Sashe 11
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kyar ya samu ya dawo parlour kan 3 seatter ya kwanta bayan ya kunna room heater. saboda masifeffen sanyin da yakeji har cikin hanjinsa da ƙashi da bargon jikinsa wanda yasa ko idonsa baya iya buɗewa. Yah Saleh dake shigowa ne yayi saurin ƙarasowa ciki tare da cewa. “Yah Salam Mahmoud lfy kuwa? Meke damunka? Ina matar taka”. Ya ƙare maganar cikin kiɗimar ganin irin ƙarƙarwa da jikin Mahmoud ɗin yake da wani irin galabaitaccen yanayin ganin ba alamar zai iya magna ne yasashi saurin tallaɓeshi ya miƙar dashi tsaye yana mai kwalawa mai PA ɗin Mahmoud dake ƙasar kira. Arda! Arda! Da gudu Arda ya iso, key ɗin motarsa ya miƙawa Arda tare da cewa ya juyo motar. Suna shiga ba inda suka tsaya sai tamfatsetsen Asibitin. Acibadem Maslak Hospital. Ita kuwa Fariyda Chart take yi da Aunty Saddiqa. “Nifa ban san inda yake bama, Aunty Saddiqa tun ranar da mukazo da ya fita bai ƙara shigowa ba, kuma wai Umminsa tace bai da lfy Mamy ma na tambayata ya jikinsa jiya har Baba Malam kirana yayi wai ya jikinsa Abba yace mai baida lfy yana kiran wayarsa kuma bai ɗagaba”. Cikin kaɗuwa Saddiqa tace. “innalillahi ke Fariyda bashi da lfy kuma baki san inda yake ba, baki kuma faɗawa iyayensa ba, in har ke bakya bukatar rayuwarsa ai su kam suna buƙatar ɗansu, ta yaya ma ke da bakinkifa kikace tun ranar da kuka baro India kinga kamar baida lfy, Sannan ya fita bai dawoba ai sai kiyi gaggawar gayawa iyayensa, su san cewa bakwa tare da shi wuri ɗaya”. Da sauri tace. "To ai ranar da Ummi ta kirani suna Katsina nace mata baya nan ma ai”. Cikin sauri tace. “No Fariyda wannan ai ba hujja bace, ko ni da kike cemin baya nanma fa in muna waya ai a zatona kawai irin ya fita ɗin nanne to ya zasu gane? yanzu kin san halin da yake ciki gashi ana kiransa baya ɗaga waya kin san kuwa illar da sakacinki a kanshi zai iya jawowa wlh in wani mummunan abu ya samu Mahmoud nasan Ummi da Abba ba zasu taɓa yafe miki ba, ke su Zaid ma in sun girma bazasu yafe mikiba in sunji labarin sakaci da kikayi da rayuwar mutumin da ya meye musu gurbin uba ya hanasu kukan maraici ya hanasu amsa sunan agola da yin agolanci”. Numfashi mai sanyi ta fesar cikin jin tsoro ya ɗan ɗarsun mata a zuciya murya a sanyaye tace. "To Aunty Saddiqa ai ban san inda yake ba”. Cikin faɗa tace. "Me amfanin wayarki”. A hankali tace. "Ai bani da number sa”. Cikin al'ajabi tace. “Innalillahi Fariyda mijin nakine kike cewa baki da number sa”. Idonta na cikowa da kwalla murya na rawa tace. "Aunty Saddiqa nifa mijina ya rasu, number Yah Amin ko a bacci aka tasheni zan faɗeshi”. Cikin faɗa Saddiqa tace. “Kin shiga uku Fariyda wlh Allah bazai barki ba, wai duk wannan abun akan Aminullah da ya rigada ya bar doron duniya kikeyinsa, Wlh ko shi Aminullah da ace yana raye sai yayi fushi dake akan riƙon sakainar kashin da kikeyiwa ƙaninsa, har zaki cemin ba mijinki bane mijinki ya rasu to maza sa himma shima Mahmoud ɗin in ya mutu sai ki zubda ruwa ƙasa kisha, kiyi sabon takaba in kin fita ki auri Yah Mujahid ɗin da