← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 95

Sashe 3

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Numfashi mai nauyi Abba ya fesar saboda jin Mahmoud yayi shiru, alamun amsa yake jira, cikin tausasa lafazi yace.
“Nakasa tana nufin mutumin da wani sashi na gangar jikinsa yake da tawaya, kamar ƙafa! hannu! ido! kunne!”. Murya na rawa yace.
"Abba kuma duk mai wata makamanciyar wannan ba cikekken mutum bane”. Da sauri Abba ya fara girgiza kai kamar suna tare yace.
“A'a Mahmoud cikekken mutum ne mana, sai dai bashida cikakkiyar halitta shi yasa za'a iya kiransa da nakasa dan tauyeyyen halittar shi”. Zuwa yanzu muryarsa ta fara disashewa cikin rawan da muryar tasa take yace.
“Abba kenan nima nakasashshe ne, ban cika mutum ba, tunda naksata ma ai tafi ta hannu! da ƙafa! da ido! da kunne! tafisu illa da nakasa rayuwar mutum, amman ai Abba bani na ɗaurawa kaina ba ko? Allah ne ya ɗaura min duk da nasan na saɓa masa da lafiyar da ya bani a baya na kasance ma”. Cikin kamala Abba ya fara jujjuya kai yana faɗin.
"Kul Mahmoud kada kace komai, ka tsaya iya Allah ne ya ɗaura maka, kuma jarabtace zaka kuma cinyeta in sha Allah, kada kace komai kayi haƙuri, shi Allah gafurun ne kuma rahimunne”. A hankali Ummi ta zauna gefen Abba kib dashi, fahimtar da Mahmoud yake mgna ne yasata sauƙe numfashi mai nauyi
Shi kuwa Mahmoud Da sauri ya fara magna cikin fizgo mgnar da rawan murya yace.
"Abba dan an min gorin banda lfy bazan haihuba ni ba cikekken mutum bane bazai sa in butul cewa Allah ba na godewa Allah a hakama da ya bani rai da lfy, Allah ne kaɗai fa yasan adadin mutum nawane suka mutu a wannan iftila'in ni kuwa ya barni da rai da ji da gani da tafiya, kawai dan ya nakasa min sashin da rasashi ya zame min al'khairi ya hanani saɓa masa ai bazanyi kuka ko ƙorafi ba. Matsalata ɗaya ce da kuka ƙi yarda da mgna ta, kuka bi ta Yah Amin da yafaɗa cikin zafin fitan rai kuka haɗani da abinda zai iya sawa inji cewa Allah ya tauye min halitta ta”. Cikin cushewar tunani Abba yace. “Mahmoud ka raunata min zuciya zaka sani hawaye, yanzu kana inane”. A hankali yace.
“Kayi haƙuri Abba kada kayi min kuka, ina Kerala ne naje ganin Dr Avinash”. Cikin sanyi Abba yace.
"Yaushe zaka koma, dan hankalin Fariyda ya tashi itace ta gayawa Amina bata san inda kake ba, ga can su Zaid nata kuka da kiranka, tace baka gaya mata ina zakaje?”.
Cikin danne zuciyarsa yace.
"Eh gobe zan je dan zan maida Zaid wurin Dr Imran Patel zai ƙara dubashi”. Cikin taussa lafazi Abba yace.
"Allah yayi maka al'barka, ya rufa maka asiri duniya da ƙiyama, Allah ya raya maka yaranka yayi musu al'barka”. A sanyaye yace Amin kana daga nan sukayi sallama.
Da sauri Ummi tace.
“Yana ina ne wai? Me yake gaya maka”. Cikin girma Abba yayi mata bayanin yadda sukayi dashi, A sanyaye tace.
“Yanzu dai na gama gamsuwa Mahmoud bai samu lfy ba, kuma bazai iya zaman aureba, tunda aka fara wannan ta ƙaddamar a tsakaninsu bamu da wata madogara a haɗasu zaman aure”.
Cikin karaya Abba yace.
"Shike nan ni kuma haka Allah ya ƙaddara min kan yarana. Allah na tuba ban butulce maba wanima bai taɓa haihuwar ba”.
Ahmedabad.
Cikin sanyi take kallon Amina murya a sanyaye ido cike da hawaye tace.
“Driver yace min Airport ya kaishi Amman bai san jirgin ina ya shigaba, kuma shima tun ranar basu sake yin mgna da shiba”.
Shigowar Ummi ɗakin Goggo Dada inda Amina ke zaune tace.
“Da Fariyda ne kuke mgna”. Da sauri ta miƙa mata waya tare da cewa.
“Eh Ummi itace gata taƙi bacci ita kuka su Zaid kuka”.
Da sauri ta saki wani raunataccen kuka murya na rawa tace.
"Ummi ban san inda ya tafi ba, kuma har yanzu bai dawoba, gasu Zaid ma sunƙi bacci sai kuka sukeyi suna kiransa, ni kuma bansan inda yajeba, ba kowa sai ni dasu tsoro nakeji ban san ina zanje in nemoshi ba”. Cikin mmki Ummin ke kallon yadda take sheshheƙan da zubda ƙwalla cikin murmushi tace.
