← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 95

Sashe 49

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

"Mu ma yanzu muka iso da Salma tana ciki tare dasu Jidda da ƙawarta.
Murmurshi ta ɗanyi tare da rusunar da kai ta gaida Bappa Lawan cikin kulawa ya amsa ya daura da cewa.
“Allah yayi muku al'barka ya raya muku yaranku”. Amin tace tana ɗan kallon Mama tace.
“Mama ina kwana”. Shiru tayi kamar bata jitaba, haka yasa ta ɗan ƙara sautin murya tace.
“Mama barka da safiya”. Shirun da tayi ne sai ma meda kallonta da tayi kam Salim tana masa magna yasa Bappa Lawan cewa.
“Kina ta surutu ko gaisuwar bakya ji”. Shi kuwa Mahmoud kamar baya parlour sai wayarsa yake ɗan lallatsawa
“Ina kwana Mama ya jiki?”. Ta kuma faɗa ba tare da ta kalli Maman ba A daƙile tace.
"Ni lfyta lau”. Ido Salim ya zuba mata hakama Bappa Lawan ɗin.
A hankali tace.
"Allah ya ƙara lfy da nisan kwana”. Tana miƙewa tsaye tace.
"In sha Allah kuwa”. Daga nan tayi ciki, fitarta da kamar 10 minute ne Salim ya kalli yadda take zaune a takure yace.
"Fariyda isa ciki Salma na can”. Tana ɗan rusunar da kanta tace.
"To Bappa a huta lfy”. Cike da Dattaku yace.
"To Ngd Allah ya baku ladan ziyara, zamu wuni ai ko?”. Gefen da Mahmoud ɗin yake ta kalla a fakaice tare da cewa.
"Eh da yake zanje gida in gaida malam shiyasa da zamu wuni”. Bappa Lawan yace. “Ato ku gaida min shi in kunje, kwana biyu bamu haɗuba tun bayan auren Salim da mukaje godiya, kice ina gaidashi”. Tana miƙewa tsaye tace in sha Allah.
Ƙofar da Mama tabi Salim ya nuna mata, a hankali ta shiga parlour tare da sallama a bakinta.
Murmurshi jin dadi Salma tayi ta miƙe tsaye ta rungumata cikin shaƙuwarsu da ƙarfin jinin yan uwan taka tace.
“Muna zuwa ne kuwa Babe yace sai mun koma da dare zai kaini muyi hira wai ki koya min girkin da kikayi musu jiya, nace ai ta kwana gidan sauƙi tunda kece malamar”. Murmurshi tayi sai kuma suka saki juna duk suka kalli Jidda da ta ja wani wawan tsaki.
Mama dake gefe ta kauda kai ta daura ɗaya kan ɗaya.
Salma taja hannunta tana faɗin.
“Bismillah zauna mana”. Ta sunkuyo da niyar zama, sai kuma ta miƙe a hankali ta juyo kan Jidda dake cewa.
“Ke kul bororoji karki zauna mana kan sofa!”. Cikin tsananin mamaki Salma da ƙawar Jidda suka zuba mata ido Salma ne tace.
“Meyasa zakice karta zauna?”. Cike da izza da izaya tace.
“Kin san kowa da tsarinsa, wasu in anje gidajensu bedroom nasu ne suke hana shiga duk da ba gidan ubansu bane, to Ni kuma nan da yake gidan ubanane tsari nane kaska ko ince mayu masu aure Yaya su lashe jininsa su kashe su kuma dawo kan ƙani a kalallame mai rayuwa, basa zama mana a gidanmu, dan mu dai kurwarmu ɗaci gareta Yah Mahmoud ɗin ma in sha Allah na gani nan bari yafi karfin tsoffin Mayu ma bare sabbin mayu Yah Amin ɗin da da aka cinye mana ma Allah ya isa kuma dagashi ba ƙari”. Tunda ta fara magnar duk suka bushe a tsaye, ita kuwa Mama sai kai take jinjinawa.
Salma kuwa cikin kaɗuwa da fara fusata ta tsuƙe fuska tare da cewa.
"Wannan wacce iriyar mgnar banza ce Jidda”. Da sauri Mama tace.
