← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 95

Sashe 84

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tana isa wurin motar Sulaiman ɗin, gaba Sulaiman ya buɗe mata ta shiga ya maida marfin ya rufe Aunty Rashida da Saddiqa kuwa suna baya sai dariya sukeyi suna kallon Fariyda data kwaɓe fuska ta tura baki.
Shi kuwa Mahmoud yana tsaye gefen ta.
Hannu Bashir ya bashi suka gaisa cikin girmamawa yace.
“Mun gode da ɗawainiya fa Daddyn twins mun saka tafiya baka hutaba motarka bata hutaba sannan komai ka biya kuɗinshi harda na waɗanda suka tsaya a wancan Restaurant din Ngd big broz Allah ya ƙara buɗi da kariya”. Cikin kamala yace.
"No ba komai ai yiwa kaine”. Daga nan duk suka shiga motocin, har sun fara tafiya yayi saurin tsaida Sulaiman haka yasa motarsu Raihana da nasu Aunty Sadiya tsayuwa, a hankali ya fito baya ya buɗe ya ɗauko Zaitoon da Zaid.
Front seat inda Salma take ya buɗe fuska a tsare ya miƙa mata Zaitoon yana faɗin.
"Kuje wurin Aunty ko, MRS Salim ku riƙesu wurinku Mom ɗinsu ba lfy, mura bazata iya kula da suba, ni kuma zan yi driving”. Da sauri ta amshi Zaitoon ta miƙawa Aunty Rashida ita kuma ta amshi Zaid Sulaiman yace.
"Hmmmmmm”. Hararansa yayi kana ya juya ya shiga motarsa.
Dariya Aunty Aisha tayi lokacin da Salma ta amsa call ɗinta tace.
"Hmmmm kuma ɗin an juyeku a wata motar ko, mutum na son keɓewa da matarsa kun takurashi gashi ai ya nemo muku driver shima naga sai wani kallon Humaira yake kamar zai manna idonsa a kanta”. Dariya tayi tace.
"Ke dai Allah ya kaimu lfy akwai labarai”.
A babban pharmacy ɗin A.A. Aliyu yayi parking tana kallon duk sauran motocin suka wuce.
Jim kaɗan da shigansa ya fito riƙe da ledan maganin da Yah Nasir ya turo masa a rubuce ya saya mata.
Yana shiga suka tafi, tafiya kaɗan suka tsaya a gaban wani babban shago.
Drinks ya saya sai kuma Admiral mai ɗan karen sanyi roll ɗaya da mara sanyi roll ɗaya, sai kuma botle water shima roll ɗaya sai tarkacen su chocolate da cookies, da dai sauransu, ko inda yake bata kallaba sai duƙunƙunewa tayi wuri ɗaya dan har yanzu bai kashe Ac jarabar nan ba, a babban tukubar Al'KASIM ya tsaya gasashshiyar zabuwa aka naɗe masa kana ya tsaya gefen masu fruit suma ya saya duk ya jibgesu a seat ɗin baya.
Ya shiga motar ya ja a saba'in ɗan gudun AC ya rage ya bar kaɗan.
Cikin 26 minutes sai gashi duk ya wuce motocin su Har da tasu Ango da amarya da Sulaiman sune dai biye dashi a baya.
Admiral ya zaro mara sanyi ya buɗe mata dai-dai lokacin da suka shigo cikin Kumo miƙa mata yayi, kai ta jujjuyawa alamun a'a fuska ya tsuke yace.
“karɓi kishanye ko kuma yanzu in saki yi suck Da sauri ta amshi gorar, kai ya ɗan jinjina haɗi da ci gaba da driving yana ɗan kallonga, gyara zamanta tayi ta fara ɗan sha, haɗe da tura ɗan baki, ido ta ɗan lumshe dan ba ƙaramin daɗi Admiral ɗin yayi mataba.
Tuƙin yaci gaba dayi yana ɗan lallonta Time to Time, tana ɗan Sipping Admiral ɗin, lokacin da suka iso Kaltingo ne ya juyo ya kalleta da kyau idonshi na kanta yace.
"Komai zakici sai kinyi wasa, ba abinda kike bawa mahincin ki yima irin cin da zaki samu gamsuwa, kiyi ki shanye kisha mganinki”. A hankali tace. "Nifa na warke ba sai nasha komai ba”. Ta ƙare maganar tana ɗan Sipping guntun Admiral ɗin. Har lau idonsa na kanta yace.
"Hmmmm gudun magani ko, dole kuma ki sha”.
Ledar zabuwar ya jawo ya miƙa mata yace.
"In kin warke ci wannan in Kuma baki ciba dole kisha magni”. Amsar ledar tayi tana shaƙar ƙamshin zabuwar, dan gudun shan magani yasa ta ɗan fara tsakurar wurin farin tsokar tana ɗan ci haɗe da Admiral ɗin tana ɗan kallon motar su Raihana dake bayansu data Sulaiman dake can baya.
