Sashe 44
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
a tsakiyar ɗakin tana ta wasa, wayarta dake kan bide Side drawer ta fara ringing haka yaja hankali Zaitoon da sauri ta jawo wayar tana Balankwace da dariya, miƙa mata hannu tayi tace. "To kawo”. Kafaɗa ta maƙe tare da juyawa ta nufi ƙofar fita, tana gyara zaman wuyan rigarta tace. “A'a to ina zaki kai min waya kawo min nan”. Sai kuma ta miƙe ganin ta ja ƙofar ta buɗe ta fita, da sauri ta juyo ganin Fariyda na biyota yasa ta juya ta nufi cikin parlour tana ɗan gudu da dariya, fuska ta ɗan tsuke jin kiran ya tsinke tace. "Ke wai ina zakije ne, bani wayata ana kira kina gudu”. Jin kiran ya kuma shigowa wane yasata sauri bin bayanta, ita kuwa Zaitoon hango Mahmoud dake zaune kan 2 seatter ne yasa ta saurin nufarsa da gudu tana dariya. Dariyarta da ringing ɗin wayar ne ya jawo hankalinsa dake kan kallon wani Korean films mai masifar kyau. Hannunshi ya ware mata ai kuwa a guje ta abka jikinsa meda hannun yayi ya rungume taya yana mai kallon Fariyda da turarenta ya rigata isowa gabanshi, daga kan ƙafarta yake kallonta har zuwa kan hips ɗinta ya tsaida idonsa in second ya janye idon zuwa sama kan ƙirjinta da suke tsaye cur ziraran miraran, a hankali yayi ƙasa da idonsa. Hannu ta miƙa mishi jin kira na uku ya kuma shiga wayar ya zaro daga hannun Zaitoon sunan Yah Mujahid dake yawo a saman screen ɗin wayar ne yasashi yin mata wani irin kallon mai wuyar fassarawa, sai kuma ya zura wayar cikin aljihunsa, ya miƙe yana mata kallon da yasata fara ja da baya. Kanshi ya ɗauke daga kanta ya juya ya nufi ɗakinsa ba tare da ya kashe TV. "To ni ka bani wayata”. Ko ƙala bai ce mataba Hannun Zaitoon da ya sauƙe kafin ya tafi ta komo suka koma ciki tana jan kumatunta. Washe gari da safe zaune suke a parlour Ummi, Samira dake yiwa Goggo Dada kitso ta kalla tare da cewa. "In sha Allah zanyiwa Baba idi magna kan batun ci gaba da karatunki”. Ummi da ta shigo yanzu tana zama tace. "Wlh kuwa da kin kyauta nasan in sha Allah zai yarda”. Maman Samira dake haɗawa Fariyda damun nono tace. “Da wuya kam dan ko jiya naji yana cewa sati mai zuwa zai tafi garinmu su tsaida mgnar aurenta da ɗan yayansa”. Da sauri Fariyda tace. "Yah Salam gskya in anyi mata aure a ƙauyen can ba'a kyauta mata ba, bari yanzuma zanje in sameshi”. Har ta yunƙura sai kuma ta koma ta zauna tana kallon Ummi a hankali tace. "Ummi nima ina son yin bautan ƙasa, dama Yah Amin yace in na yaye su Zaid zanyi, tunda lokacin da na ƙarasa karatun suna jariarai”. Kai Ummi ta ɗan jinjina sai kuma ta kalli Goggo Dada dake cewa. "Amman Malam zai yarda kuwa kiyi bautar ƙasa Fariyda da aurenki”. Da sauri tace. "Ai dama yace in dai Yah Amin yaji ya gani ya yarda shi ba ruwansa”. Ummi na kallon Mahmoud da ya shigo cikin shirin fita tace. “To ai da sauƙi ga mijinki in ya barki mu, me zamu ce tunda an yaye yaran ai da sauƙi ai ance mai wuyar sati ukune ko kwana arba'in ko ohon muku”. Kan Zaid dake hannun Ummi ya shafa yana kallon Goggo Dada dake cewa. "Tun ɗazu kai Sulaiman ke jira, wai zakuje katsina ko”. Yana shafa kan Zaitoon data riƙo hannunsa yace. "In sha Allah, yanzu zamu tafi”. A tare Ummi da Goggo Dada sukace. "To Allah ya kaiku lfy ku gaida min Dadana dasu Yaya”. Shigowar Sulaiman da Hafiz ne yasa shi juyawa yana cewa. “Amin ya Allah”. Sai kuma ya kamo hannun Huzaifa da ya iso gabanshi, hannunsa ɗaya kuma kan tumbin Huzaifa ya ɗaura yana shafawa yace. "Huxy ya kamar baka raguwane kam”. Dariya su Ummi sukayi, shi kuwa Huzaifa da sauri yace. "Allah na ragu fa”. Ya ƙare mgnar yana tamke cikinsa. Hafiz na zama gefen Fariyda yace. “Ka ƙaru dai yaro shi kaɗai yake cinye kaza kamar maye ko gajiya haƙoransa basayi”. Hararan Hafiz yayi yana faɗin. "Ai kaza bata sa jiki”. Dariya sukayi sai kuma Sulaiman da ya kalli Fariyda dake ce masa Uncle Sulai Allah ya kiyaye hanya a gaida su Dada ta bamu nono”. Cikin mutuntaka yace. “Amin ya Allah in sha Allah kuwa harda ƙon zabbi ma ai zamu samo”. Salim da ya shigo Salma na bayansa ne yace. "Dan Allah ku fito mu tafi rana tayi fa”. Daga nan suka juya suka tafi, suna fita Fariyda taja hannun Salma suka haura sama. Hafiz kuwa makaranta ya wuce. Huzaifa ne ya shiga kitchen dashi da Samira da Mamanta yana cewa. "Ayya Aunty Samira ɗan gasa min nama mana zan tayaki aiki”. Dariya Maman Samira tayi haɗe da cewa. "Aifa Huzaifa bazaka ragu ba”. A can parlour kuwa numfashi mai sanyi Ummi ta fesar tana kallon Goggo Dada tace. "Tunda fa yaran nan suka dawo ko sau ɗaya banga inda suka yiwa juna magna ba, ko kallon juna basayi, nifa na gama karaya auren nan ya fita kaina, ana cutar da yarinyar nan, Wlh ni na gamsu Mahmoud bai warkeba dan wlh in dai lafiyarsa ƙalan dole zai buƙaci aure in ma ita Fariyda bai sotaba”. Cikin sauƙe dogon numfashi Goggo Dada tace. “Bare ma babu wani ɗa namiji mai lafiya da zai zauna da mace kamar Fariyda ace bai bukatu da itaba, tabbas Mahmoud baiyi lfy ba ni kaina na gamsu da batun raba auren nan”. Cikin gamsuwa da hakan Ummi tace.