"Yi shiru Salma ba dake takeyi ba, ke dai ki zuba ido kawai, ai gaskyarta shi maye bafa amana ne da shiba”. Tuni idon Fariyda ya ciko da hawaye, yayinda Salma kuwa tuni sun zubo mata ma, cikin sanyi da ɗan girmamawa tace. "Mama ai in anyi da Fariyda to tabbas anyi da ubanda da ya haifeni ma bare kuma ni, sannan kalmar mayu dai kam bazan iya lamuntar fahimtar ta bama, saboda mu zuriyarmu a tsarkake take. Mama kiji fa abubuwan da Jidda ke faɗa”. A kufule tace.
"To ƙarya ne? Duk abinda ta faɗa ai haka ne, ba cinye Aminullah ɗin akayi ba yaro lfyarsa lau ya fita aka haɗashi da ƙarfe yayi Acsident sai gawa, da yake Mamansu ba mai bin diddigibane ta yarda aka sake aurawa ɗan ɗaya ɗayanta aure da ita”.
Da sauri Ƙawar Jidda ta fara girgiza kai tana kallon Fariyda da shock ya hanata iya cewa komai sai idonta da ya fara dilalo da hawaye.
“Mama bai kamata kice haka ba, baƙonka kafa annabinka ne”. Tayi mgnar tana matso kusa da Fariyna ta ɗaura da cewa. "Baiwar Allah zauna”. Cikin izaya Mama tace. "A ina ɗin wlh karki kuskura ki zauna min parlour, ki tarkata maitar jarabarki duk kinbi kin lashewa mutane zuciya duk wanda ya ganki sai yace yana sonki, bayan kyan ɗan macijine, wlh in sha Allah Mahmoud kam yafi ƙarfinki”. A hankali ta juya ta nufi hanyar fita zuwa can waje.
Ƙawar Jidda ta kamo hannun Jidda tana cewa.
“Ƙawata gskya baki kyautaba”. Salma kuwa da sauri ta juya tabi bayan Fariyda.
Jingine ta sameta jikin motar Mahmoud ɗin ta kifa kanta a jiki.
Dai-dai lokacin Mahmoud ɗin ya fito tare da su Zaid sai kuma Salim da ya fito ta parlour Mama Yana cewa. "Ashe ma gata har ta fito”. Salma ne ta kalli Mahmoud ɗin da ya buɗe baya yasa su Zaid yana zagayawa tace.
"Appiyn Zaid ina yini”. Fuska ba yabo ba fallasa yace.
"Alhamdulillah”.
Salim ne ya buɗe front seat yace.
“Bismilla Madam kin san oganki baya jira sai dai a jirasa”.
A hankali ta shiga motar dan ta ƙosa da ta samu ta bar gidan taje gidansu.
Salma ne ta ɗan matso baya Salim ya rufe ƙofar, Ƙasa tayi da murya tare da cewa Fariyda. “Kiyi haƙuri in na dawo zanzo kuma wlh anyi da yan halas”. Da sauri Fariyda ta fara jujjya mata kai tare da cewa. "A'a Salma”. Sai kuma kawai kukan da take dannewa ya kwabce mata.
Da sauri Salim yace.
"Yah Salam Salma Meya faru me kika raɗa mata kika sata kuka”. Kai ta fara jujjuyawa cikin jin itama kukan zai zo mata to ta ina zata fara faɗin tijarar da kanwarsa da uwarsa suka yiwa yar uwarta, haka yasa kawai ta juya tayi cikin gida.
Shi kuwa Mahmoud ganin Salim na shirin matsowane yasashi daga glass ɗin motar duka, ya kunna motar tare da sakin AC.
Kukan takeyi mai nannauyan sheshheƙan kuka, bai ja motar suka tafiba bai kuma ce mata komai ba, Salim kuwa ganin haka ne yasa yayi saurin bin bayan Salma tunda Mahmoud ya ɗaga glass bashi da damar yin mgna da su.
Kusan 6 minute bai tafi bai kashe motar bai ce komai ba, ita kuwa har yanzu kuka take yi cikin sauti mai tafe da rauni.
Numfashi ya fesar yana ɗan juyowo kanta yace.
“Baki da lfy ne?” shiru ba magna sai kuka.