“Ba komai Fariyda yanzu yayi waya da Abbanku, yana lfy ba abinda ya sameshi K...”. maganarce ta maƙale mata a maƙoshi jin sautin nannauyar ajiyar zuciya da Fariyda ta sauƙe ta lumshe idonta ta buɗe gami da cewa.
“Alhamdulillah”. Aminace tayi dariya gami da cewa.
“To sai a bar ni inyi bacci a lallaɓa min yara tunda anji labarin inda Habibi da'iman yake”.
Baki ta taɓe tare da yin ƙasa da murya yadda Ummi da Goggo Dada da suka nufi parlour bazasu jiba tace.
“To ni me gamina dashi, yaje yayi ta yajinsa mana in yaga dama kar ya dawo ya jira ayi bikonsa, tunda yaji yayi, ni tausayin Ummi da Abba ne ya hanani nitsuwa Yah Amin ya tafi shima ɗan bala'in sarkin faɗa ace babu shi ai zuciyar Umminmu zata tsaya, ga kuma su Zaid suna damuna da kiransa, in babushi zasu zama marayun gaske shiyasa hankalina ya tashi ina tsoron su rasashi”. Da sauri ta katse kiran jin Goggo Dada na cewa.
“Oh wato ke banda ke a damuwar rashinsa”.
Anan akan sallayar ta kwanta kusa da su Zaitoon da ta samu bacci yayi gaba dasu.
Kano
Washe gari da safe Ummi zaune dasu Mamy a parlour ta, Aunty Amarya ce tace.
"Mu ai tun jiyan mukaso zuwa, ganin dare yayine yasa muka haƙura, to ta kira Saddiqa ita kuka su Zaitoon kuka wai kwana hudufa ba'a ga Mahmoud ba sannan kuma bakwa samunsa a waya, harda cewa wai kada ace ita ta batar dashi”. Dariya Amina tayi tare da cewa.
“Yoh in dai bai badda ita ba ai bata badda shi ba”.
Nan dai sukayi yar hira kana Dr Nasir ya tafi dasu.
Ahmedabad
Harara ta liƙawa akwatinsa sai kuma ta ɗan jawoshi gabanta, buɗe zip ɗin tayi.
“Shmhummm”. Taja dogon numfashi sabida ƙamshi turarensa daya buɗe mata hanci ido ta zuwa kayan saboda ganin zip box hawa-hawa a cikin akwatin da alamu komai da wurin zamansa, box na firƙo ta buɗe kaya baccinsa dake jere a ciki wanda suke a wanke a goge, ɗagawa ta farayi a hankali tana ajiyewa kan kujera, wasu tattausan gajeren wondo da yar top ɗinsa mai guntun hannu nevy blue masu masifar kyau da taushi ta ɗan ware tare da, sunsunarsu ta mannasu kan fuskarta ƙamshinsu da laushinsu yasata warware su, a fili tace.
“Wlhi ɗaukesu zanyi duk abinda zai faru ya faru”.
Sai kuma ta buɗe ɗaya zip box boxers ɗinsane da singlet ɗinsa suma wanke ƙal a goge sai dai su ƙamshisu ba irin na jikin kayan baccinsa bane, wani irin sassayan ƙamshine mai shiga zuciya sukeyi.
ɗaya ta kuma buɗewa glass's ɗinsa ne da agogonshi da ring sai car keys guda biyu. Da sauri ta buɗe na kusa dashi, turarukan sane da man shafawansa na jiki da kai kusan kala uku-uku, sai kum ɗinsa da suke cikin paket ɗinsu
gefenshi kaɗa taga ƙaramin box ta buɗe brush da Makilin ɗin one family na yayan strawberry. Sai sabulun guda uku da ba'a buɗeba komai masu masifar tsadar gaskene a ciki.
Manyan ta fara buɗewa ganin kayan sawansa ne a ciki ɗaya wondunan jeans ne na kansa rigunan ɗaya kuma jompa ne guda biyu sai suit kusan uku, sai ɗaya kuma 3 quarter ne a ciki da rigunansu, da pajamas fara maidawa tayi bayan ta cire turarukan nasa biyu ta bar mai ɗaya.
“Mutum sai ƙa'ida komai da ƙa'idar wurin zamansa”. Rufe wa tayi gami da maidashi wurin zamansa.
Kan gado ta ajiye riga da wondon, da turarukan wanka ta shiga, tana fitowa tayi sallan azahar, mai kawai ta ɗan shafa ta gyara gashin kanta ta tubkeshi da ribbon ɗin ba ta kitse jelarba, ta fara saka kayan, murmushi mai sauti tayi lokacin da ta tsaya gaba dressing mirror, ganin yadda rigar tayi mata ruwa-ruwa sai wondon kuma da ya cika cib da hips ɗinta, wondon iya karsa guiwowinta, wuyan rigar da yayi mata sakayau da faɗin rigar ya taimaka wurin bayyana ƙirjinta dake tsaye, haka kuma yasata jinta so Comfortable sosai kayan suka mata daɗi a jikinta turarensa ta fesa a karo na uku dan ƙamshinsa da yake ƙara sata fesawa.
Chapter 3 · 0% Book details