Sashe 63
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zakuje asbiti domin yin gwaji”. Hmmmmm yace ya juya ya fita. Zaune suke a parlour Mamy akwatunan kayan lefen Raihana jere a gabansu. Salma da bata daɗe da zuwaba, ta kalli Sadiq da ya shigo riƙe da iv a hannunsa da wasu manyan jakukkuna guda biyu, wanda ya amsa so daga tasha saƙon angon Raihana daya turo daga Taraba. Raihana ya miƙawa, amsar jakukkuna tayi tana faɗin. "IV ɗin Malam zaka bawa ba niba.” yana ɗan murmushi yace. “Ai na bawa malam nasa wannan nakine na mutanenki”. Amsa tayi tare da juyowa tana kallon Aunty Saddiqa dake cewa. "Ai ban san zaka je tasha ba, nima ina da saƙo a tashan na'ibawa”. Yana zama yace. “Daga ina”. Tana kallon Salma dake ce masa. "Dan Allah shigar da akwatunan nan mu samu mu sake, duk sun cika parlour haka a gidankima zasu takuraki ni dane nake ganin yawan kayan lefe da akwatuna abin sone wlh duk su zame ma tarkace a gida”. Kai ya gyaɗa yana dariya yace. "To ni duk ku tattaro nakun ku bani na hutan neman na kayan aure”. Da sauri Fariyda tace. "Wlh na baka nawa, ka ɗauka set ɗaya kawai zaka barmin shima dan tafiya”. Ta ƙare maganar tana kife wayarta da kiran Mahmoud ya shigo a karo na uku. Humarai da Zainab suka miƙe suka fara shigar da akwatunan suna cewa mu dai gwara a kawo mana in mun gaji dasu ma saida musa kuɗi a kasuwanci, shi kuwa Sadiq Aunty Saddiqa yacewa. "Saƙon daga inane bani number wanda kayan yake wurinsa, in karɓo miki dan anjima zan tafi kallon ƙwollo ne”. Da sauri tace. “Daga Adamawa ne, in kaje tashan na'ibawan kawai kace a nuna maka Rabi'u malawa shine kayan suke wurinsa”. Yana miƙewa tsaye yace. "Ki dai bani numbersa zaifi, kuma menene saƙon”. Cikin ƙosawa tace. "Kai Sadiq mutum kamar ɗan jarida, to ga number tasa, sannan kayan biyu ne ɗaya Ghana masgone ɗinku nanmune a ciki ɗaya kuma farar ledace mai girma wacce jikinta ke da tambarin GARKUWAR MARUBUUTA.”. yana fita yace. "TO ai haka yafi yauwa kuma wacce number ce akan kayan dan sai sun tambayeni number dake kan saƙon”. Tana kallon wayar Fariyda dake ɗan Vibrating alamun tace masa. “Number MTN nane a kai”. Kai ya gyaɗa ya juya ya fita. Kai ta maida kan Fariyda dake cewa Humarai kince kin biya gidan Goggo Abu ya jikin Yah Mujahid da sauƙi ko”. Dariyar da Salma tayi ne yasasu zuba mata ido, ai kuwa ta fara basu lbrin yadda Salim yayi ta dariya da yadda kamannin Yah Mujahid ya sauya. Humaira da bata cika sheƙiyancin bama dariya tayi tana faɗin. "Yanzu dai kumburin da sauƙi amman fa fuskarsa ba kyan gani baki ya zama wawulumon ba haƙoran gaba”. Cikin haɗe fuska tace. "Ciwo kukeyiwa dariya ko zalumtarsa da akayi, ai wlh Allah zai saka masa”. Sai kuma ta juyo da sauri jin kukan Zaitoon da Zaid har suna haɗa baki wurin kiran Appiy! Appiy!! Mamy ta miƙa matasu tana faɗin. “Wlh ni dai na fara gajiya da wannan abin tausayi yara kullum sai sunyi ta kuka suna kiransa yanzu ya tafi tun ɗazu yana parlour Malam dasu yana fita ajiyesu yara sukayi fara kuka, ko tunashi sukayi haka suke ta wannan kukan abin tausayi sai ansha fama kafin su natsu tabbas wannan