← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 95

Sashe 26

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 55
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Tace “Arda”.
kai ya ɗan rusunar ya gaita ya ɗaura da cewa. Ita ake jirafa tayi sauri kar suyi missing flight. Cike da mmki ta maimaita flight a kan lips ɗinta kai ya gyaɗa alamar eh ya ƙara da cewa. 11:00 Am jirginsu zai tashi gashi yanzu har 9:48 Am kuma zuwa Airport ɗin ma zai ɗaukesu 36 minute. Travelling luggage ɗinta ta nunawa Arda ɗin tana mai warware ɗan kwalin Turkesh Abaya dake jikinta, tayi Rollin kanta dashi, handbag ɗinta ta ɗauka bayan Arda ya fita, turarenta dake kan mirror ta fesa tare da tattare ƴan kananan tarkacenta da nasu Zaitoon tasa a ciki jalartan ta juya har taje bakin ƙofar sai kuma ta ɗan juyo tana kallon ɗakin ko akwai abinda ta manta, aikuwa da sauri ta dawo ta ɗauki wayarta tabi bayan Arda.
Ƙarfe sha ɗaya saura kwata da kyar take tura akwatin nata saboda nauyin da yayi na cika da kaya duk da ba wani ƙato bane, yana gefenta tare da su Zaitoon kai bakace ma tafiyarsu ɗaya ba.
Da sauri ta kalli gefen hagunta jin an riƙe akwatin.
"Wannan ai aiki nane babe”. Numfashi mai nauyi ta fesar jin daɗin amsar mata tura jakar, cikin kallon dake bayyana sirri so daga zuciya zuwa fuska yace.
“Sunana Faisal Uman Guroje, kefa?”. Hmmm tace tana gyara riƙon handbag ɗinta tana kauda fuskarta gefe dan kallon mayata da yake mata.
Dai-dai lokacin suka isa bakin steps ɗin jirgin gefe ya ɗan matsa ya nuna mata matakalar cikin taushin murya yace.
“Mata sune gaba akan komai saboda rauninsu”. Juyawa yayi ya ɗan kallesu saboda jin surutun yayi yawa a bayansa, dai-dai lokacin ta fara take step ɗin shi kuma Faisal ya ɗaga akwatin. A saman lips ɗinshi daya taɓe yace.
"To iliya ɗan mai karfi”. Kwaɓe fuska yayi kana ya juya yaci gaba da tafiya. Shi kuwa Faisal tafiya yake duk hankalinsa na kanta ita ke duba seat number ganin ta tsaya ne yace.
“Babe nanne seat naki?”. Kai ta gyaɗa masa alamar eh, ɗan matsowa ciki yayi ba tare da ya lura da Mahmoud da tuni ya zauna ya rungume su Zaid ɗaya a gefen dama ɗaya a gefen hagu yana latsa wayarsa. Akwatinta yasa cikin drawer jirgin kana ya ɗan juyo ya kalleta yana mai nuna mata seat ɗin yace.
“Bismillah zauna kinga ko ƙaddarama haɗamu makwataka tayi a jirgi, in sha Allah aure kuma zai haɗamu a inuwar jannatul firdausi”. Ido ta ɗan zuba mishi ganin ya zaro tissue ya ɗan goge seat ɗin, gefen ta ya ɗan rusuna bayan ta zauna a hankali yace. "Ko sai na biyane za'a faɗa min sunan?”. Tana ɗan kallon gefen Mahmoud ɗin jin Zaitoon na dariya, kanta yake shafawa da sumbatar goshinta.
“Fareeydah”. Ta faɗa a mutunce. Da sauri yace.
"Kin gani ko Allah ma ya haɗa alaƙar tun a sunayenmu Fareeydah mrs Faisal ai ya tafi sosai ko”. Ganin flight Attendance ɗin na ta duba zaman passengers da gyara rufe durowowinsu yasa shima zama a kujerar dake kusa da tasu Zaid da ba kowa akan kujerar dan Mahmoud ɗin na rungume dasu.
Sha ɗaya dai-dai jirginsu ya tashi zuwa Nigeria...
