Sashe 12
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ta juya ta fita ido cike da hawaye saboda tsoron yanayin data hangoshi yasa ta kasa tsayuwa a wurin sai kiran Amina data amsa. Cikin nuna kulawa Aunty Maryam ɗin ta iso bakin gadon tana faɗin. “Innalillahi Mahmoud jikin har haka ne?”. Amira kuwa gefenshi ta matso gab dashi tana mishi mayataccen kallon so cikin kirsa da yauƙi tace. “Wash Allah na, Aunty Maryam a kira Dr suzo su duba min shi ga yadda yake kakari fa”. Ta ƙare maganar tana yiwa Fariyda wani irin mugun kallo. Ita kuwa Fariyda cikin tsinkewar zuciyar ganin mawuyacin halin da yake cikine yasa ta ƙara matsowa bakin gadon kusa da Arda dai-dai kanshi ido cike da ƙollah ganin wani sabon yunƙurin daya taso masa mai haɗe da shaƙuwa da rawan sanyin da yayi masa rubdugu. “Innalillahi Appiy sannu”. Ta faɗa da narkekkiyar muryarta da yasashi ɗago kanshi da sauri, cikin rawan jiki ya fara motsa lips ɗinshi dan yin mgna amman ina kakarin ya hanashi sukuni, hannunsa da ya ɗaga yake yafitota da yatsunsa alamun ta zo kusa ne yasa tayi saurin matsowa gab dashi saboda matsawa da Arda yayi. Da ƙarfi ya fizgo hannunta tare da fizgo magna. “Ina s...” sai kuma mgnar ta carke saboda shaƙuwa da kakari rawan sanyin da yake yi ya tsananta. Kai ya rinƙa jujjuyawa dan jin numfashinsa na carkewa cikin shaƙuwar innalillahi shine abinda Yah Saleh da ya shigo Doctors na biye dashi a baya ya faɗa. Da sauri Nurses ɗin da suka shigo suka cewa su Maryam su basu wurin. Haka ne yasa Arda saurin matsawa. Aunty Maryam ta kalli Fariyda a yatsine tace. “Ki matsa a wurin ki barsu suyi aikinsu mana tunda ke dai ba likita bace. Amira ke ki matso kusa tunda ke Nurses ce bazaki rasa taimakon da zakiyi masa ba”. Da ƙarfi ya ƙara damƙe hannun Fariyda dake cikin nasa tare da fara jujjuya kansa, alamu a'a karta tafi, ganin haka ne yasa ɗaya Dr yace Fariyda ta tsaya. Yah Saleh kuwa da Arda gefe suka tsaya haka ne yasa Aunty Maryam zuwa kasa dasu, Amira kuwa wurin sawunsa ta tsaya. Da sauri Dr ya haɗa wata allurar yayinda ɗayan kuma ke haɗa wasu na'urorin, sai Nurses ɗin da ta tsaya ta ɗaya gefen tana sa mishi drip tare da ɗaga kan gadon. Cikin karkarwa da yunƙurin da yafi duk sauran gami da rawan jiki ya ƙara matse tafinta hannunta cikin nasa da suka zama tamkar ƙanƙara murya a naɗe yace. “Zaid Zaitoon i... In ... Ina suke!?”. Ya dire mgnar da karfi. Idonta dake malalar da hawaye ta rumtse cikin subcewar kuka mai sassayan sauti ta fara girgiza mishi kai tare da fara murza tafin hannunsa cikin nata murya na rawa tace. "Kayi shiru ka daina magna numfashinka”. Kai ya fara jujjuya mata ido a birkice ya kuma fizgo mgnar cikin shaƙuwar yana mgnar cikin karyayyiyar murya yace. “Ina son ganinsu, kice musu Appiy yayi missing nasu ki rinƙa gaya musu ina sonsu”. Yadda muryasa tayi ƙasa ne yasa basa jin me yake faɗa sai ita kaɗai ke iyajunsa itama sai da ta sunkuyo kanshi sasai kunnenta na kusa da bakinsa. Sassayan kuka mai sarƙafe da kiɗima gigita gami da tashin hankali mai fidda nutsuwar mutum ta saki lokacin da taga duk jikinsa ya sake indonsa sun fara wani irin lumshewa murya can ƙasan maƙoshinsa yace. “Fariyyha zan mutu zan barki da maraicin su Zaid waye zai tayaki riƙe mana su. Please Farriyyha dan Allah karkiyi aure ki kaisu gidan wasu ki zauna a gidanmu har sai sun girmah”. Sai kuma kawai yaja wani dogon numfashi tare da sake hannunta.......