kike yawan kira. Bawan Allah ai ko dan yadda yake mutuwar son yaranki da yadda yake mutuwa akansu ya cancanci ki binciki ransa da lfyarsa”. Hawayen da suka fara silalo mata ta share a hankali tace. "To ta ina zan nemeshi ni da ban wani san garinba kuma ko na nuna zan taimaka mishi gwatsaleni yakeyi yayi ta hantara yace na addibi rayuwarsa in fita harkata fa yace min wai in daina kallonsa har mayyafa yake ce min”. A faɗace tace. "Ki dai ji tsoron Allah ai kince wayar Aminullah na hannunsa ba sai ki kirata ba, kuma wlh yanzu zan kira Mamy in gaya mata”. Da sauri tace. "To ai zan kira dan Allah karki gayawa Mami wlh yanzu zan kirashi karki gaya mata zatayi fushi dani”. Daga nan ta katse kiran. Ido ta zuba wa number Yah Amin da a ƙalla watanni goma zuwa sha ɗaya kenan rabanta da kira tun washe garin rasuwarsa. A hankali ta manna wayar a kunnenta, numfashi ta fesar jin har tayi ringing ta gama ba'a ɗagaba, kai ta jujjuya tana kuma kiransa a karo na uku shima ba'a ɗagaba kwallon daya cika mata ido ta zumbu da Yah Amin ne ringing ɗaya ma bazaiyi na biyu ba yake amsawa. Aunty Saddiqa ta kuma kira ta gaya mata baya amsawa. “Shike nan ai hankalinki ya kwanta, tunda Malam ma yace baya amsa kiransa kema kin kira baya amsawa sai ki shirya abinda zaki gayawa iyayensa na cin amanar da suka baki na ɗaya-ɗayan ɗansu da ya rage musu, wlh ko Amina yanzu na kirata tace min yanzu kam ma wayarsa bata shiga tace ta kiraki wayarki kina waya, nace mata dani muke waya.” A hankali ta miƙe tsaye tana kallon su Zaid dake wasa haɗe da kiran sunansa Appiy owo owo Appiy. Sai kuma ta koma ta zauna cikin sanyi ta katse kiran Aunty Saddiqa saboda kanta daya cushe so take ta nitsu ko zata samu mafita. Gashi duk masu kawo mata kaya da abincinma bata da ko numbersu iyakarta dasu gaisuwa sai su tambaye ta ko tana buƙatar wani abu. A hankali ta kalli wayar ganin kiran Amina ba tare da ta amsa sallamar Fariyda ba tace. “Fariyda wai ke ɗin a ina kike ne to?”. Cikin sanyin murya tace. “Homey Airport hotel inda mukayi transit har yanzu a nan nake”. Cikin tashin hankali tace. “To shi kuma Mahmoud ɗin fa inaga yana gidane matsalata wayarsafa bata shiga sai ta Yah Amin ita kuma baya ɗagawa kuma su Yah Saleh da matarsa basa Istanbul sun ɗanyi tafiya Ankara”. A hankali tace. “Nima ban san ina yake ba Aunty Amina ina ta kiran layin Yah Amin baya ɗagwa”. A hankali tace. “Tun ranar da yace min baida lfy na kira Yah Saleh dan in gaya masa ko zai faɗawa mai aikinsu ya shiga ya duba mana shi, dan number Arda da muke da ita ma bata shiga to kuma shima Yah Saleh yace tare suka tafi da mai aikin nasu kuma ya kira Arda ɗin baya shiga a ranar”. Cikin sauri ta miƙe tsaye tare da cewa. “To bari inje gidan in duba”. Amina tace. “Yauwa yi sauri dan Allah”. Shiru Abba yayi yana sauraron jawabin Yah Saleh dake gayawa Abba masa sun dawo daga Ankara ya shiga gidansu dan duba Mahmoud ɗin saboda kiransa da ake baya shiga dashi da Arda sai layin Aminullah kuma da ba'a ɗaga kiran shine ya dawo dashi daga inda ya tafi da iyalan nasa, sai kuma ya