A hankali ya buɗe idonsa daga baccin da ya ɗaukesu shi dasu Zaid ɗin saboda surutun Faisal dake yiwa Attendance dinsu bayanin su buɗawa Fariyda kujerar zuwa gado su kawo mata blanket, ido ya zuba mishi cikin mmki ya taɓe baki yana nazartar Faisal ɗin “Gashi dai kamar Gentle man amman da ganin wannan abar duk ya susuci ya zama kamar mawaƙi surutu kamar kabarai duk ya gigice ya hanamu bacci cikin salama sabida sakarci mutum kamar bunsuru ya faɗa a cikin ransa. A fili kuwa harara ya auwana side ɗin da Faisal ɗin yake haɗi da jan dogon tsaki mai manyan wasula ya ƙare da taɓe fuska kamar yaga abun ƙyama.
Shi kuwa Faisal numfashi ya fesar tare da cewa.
"Good night babe kiyi bacci mai daɗi da kekkyawan mafarki”. Hmmm kawai tace mai kamar yadda duk mgnar da yake yi bata wuce ce masa hmmm ko uhmmm daga sunanta da ta faɗa bata kuma ce mai komai ba.
Gyara kwanciyarsa yayi bayan ya buɗa gadon ya amshi blanket ya rufe su Zaid dake rungume dashi daga nan ya maida baccisa.
Istanbul to Logos tafiya 7 hours and 17 minute gashi tafiyar darene, haka yasa mafi akasarin mutanen sunyi bacci, Cikin sanin makamar aiki pilot ɗin ya rinƙa farara gudu, cikin duhun dare da duhun gajumare a sararin samaniya, karfe 6:20 Am dai-dai sukayi landing a Murtala Muhammad International airport Lagos. Bayan sun fito ne ta kalli gefe inda yake tafe dasu Zaid ba komai a hannunsa iyaka system nashi ko akwatinsa bata ganiba kuma suma jakar kayan sanyin ya hana Arda fito dashi daga motar ma.
Numfashi mai sanyi ta fesar lokacin da ta shiƙi ni'imtaccen iskar ƙasarta da tayi wata biyu cib harda ɗorin kwanaki bata shaƙaba, tana biye dashi a baya Faisal na maƙale a gefe yana tura akwatin ta suka fito daga cikin Arrivals ɗin shima Faisal yar karamar jakace goye a bayansa, kusan a tare suka fito, mutanen dake ɗan cike a wurin waɗanda suka zo ɗaukar yan uwansu ne ke ɗan dudduba fuskokin masu fitowa, daga gefen ƙofar da suka fito akwai wata ƙofar itama matafiya ne ke fitowa daga ciki bisa dukkan alamu kusa a jere a jere flights ɗin suka sauƙa.
Yana gaba Zaid da Zaitoon na gabanshi cikin kekkyawar shigarsu.
Ita kuwa Fariyda suna bayanshi kaɗan ita da Faisal ɗin.
Ido ta zuba mishi cikin tsananin sabo da shaƙuwar da ko an shekara goma ba a haɗuba baza'a gaza gane junaba, cikin zaro ido tayi kanshi da sassarfa tana ƙara tsareshi da ido, hankalinsa na kan Zaitoon da Zaid ya shakumo gashin kanta da ƙarfi yasa hannunsa daya zai ƙwace tab ɗinsa da ta fizge, a hankali ya ɗago kansa jin muryarta tace.
“Papi”. Ido ya ɗan zuba mata in second yace.
“Fadila”. Yayi magnar tare da taɓe baki gami da ɗan ɗaga girarsa ɗaya da ɗan kwaɓe fuska .
Wani irin tsalle tayi ta nufi abkawa jikinsa, da karfi ya dafe filar dake gefensa tare da rumtse idanunsa lokacin da ya kaucewa rungumar ya ɗan tureta yace. “Har yanzu bakiyi hankali ba kenan”. Sake hannunshi da ta riƙe lokacin da yasa hannun dan tureta tayi tana dariya mai cike da tsananin jin dadi tace.
“Kamar dai yadda har yanzu baka da mutunci ba fara'a haka nima”.
