Sashe 64
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kika kuskura kika ƙara sata kuka wlh sai nasa kin zubda wahaye jini banza mayya kin addabar bata miji da kallo da naci duk bata kulaki ba sabida ita ba mate ɗinki bane shine zaki mata rashin kunya dan tazo gidanku. Wlh Mama kanta tsoronsa takeji dan sit tayi ta koma gefe sai ƙirƙif ta ido takeyi lokacin da ya juyo kanta yana kallonta ido cikin ido yace. “Mama ki gaya mata matata ba mate ɗinta bace, ko kallon banza ta ƙara yi mata zan tsole idonta, karta kuskura ta ƙara yi mata rashin kunya dan zan iya komai akan farin cikin matata”. ƙawar Jidda kuwa sai murmushi jin dadi takeyi dan dama bataji daɗin abinda suka yiwa Fariyda ba, ni kam farin ciki yasa banma san sanda nayi dariya ba. Yah Salim kuwa Appiyn Zaid na fita shima ya kwaɗa mata mari, da yake shi an rainashi Mama ta fara masifa harda cewa in ya kuma taɓa mata yarta zata ja masa Allah isa hegiyar tsohuwa so take ta mishi baki akan jakar yarta ta cuceni tasa mijina ya susuce”. Dariya sukayi baki ɗayansu banda Fariyda dake cewa. "Sabida ɗan uwansa yayi ba danniba in banda munahinci shi ɗin sau nawa yana sani kuka, ya targaɗani ya ƙara kamar ya samu ƙashin ƙaza, ko kwana kuka nakeyi ba kulani yakeba kai ko kallo ma ban ishesa ba, lokacin da ya targaɗemin hannu a India kukan jinine kaɗai banyi amman ko a jikinsa da yake ya ƙware a mugunta sahu-sahu ya iya saifa da Ummi tace zata jamai Allah ya isa kafin ya gyara min hannu a haka zaki wani ce yana sona, wlh Salma kin cuceni Allah ya isa da kikace wai nima ina sonshi ai wlh ko mafarkin ina sonshi kikayi ya kamata kiyi sadaka”. Numfashi mai nauyi Adda Nana ta fesar tana kallon Zainab da Humarai da Raihana da mamy ta kirasu su zo su shiga kitchen su ɗaura lunch, har saida suka bar bar wurin Adda na tace. "Tabbas Mahmoud yana sonki kece dai baki kula dashi a matsayin mijiba”. Aunty Rashida tace. “To tunda kikaji tace ba iddarsa a kanta ai kin san ta dakon zunubin tauye haƙin bawan Allah ai dole ya miki ko wacce iriyar muguntama shi ba muguntar kike masaba”. Shiru tayi tana kallonsu cikin jin tsanar yadda suke wani karesa da yabonsa. Sai kuma suka kalli Aunty Saddiqa dake cewa. "Ai Fariyda a dai wannan halin naki na ƙin maza wlh Yah Muhajid ɗin ma zaman sai a hankali dan in banda Yah Amin bawan Allah mai haƙuri wa zai iya juriyar ganin tsaleliyar mace kamarki a kusa dashi, ba tare da ya samu hutawa da itaba a duk sanda yake soba”. Sai kuma ta ɗanyi ƙasa da murya yadda su Raihana dake kitchen bazasu jiba tana kallon Aunty Sadiya tace. “Kin tuna lokacin da akayi aurenta da Yah Amin duk haƙurinsa saida ya kawo ƙararta wurin Yah Nasir sun kusan kwana arba'in bata bari ya kasance tare da ita ba daya fara zata fara kuka da magiya shi kuma mai tausayi ya barta in ya tsananta ta sume mishi.” a hankali Aunty Sadiya tace. "Ai lamarin Fariyda sai ita to mutumin da har bayan ta haihu yake gayawa Yah Nasir zai irga sau nawa suka kasance kafin tayi ciki, tana ciki da asbiti suka bata betres shike nan ta samu ma faka, data haihu kuma tace CS ne ai sai bayan