← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 95

Sashe 43

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ƙara Jawota jikinsa ya kwantar da ita manne dashi, a hankali yasakafanshi ya gyara mata ƙafafunta sannan ya jawo duvet ɗin ya rufesu zuwa wuya hannunsa da ya ɗan miƙar yayi mata pillow dashi ya kuma gyara mata yadda zataji daɗin baccin, numfashi mai sanyi ya shaƙata tare da ƙara haɗe bayanta da ƙirjinsa, cikin ƙanƙanin lokacin bacci mai nauyi ya danneshi. Ƙarfe tara dai-dai Amina ta shigo parlour nasu da sallama da basket ɗin abincin da tayi masa tunda Goggo Dada ta gaya mata bashi da lfy ta tashi da sassafe ta shirya mai breakfast jin Mahmoud ɗin ne ba lfy yasa Daddyn Hafiz bai hanata zuwaba musamman da ta bashi lbrin abinda ya faru jiya na zuwan idaya. Akan Dinnin table ɗinsa ta ajiye basket ɗin har kamar zata nufi corridorn ɗakinsa sai kuma ta juya ta nufi ɗakin Fariyda tana faɗin. “Kema baccin kikeyi kenan”. Ta ƙare maganar tana tura ƙofar bedroom ɗin, kwance ta hangosu kan gadon yana rungume da ita bayanta na manne da ƙirjinsa tamkar zai maida ita cikinsa, dogon gashinta na zube har kan fuskarsa da nata, Sai fitinennen ƙamshin da sanyi mai ratsa jiki da taji yana busota haka yasata saurin jawo ƙofar ta rufe a hankali ta juya ta fita tana murmushi tare da jinjina kai a fili tace. "Hmmm muje zuwa dai zamuga inda game ɗin zai tsaya, miskili da mai jan aji”. Motsin rufe ƙofar ne yasashi farkawa a hankali yake fesar da numfashi yana mai buɗe lumsassun idanunsa da suke ɗan ɗauke da rogowar bacci, cikin kasala ya ɗan yunƙura haɗi da juyawa ya dawo ta gabanta dan tsamin da hannunsa ya ɗanyi, lip ɗinta na ƙasa da ta ɗan turo tana tsotsar na sama ya zuba wa ido. Lumshesu yayi yana mai manna lips ɗin shi kan nata, na ƙasan ya yayiwa ɗan wani irin lasa haɗe da ɗan kamawa numfashi ya fesar cikin yanayin da bai san ya shigeshi ba dan jin taushin lip ɗin tamkar kunnen fure, cikin baccin taji lip ɗinta na sama ya saɓule mata daga tsotsar da take masa muddin tana bacci, ba tare da ta buɗe idoba ta ɗan turo tongue dinsa da numfin kama nata lip dinta na sama, dai-dai lokacin shi kuma ya ɗan sa tongue dinsa dan lasar lip ɗinta na sama da ya saɓule mata,. “Hsyttthhhh”. Yaja nakasashshe numfashi mai haɗe da ajiyar zuciya cikin maƙoshi dan jin yadda tayiwa tongue dinsa amintaccen kamu ta ritsashi da tsotso tamkar ta samu alwar yara. Idanunsa da suka fara tsatstsafo wasu kafuran hawaye ya zuba mata kan fuskarta, baccinta take cikin salama da amincin ta ritsa mai harshe tamkar yadda take ritsa lip ɗinta wanda zuwa yanzu ya gama gamsuwa da tabbatarwa kansa wanan halitartace haka. Tsuma jikinsa ya farayi ta can cikin naman jikinsa haka yasa jikinsa sakewa ya kasa koda ƙebta idonsa ne daga kallon kekkyawar fuskantar. “Hgyymmmmm”. Yaja numfashi mai sarƙafe da zazzafan yanayin da yasa idonsa rikicewa i zuwa kalar mshayin giya da yayi tatul sai sheƙin hawaye suke yi. Numfashi da ya jane yasa tongue dinsa ɗan zame mata, da sauri ta ƙara matso da kanta haɗe da lalumo shi. Lip ɗinta na saman ya ɗan ɗaura kan tongue shi data samu damar limtsimewa