kaɗai ya isa a maidasu gidan ubansu gani fa a cikin sati ɗaya duk sun rame ina dalili a rabasu da gidansu da ubansu”. Da sauri Raihana ta amshi Zaitoon ta ɗaura a bayanta, ita kuma Fariyda Zaid ta amsa cikin tsoro da sauri tace. "Mamy zasu bari ai, dan Allah ki daina cewa za'a maidasu, shima me yasa yazo tunda yasan in sun ganshi yadda sukeyi”. Kwaffa tayi ta juya ta koma parlour Malam inda suke lissafin abubuwan buƙatar hidimar bikin Raihana kafin Mahmoud yazo. Ita kuwa Fariyda marin ƙeyar Zaid tayi tace. "Kai da Allah rufe mana baki, yara kamar mayu, ko uwar me zai baku da zaku addabi rayuwarmu da kiran sunansa, ko ni bakwa damuwa da nemana kamar shi, gashi har kunsa an fara kiran maidaku”. Aunty Sadiya tace. "Ai kam yaran nan kam da wuya zamansu ya ɗaure a nan”. Saddiqa na miƙewa tsaye tace. "Kingansu tunda suka dawo kullum sai sunyi wannan kukan da kiransa in zasuyi bacci”. Ta ƙare maganar tana shiga bathroom ɗin parlour al'walar sallan azahar tayi ta fito. Su Zaid da Zaitoon da sukayi bacci ta kalla tana sauƙe numfashi barkansu za'a barsu su sarara. Fariyda ta ɗan kalleta tace. "Akwai ruwan ɗumi a bathroom ɗin ne”. Cikin kulawa Aunty Saddiqa tace. "Wai ni har yaushe kika fara amfani da ruwan ɗumine ke dai nasan tunda kikaji ance ruwan ɗumi na ƙara tsuke mace kikace banda ke a ciki, bakya amfani dashi yanzu tunda kika fawo bini-bini ki kin shi ga ruwan ɗumi kamar wacce akayiwa karon huce haushi, ko dai Mahmoud bai baroki ba saida ya turmushe sadakinsa ne, dan wlh na lura tun randa kika dawo baki da lfy tafiyarki saiɓi-saiɓi ga uban magungunan zogi dana zazzaɓi”. Tuno abinda yayi matane yasata rumtse idonta da suka cika da ƙwalla ta fara jujjuya kai tana taɓe baki tace. "Ya isa inama zai ganni bare ya sameni, kawai dai zazzaɓi ne kuma ruwan ɗumin ai dan yanzu an fara sanyine shiyasa”. Aunty Sadiya ne tace. "Hmmm Saddiga ai wlh ni tun ranar nace mikiba Fariyda fa kamar ta shiga hannun maza kin santa da longomi duk yadda take yi kamar yadda Yah Amin ya samu angwancewa ne ga ido a kumbure ansha kuka har murya ta disashe, wai ta wani ce su Ummi ne suka bata tausayi suka sata kuka”. Kwaffa yayi ta miƙe ta shiga bathroom ɗin. Jin Salman na cewa. "Ai kuwa da Appiy ya san kan tsiya”. Suma duka tashi sukayi al'wala, bayan sun isar da sallane Adda Nana da tun ɗazu take kitchen da Ameera suka fito musu da abincin. Nan suka fara cin abinci suna hira cikin nishaɗi da tsara yadda bikin Raihana zai kasance. Adda Nana tace "To mu ai biki sai a Taraba tunda nan iya walima da sisters day kaɗai zamuyi”. Da sauri Fariyda tace. "Ai za'ayi kamu ko”. Aunty Saddiqa tace. "Sosai ma kuwa”. Salma na ɗan gyara zamanta tace. "To me dame za'ayi a Taraba”. Zainab tace. "Ai a Gembu membila ne za'ayi dinner da fansan ido”. Da sauri tace. "Ai mu duk ko ina damu za'ayi”. Aunty Rashida dake shigowa ne tace. “Ke yaushe ma akayi aurenki da har Salim ɗin zai barki zuwa aure har Taraba”. Ta ƙare maganar tana zama kusa da Fariyna dake cewa. "Tab ai to shima dai yasan ai dole zamuje”. Da sauri Adda Nana tace. “Zamuje dai ai ke kan Malam yace