Ido Fariyda ta zuba musu tun sanda ta kira sunan da ta fara ji a wurin Idaya da ta tabbatar mata ita karuwarsace sai kuma yau da taji a bakin wannanr matar da ta hango ta kai mishi harin rungumeshi.
Ita kuwa Fadila hannu ta miƙa masa tana cewa.
“Ya kake”. Ɗan buge cikin tafin hannunta yayi da bayan tafin hannunsa a taƙaice yace. “Lau”. Sai kuma tayi wata iriyar dariya mai cike da jin daɗi haɗuwa dashi.
Shi kuwa Mahmoud a hankali ya ɗan juyo kansa inda suke ya zubawa ido yanayin fuskarsa na sauyawa.
Ƙeyar Faisal da ya miƙa mata wayarsa tare da faɗin.
“Ki taimaka ki samin number ki dan in samu sauƙin tafiya da zuciyata da zakiyi”. Tana ɗan kallon Mahmoud ɗin ido cikin ido sukayi dashi sai kuma tayi saurin yin ƙasa da kanta dan kallon da ya watsa mata yasata jin bazata iya ci gaba da tsaida idonta cikin nasaba. Idansa ya maida kan ƙeyar Faisal ɗin yana taɓe baki.
Fadila da ta kuma matsoshi ya ɗan kalla a fakaice yana mai meda kallonsa kan Fariyda da ta amshi wayar Faisal yace.
“yanzu me kikeyi”. Tana mishi kallon dake nuna shaƙuwarsu tace.
“yi a hankali yanzu da yar jarida kake tare yanzu zan bazaka a duniya”.
Ɗan guntun murmushi iya ƙurewar fara'arsa da taga yakeyiwa su Zaid yayi sai kuma ya ɗan juyo ya kalli inda su Fariyda suke idonsa na kan Fariyda yacewa Fadila..
“Yaranki nawa? A ina kike aiki? Ina Umma”. Numfashi ta fesar tana kallon inda yake kallo tace.
“Banyi aureba Umma tana lfy, ina aiki a nan Lagos kasan mun dawo nan ai tun bayan rasuwar Abbana muka dawo Lagos wurin Yah Ismael da Umma”.
A hankali yace.
“Ke sai kin tsufa zakiyi aurene me kike jira”. Tana dariya tace.
“Kai nake jira”. Ɗan kallon Fariyda yayi ido cikin ido sai kuna ya ɗan lumshe nasa idon tare da cewa Fadilan.
“Zaki bani number ki in kaiwa Fadil”. Ya ƙare maganar yana ɗan juyo fuskarsa kanta.
Cikin kwaɓe fuska tace. “Meyasa sai Fadil kai baka bukatar number ta kenan”. Ƙara juyowa yayi yana kallon Fariyda dake yiwa Faisal murmushin da ya subce mata saboda ce mata da yayi. “Next Mount uwar haka zamu sake tafiya Istanbul ko Canada Honeymoon”. Kauda kanshi yayi tare da cewa Fadila.
“Saboda shine sunanku iri ɗaya dashi”. Dariya mai cike da tuna baya tayi tace. "Allah sarki Fadil da gaske kuna tare? Yanzu me yake yi? Yayi aurene?”. Kai ya jujjuya mata cikin ɗan shaƙuwarsu ta ƙawancen ƙuruciya yace.
"Ai tuntuni ya zama Pediatrician, kuma yana Kano shine ma Dr twins na aure kam ai yace har abada bazai yiba sai ya jiraki duk inda kika shiga”. Da sauri tace.
“Dama burinsa kenan ya zama likitan yara”. Sai kuma ta ɗan kalleshi ganin ya sunkuyo cikin mmki take kallon su Zaitoon more Especially Zaid ido cike da fargaba tace. “Waɗan nan fa”. Ido ya juya cikin nuna girma yace. “Ƴaƴana”. Sai kuma ya ɗan shafa kan Zaitoon tare da cewa.