ɗan danna lip ɗinta na saman yayi da teeth ɗinsa. A hankali ta fara buɗe idonta tana mai ci gaba da mishi tsoysar da yashi fara tsuma a fili. Da sauri ta maida idonta ta rufe haɗi da janye bakinta daga nashi ta janye jikinta da sauri ta miƙe tsaye cikin rawan jiki ta fara tattare gashin kanta har lau idonta a rufe cikin masifeffiyar kunyar data rufeta ta dira ƙasa daga nan ta juya ta fita ba tare da ta kuma kalli ta inda yakeba ta fi da gyalen Abayar ta a hannunta tana rufe fuskarta da shi. A parlour Ummi ta samesu cikin kulawa Ummi da Goggo Dada ke tambayata ya kwanan mai jiki ya samu bacci ko, tana ɗan sunkuyar da kanta tace. “Alhamdulillah da sauƙi sosai.” Sai kuma ta rungume su Zaid da sukazo gabanta tana kallon Amina dake cewa. "Na shiga ai na samu kuna bacci, anya kuwa kun samuyin baccin dare”. Da sauri tace. “Yana ɗakinsa ai, tun da ya farka ya koma can”. Dariyar da Aminan tayine ya ƙara mata tsarguwa cikin kunya mai tafe da takaici ta kauda kanta, ta amshi cup ɗin tea da Goggo Dada ke miƙa mata. Ƙarfe goma dai-dai Goggo Abu da Yah Mujahid suka zo bayan sun gaggaisa ne Ummi tace. "Fariyda je ki kira Mahmoud ɗin yazo su gaisa da Goggo Abu naku”. Cikin kauda kai ga mayataccen kallon da Yah Mujahid ɗin ke mata na son su haɗa ido ita kuma taƙi kai a sunkuye tace."Toh Ummi.” Ummi ne ta kalli Goggo Abu dake cewa. “Tunda suka dawo ina son inzo in duba jikin Zaid in musu Barka da dawowa zazzaɓi ne ya hanani sai yau da naji sauƙi nace Mujahid ya kawoni kafin ma ya fita”. Ummi tace. “Ayyah ai haka ake fama da zazzaɓuɓɓukan nan Allah dai ya sauwaƙa”. Goggo Dada tace Amin. Amina kuwa Mujahid da yabi Fariyda da kallo take masa kallon kallo. A hankali ta tura ƙofar bedroom ɗin idonta a ƙasa, har yanzu yana kwance inda ta barshi, wayarta dake kan mirror ta ɗauka tare da duba lokaci ƙarfe goma harda kwata kanshi ta ɗan sunkuyo cikin sanyi tace. "Har yanzu bacci yake yi, ne Yah Nasir ya bashi ne kam”. Ta ƙare maganar tana ƙara sunkuyowa kanshi dai-dai kan fuskarsa dan a zatonta bacci yakeyi. Da sauri ta rumtse idonta jin ya jawota jikinsa ya rungumata tsam a hankali ya juya ta zama tana ƙasa shi yana samanta, yana kallon fuskar data rufe ido gam, murya can ƙasan maƙoshinsa yace. “Ina kika gudu kika shigane tun ɗazu”. Tana mutsu-mutsun tace. "Ina parlour Ummi ne munyi baƙi”. Kanshi ya kai tsakanin wuyanta da kafaɗarta ya manna hancinsa kana a hankali yace. “Zan rama fa”. yar-yar tsikar jikinta ya fara zuwa baki ta ɗan tura haɗi da cewa. "Me ɗin”. Lips ɗin ta ya ɗan lasa yace. “Tsinke min tongue da kikaso kiyi mana”. Kwaɓe fuska tayi cikin fitinenniyar kunya tace. “Ni ka sakeni. Munyi baƙi fa Ummi tace in kiraka”. Yana kallon ƙirjinta murya a sanyaye yace. "Su waye ne?”