Haka dai tana ci kamar zatayi kuka har ta shanye goran Admiral ɗin, sassayan gyatsa tayi hadi da hamdala lokacin da suka shigo yankin Adamawa zafin weather ɗin Adamawa ne yayi welcoming nasu da ɗumin mai haɗe da zafi duk da wai lokacin sanyine, a hankali ta maida ledan zabuwar baya, tana ɗan gyara zama tace.
"Appiyn zafi”. Ac ya sake musu dan shi ya fita jin zafin ma, dama dan itane ya rage.
Ledan A.A Aliyu Pharmacy ɗin ya ɗauko ya zaro kolban maganin da hannu ɗaya ya ɓalle marfin ya juyo kanta fuska ba wasa yace mata.
"Haa”. Kwaɓe fuska tayi ido na kawo ruwa ta buɗe baki da nufin yi masa magiya ya manna mata bakin ƙolbar a baki, ya ɗan zira mata ruwan maganin, zaƙinsa da ɗan yaji-yajinsa yasa ta haɗiye, siyaya mata ya kumayi, da sauri ta haɗiye tana janye kanta tace. "Appiy zai min yawafa, rabin marfi ake banifa shima sai ya bugar dani yana kallon adadin da ya batan wanda bazai gaza 15 to 20ml bane yasa ya rufe ya maidashi shi baya.
Apple ya miƙo mata ganin tana ta ɗan yawo da harshenta cikin bakinta, amsa tayi ta fara ci, tana ɗan latsa wayarta. Shigowarsu Sabana ne yasata ajiye wayar tana kallon dajin Allah daya shimfiɗe da ni'imar raki iya ganin mai hange, sai kuma Fulani makiyaya dake sheidawa dukkan matafiyi sun shigo yankin Aliyu Mustapha garin Jaɓɓama Jippu jam garin fullo be nage. Garin kosam da dakkere, ƙarfe uku da kwata tayi musu cikin garin Numan gefen yanki rigar su Ayshan Yah Sheikh.
Suna barin numan ta fara jin idonta na lumshewa dan maganin ya ɗan fara jiƙa.
Ƙarfe huɗu dai-dai tayi musu a Gurore zongon baƙi garin kazo nazo. Daga Guroren ne suka yanka suka ɗauki hanyar taraba dan hanyar ta ɗanfi kyau akan gefen ta numan.
Huɗu da kaɗan suka iso Mayo Balwa garinsu Fati yar asalin mayo Balwa.
A nan suka tsaya a wani gidan mai suka ɗan ƙara mai a motocinsu masu buƙata sukayi buƙata, suna gama fita sauran motocinsun na isowa.
Tunda suka shiga ta jingina kai jikin marfin motar ta lumshe idonta saboda wani irin mayataccen bacci da yayi mata dirar mikiya jikinta duk ya sake, tafiyar awa ɗaya yayi a haka, numfashi ya ja ya fesar gefen titin ya ɗan sauƙa ya tsaya kaɗan jawota jikinsa ya mannata da fakaɗarsa kanta na kan ƙirjinsa, cikin nauyin baccin ta sauƙe numfashi tana ƙara maƙale mishi cikin alamun ta bugu dan yasa tayi mankas da maganin murar daya ɗura mata.
A haka dukaci gaba da tafiya.
Alhamdulillah ƙarfe bakwai dai-dai tayi musu ta cikin Taraba.
A wani Restaurant suka tsaya sukaci suka sha kana sukayi sallan magrib da isha.
Daga nan kuma suka ɗauki hanyar Gembu membila.
Duk da cikin buguwar bacci take, suna shiga yankin Gembu membila ɗan karen sanyinsu mai ratsa jiki ƙashi da jijiya yasa ta ƙara takure jikinta, haka yasa ya ƙara jawota jikinsa da kyau, sit belt ɗin ya haɗe shi da ita duka a ciki, yaci gaba da tuƙi dai-dai misali dan yanayin hanyar haka yasa duk suka tafe a jere bamba to bamba, motar su Aunty Amarya ne gaba, sai tasu Raihana amarya da ango sai kuma ta Mahmoud ɗin sai Sulaiman dake binsa a baya, sai sauran suma duk suna jere. Suna tafiya cikin sanin tsarin hanyar garin.
Ƙarfe sha biyu saura suka iso cikin garin Gembu membila.
Da mamaki Sulaiman yabi motar Mahmoud ɗin da kallo ganin ya yanki hanya ya bar hanyar da suke kai ɗin.
Kai ya jujjuya kana yabi bayan motar su Raihana.
Daga nan suka hanyar gidansu Ango Bashir
Chapter 84 · 0% Book details