“Mararki ne ke ciwo”. A hankali ta jujjuya kai alamun a'a. “To me ya sameki”. Ya tambaya yana kafeta da idonsa da suka yi jazir.
Cikin Muryar kuka tace.
“Ayyah Appiy dan Allah ka kaini gidanmu ina son ganin Mamy na”. Fuska a haɗe yace.
“Ke meya saki kuka nake son ji”. Kai ta kife kan guiwowinta taci gaba da kuka, sai kuma ta ɗago kanta jin ya buɗe motar ya fita. Parlour Mama ya shiga, Salma ya samu zaune ita da Salim da mmki Salim ke kallonsa jin yana cewa Salma.
“Mrs Salim zo”. Da sauri ta miƙe dan a zatonta Fariyda ke kiranta,
Bakin ƙofar parlour ya tsaya tana ta ciki yana ta waje. Kai tsaye yace.
“Me ya sameta take kuka? Me akayi mata?”. Cikin jin zafin abin da itama take jin tamkar ita akayiwa ta bashi labari.
Salim dake bayanta wanda tunda suka shiga yake tambayarta taki ta gaya mishi ne sai yanzu da take gayawa Mahmoud ɗin duk yadda sukayi yaji.
Shi kuwa Mahmoud juyawa yayi ya koma cikin motarsa.
Ita kuwa Salma kuwa ɗakin Jidda inda hand bag dinta yake ta nufa, zaune ta sameta ita da ƙawarta na ce mata bata kyauta ba.
Bathroom ta wuce ba tare da tace musu komai.
Tunda ya shigo baice komai ba sai kallonta yake yi yana mai kaɗa ƙafarsa har lau yana taune da lip ɗinshi, sai kuma can taji ya sake buɗe marfin motar ya fita, a parlour ya wuce Salim da Mama kai tsaye ɗakin Jidda ya wuce.
Bayan kamar 7 minute da shigansa cikin gidan ta kuma jin ya dawo ya buɗe ƙofar motar ya shiga ya zauna jin bai ja motar bane yasa ta ɗago kanta ta kalleshi, shima ɗin ita yake kallo idonta na silalo da wasu hawayen tace.
“Ayyah dan Allah Appiy ka kaini gidanmu”. Har lau idonsa na kanta murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Farriyyhah kina kukan ne zan kaiki wurin Baba Malam”. Da sauri ta fara share hawayenta da tana share wasu wasu ke biyo bayansu, numfashi mai nauyi ya fesar tare da miƙar da hannunsa hankali ya ɗaurashi kan fuskarsa babbar yatsarsa yasa kan kuncinta ya fara goge mata hawayen har lau idonshi na cikin mata dake zubda siraran ƙollan, kai yake ɗan jujjuya mata haɗe da cewa.
“In kina son zuwa wurin Baba Malam to ki daina kukan haka”. A hankali ta fara gyaɗa mishi kai tana ƙoƙarin tsaida hawayenta tace.
"Appiy na bari”. A hankali ya janye hannunsa murya a sanyaye yace.
"In kin sake cemin Appiy bazan kaiki ba”. tana kallon yadda ya zuba mata mayatattun idonsa tace. "Na bari”. Kai ya gyaɗa tare da jan motar yana faɗin. "To da me zaki ni”. Cikin sanyin murya tace.
“Muody”. Yadda ta fitar da harafin ne yasa murmushi subce mishi, itama ɗan murmushi tayi tace. “Shi yayi ko”. Baki ta ɗan taɓe yana jujjuya kai alamun a'a. Sai kuma ya maida hankalinshi kan tuƙin da yake ba tare da ya kuma ce mata komai ba, itama Fariyda shiru tayi a haka suka isa gidansu.
Parlour Mamy Sadiq yayi masa iso dan Baba Malam ya fita.
A tare suka shiga yana rungume dasu Zaid da suka fara gengeɗi.
Aunty Saddiqa da Raihana da Zainab da Aunty suka samu a parlour Mami suna ta hira.
Aunty Saddiqa ne tace.
“A'a Barka da zuwa yau manyan baƙi garemu kenan, Mahmoud Bismillah iso ga wurin zama”. Tayi mgnar tana nuna masa sofa.
Zainab da Raihana kuma rungume Fariyda sukayi.