ɗaura. Da mishi bayanin mawuyacin halin da ya samu Mahmoud ɗin haɗi da cewa. “Abba kuma kunce da matarsa suke tare da ita kuke magna aji ya jikin nasa, to kuma ba kowafa a gidan shi kaɗaine ba kowa ban gantaba”. Cikin fargaba Abba yace. “Yanzu dai ya jikin nasa, ina Arda ɗin kuma”. Yana kallon ƙofar ɗakin da suka dashi yace. “Har yanzu basu fito da shiba, Arda kuma muna tare yacemin ai shike kula dashi, wayarsa kuma ta ɓacine shiyasa layin baya shiga kuma baya son fita ya kai gyara ya bar Mahmoud ɗin shi kaɗai lokacin da najema ya shiga toilet ne shiyasa na samu Mahmoud ɗin shi ka ɗai, yace bai san meyasa kuma wayar Mahmoud ɗin bata shigaba”. Cikin sanyi yace. “Ka tambayeshi yasan inda Fariyda take ne?”. Kai Arda ya gyaɗa masa bayan ya tambayeshi a hankali yace. “Abba yace a hotel take”. Cikin nazari Abba yake kallon Ummi dake jin duk abinda suke tattaunawa tace. “Ita Fariyda a hotel take yanzu Amina ke gaya min wai ai dama tuntuni da muke waya dasu basa tare”. Cikin gamsuwa Abba yace. “Saleh a duba inda Fariyda take da yaran, in sha Allah gobe zan taho in na samu dama”. Ya ƙare maganar cikin damuwa da yake dannewa a zuciyarsa, da sauri Yah Saleh yace. "In sha Allah Abba ba sai ka zoba, inaga abin ba wani mai tada hankalin bane.” nan yayi ta kwantar masa da hankali har saida yaji Abban ya ɗan samu natsuwa. Rungume su Zaid tayi kumayi da ƙarfi tare da rumtse idonta saboda sanyin weather ɗin da suka fito duk da cikin motane amman sanyi na ratsasu, wasu zazzafan hawaye ne taji suna ciko mata ido lokacin da Amina ke ce mata. “Fariyda Mahmoud baida lfy sosai, Yah Saleh yace suna Acibadem Maslak Hospital zan tura miki location ɗin Asbitin da room number da aka medasu, kiyi sauri kije can kada kije gida baya can”. Seat din Driver ta ɗan taɓa ta faɗa mishi sunan Asbitin, hakan ne yasa ya karya kwana ya sauya hanyar tafiyar tasu. ƙara rungume Zaid da yafi ƙarƙarwa tayi duk da Sweater and Scarf Socks gloves dake libge a jikinsu. A hankali hawayenta da suka cika mata ido suka sauƙe dan yadda suke haɗa baki wurin kiran Appiy! Appiy!! A haka suka isa Asibitin. A gajiye take ɗaga kafarta sabida nauyin su Zaid dake hannunta na dama Zaitoon a na hagu. Tafiya takeyi tana ɗan duba rooms number ɗin. Numfashi mai sanyi ta fesar tare da shan wata kwanar. Da sauri ta nufi ƙofar inda ta hangi Yah Saleh ya fita da sauri. tana isa bakin ƙofar Sajida ƙanwar Yah Saleh yar Aunty Firdausi da Maryam matar Yah Saleh da ƙanwarta Amira suka iso, cikin sauri Sajida ta nufi Fariyda tare da miƙa hannunta ta amshi su Zaid duka biyu tana rungumesu da faɗin “Aunty Fariyda kin iso”. Kai Fariyda ta gyaɗa mata da sauri tabi bayan Aunty Maryam da ta kalleta a yatsine ta wuce ciki Amira na biye da ita tana yiwa Fariyda wani irin kallo kishi. Da sauri duk suka kutsa kai ciki. Arda na tallaɓe dashi kan gadon asibiti wani irin gigitaccen kakarin amai mai dukan ƙirji yake yi wanda yake haɗe da shaƙuwa mai ƙarfi, sai ƙarƙarwa da jikinsa keyi tamkar mazari yunƙuri yake yi tamkar zai harar da hanjin cikinsa. Cikin sauri Sajida