wata shida haka yayi ta fama da ita”. Tana yin ƙasa da kanta tace. “To ai bazaku gane bane nifa kullum fa kamar ranar ne farko zafi, kuma shi Yah Amin yana tausayi wlh wani lokacin na shi ke cemin ya haƙura ba komai ya yafe min ai yasan ba da gangan bane, ni kuma a haka ina daurewa dan farin cikinsa tunda shi yana so kawai dan ganin yadda yake farin ciki da samin al'barka ne yasa nake daurewa dan ina ɗan jin zafi kam daga farko, shiyasa gsky bana son takura a addabi rayuwar mutum da abu a hanaka bacci a saka jiƙa kai ga fama da ruwan ɗumi duk ranar da akayi”. Da sauri Salma tace. "Ikon Allah naga kuma harda ciwon marar rashin miji kikayi a India”. Cikin mmki da takaici ta zaro ido tare da cewa. “Innalillahi kai Salma Allah ya isa tsakanina dake wai ciwon marar rashin miji, amman ke dai anyi mara kunya, kenan ba dama inyi ciwon mara sai kice na rashin mijine, ni yaushema nasa na miji a raina da har zanyi ciwon mara amman wlh tallahi kin cuceni na ramtse da Allah ba zan yafe mikiba”. Ta ƙare maganar da iyakar gaskyarta da ƙoƙolwarta baƙin ciki, tunda Ita dai tasan bata wani jin begen namiji a rayuwarta”. Aunty Rashida ne ta ɗan dafa kafaɗarta ganin idonta na cika da hawaye a hankali tace. "Farriyyhan Mahmoud ai ba wai sai jarababbiyar mace ko mai jin buƙatar kasancewa da namiji ne kaɗai ke ciwon marar rashin namiji ba. No duk mace ko na miji in dai lafiyayyune akwai lokacin da zasu iya jin wannan ciwon marar ko ya ɗau lokaci, musamman in akwai jin dadin rayuwa ci da sha mai kyau da tufafi da ni'imar wurin zama da yawan shan fruits kan iya sa jikinki ya buƙaci na miji koda a zuciyar da ƙwaƙwalwarki bakiji sha'awar ba kaha zai sa ke bazaki san cewa sha'awa bace silar ciwon”. Hawayen takaicin na zuba ta kaiwa Salma dake dariya duka tana faɗin. “Ni dai wlh kawai ciwone to baima taɓa yi min ba sai ranar kuma har yau bai sake min bafa”. Cikin dariya Salma tace. "Wanne maganin kika sha ya bari”. Ba tare da fahimtar manufar tambayar ba tace. "Lemon tea kawai Appiyn Zaid ya bani ina sha ya bari”. Dariya Aunty Sadiya tayi tana kishingiɗa tace. “Sammakal inji babarbare shima har ya ganoki”. Dai-dai lokacin Sadiq ya shigo da saƙon Aunty Saddiqa, nan suka fara warware ɗinkunansu data turawa idris telan a Yola, ɗinki na Fariyda kala 8 Ameera 4 Aunty Saddiqa 5 sai na Zainab da Humarai uku uku, sai kuma na Mamy da Aunty Amarya biyar biyar suma, sai Aunty Sadiya nata huɗu, sosai ɗinku nan sukayi kyau dan sun samu aiki na musamman haka yasa Aunty Rashida ma amsar numbersa, Washe da safe, juyi yake tayi kan gadonsa a hankali ya kife kansa kan pillow yana mai jin tamkar yasa kuka haka nan gidan baya masa daɗi pillow ya jawo ya rungume da ƙarfi, sai kuma ya zare pillow ya ture gefe, idonsa ya rumtse jin kiran na shigowa wayarsa da ya kirata sau biyu bata ɗagaba, Sa'ad ne, a fili yace. "Kai maye ko zaka sha mamaki abinda maitar zai jazamaka”. Kai ya jinjina yana mai tsaida hukuncin da ya yankewa kansa akan su Sa'ad da Faisal, makirin murmushi yayi a hankali yace. "Uhmmmm”. Sai kuma ya ajiye wayar Yah Amin ya jawo wayarsa.....