Aunty Amarya ta miƙe tana gyara mayafinta ta nufi bedroom ɗin Mamy dan kiranta.
Jim kaɗan da shigarta suka fito a tare.
Cikin girmamawa ya gaidasu, Mamy na miƙawa Zaid hannu tace.
"Yanzu kam ya bar rikici ko”. Yana miƙa mata Zaid yace. "Alhamdulillah yanzu kam bayayi”. Aunty Amarya ta amshi Zaitoon.
Su Fariyda kuwa a kan carpert suka zauna dasu Raihana dake gaisheshi.
Sallamar Yah Mujahid ne yasasu kallon ƙofar parlour.
Murmurshi mai cike da jin daɗi yayi kai tsaye ya wuce kusa da Fariyda kujerar dake bayanta ya zauna ya zama tana gabanshi, sunkuyowa yayi kamar zai faɗo kanta yace.
“Haba shiyasa tun bakin gate nake jiyo gidan yana ƙamshi ashe flower tace ta iso gidan.
Kauda kanshi yayi daga ta inda suke ya maida kanshi kan Dr Nasir da ya shigo yana miƙa masa hannu ya zauna kujerar dake kusa dashi yana faɗin.
"Ya jiki dai”. Murya a cushe yace. “Alhamdulillah”. Shi kuwa Mujahid miƙewa yayi yana leƙa fuskarta ya ɗan kamo gefen Veil ɗin ta ya kai hancinsa yana faɗin. “Kai turarenkin nan duniya ne ƙamshi kaɗai ya wadatar wurin samar da farin ciki”.
Tsuƙe fuska Mami tayi tare da cewa.
“A'a Mujahid ai ka gaisa da mijinta tukun ko”.
Aunty Amarya tace.
“Da dai yafi kam”.
Aunty Saddiqa kuwa Mahmoud ɗin take kallo ta gefen idonta.
Shi kuwa Mujahid yana cewa. "Ai turaren natane ƙamshinsa daɗi garesa”. Ya ƙare maganar yana
miƙawa Dr Nasir dake hararansa hannu suka gaisa ba tare da ya lura da hararan da yake masa ba.
sai kuma ya miƙawa Mahmoud ɗin hannu tare da cewa.
“Ya kake”. Tamkar bai jishi ba haka yayi sai kanshi da ya sunkuyar yana danna wayarsa.
Hannu ya ƙara miƙa masa tare da cewa.
“Hello”. Miƙewa tsaye yayi cikin muryar da tasa Fariyda kallonshi yace.
“To Mami mun gaisheku, in Malam ya dawo a gaidashi”. Ya ƙare maganar yana yiwa Mujahid wani irin azabebben kallon sai kuma ya zaro kuɗi naɗi uku yan dubu ɗaɗɗaya ya ajiye gaban Mami.
Kana ya juya ya nufi hanyar fita yana cewa.
"Ke taso mu tafi”.
Mami ne da Aunty Amarya suka haɗa bakin cewa.
“Mun gode matuƙa ka gaida su Ummi.” sai kuma Mami ta kalli Fariyda tace. “ke Fariyda tashi ku tafi ɗauki yaranki”. Cikin kwaɓe fuska tace.
"Mami wuni zanyi fa”. Fuska Mami ta haɗa ta nuna mata hanya tace. “Cewa yayi ki taso mu tafi dan haka bana son nunkufurci miƙe maza ku tafi”. Tayi mgnar cikin bada umarni da haɗe fuskar da yasa Fariyda miƙewa tana faɗin. “Mami ko gaisawa da Malam fa banyiba, kuma lefen Raihana ma ban gani ba”.
Dr Nasir dake kallon Mujahid cike da takaicine yace.
"Ke tashi ku tafi miƙe bana son gardama”. Cikin ƙolulun baƙin ciki ta miƙe tsaye tare da juyawa ta fita ido cike da hawaye.
Raihana da Zainab suka bita dasu Zaid.
A cikin motar kuwa wayar Yah Amin dake aljihunsa yana ta Vibrating ya zaro yana mai buɗe idonsa daya lumshe ganin kiran Faisal ne yasa shi sakin azabebben fusataccen haɗi da damƙe......
Chapter 49 · 0% Book details