“Zaitoon banda fadan rashin gskya je wurin Ammiy ki amshi naki tab ɗin”. ya ƙare maganar yana nuna mata Fariyda da yatsarsa. Da gudu kuwa ta nufi wurin Fariyda shi kuwa Mahmoud wayarsa ya miƙa mata tare da cewa.
“Samin number zan kaiwa Fadil dan al'kawarin nayi masa”. Ido cike da karaya take kallon Fariyda dake wani irin ƙyalli har yellow yellow take yi fatarta sa wani irin shegen glowing yakeyi, afuskarta ta zuba wa ido more Especially lips ɗinta da take motsawa alamun tana yiwa Zaitoon mgna kan gashin girarta ta maida idonta zuwa saman goshinta inda wani irin tattausan suma mai sulɓin gaske dake kwance lip lip ɗan jikinta da yake tafiya da shekarunta da bayyana asalin ƙuruciyarta da ziryar madaran kyanta ta kuma kalla duk da Abayace amman cikar surarta ta bayyana, handbag ɗinta ta buɗe ta zaro tab ɗin Zaitoon ta miƙa mata fahimtar abinda take so da kuma ganin da tayi Mahmoud na nuna mata ita, sunkuyowar da ta ɗanyine yasa jelar gashinta fitowa ta gefe, miƙewa tsaye tayi tana kallon Faisal dake cewa.
“Gacan brother na yazo ɗaukana muje ku gaisa ko”. Kai ta jujjuya da sauri tare da cewa.
“A'a nima gacan yayana tare zamu tafi”'. Yana kallon Zaitoon ta juya a guje ta koma wurin Mahmoud yace.
“Wai tare kuke da shine?”. Kai ta gyaɗa mishi da sauri ya sa hannu ya kama kanshi.
“Babe baki gaya min yayanki bane wlh ban kula da kamar da kukeyi dashi Bama sai yanzu shi yana nan tamkar Aryan Khan ɗan SRK naga sam baya dariya ke kuma kamar Suhana Khan wlh sai yanzu na lura da kamarku bari inje in gaidashi duk da dai kamar ƙanine a wurina amman tunda yayankine ai girma ya dawo nashi”. Kafin ta iya cewa komai ma tuni ya tafi.
Hannu ya mika Mahmoud ɗin tare da cewa.
“Afwan babban Yaya nayi laifi a yafe min amman in sha Allah zanzo har gida in bada haƙuri”. Ya ƙare maganar tare da sauƙe hannunsa dan Mahmoud ɗin bai bashi hannunba sai kai daya jinjina masa tare da cewa.
“Sai kazo ɗin”. Ya dire mgnar yana ceje gefen lip ɗinshi na ƙasa da ƙarfi. Kai Faisal ɗin ya ɗan shafa yana murmurshi ya juyo kansa kan Fadila da har yanzu idonta na kan Fariyda shiyasa bata ji gaisuwar da yayi mata bama ganin wani irin kallon wulaƙancin da ƙasƙancin da Mahmoud keyi masane ya sashi juyawa wurin Fariyda ya dawo yana faɗin.
“Sai kinjini”. Ya faɗa yana saven number Yah Amin da ta saka mishi.
Jin alamun ana kallonta ne ta ɗago kanta tare da juya lumsassun idanta cikin sanyi Fadila tace.
“Kai baka buƙatar number tawace”. Yana ɗan nunata da yatsa yace.
“Ni number Yah Isma'el zaki samin”. Ya faɗa idonsa na kan Fariyda har lau yana cije da lip ɗinshi yana ɗan daddatsawa da sauri-sauri, murya cike karaya Fadilan tace.
“Papi na karaya da cikar muradina amman ban cire raiba,”. Ta ƙare maganar da amsar wayarsa da yake miƙa mata number ta ta fara sa mishi tana maida hawayen dake ciko mata ido sai kuma tasa mishi number Yah Isma'il, miƙa mishi tayi tana kallon yadda ya rungume Zaid da Zaitoon cikin sanyi tace.
“Bari dai inyi maka hug ɗin welcome back in my life”. Kafin yace wani abu ta ƙaraso gareshi ta buɗe hannunta ta ronƙofowa kasu tayi musu wata iriyar run...........
Chapter 26 · 0% Book details