bazaki jeba tunda kina cikin idda in kuwa zakije saida yardar Mahmoud dama dai kin gama iddarsane”. Kwaɓe fuska tayi cikin takaici tace. "Na rantse da girman Allah ni ba ruwana da shifa dan girman Allah Adda Nana Ku ƙara faɗawa Malam da Mamy su barni in sake, ta yaya za'ace bazan je auren Raihana ba ni ba wani iddarsa a kaina”. Ta ƙare maganar cikin tsinkewar zuciya. Aunty Rashida ne tace. "Kamar ya baki da iddarsa kuyi aure da mutum a ƙalla tsawon wata takwas fa, ku tare a India wata kusan biyu ku biya Istanbul kusan kwana goma wai kice mana baki da iddarsa ai ji dai kam ya zama dole amman yarda sai mun bincika, ta yaya ma ke ɗin ne namiji kamar Mahmoud zai zauna dake tsawon wannan lokaci ya kasa ɗaura miki iddarsa wannan ma ai tatsuniya ce.” fuska cike da takaici tace. “Baya sona fa, bana sonshi to me zai haɗani dashi ƙanin Yah Aminnefa to wlh tallahi har mukaje muka dawo ba wannan maganar ku yarda dani dan bana sonshi kuma shima baya son”. Da sauri Salma tace. "WALLAHI yana sonki Fariyda Mahmoud yana sonki kuma kema kina sonshi”. Wani irin harara mai wasali ta watsa mata haɗi da cewa. "Baki da hankali ai, in dai har zakice wai ni dai ina son Appiy wlh har abada hakan bazai faruba, kuma shima hakane a wurinsa mutumin da in ya samu dama zai iya kasheni zaki wani ce wai yana sona”. Cikin sauri Salma ta kalli Aunty Saddiqa data zubawa Fariyda ido ba ko ƙibtawa. Dafa guiwar Aunty Saddiqa tayi tare da cewa. "Kin san Allah Aunty Saddiqa wlh Appiy yana son Fariyda, sai dai ko in shi kansa bai san ma yana sonta ba, ranar da abin nan ya farufa kin san ta gidansu Yah Salim suka fara zuwa kafin su zo nan ai”. Nan ta gyara zama ta fara basu Labarin duk tijarar da Jidda tayiwa Fariyda ta ɗaura da bayanin yadda Mahmoud yazo ya kirata ya tambaye ta me yasa Fariyda kuka da yadda tayi masa bayani, numfashi mai nauyi ta fesar haɗi da cewa. "Kunsan me wai Farriyyhah mafa yake kiranta, sunan ya masifar min daɗi yafi Farida daɗi, kun san me yayi”. Da sauri Aunty Rashida tace. “Fesa mana yar uwa“. Cikin tabbatar da iya gskya Salma tace. “Bayan ya fita baifi 9 to 10 minutes ba ya dawo ni kuma lokacin ina bathroom ɗin Jidda”. Aunty Saddiqa ne tace. “Me yayi?”. Cikin son gamsar dasu tace. "Wallahi yana shigowa ɗakin ya fara watsawa Jidda mari hagu da dama, yana faɗin akan me zaki sata zubda wahaye, ke kin san darajar hawayenta kuwa? Hawayenta shine hawaye na uku bayan na Ummi, Abba, sai nata sune hawaye uku na duniya da Yah Amin ya barmin wasiyyar kada in bari su zubo ƙasa, shine zaki sata zubda wahaye”. Tana kallonsu taci gaba da cewa. “Wlh yana mgnar ne yana watsa mata mari babu ƙaƙƙautawa gefen hagu da damanta duka, ita kuwa mayya uwar naci sai juya masa kunci take yi tana faɗin. “Ka kai ne ka isane kamin fiye da hakama Yah Mahmoud wannan ma abin alfahari ne a gareni duk da kan tsinenniyar yarinyar nan kake marina. Tana faɗin haka ya watsa mata tsawar da tasa Yah Salim da Mama duk suka shigo a guje, da yatsa ya nunata cikin faɗa yace mata. "Wannan ya zama shine na farko kuma na karshe a rayuwarki da zaki sata zubda wahaye, in