganinta bama fatan ganinta ko ƙara jin sunanta a duniyar nan”. Yana durƙushen yace.
"Ummi kuyi haƙuri Abba nefa yace kuje parlour shi, tunda har shi ya saurareta kuma ku saurareta kuji dame take tafe dan Allah Ummi kuyi haƙuri”.
Muryar Abba suka jiyo yana faɗin.
“Sulaimanu ina kuke kuzo da iyayen naka Salim taho”.
Haka da suka jine yasa su nufar parlour Abba.
Kan kujerar ta zauna tana mai mgnar zuci.
“To meke faruwa ne? Wacece basa son ganinta? Me ya ɗaga musu hankali har haka”. Tana cikin nazarin taji Goggo Dada na cewa.
“Fariyda je ki kira Mahmoud kice Abba na son ganinsa, ku taho tare dashi”. Cikin sanyi ta juya ta fita ganin yadda duk yanayinsu ya nuna ƙuncin zukatansu haka yasa ta gita da sauri ta haura sama.
A hankali ta nufi ƙofar corridorn da bedroom ɗinsa ke ciki, tafiya take cikin nazari to meke faruwa ne a gidan yau.
A bakin ƙofar corridorn ta ɗan tsaya, ƙamshin turarensa daya bugi hancinta ne ya bata tabbacin yana ciki.
Hannu tasa ta buɗe labulen ta shiga cikin corridorn da ƙamshi da sanyi mai ratsa jiki ya cikashi, ido ta tsaida kan mirror console ɗinsa dake gefen dama, tsadaddun turarukansa dake jere a kai a ƙalla kala biyar, a hankali ta isa gaban mirror ba tare da ta lura dashi, inda yake tsaye a gaban drawer takalmansa ba, tunda ta shigo ya zuba mata ido ba tare da yayi motsi ko ce mata wani abu ba, turaren ta fara bubbuɗewa a hankali tana fesawa ɗaya bayan ɗaya, ta fesa na ukun ta ɗauko na huɗu ta ɗago kai da niyan fesawa a wuyanta ne sukayi ido biyu dashi ta cikin mirror, da sauri ta jiye turaren tare da juyowa ta fuskaceshi, da sauri tayi ƙasa da kanta ganin yadda ya kafeta da mayatattun idonsa.
“Ina kwana”. Ta faɗa cikin ɗan ƙarfin hali mai haɗe da daburcewa.
“Bana son muna furci, dama kina gaishi ne, da yau zaki wani cemin ina kwana da yake na kamaki kina min sata”. Ya faɗa yana takowa zuwa kusa da ita, baki ta ɗan tura tace.
“To na ganka ne bare kace ban gasheka ba, in na gaishema ai baka amsawa”. Tayi mgnar tana ɗan komawa baya, idonsa na kan lips ɗinta yace. “Yau da kike son ganina ai kinzo inda nake, gaisuwa kuma bazan amsa ɗin ba dan ba da zuciya ɗaya kike yinta ba”. Ido ta jujjya haɗe da murguɗa baki tace.
"Ni ba nike son ganinka ba Abba ne ya aikoni yace in kira muje yanzu yana son ganinmu”.
Ta ƙare maganar tare da juyawa zata bar wurin, da sauri ya riƙo hannunta ya fizgota baya, hannunta duka biyu ya haɗe a bayanta ya jawota kusa dashi ya zama su duk biyu suna fuskantar mirror a daƙile yace.
“Na sallameki ne da zaki tafi? Ni mate ɗinki ne da ina mgna zaki juya min baya ki tafi ki barni a tsaye? Nace miki na gama mgna da kene?”. Ya ƙare maganar cikin zuba wani irin tsumemmen........

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 60
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Chapter 35 · 0% Book details