. Tana jan numfashi tace. “Goggo Abu ne da Yah Mujahid”. Wani irin kallo ya bita dashi tare da zamewa ya kwanta gefenta ba tare da ya sake cewa komai ba, idonsa daya rumtse da ƙarfi ta ɗan kalla sai kuma ta kalli lip ɗinshi na ƙasa da ya datse na da ƙarfi, duvet ɗin yaja ya rufe jikinsa har zuwa kanshi. Idon ta na kanshi tace. “Ummi tace ka zo ku gaisa dasu Yah Mujahid ɗin”. Shiru bai kulataba bai buɗe idonsa ba bare ya kalleta, numfashi ta sauƙe a hankali tace. “Appiy ka je Ummi na kiranka ka gaisa dasu”. Ta ƙare mgnar tana kallon yadda jijiyoyin kansa suka fara ɗan tasowa musamman na kan goshinsa har wani harbawa take yi sai kafafunsa da yake ƙarƙarɗawa, haka yasa ta ɗan sunkuyo tana faɗin. "Appiy ka tashi kaje ku gaisa, ko dai kayinka ne yake ciwo”. Wani zazzafan numfashi ya fesar ba tare da yace mata komai ba, tana leƙo fuskarsa tace. “Ko inje in iso dasu nan ku gaisa da Yah Muhajid ɗin”. Da sauri ta matsa cikin zaro ido ta jingina bayanta jikin Wordrobe ɗinta jin yadda yayi mata tsawa murya a hargitse cikin tsananin fusata yace. “Ke bazan jeba! Kuma Wallahi tallahi in kika kuskura kika yi gigin kawo min wani ƙaton bamagujen banza jahili ya shigo min parlour na Kai ko upstairs na ya tako wlh sai na sa an baddashi batarwar da bazai ƙara ganin hasken ranaba a rayuwarsa, ki fice min da gani kar in ɓaɓɓallaki”. Ya ƙare maganar cikin rawan jiki da nuna mata hanyar fita da hannunsa dake ƙarƙarwa tamkar mazari fuskarsa tamkar zata zubda jini dan haɗewa da fusata numfashi wani na korar wani. Cikin tsoronsa da bata taɓa jibi kamar na yauɗin saboda tsananin sauyawar kamanninsa da kaushin muryasa da zafin amonta yasa jikinsa ƙarƙarwa. Hakan yasa ta rufe idanta da karfi tasa hannunta ta kare kanta lip ɗinta na ƙasa ta turo cikin kwaɓe fuska murya cike da tsoro tace. "Appiy Ummi cefa ta aikeni tace kaje ku gaisa da”. Da sauri tayi waje da sassarfa saboda jin tsawan da ya auna mata cikin muryarsa data disashe dan cushewar numfashi. Tana tafiya tana juyo bayanta, dan tayi zaton ya biyo bayanta. A parlour ta zauna gefen Ummi cikin sauƙe numfashin tsoro tace. “Ummi yana bacci fa”. Goggo Abu dake riƙe da Zaid tace. “Laa ba komai fa ku barshi, in ya tashi a gaida min shi da jiki”. Sai kuma ta kalli Majahid da ya tsare Fariyda da kallo tace. “Kai tashi mu tafi ko”. A hankali ya miƙe tsaye jin ta kuma cewa, mutafi ko, baki Amina ta taɓe tana mai kauda kai daga kanshi, Fariyda ta miƙe tabi bayan Goggo Abu ita dasu Ummi sukayi musu rakiya. Tun safe har akayi azahar bai sauƙoba, Ummi ne tace. "Fariyda je ki duba min Mahmoud lafiya kuwa har yanzu bai sauƙoba ko dai jikin ne”. Kai ta gyaɗa ta miƙe ta fita. A hankali take taka upstairs ɗin da sauri ta ɗan ja da baya lokacin da ta isa bakin ƙofar parlour ganin ya turo ƙofar. Zaitoon dake hannunta ne tayi dariya mai sauti tare da miƙa mishi hannu tana kallonshi tace. “Appiy ina kwana ya jiki?”. amsar Zaitoon ɗin yayi ba tare da ya kalleta ba yace. "Ba ruwanki dani da jikina ke da kike min addu'ar mutuwa ai in banda lfy dariya zakiyi”. Cikin sanyin jiki tace. "Allah ya baka haƙuri ya baka lfy”. Bai kulata ba bare ya amsa ya sauƙa ƙasa ita kuma tayi ciki. Washe gari wunin ranar duka bata ganshi ba, wuraren ƙarfe tara da rabi na dare tsaye take gaban mirror cikin wasu tattausan riga da wando na bacci, wondon iya guiwa ne ya lafe a cikinta sai yar rigar mai hannun bra, hularsa ta ɗauka a Istanbul ta sa kanta, tana fesa rurarukan hadi da kallon Zaitoon dake tsaye
Chapter 43 · 0% Book details